Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Love

Chapter   9 / 14

24K to 27K   out of 40.7K words

Kuma duk sanda su ka yi hutu zasu iya kawo mun ziyara." Da haka maganar ta mutu. Washe gari a sabuwar motata muka kama hanyar Jos. Sani sai tsiya yake yi mun wai yaushe harna iya mota haka.
"Umma da ko titi falfalawa kike yi da gudu in zaki tsallaka." Dariya na kwashe dashi, Yaya Use dake gaban mota tai ma Sani daƙuwa tace.
"Ungo naka, wato ka mayar da Tani kamar wata kakarka ko?" Cikin raha mu kai ta lula hanya. Dana gaji Sani ya amshe tuƙin, sai murja sitiyari yake yi da halamun ƙwarewa, bana ko gajiya da kallon Sani, gabaki ɗaya girma da kuɗin da kaila yake sakar musu yasa yaron ya goge, dake kuma ɗan jami'a ne sai naga yana da wayewa. Wai yau ni Shanono ƙazama bagidajiya, baƙauya ni da yaranane muka zama ƴan birni gogaggu? Duk macen da ta ganta a ƙasa itace ta kasa tsaiwa ta fuskanci matsalolinta. Duk da nasan akwai ƙaddarar da duk yanda bawa yaso fita, ubangiji baya bashi wannan hanyar, sabida yana cikin ƙaddararshi ta zaman duniya. Ko da muka shiga jos, sai na shiga zazzare idanuna ina ganin gari. Babu canji a garin ko na titin mota, ballantana sababbin gidaje. Babu wani ci gaba da Jos take samu, sakamakon yaƙe_yaƙe daya kassara jihar. Ƴan taya muka nufa wajan barar su Inno. Ina hango kwanar layin garejin su Kaila. Sai nake hango sanda nake zuwa ba Kaila kuɗin abincin rana, ko kuma zuwa ganinshi. Idanuna na runtse.
"Inno bata nan wajan Tani. Muje babban masallaci Sani wajan barar su Baffa." Can ma muka je ba Baffa ba Inno. Kai tsaye muka zarce gida, muka tarar basa nan.
"Tani inaga fa ba lafiya. Bari in kira Karime inji ko lafiya" Ni dai gabaki ɗaya na bi na tsure. Tana kiran Yaya Karime take sanar mana ai suna hanyar Shanono Baffa yana ta kukan shi a mayar dashi shanono ya rasu a cikin danginshi." Ba shiri muka nufi hanyar Kano muka sake niƙan hanya. Muna hanya Habiba Bala ta kirani da number ta na Najeriya.
"Ƴar uwa abun wuya. Na dawo fa, yanzu na shiga Bauchi, Dauda nake jira ya kaini gida" Take faɗa mun. A gurguje na bata labarin ɗan abubbuwan da suka faru dai.
Zamu yi waya duk yanda ake ciki. Da na shiga shanono zan wuce dashi asibitin Kano."
"To shikenan ƙawata, ko in tawo ne?" Allah sarki Habiba Bala, masoyin mutum kenan.
A'a Habiba Bala ki zauna kema ki huta. Sai na zo Bauchin" Sallama mu kai da juna na ajjiye wayar. Ba fa mu muka isa Shanono ba sai yamma sakaliya.
Muna yin kwanar layin su Baffa muka hango kawu Yusuf da kawu Junaidu suna riƙe da Baffa za'a kaishi Asibiti ranga_ranga. Da gudu na fito na kamo Baffa tare da cewa.
Subuhanallahi jikinne yayi tsanani haka Baffa?" Gabaki ɗaya mutanen wajen suka riƙe baki suna kallon yanda nayi kilin. Inno ta nunoni da yatsa.
"Tani ashe zamu sake ganawa dake? Allah na gode maka" Hawayene suka zubo mun. Baffa sai nishi yake yi. A mota muka sashi, Inno da Kawu Yusuf suka shiga. Muka nufi Asibitin Murtala. A gigice muka shiga cikin asibitin sosai, dan Baffa baya ko numfashi. Saina tuno irin gigicewar da nayi a lokacin da muka shigo da Dauda cikin asibitin. Cikin gaggauwa aka ba Baffa gado. Ni kuma na je na yankar mishi kati, aka buɗe mishi fayil, sannan na dawo wajensu, duk fa inda na ɗaga ƙafata a wajen Sani ke saka tashi, yana biye dani kamar jela, jakata da wayata duk tana hannunshi.
"Tani dama ashe zaki waiwaye mu, ince dai baki yi fishi damu ba? Ni nasan damuwa da tunanin halin da zaki riska a gida, da tsinuwar da Baffa yace zaiyi miki ne yasa kika gudu babu wanda ya sake jin ɗuriyarki. Tani sai na ganki a cikin sabon yanayi da kyawun shiga." Hawaye na share, hannuna ɗaya yana cikin na Sani.
Inno ku yafe mini in nayi muku laifi. Wallahi ba dan fishi daku bane yasa na tsallake na barku ba. Fishi da zuchiya nayi akan Kaila kinji dalilin tafiyata." Kawu Yusuf yace.
"Amman kinsa ƴan uwa a cikin taraddadi. Duk da muma mun yi kuskure cikinmu babu wanda ya kai cigiyar ɓatanki ko da gidan radiyo ne" Yaya Use da se yanzu ta yi magana tunda muka zo asibitin tace.
"Inno duk wani kuɗi da kayan abinci, da sutura, zuwa sabuwar keke da aka sake miki. Duk Tani ke turowa nake yi muku. Ni nasan inda take kullum sai mun yi waya da'ita. Inno Tani yanzu mai shari'a ce a kotu, ta game karatunta da jimawa." Kuka Inno ta fashe dashi tana sambatu.
"Tun tasowarki kike son karatu Tani. Allah mai iko ashe zaki zama wani abun ta dalilin karatu. Allah na gode maka da yasa kika bar gida kuma kika tsare kan ki. Allah yayi miki albarka." Da Ameen dukkanmu wajen muka amsa. Bamu muka samu damar ganin Baffa ba sai bayan isha, lokacin har mun yi Sallah na ba Sani keyn mota ya je siyo mana abinci. Muna shiga muka tarar da Baffa babu inda yake. Dr ya sanar mana ciwon siga da ciwon tsufa suke damunshi. Amman siga ta cinye mishi jiki sosai. Dan tun da na taso ban taɓa ganin Baffa ya je asibiti ba ko yasha ƙwayar bature ba. Ko ciwo yaji sai dai ya sa a dafa mishi ƴan saƙesaki yasha, ko sirace." Kwanan Baffa biyu a asibiti bai san inda kanshi yake ba. Har Habiba Bala tazo ta dubashi. Rahma kuma kullum ita ke sintirin kawo mana abinci, abokan aikina duk sun zo sun gaishe da Baffa. Sabira suna hanyar zuwa. Yau Baffa ya tashi jikin Alhamdulillah da sauƙi. Ƴan shanono sai sunturi suke faman yi. Duk wanda kuma ya ganni sai ya shiga mamaki. Da daddare muna komawa gida mu kwana, Kawu Yusuf ne yake jinyarshi. Ranar da Inno muka tafi da ita gida, tayi murna tayi farin ciki sosai. Da sassafe muke komawa asibiti. Sani kuwa da ƙyar na kaɗa shi ya koma bakin karatunshi. A cikin kwana na bakwai Baffa yayi ras dashi harma ya gane muryata.
"Inno wannan muryar ai Tani ce. Tani dama zaki zo garemu?" Tsugunnawa nayi har ƙasa na riƙe hannun Baffa na dinga roƙonshi gafara akan ya yafe mun. Cikin sanyin murya tare da jan ajjiyar zuchiya yace.
"Tashi Tani. Wallahi na yafe miki, Inno ki yafe mata kema kinji ko? Yaranki sun ganki kuwa Tani?"
A'a Baffa Sani ne kawai ya ganni. Yaya Use ta labartama Baffa hidindimun da na dinga yi dasu ba tare da sun sani ba. Ai nan Baffa ya shiga kuka tare da ƙara shi mun albarka. Ko da aka sallami Baffa kai tsaye gidan dana sai musu muka wuce dukkanmu, ban ma kowa bayani ba, na dai ce su biyoni zamu tattauna in mun isa inda zan kaisu. Harda su Kawu Yusuf. Sauran ma zasu tawo daga Shanono, bisa jagorancin Ige Ƙanwar su Baffa, nayi mata kwatancen layin da gidan, dake tana yawan shigowa Kano , tace zata gane gidan ma in suka shigo layin, matanbayi baya ɓata. Na bada aikin abinci, da abun sha dan ƴar ƙwarya_ƙwaryar walima nake son haɗawa. Dauda da yaran ma suna hanyar zuwa bisa jagorancin Sani........✍🏻
[17/10, 1:23 p.m.] +234 803 831 1474: NA FADO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU


LAMBA TA 10




"Kaga Babbar kawar Amarya, maraba da zuwa." Inji Dr Nauwara kenan. Habiba Bala ta watso mun harara tace.
"Dama zamanki ki ka yi a Kanon ai daya fi miki. Tun jiya nake jiranki, wasu abubbuwan kinsan dole sai dake zanyi. Wayarki na dinga kira a kashe, kuma nasan sabida ni kika kashe" Dariya ma ni ta bani wallahi.
Ki haƙuri ƙawata, baga ni ba nazo. Kinsan aikin lauyoyi akwai wahala, kinsan da yaya ma ogana ya barni na ɗebi hutun kwanaki biyar ɗinnan ma? Hmmm da ƙyar ya amince. Sabira yau kika ƙaraso?" Sabira ta bani hannu muka tafa tace.
"Ko awa guda banyi da shigowa ba ma. Kixo ki ga akwati dan nasan dai a waya kika gani" Hakanne kuwa video call Habiba Bala ta kirani, ta dinga ɗaga mun kayayyakin ina gani. Zama nayi na darje kallo gaskiya an kashe kuɗaɗe sosai a cikin akwatunan da akaima Habiba Bala. Mijinta babban ɗan kasuwane a kwari yake, shi yasa aka saka mata kaya kyawawa masu yawan gaske. Dan Alhazan cikin kwari in zasu auri mace suna ƙaryar sutura gaskiya. Daga nan muka shiga hada hadar shirye_shiryen duk abinda ya dace. Habiba Bala Dinna kaɗai zata yi mana a nan garin Bauchi sabida ƙawayenta da ƴan uwanta. Da an gama Dina kuma sai mu yi zugar kai amarya. To fa wanna dina ita ta cinye mana lokacin mu. Mun dai nemi masu yin abincin biki mun biya su kuɗin abinci mun basu time, haka masu snacks da zoɓo ma mun sallamesu. Ana gobe ɗaurin aure sai ga su Sani da yaran suma sun zo, wucewa mu ka yi shagon saloon da lalle. Muka sha gyaran gashi da jan ƙunshi mai kyau, damu da su Halima Bawa, ƙawayenmu na makaranta duk mun hallara, dan ana zumunci sosai babu laifi. Duk shirin bikin a group muka gudanar dashi tare da kowa da kowa. Abokan ango a daren alhamis suka shigo Bauchi, a hotel suka sauka. Mu duka hidima ta hana mu ganawa da ango da abokanshi. Washe gari da misalin ƙarfe goman safe aka ɗaura auren Habiba Bala da angonta Alh Nura bisa sadaki dubu hamsin. Muna ɗakin Habiba Bala, kowa na hidimarshi, ina sanye da angonmu na ƴan makaranta farin lace sol mai duwatsu da baƙin ɗankwali. Iya kyau ni kaina dana duba madubi sai da nace masha Allah. Amarya kuma tana cikin jan lace mai adon baƙi_baƙi a jiki. Anyi mata kwalliyar zamani ta fito kamar ma ba itaba, dan ire_iren kwalliyarnan sauya ma mutum kamanni suke yi. Ni shi yasa naƙi yarda ayimun fur.
"Shanono ya kamata muje haka ko? Tun ɗazu Alh yake ta faman kiran wayata. Ki kira mun Dauda ya zo ya kaimu." Cewar Habiba Bala kenan. Waya na ɗaga na soma kiran layin Dauda.
"Innata, ina waje ku nake ta jira, muna tare da Sani ma"
To shikenan gamu nan fitowa muma" ƙit na kashe wayar nace.
Sabira, Halima Bawa bari mu je mu dawo. Ba jimawa zamu yi ba. Sabira su Yaya Use suna hanya." Hannun Habiba Bala na kama muka ratso mata muka fice. Dauda na ganinmu ya buɗe murfin motar. Sani kuma ya sara mana, har da cewa.
" Kaga manyan iyayenmu, alkhairin Allah yaci gaba da kai muku har gadon baccinku. Farare basui farin banza ba" Dariya dole Sani yasa muka tuntsure dashi. Dauda kuma yana gefe yana cin dariya. Motar muka shiga, Dauda ya ja mu zuwa hotel ɗin da Angwaye suka sauka. Tare da su Sani duka muka ɗunguma zuwa cikin hotel ɗin. A room 7 muka tsaya, Dauda ne ya ƙwanƙwasa ƙofar a hankali. Mu kuma muna daga gefe Habiba Bala na mun raɗa.
"Baki ji yanda gabana yake faɗuwa ba Shanono, nifa ji nake yi dama banyi auren ba wallahi, yana kirana da yace an ɗaura, shikenan gabana ya shiga aikin bugawa, ku tayani adda'a ke da yaran"
Haba ƙawata, in sha Allah auren karshe kika yi daga gidan Alh Nura sai kabarinki." Ƙaran buɗe kofar ne yasa muka zuba ma kofar idanu mu duka. Wani matashi muka gani a tsaye a kofar ɗakin, yana sanye da angon ƴan ɗaurin auren. Habiba Bala tace.
"Alh Nura muke nema dan Allah " Murmushi yaron yayi yace.
"Dady acan ɗakin suke, bari in muku iso" Shi ya shige gaba, muna tafe ƙwas_ƙwas_ƙwas har zuwa room 10. Shi da kanshi ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin wani dattijo yazo ya buɗe mana.
"A'a Jega kaine tafe da iyayen naka? Bismillah Hajiya Habiba Bala ku shigo, Samari bismillah." Tare muka shiga cikin ɗakin hotel ɗin. Cike tab da abokan ango, suna saye da shaddaji mai ruwan sararin samaniya, da hulunansu masu ruwan baƙin blue, haka aikin gaban rigarma yake. Kujera dogowa da suka nuna mana muka zauna, ango ya rasa inda ma zai tsoma mu, ni kuma duk sai naji inata kunyar yara, sai satar kallonsu nake yi, Amman su naga hankalinsu ma akwance yake, sai gaisawa suke da abokan ango.
"Hajiya Shanono barkanki, idanunki kenan na ɗauka ai aikinku na lauyoyi bazai baki damar halartar taron bikin mu ba." Cewar ango, dariya nayi mishi, shima da zolaya yayi zancan.
In aikina zai iya zame mun katangar da zata hanani zuwa bikin Habiba Bala, da tuni na ajjiye aikin, dan Habiba Bala ta fi mun aikina muhimmanci. Guda da bari ce a wajena. Ango Allah ya sanya alkairi yasa gidan zamanta ne" Dariya yayi mun yace.
"Ameen Ameen mungode da yabo Shanono." Uwar ɗakin cikin falon Alh Nura ya ja Habiba Bala. Ni kuma sai faman daddanna waya nake yi, wani saƙon neman shawara aka turomun, duk da tace mun. Malama ki ɓoye sunana. Amman na tausayama wannan baiwar Allah ainun. Copying nayi na tura cikin group ɗina, da shafina. Shine aketa tabka muhawara iri_iri. Inason karanta comments, wasu abun kayi dariyane, wasu kuma abun haushine sosai tattare da amsarsu. Wannan lamarin shi ya ɗebe mun hankalina har bansan lokaci ya ja ba, sai da wayar ɗaya daga cikin abokan ango ta doka kiran Sallah. Sai lokacin na duba agogon wayata ƙarfe ɗaya saura. Su Dauda na duba suma ni suke kallo, farfesun kaza suke sha hankalinsu kwance. Sani ne ya ɗebo farfesun a cokali ya nufo bakina dashi. Cikin farin ciki da jin daɗin yanda yaron yake kulawa dani na wangale mishi bakina ya sa mun farfesun. Dai dai fitowar Habiba Bala. Hakanne yasa na miƙe da sauri, tare da ango muka fice har gaban motarmu yai mana rakiya.
Shine kika shanyani a zaune ko?" Cikin raɗa dan kar yara su jiyo mu nace.
Ke daɗi miji ko?" Zungurata tayi tana nuna mun yara. Harararta nayi cikin wasa. Bayan mun koma gidane, na tarar da su Yaya Use sun ƙaraso, anata hada hadar rabon abinci dasu. Su Amina na gani sun cakare gaye sun yi kyau kamar ba ni na haifesu ba. Kayan jikinsu komai mai tsada ne sosai. Lallai kaila yayi kuɗi, har ya iya siyama yara tsadaddun kaya haka? A wajensu na tsaya Habiba Bala kuma ta shige ciki. Haka dai al'amuran biki su kaita gudana har zuwa dare. Da misalin ƙarfe takwas na dare muka fito tsab damu, a lokacin jama'ar biki sun daɗe da tafiya can hotel ɗin da za'a yi dinna. Su Sani sun sha jigilar kaiwa da dawowa ɗaukar mutane, motata tana hannun Dauda, Sani kuma da motarshi dama ya tawo Su Yaya Use duk sun tafi. Manyan ƙawayen Amaryane kaɗai muka rage mu huɗu, sauran ƙawayen suna can suma suna jiran isowarmu. Sanye muke da ankon wani material mai wawal_wawal ruwan gorone kalar kayan, sai muka ɗaura ɗankwali mai ruwan madara. Ƙatuwar sarƙar azurface a wuyana da kunnena, da tsintsiyar hannuna, har zuwa yatsuna uku da suke maƙale da zobunan azurfa suma. Takalmina da jakata masu ruwan madara na saka, takalmina yana da tsini sosai, sai ƙwas_ƙwas yake yi. Inata bige ƙamshin sihartacciyar humrarnan ta manyan mata wanda nake siya a hannun Mrs Bukhari gidan ƙamshi ƴar mutan Kanuri. A kusa da Habiba Bala nake, Sabira na kusa dani, sai Halima Bawa, sai Dr ƙawar Habiba Bala. A jere muka fito zuwa kofar gidan, motoci muka tarar guda uku a jere. Ta tsakiyar itace ta amarya da angonta kaɗai. Na gaban kuma su Halima Bawa suka shiga, har na isa bakin motar matuƙin motar yace.
"Hajiya ki shiga waccar motar, wannan ta cika" Cikin takun hajiyoyin mata na isa motar ƙarshe, gaban motar na shiga da sallama ɗauke a bakina.
"Ameen wa'alaikissalam Barista Tani Shanono Naroro, Ƙwararriyar lauya mai kare hakkin mata. Mamallakiyar Mu farka mata group, malama mai sauraron koken mata, mai burin buɗe gidauniya dominsu, Bazawara mai aure shida." Da ɗumbin tulin maɗaukakin mamaki na bi matuƙin motar da idanu. Wannan saurayin da muka kwankwasama ƙofa ne ɗazu a hotel wanda akaima laƙabi da JEGA Ƙur muka zuba ma juna idanu. Ni ina mamakin rashin ta'idonshine, dan banyi mamakin jin ya ambaci sunana da aikina, da kuma lambobin aurena ba, dan abune dana ɗaura a shafina na facebook, nasan labarina ya yaɗa inda ma banyi tunani ba, dan akwai wata hira da akayi dani bayan naci nasarar wata shati'a, to na ɗan ba da taƙaitaccen labarina, kuma na wallafa videon yana shafina. Shi kuma saina kasa gane irin fassarar da zanyi ma kallon da yake yi mun. Dan naga idanunshi kamar sun ɗan cika da ruwan hawaye, in ba dai nice ban gani dai_dai ba. Zare idanuna nayi daga kallon ƙudan da mu kai ma juna na kawar da kaina. Bin jerin motoci biyunnan yayi a baya, a madadin yayi gudu sai naga yana tafe a hankali. Ni dai bance dashi komai ba, ban kuma yarda mun sake yin ido hudu ba.
"Na daɗe ina mafarkin saki a idona, na daɗe ina mafarkin gaki a cikin motata. Na daɗe ina mafarkin hotunanki. Abunda yafi komai burgeni shine, kinfi a hoto kyau, kinfi a video kunya. Yau babbar ranace a gareni mai ɗunbun tarihin gaske. Kar in cika ki da surutaina, da Farko Sunana Ahmad Jega, amman abokai da ma dangina da Jega suke kirana. Nine babban ɗa ga Alh Nura mijin ƙawarki, iyayena duk suna Kano da zama, ni kuma ina garin Kaduna da zama a cikin garin Jega, cikin tsotson mahaifiyata" Mamakin iya tsarin zancenshi nake yi. Gashi dai yaro, abun mamaki ya iya abubbuwa irin na manya, kuma akwai ƙwarin guiwa a tattare dashi. Lallai yaran yanzu akwaisu da rashin kunya. Nayi mamakin Jega yanda yake iya furta ra'ayinshi a kunnena. Yarone da bazai wuce shekara talatin ba, duk da dai yana da kamala, Amman dai yarone ƙarami. Da tunane_tunane fal kwanyata muka iso hotel ɗin da ake dinna. Yana gama parking na murɗa murfin motar da zummar ficewa ko zan shaƙi numfashi mai kyau.
"Barista Shanono baki ce komai ba, yanzu a haka zaki barni

9 / 14