Author : Billyn Abdul Category : Love
me kikace, tunda kema yarannan naki ne?"
Baffa yara dai sun dawo hannuna kenan. Ba yardarshi nake nema ba, asalima shi yasa ban nemi amincewarshi ba. Ina da damar da zan iya riƙe yarana. Ko kotu muka je mu kai shari'a alƙali zai bani yarana." Carab Kaila yace.
"Bazan iya rabuwa da yaran bane Baffa, sune makwafinta a Idanuna. Dan haka zan tafi da yarana"
Wallahil azeem baka isa ka taɓa mun yaraba. Yara sunzo kenan zama daram tare da ni uwarsu, kaila ka fice a cikin idanuna in rufe. Ba wannan shanonon daka sani bace a baya, ƙaramar katangarka mai daɗin tsallaka. Yaran ƴar jagora, mabarata, maƙasƙanta su kake son su zame ma sanyi a idanunka? Baka isa ba wallahi." Baffa yace.
"kinci gidanku nace"
"A'a Naroro Tani tana da gaskiya fa, a baya ma dokin zuchiyane yasa harta iya biye ma zuchiya ta bar yaranta. Ai tsakanin ɗa da uwa sai Allah. Ni ina ganin kai Kaila kayi haƙuri kawai yara dai kasan inda suke, a hannun gyatumarsu, duk sanda kake son ganinsu babu mai hanaka zuwa ka gansu. Zancan tashin hankali ma bai taso ba." Cewar Goggo Ige.
Basshi Ige in yaji bazai barmun su ba, ai sai mu shiga kotu. Kaga hakkinsu na baya da ka kasa saukewa, ayi maka list ka biya. Sannan alƙali ya karɓarmun dukiyata daga hannunka ka koma matsiyaci yanda kake a baya" Na kakkafeshi da Idanuna da suka kaɗa su kai jawur, wallahi ji nake kamar in dira a wuyanshi. Ganin irin fusatar da nayi ne yasa Kaila saurin janyewa.
"To shikenan Shanono, ni bazan yarda mu tsaya a gaban kotu dake akan yaraba. Amman ina roƙonki da girman Allah ki koma ɗakinki mu mayar da aurenmu, Isa bakace komai ba fa har yanzu" Murmushin mugunta nayi ina binsu da idanu kawai. Isa ya soma jawabinshi.
"To hakane maganarka. Maganar tsaiwa a kotu bama ta taso ba. Mu alfarmar da muke nema a wajenku Baffa, umman Sulaiman ki yi ma Allah ki dawo ɗakin ki ko dan sabida yaranki. An riga da an haɗu tunda yara bakwai sun haɗa. Komawarki shi zai samar ma da yaran daraja. Su Amina sun riga sun kawo girma ba daidai bane ace kina matsayin bazawara yaran a hannunki zasu zauna ba. Da uba ake ado, darajarsu gidan mahaifinsu. Ni shawarata Umman Sulaiman ki daure ki sake ba Kaila dama ta barkatai. Nasan yana da tulin tarin laifuffuka da dama awajenki. Ni na san komai, babu kuma irin rikicin da ni da shi bamu yi ba akan irin zaman da yayi dake a baya. Wallahi Tani daga ranar da kika fita cikin rayuwar Kaila daga ranar ya shiga taitayinshi, ya gane matsayinki. Hidima kam kinyi da Kaila sai dai muce Allah ya baki lada." Falon ya ɗauki shiru. Ni kuma sai kokawa nake da hawayen da suke shirin zubo mun. Sam bana fatan Kaila yaga hawaye a fuskata. Kuma in mutuwa yake yana dawowa banga wani mutum a duniya da zai sa in koma aure da Kaila ba" Baffa yace.
"Malam Isa zancanka babu son zuchiya a ciki. Amman mu bamu da ikon tursasa Tani ta koma ma tsohon mijinta, face in tana son komen. Wannan ya rage ga Kaila ya nemi yarjewar Tani. In ta aminta shikenan, in bata aminta ba shikenan. Amman Tani naji kina maganar dukiyarki, kuɗaɗenki ne a hannunshi ko ya abun yake?" Inno da bata ce komai ba tace.
"Kar ka shiga wannan layin Baffa. Tunda har ya yarda yara su zauna a hannun uwarsu ai mun fita. Batun kome kuma sai in ta amince. Ige mu basu waje." Sandar Baffa Inno ta riƙe suka fita, ɗakin ya rage sai mu uku. An rasa me cewa komai.
"Shanono wallahi da gaske nake son ki dawo ɗakinki ba yaudara bace. Isa shine shaidata tun ranar da kika tafi nayi nadamar fitarki a rayuwata. Kullum a cikin tunaninki nake tsawon wannan shekaru da suka shuɗe. Da zaki yi mun rai sai mu koma......" Irin kallon dana watsa ma Kaila ne yasa ya shiga in_ina ta dole. Ƙare musu kallo nayi tas cikin nutsuwa na miƙe tsaye, ya ƙara kafeni da idanu kamar zai cinyeni. Murmushi na sakar mishi na girgiza kai. Sai da na kai bakin ƙofa kana nace.
Ku sauka lafiya" Nayi ficewata ina ji suna haɗa baki wajen kiran sunana. Ina fitowa Sani na shigowa cikin gidan. Da ganin idanshi yaci kuka ya gode Allah. Tausayinshi ya kamani, Sani yana burgeni yanda yake tsananin ƙaunata. Hannunshi na kama muka bar gidan zuwa nawa gidan. Yaran na samu sai hira da shewa suke yi Dauda na zaune yana waya, sai wani kashe idanu yake yi. Suna ganin shigowarmu duk suka yo kaina. Zama nayi na ɓoye damuwata na shige cikinsu muka ɗan taɓa hira. Ige ce tayi sallama ta shigo.
"Tani yaran su zo Babansu zai musu sallama" Umarnin fita na basu, Sani kuwa har ya fita ya dawo.
"Umma yaya kukayi ba dai tafiya dasu zai yi ba ko?" Dariya nayi na ɗan kai mishi dukan wasa. Shima dariya ya saka.
"To Habiba Bala in ka dawo sai in baka labari ai" Dauda ya fashe da Dariya shima jin na ambaci uwarshi. Sai lokacin naga Sani ya sau ajjiyar zuchiya. Suna fita na kalli Dauda nace.
Ka shirya week end zan kai ka gidan mahaifinka ku gaisa. Mu shiga mu yi zumunci da yara duka."
"To Innata Allah ya nuna mana"
Ameen. Dawa kake waya dan na fahimci kamar macece ko?" Kai ya shiga sosawa yana dariya ƙasa_ƙasa. Murmushi nayi wai Dauda har ansan soyayya.
Toh na fahimta budurwace kayo kenan ko? To yayi ai. A ina take yarinyar, meye matakin karatunta?"
Yarinyace shekararnan zata gama sakandare. Kuma tace Babansu sai yayi musu aure suke jami'a. A Bauchi take" Kai na gyaɗa nace.
Gyatumarka tasan kana da budurwa ko bata sani ba to?"
"Bata Sani ba Innata. Da naso sai mun fahimci juna ne"
La hakan kuskurene, in ka je ka sanar mata dan tasan ka girma. Sai yaushe zaka soma zuwa aiki, da batun shago kuma fa?" Zama ya gyara yace.
"Monday zan soma zuwa wajen aiki. Shagon kuma Ummata tace zata sa Abba ya nema mun inda yafi fuskar jama'a haka" Kai na gyaɗa.
To Allah yasa mu dace." Kiran sallar azahar ne ya sa na miƙe zuwa cikin ɗakina. Shi kuma Dauda ya fita dan zuwa masallaci. Na daɗe a bayan gida ina kukan da in ba yinshi nayi ba zuchiyata ba zata samu sassauci ba. Sai da na ƙoshi kana na ɗauro alwala na fito. Ina idar da Sallah na kunna wayata. Saƙonni uku suka shigo a Jere. Biyu na Jega ne, ɗayan na Oga Rashid ne. Kuma dukka zafafan kalaman soyayyane, kowa na ƙoƙarin kafe tashi gwamnatin. Ido na lumshe ina hangosu dukka biyu a idanuna. Sallamar Dauda ne yasa na fito
"Innata Su Sani fa basa gidan Inno. Kuma ban haɗu dasu a masallaci ba" Dam gabana ya yanke ya faɗi na shiga doka kiran wayar Sani har wani dashi_dishi nake gani....✍🏻NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA 15
Sai da wayar ta kusan tsinkewa Sani ya ɗaga.
Kuna ina Yayanku yace bakwa gidansu Inno?* Dariya Sani ya fashe dashi.
"Umma muna sahad store Baba zai ma su Amina siyayya. Ni banso binsu ba ma, ina tsoron kar ya gudu dasune shi yasa na bisu" Wawuyar Ajjiyar zuchiya na sauke.
To shikenan sai kun dawo. Ni fita ma zanyi yanzu zan koma aiki. Sai ku zauna gidan Inno" Sallama mu ka yi na ajjiye wayar. Na koma ciki, wanka na sabunta na sake kaya na fito. Tare da Dauda muka fito, ya kulle gidan ni kuma na shige mota na bar anguwar dan bana ƙaunar abinda zai sa ma mu haɗu da su Kaila. Kirane ya shigo wayata, na duba number da kyau, number da maras kunyan yaronnan ya kirani dashi ɗazu ne. Banza nayi da wayar, ina tunanin to ni me zance ma Oga Rashid gobe in yazo wajena. Da wannan tunanin na ƙarasa gidan Habiba Bala, me gadi ya wangale mun get na shiga. Fitowa nayi ina tafe gabana na faɗuwa. A falon ƙasa na tarar da Hajiya kilishi, da Khadija matar JeGa, da wasu mata dai haka. Da fara'a na gaishesu. Suma suka amsa mun cike da fara'a a fuskarsu. Bayan mun gama gaisawa sai na haura sama zuwa ɗakin Habiba Bala. Tana zaune a kujera tana kallo tayi ado shar da'ita fuskarta har wani annuri ta sake fitarwa.
Amarya ba kya laifi. Irin wannan kyau haka Habiba Bala zaki kasheni" Dariya mu ka yi ta bani hannu muka tafa tabb. Waje na samu na zauna.
Ince dai Angon ya fita dai ko?"
"A'a da muna zaune ma muna kallo, to Babban yaronshi ne zasu wuce JeGa da iyalinshi. Shine ya buƙaci yana son su tattauna wata mihimmiyar magana to ya garin?" Tana faɗar haka cikina ya murɗa. Shikenan yaro na shirin tona mun asiri in kasa fita daga gidan dan tsananin kunya.
"Ya dai ƙawata lafiya kike kuwa?" Na ji Habiba Bala na tambayata.
Hmm lafiya ba lafiya ba, ina cikin tsaka mai wuyar fita Habiba Bala, da farko dai. Kaila na cikin garin Kano, Ko ince miki yana sahad store wai yaje yima yara siyayya. Da yazo tafiya da yaranshine, da dai yaga a tsaye nake kamar nonon maza shine ya janye. Ni ai naso ya kafe, dan sha'awar rikicin nake yi ƙawata." Dariya ta saka tace.
"Kuma har ya iya fuskantarki akan shi yazo tafiya da yaran? Lallai Kaila bashi da kunya. Yaran da ada tsakaninsu dashi zagi da hantarane, sai yanzune yake son kasancewa tare dasu. Lallai ya kyauta.
Hmmm kuma ma har suna batun in koma ɗakina sabida yara, shi da abokinshi yana ta faman kwatanta mun Kaila yayi nadamar sakina, ke soki burutsun zance dai. Da yaji inason fasa mishi taya ne fa ya haƙura. Ni duk bama wannan ba Habiba wallahi a cikin matsala nake wani al'amarine yake shirin faruwa a cikin gidannan naku. Habiba Bala koma ince miki asirina ya kusan tonuwa, bansan irin kunyar da zanji ba in abunnan ya fasu, ban san ya uwargidanki zata fassara lamarin ba" Shiru nayi duk na daburce.
"Uwargidana kuma Shanono, wai meke shirin faruwa da kike son ɓoyemun ne? Shanono ashe kina mun ɓoye_ɓoyen sirrinki kenan ni ban sani ba ashe? Yawu na haɗiye nace.
Ba ɓoye miki nake yi ba. Bagatatan abun ya riskeni, da na ɗauki maganar a matsayin shirme da bankaura irin na yara. A yanzu kawata dole in bayyana miki abunda ke faruwa, ko dan mu haɗu mu yi mafita " Kai na sauke na kasa cewa komai. Habiba Bala kuma kafeni da ido tayi tana sauraren me zai fito daga bakina. Muna cikin wannan zama na kurame, muka jiyo sallamar Alh Nura daga bakin ƙofa. Gabana ya tattake ya faɗi, ji nayi tamkar ƙasa ta tsage in faɗa ciki, sabida tsabar yanda na muzanta, jina nake kamar tsirara."
"Alh ka shigo, har su Jegan sun kama hanya kenan?" Ajjiyar zuchiya me mugun nauyi ya fesar kafin yace.
"Tafiyar zata iya kaiwa gobe dai. Barista barka da zuwa. Habiba sameni a ɗaki mu yi magana zamu fita ne da JEGA" In bude baki in amsa Alh Nura na kasa, bani da kalma ko guda a bakina. Lallai Jega ya zubar mun da mutuncina, ji irin gaisuwar yau da Alh Nura yai mun. Kamar ba shi bane ɗazu suka kirani a waya cikin fara'a ba. Wannan yaro ya ɓarar mun da gari. Bani ba sake zuwa gidan Habiba Bala har gaba da abada. Ita kanta a sanyaye tace.
"Ƙawata ina zuwa bari in dawo" Bayanta na bi da kallo, tana shigewa nima nasa kai na fice. Tafiya nake kamar munafuka, inata leƙo, tsorona Allah tsorona kar in haɗu da kishiyar Habiba Bala a hanya. Itama ƙila labarin ya isa kunnenta. Cikin sa'a kuwa na fita har tsakar gida ban haɗu da kowa ba. A wajen ajjiye motoci naci karo da JEGA yana jingine a jikin motata. Kallo na kare mai da halamun yana cikin tashin hankali mai girman gaske, idanunshi yayi jawur. Kur ya ƙura mun idanunshi ya kasa ce mun komai, nima ban tankaba na shige motata kawai. Abun mamaki har na soma tafiya JEGA bai ce komai ba, bai kuma dena bina da idanu ba. Kallon da yake mun yana bani kunya ainun a shekaruna. Wani tunanin ne yazo kaina.
JEGA gobe da yamma ka kirani zan baka adireshin inda zamu haɗu inason mu tattauna kafin ka koma garinku. Sannan kar ka bari damuwa ta damu rayuwarka, ka cutar da jikinka da iyalanka. Duk abinda mahaifinka yayi maka kai ka jama kan ka. Mai taurin kai zai iya fuskantar halin matsi fiye da wannan " Har zan wuce yayi saurin zuwa daidai windona.
"Barista masoyi ba maƙiyi bane. JEGA masoyin gaskiya ne, mai ɗauke da burin kawo miki sauye_sauye a cikin rayuwarki. Duk da dama nasan bazan sameki a cikin sauƙi ba. Amman yafi kyau iyayena da iyalaina su san da zamanki a cikin rayuwata. Zuwa yanzu nayi imani kowa na cikin gidannan yasan meye sirrin zuchiyata. Allah ya kaimu gobe zan kiraki, in babu damuwa mu haɗu a munjibir da misalin 5zuwa 6 na yamma. Nagode da wannan gaiyatar da ki kai mun. Duk da na tabbatar shirin yaƙata kike yi. Amman ni ba matsoraci bane in dai a kan ki ne. Dady kanshi ai ko babu komai yasan ya haifi jarumi. Kawar matarshi nake so, kuma zan aura da yardar Allah sai na ɗura miki cikin yan biyu" Yana kaiwa ƙarshen maganarshi ya juya ya shigewarshi cikin gida. Kuri nayi na bi takunshi da kallo.
Kyakkyawane irin kyawu na matasanmu na Arewa, yana da tsayi, da cikar zati da kamala. Shi ba mai ƙiba ba, kuma ba siririba. Fatarshi kuma wankan tarwaɗane, sumar kanshi bata da yawa, kuma ba mai sulɓi bace, yana da ƙasumba, da cikar gemu irin na mahaifinshi sak. Wannan gemu ya ƙara mishi zati, da kamala, ya kuma boye ɗanyantakar dake fuskarshi, dan in a fisge ka kalleshi ba za'aimai kallon yaro ba. Muryarshi tana da kauri sosai, irin na cikar mazantaka, domin karamar murya ga maza ba abun burgewa bane sam. JEGA dai yana da madaidaicin kyau a taƙaice zamu ce, bashi da wani aibu na zahiri, sai kusakurai da ba'a rasawa a rayuwar ɗan Adam. Ɗan kasuwane shi, kuma yayi digri a fannin kasuwanci domin gadar mahaifin nashi. Ƙaton uba uban shagon kayan atampopi da lesuka yake dashi a garin na JeGa. Kusan kab Jega babu shagon da yakai na Jega yawan kaya, da yawan kostoma. Daidai gwargwado yana zaune da matarshi da su kai auren soyayya lafiya, yana kuma iyakar ƙoƙarinshi wajen bawa diyoyinshi tarbiyyar islama. Amman yana da yawan Fishi, da zafin kishi akan abunda yake so. Sannan yana da ƙulafaci, gami da naci akan duk abinda ya saka a gabanshi. Yana da ƙanne biyu rak duk mata suna aure, ɗayar na Aure a jihar Borno, ɗayar kuma tana cikin garin Kano.
Wannan shine takaitaccen tarihin JeGa."
KAILA:
Bayan sun dawo da yara gida da uba uban kaya cike da both. Yaso ya sake samun damar keɓewa da Shanono amman sai su kai rashin sa'a bata nan. A cikin gidan su Inno aka jibge kayayyakin. Su buhun shinkafane, katon_katon na su taliya, macroni, couscous, omo, sabulun wanki, sabulun wanka, suturu, kayan kwalliya. Babu dai tarkacen da bai siyo ba, dan yace baya buƙatar Shanono tasa ko ƙwandala a sha'anin ciyar da yaranshi, tufatar dasu, neman lafiyarsu, iliminsu. Shi zai tsaya musu akan komai , duk abinda ya taso a kirashi a faɗa mishi. Dubu ɗari biyu yaba Inno a ajjiyema Shanono na dangane da karatun yaranshi. In ma basu isa ba zai ƙaro ko nawa ake buƙata. Sannan su yara matan yace zai sa Amadudu mijin Hindatu ya kawo musu mota sabida su dinga zuwa makaranta, tunda Sani shima karatunshi yake yi. Yayi ma Sanin alkawarin zai yi mishi cuku_cukun ya samu tranpa daga jami'ar Jos zuwa Bayero unibasiti. Bayan sun gama sai suka nufi hanyar Zaria. Kaila na jingine da jikin kujerar mata, yayi zurfi cikin tunanin shanono, Allah ne ya jarabceshi da wata iriyar azababbiyar soyayyar Shanono, ya rasa ma inda zai tsulma kanshi ko zaiji sanyi.
"Isa bazan iya haƙuri da Shanono ba maganar gaskiya. Baka ji ƙirjina yanda yake yi mun ba akan sonta. Allah ne ya jarabceni da soyayyar shanono a karo na biyu. Abinda ban yi tsammani ba, gashi naga ta ɗauki zafi fiye da tunanin me tunani Isa" Harararshi Isa yayi, ya girgiza kanshi kawai.
"Kaila kenan, in banda abunka ai dole ma ka jarabtu akan Tani. Ni fa duk irin abinda nai ta guje maka kenan tun a baya. Kasa ƙafa ka shure. Ya Tani ba zata ɗau zafi ba, cin mutunci wannene ya rage baka yi mata shi ba? Ni kaga bazan sake rakoka Kano wajen Shanono ba. Zariar ma ina ajjiyeka a gidan Bilkisa zan dawo Kaduna abuna, babu ruwana da shiga sabgarka da iyalanka. Ka dawo a motar haya Kadunan " Ya ja baki ya tsuke. Kaila ma bai ce uffan ba, haka su kaita yawo a saman kwalta har Allah ya kaisu Zaria lafiya. A Samaru ya ajjiye Kaila ƙofar gidan Bilkisa.
"To Isa sai na dawo. Kwana ɗaya zanyi ma mu tattaro mu dawo"
"Wai in taƙi fa yaya zaku yi kaila?" Murmushi yayi na takaici dan son Tani sai muƙarƙusarshi yake.
"Ni ke aurenta, in dai da gaske tana sona, dole ta biyoni nike da ikon ajjiyeta a duk inda nake so. Kai dai saina dawo zanzo har gida. Ka gaishe da iyalan" wucewa Kaila yayi zuwa cikin gidan. Isa kuma ya ja motarshi ya bar wajen. Ya ko taki sa'a Bilkisa tana gida yau night take dashi a wajen aiki. Tana falo ita da yara Kaila ya shigo da sallama babu kuzari a jikinshi. Zazzaɓine sosai a jikin nashi, bakinshi har ɗaci yake yi.
"Kaine a tafe da yamma haka, yau an tuno damu kenan? Hmmmm Kaila kenan, ga waje zauna" Ta nuna mishi kujera ya zauna. Yaran ya kira suka zo inda suke yana kallonsu. Gabaki ɗaya basu saba dashi ba sam. Shi