Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Love

Chapter   4 / 14

9K to 12K   out of 40.7K words

cikin sukuni, ga arzikin Kaila ko wanne daƙiƙa ƙara burunƙasa yake yi." Katseta nayi da faɗin.
Ni aurena bai mutu ba. Sallama nazo yi miki zan tafi Kano ƙaro karatu?" Idanu ta zare tace.
"Da yawun wa, ko da yawuna kike son kice zaki tafi ni Inno? Tani kina cikin nutsuwarki kuwa, to dawa zaki bar yaran, shi kaila yaya zaki yi da aurenshi dake kanki? Kin dawo da maitar son karatunnan, kinsa ƙafa kina son shure musabbabin abinda ya rabaki da Aurenki na Farko ko? To bari kiji babu wani karatu da zaki je ƙarowa, wanda kika samu ma ɗaga hannu ki gode ma Allah. Kar ki sake Baffa ya ji wannan labarin, dan tsine miki zaiyi tsab ki kasa yin albarka.
Inno ni sai yaushe zaki kama hannuna ki sa mun albarka, ko ki zaunar dani kiji damuwata ne. Inno daga ke har Baffa kunsan Kaila mafaka kawai ya bani. Aurenshi sunane kawai, amman shekara sama da shida ban sake taka ƙafa zuwa turakarshi ba. Bai nemi yasan daliliba. A matsayina na mace mai jini a jika ban taɓa yin ƙorafin hakan ba. Yarana da gobensu kaɗai nake dubawa. Hajiyayye yanzu haka ma'aikata sama da biyar ne suke aiki a ƙarƙashinta take biyansu albashi duk wata. Ga mota tana ja, jan rayuwa take yanda taso. Bilkisa tana aikinta kuma bai hanata zaman aure ba. Yanzu haka jita_jita nake ji a gari wai Kaila na gina mata asibiti. Inno ni sai yaushe zan zama kamar kowa ne, kefa uwace ya kamata ki tallafeni raunine a jikina limlib. " Maganganuna sun shiga Inno sosai. Ajjiyar zuchiya ta sauke.
"Hakane da duk abinda kika faɗa gaskiya ne. Tani Allah ya baki nasara, in mijinki ya amince miki, nima na amince, ina miki fatan nasara tare da samun dace. Wannan batun karma ki tari Baffanku dashi, ki je ni zan yi mishi bayani in an kwana biyu. Sannan yaran wa zai kula miki dasu?. Yarinyar Yaya Use Hasiya ita zata zauna dasu, da naso mai aikin gidanmu ta kula dasu. To dana tuntuɓeta da batun sai ta ƙi amincewa. Shine Yaya Use tace Hasiya zata kular mun dasu."
"To shikenan Allah yasa a dace." Daga haka mu kai sallama da Inno. Indo na tuƙata a keken guragun dana siya mata. Gidan Yaya Karime na soma zuwa nayi mata sallama. Daga bisani na je gidan Yaya Use na tawo da Hasiya. Gidan Sabira ne gida na ƙarshe daga nan muka nufo gida. Sabira tayi mun alƙawarin zata dinga zuwa duba mun yaran, in da hali ma zata ɗauki Salis ya dawo hannunta.
Da daddare na gama ninke kayana tsab na rufe sabon akwatina mai ruwan goro. Sani ya dubeni.
"Umma ji nake kamar in kika fita a gidan kamar ba zaki dawo ba. Amman inason kiyi karatu umma" Murmushin ƙarfin hali nayi mishi nace.
"Duk juma'a da izinin Allah zan dinga zuwa. Ina Jos ina Kano. Ga Hasiya nan ku dai ku bi umarninta duk abinda tace muku kuyi. Banda ɗakko rigima a cikin gida. A gidannan duk kaine babba ko wanne yaro an sameshi ne bayan wanzuwarka. Wata rana kaine jagora a cikin gidannan. Sabida haka ka kwatanta adalci a tsakankanin ƙannenka da baku fito ɗaki ɗaya ba." Muna cikin wannan maganar muka jiyo shigowar Kaila babban falo.
Ina zuwa bari in je in ma mahaifinku Sallama." Mayafina na zara na fita babban falon.
A cukume na iske Kaila a hannun Bilkisa tana rantsuwar sai ya saketa tare da faɗin.
"Na fi ƙarfin ka haɗa ni kishi da mai aikina. Dan cin Amana wato soyayya kuke yi da Shamwilar shi yasa take yi min gani_gani. Yau bazan kwana a gidannan ba wallahi. Ɗan iska mai biye_biye, wanda ya kasa tsaida idanshi akan matanshi kaɗai, ni zaka kawo ma kayan faɗar kishiya, kishiyarma ƴar aikin gidanka dan lalacewa.........✍🏻


Ina sake godiya a gareku masoyan ShanonoNA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU


LAMBA TA 4

Ni kaina saida naji wani gingiringin. Da jin furucin Bilkisa. Kallon Kaila nayi ido a cikin ido, yana shaƙe a hannun Bilkisa, ba abun ya daketa kamar yadda ya saba mangareni ba, iyayenta su yo zuga domin jin dalili. Maganin biri karen maguzawa, nice ƙaramar katangar kaila mai daɗin tsallaka. Bilkisa tayi bigi bigi da wasu akwatuna da nake tunanin na dannar ƙirjine. Ana haka Hajiyayye ta fito da tulelen cikinta tana turawa. Da Bilkisa ta daka wani ihu, sai ga Hindatu a guje ta shigo.
"Meke faruwa anan kuma? Baby kai kuma kana tsaye kana kallonta ta cukumeka? Cewar Hajiyayye tana magana tana farfari da idanu Dariya nayi kawai. Bilkisa tace.
"Malama babu ruwanki. Kaila ka sake ni nace, ko in ƙone gidannan uban kowa ya ƙone"
"Kaila, Gwanda ta ruɓe kenan, ikon Allah na kwance ya faɗi. Hajiyayye ta sake fesama Bilkisa magana.
"Daka auro Shamwila ina cikin gidannan na gwammaci mutuwa ta ɗaukeni." Hajiyayye jin an ambaci Shamwila ta soma salati, cikin rishin kuka.
"Kaila kaji kunya Wallahi, na jima ina zarginka yanda ka damu da Shamwila, baka da aiki bini _bini sai fita tsakar gida. Ashe zamewa kake kaje wajenta, Wallahi nima bazan zauna ba. Ke kuma ai duk ke kika jawo mana matsiyaciya, ke uwar son jiki, turakar miji ma sai an gyara miki, to gashi har mijin take garewa ashe, dan nayi imani da Allah Kaila ya gama da yarinyarnan tare yake yi mana rabon kwana ƙila ma kasonta ya fi ƙarfin namu" Tana ƙarashe faɗar hakan kaila ya fincike rigarshi a hannun Bilkisa.
"Babu wacce na riƙe nace sai tayi zaman gidana. Akan Shamwila zan iya rabuwa da kowa nawa. Wallahi ko Rammai bata isa ta hanani auren Shamwila ba. Itace wayewarta tayi daidai duk cikinku babu wacce zata iya ɗaukeni kamar yadda Shamwila zata yi. Ku bani waje dallah, ƴan iska mahaukata." Gaga_gaga ya tawo zai bangajeni, ba shiri na kauce.
Lallai sha'anin maza akan mata abun azimunne, banyi tunanin akwai macen da zata shiga rayuwar Kaila ta ture matsayina ba, kamar yadda Hajiyayye ta shigo ta ture matsayina itama tunaninta babu macen da zata ture ta. Cikin ikon Allah sai ga Bilkisa. Ni na ɗauka itace ƙurewar daraja a idanun Kaila, ashe ƴar aikinta ce cinyewar Kaila. Ni al'amin Kaila da matanshi baya gabana, ci gaban rayuwata da kafuwar yarana shine burina. Juyawa nayi da sauri na fita tsakar gidan. A bakin ƙofar ɗakin Shamwila na hango Kaila. Yana ganina yayi firgigit ya tawo, sai wani muzurai yake yi mini.
Kaila inaso mu yi magana "
"Dakata Shanono kar ki sake in ji ƙazamin bakin ki a cikin wannan maganar. Banga ubanda ya isa ya hanani wannan auren ba. Kin tawo faram_faram a tunaninki kina da darajane a wajena ko me? Zaman ƙaddara. Ni dai nayi nadamar auren bagidajiya kamarki, jibakki wai a hakan gani kike ke kin kile ko?
Ya isheka haka, kullum aikin ka kenan nadamar aurena, yau turarka ta kaini bango Kaila. Shin me yasa kaketa riƙe ijiyar auren ƙaddara na tursasa maka ne, ko kana tunanin in bana zaune a gidanka mutuwa zanyi? Nice nake zaman aure na ƙaddara da kai Kaila. Kaila kaci amanar ƙauna ka zalunci alƙawari. Ka mance sanda kake a cikin gareji cikin ƙazantar baƙin mai? Duk taƙamarka da homarka dai Tani daka raina itace silar fito da sunanka, domin itace sila kuma matattakalar arzikinka, matattakalar samun nutsuwa da sauyi a cikin rayuwarka. Kai butulu ne Kaila. Ka zalunci baiwar da ta yarda da ........"
Tas naji saukar mari zazzafa a kan kuncina. Da sauri na dafe kuncina na saki kuka mai motsa rai, dan yau na kai bango, bana gudun duk abinda zai je ya zo. Ya daɗe bai ma zo ba. Cikin kumfar baki yace.
"Ke baki isa ki mun gori ba. A bazawara karuwa na aureki mai yawo kwararo_kwararo ƴan cirani da kanukawa suna hutawa dake, suna baki kuɗi. Tunda bara da tumasanci shi uwarki da ubanki suka koya miki. Rammai babu yadda bata yi dani ba dan kar in aureki amman na ƙeƙashe na aureki, na haɗa jini da tsiya, mitsitaciya....." Tas na zuba mishi mari, kafin ya fita a cikin mamaki na sake zuba mishi mari, wallahi sai da ya kifa. Bai san sanda ya danna ihu ba. A guje Hajiyayye da Hindatu suka fito, Bilkisa kuwa ko oho. Mamaki da tsorona ya hana Kaila iya furta kalma, sai ajjiyar zuchiya yake saukewa. Ni kuma a yanda nake ji banƙi in dira a wuyanshi in ta dukan ɗan kutumar uba ba.
"Kije na sake ki sati biyu. Ki tattare kayanki ki bar mun gidana yau ba sai gobe ba. Aurena dake ya ƙare har abada, aje a auri miji na shida" Ji nayi kamar ya buga mun guduma a maɗigata. Bansan yanda zan musalta muku zafi da raɗaɗin dake cikin kalmar saki ba. Ji nayi kamar ya watsa mun ruwan dalma. Take na soma haɗiɗiyar zuchiya, musamman dana tuno ƳaƳana in na tafi na barsu rayuwarsu zata iya tarwatsewa ƙila fiye da yanda rayuwar Dauda ta kusan nakashewa. Gashi ina ji Bilkisa na faɗin ita tafiya gidansu ma zata yi, to Hajiyayye ce zata kular mun da yara in na tsallakesu. Hajiyayyen da bata ƙi mu mutu mu duka ba. Hajiyayye ce ta buga tsaki ta koma ciki, Hindatu kanta naga rauni a kan fuskarta. Ni kuwa ina ƙame kamar takadda a wajan. Bilkisa ce ta fito tiri_tiri da akwatuna manya. Ciccike da kaya tana jaye da hannun Fatima. A bayan motarta ta jefa Fatima, kafin ta shige motarta, Kaila ya isa a zabure yana ƙoƙarin hanata tafiya. Hmmm duk wannan abun da akeyi ashe Shamwila tana bayanmu a gaban idanunta komai yake wakana. Murmushi tayi mun irin na mugunta. In dai Kaila ne gata gashi, daya ci moriyarta zai watsar da'ita a kwandon shara, ayi dai mu gani. Bana ko gani na shiga ɗakina. Yaran sai wasansu suke yi Hasiya na musu tatsuniya. Zamewa nayi na yi ciki. A kan gado na faɗa na saki kuka mai ciwo. Kashedin Inno da Baffa ya dinga yawo a kaina, shikenan tawa ta ƙare, babu mai yarda dani, nasan Inno zata yi tunanin sabida batun karatunane Kaila ya sake yi. Ko Qur'ani zan haɗiye in dinga aman surori babu mai yarda dani. Ni ba Kaila nake so ba, yarana nake so, gobensu nake tunani, yaya zasu rayu babu ni tare dasu, kuma bacin ba mutuwa nayi ba? Gashi yarana dani kaɗai suka saba, a gabana Hajiyayye ta kusan hallaka mun Ɗa, haka ma Hindatu ta ƙona mun ɗiya ina gani, haka ina cikin gidan kaila ke ma yarana dukan shan gishiri, yau in na tsallake na tafi yaya makomar yarana?"
"Shanono ke shanono. Ki tattare inaki inaki ki zo ki fice mun daga gidana, babu aure a tsakaninmu baki isa ki kwana mun a gida ba. Harni zaki sa hannu ki mara, ko da yake ai kun saba cukume maza, da ƴaƴan jagora da ƴan tasha bansan wa yafi dama_dama ba" Tun kaila na yi kamar wasa, sai abu ya rikiɗe zuwa zagin iyaye da cin zarafinsu. Hakan bai mishi ba sai gashi ya shigo uwar ɗakina a fusace. Da sauri na miƙe tsaye, hannuna riƙe da akwati da ƙatuwar ledar provision na makarantana.
"Zo ki fice kuma kar ki kuma tako ƙafarki da sunan zuwa ganin yara. Gidanma siyarwa zanyi in bar garin, ba dan komai ba sai dan sabida fitina da nacin iyayenki, kar su zo suita mun magiya da suntiri. Zo ki fice maza umma ta gaida assha." Ji nake kamar in dira a wuyanshi, haka nake ji. Idanuna take suka kafe, hawaye ya dena zuba. Yarana kuwa ina jiyo sautikan kukansu. Raɓawa ta gefenshi nayi na fito falon. Ina ganinsu na karaya, da sauri Sani yazo ya rungumeni tsam. Idanu na runtse inaji kaina na tashi sama.
"Baba dan Allah ka bar mana ummanmu. Kayi haƙuri." Yaran dukkansu suka tsugunna a gaban kaila suna kuka, abun mamaki harda Salis Auta. Kaila yayi tsam yana kallonsu, jikinshi naga halama ya mace mus, ruɗani ne tare dashi.
Hasiya zo ki daukar mun kayana muje" Na faɗa a sanyaye zuchiyata na harbawa. Da sauri Hasiya ta zo ledar hannuna ta ɗaura a kanta, akwatin kuma ta ja ta fita. Nasa ƙafa ta ɗaya a waje ɗayar a ciki, sai naji Sani ya saki kuka mai sauti yace.
"Baba mun shiga uku zata tafi, dan Allah ka ce ta dawo. Ina ɗaga ɗayar ƙafar naji Kaila ya ambaci sunana cikin muryar nadama.
"Shanono......."
Meye ra'ayinku akan Shanono, kuna ga ta tafi ta bar yaranta, ko ta ci gaba da zaman haƙuri? Kar ku mance da abinda ya faru da Dauda a sakamakon barinshi da tayi a gaban mahaifinshi. Nagode da haƙurin bin labarin, ina ganin saƙonninku masoya ina godiya marar iyaka.

Sannan inason shaida muku sai Monday zan ci gaba da post, sakamakon rashin lafiya dake damuna, ina barar adda'ar masoya.

GAWURTATTU UKU 👠👠👠

1 _KWAI A BAKA_

*(UMMU AFFAN)*

2 _ZULFA_

*(UMMU MAHEER MISS GREEN)*

3 _NA FAƊO DAGA BENE..._
_NA ZARCE RIJIYA_

*(BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI)*

_Littafi ɗaya; 400_
_Littafi biyu; 800_
_Littafi uku; 1000_

Ga masu son turo kuɗinsu ta account sai su tura a wannan account ɗin 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
0037219728
Fatima Rabi'u Sunusi
StanbicIBTC Bank


Sai ku tura da shaidar biya ta wannan number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

08104335144

Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan number 👇🏻

08104335144

*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANNIN SHAFINMU NA Facebook, whatApp, telegram, YouTube, groups, status, zamu tallata muku ne a kan farashi mai rahusa 10k ne kacal sai ku tuntuɓi numbobinmu kamar haka 👇🏻

08104335144
07068606171
08179523215

Domin tallata muku hajojinku a cikin na sati guda ya kama👇🏻

2k kacal

Sati biyu
3k ne

Idan kuma kanason har mu gama book mu dinga ɗaura maka ya kama
10k kacal.

Muna godiya da zaɓar GAWURTATTU UKU ako da yaushe. Siyan nagari mai da ƙudi 🙏🏻NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU

LAMBA TA 5



Tsigar jikina sai da ta tashi. Amma wallahi ko me zai faɗa mun bazan dawo ba. Gidansu Inno ɗinma ba zuwa zanyi ba, dan nasan Baffa ka iya illatani a banza, cikin dakiyar zuchiya nace.
Saki ne dai ka sake ni, ƙila ka ɗauka mutuwa zanyi ko? Ga yaran ga gidanka duk na bar maka, komai daren daɗewa yarana zasu tako su zo har inda nake, na fita a rayuwarka har abada, ko da kaine namiji tilo daya rage a duniya."Fuu na fice da sauri ko waige bana yi, dan muddin dai na juya, kaifin idanun yarana bazai barni ƙwatar rayuwata da ƴancina na ɗiya mace ba. A baya ma dana zauna jahilci ne ya zaunar dani Kaila yaita gasa mun aya a hannuna. Amman a yanzu Alhamdulillah duk da ban sauke Qur'ani ba amman nayi nisa sosai, kuma na haddace hadisai da dama. A makaranta na san yaya Aure yake, da zaman Aure a musulunci, anan naji yanda Arrasul Sallallahu alaihi Wasallama yayi rayuwar aure da matayenshi. Ni a al'adance kaɗai nasan aure, na kuma gane al'adu mun bari sun yi fintikau a cikin lammuran Malam bahaushe. Bance duka ba, domin akwai da dama masu aiki da ilimin muhammadiyya, da dama kuma Al'adunsu sune kan gaba akan komai bama auren ba. Dana fito a cikin gidan sai na ɗaga kai na kalli gidan, domin na barshi har abada, in yarana sun kawo ƙarfi zasu neme ni a duk inda nake, amman ni babu wanda zan sake waiwaya ya'isa haka kuma. Bana ko gani, jefa ƙafafuna kawai nake yi. Ina baya Hasiya tana gaba da kaya tiri tiri. Kai tsaye gidan Yaya Use muka nufa. Har sun rufe gidansu, Yaya Use ce tazo ta buɗe mana, dan Baban yara sana'arshi ta dare ne shima.
"Lafiya Tani mutuwar Aure a karo na biyar ko?"
E Yaya Use " Yanda taji muryata gadagau ne yasa ta bamu hanya muka shiga daga ciki. A ɗakinta muka keɓe, ko wanne gida da wuta a layin, amman su basu da'ita.
"Tani yanzu akan karatun naki ne Kaila ya gwammaci ya sakeki, sai da ya gama kwararraɓa miki rayuwa, yaranshi dashi suka tsotse ƙuruciyarki. Shin kin mance da kashedin Inno da furucin Baffa ne? Ni da kin nemi shawarata da zance miki ki haƙuri dakaratun kiyi zaman aurenki, ko dan yaranki. A baya ke kinga illar barin yara a tsakar gida, yanda hakan ya shafi babban ɗanki, da ace bamu je garinnan ba da mutuwa Dauda zaiyi. Can kuwa yaran har da mata duk kika tsallake kika bari?
Tani kiyi haƙuri, sannan kiyi tunani me kyau, kar ki zo ki aikata aikin dana sani akan rayuwar yaranki, kar ki fifita karatunki akan rayuwar yaranki. Kinga dai mu irin rayuwar da mu ka yi a gaban su Inno, rayuwar gantali da rashin zuchiya. Ki kwanta zuwa gobe da safe ƙila kin yanke hukuncin da kike gani yayi miki dai_dai. Gado ta hau ta yi baccinta. Ni kuwa a wajan na takure ina kukan baƙin ciki, haƙiƙa inason rayuwa da yarana sosai. Amman kaila ba namijin zama bane, kuma gashi da ruwan ido, da maitar mata. Allah ya gani inason karatuna, domin in taimaki ƴan uwana harda dangina. Iyayena suna buƙatar tallafi, haka zalika ƴan uwana. Meye banyi ma Kaila ba, ai nayi mishi riga da wando, ni na zame mishi matar rufin asiri, da dukiyata yake wadaƙa da ninƙaya, da dukiyar tawa ya wulaƙantani, da dukiyar tawa yaketa auren mata, da dukiyar tawa ɗakin da zamu zauna ni da yara sai da kishiyoyi suka gama zaɓe aka bani wanda ya rage. Bayan dani aka yi hidimar ginin da komai. Meye ban gani ba meye ba'ayi mini ba? Ba Kaila kaɗai ba duk inda naje da zummar zaman aure sai anyi mun korar wulaƙanci, shin auren dole ne? Ko ɗaya, in nace na gaji haka zan zauna in yi rayuwa ni kaɗai akwai wanda ya isa ya ƙalubalanceni ne? Babu shi ba'a yishi ba. Damuwa ta dameni a wannan baƙin daren haka na kwana cur a zaune, tsabar

4 / 14