Author : Billyn Abdul Category : Love
NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU
Lamba ta 1
Ina godiya marar adadi a gareku masoyan rubutuna, Allah ya barmu tare, ya sadamu a aljannah maɗaukakiya. Shanono ma tace in miƙo mata godiya.
Nagode da jimirin jira, na dawo da zafina.
Shanono. Ina ji alƙali ya buga gudumarshi dam_dam. Aka miƙe a tare, tare da haɗin baki wajen cewa.
"Kotuuu" Cikin ƙudurar ubangiji sai na nemi tsoro da fargabar da suke ɗawainiya da ruhina tun jiya na rasa. Fuskata na sake murtukewa, ina tsaye dam a kan ƙafafuna. A maimakon in sare, sai sabon ƙwarin guiwa ya ziyarceni. Kunto Salis nayi a baya na, tsabar ɓacin rai na miƙo ma Sabira.
Ki kula dashi Sabira. Kui mana adda'a. Kwana ashirin a gidan yari , ba mutuwa bane. Wani darasin na rayuwa zamu mu je koyowa" Ban karashe maganata ba, ƴan sanda suka iso inda muke suka sanya mana saƙandami a hannayenmu. Yaya Use kuwa sai zare idanu take yi, halamu sun nuna tana cikin ɗimuwa sosai. Ni dai furtawa nake.
Sabira ƴaƴana suna gidan Yaya Use, suma fama suke yi. Ki ajjiyesu a wajenki su koma karatu. Habiba Bala nagode." Inda Kaila yake na kalla, ba abun mamaki bane dan naga murmushi a shinfiɗe kan fuskar Kaila. A raina na furta.
Zaku sha mamakin shanono muddin na fito." Ƙeyarmu aka kaɗo zuwa waje. Hajiyayye sai falli da zubar da maganganu kaifafa take yi ƴan uwanta suna kuma zugeta. Lauyanmu kuma sai kalma yake bamu, yana tausarmu akan komai zai daidaita. Ni bana so ma ya daidaitan a tunanina zaman gidan yari yafi zaman gidan Kaila daɗi da samuwar ƴanci. Yara kawai nake ji, amman da da kaina zan nemi takaddata dan ta fiye mun alkhairi. Damuwa da tagayyarar da yarana zasu yi ne kawai nake ji. A motar gidan yari aka jefamu, ina kallon idan Sabira da Habiba Bala, ina kallon Salis dake riƙe a hannunta. Kasa riƙe kansu su ka yi sai aikin kuka suke yi. Ni kuwa zuchiyata dan haushi tuni ta dake, ko halamar kuka bana ji. Muna ji muna gani aka fice damu. Yaya Use sai hauka da bige_bige take faman yi tana ambaton, ta mutu ta lalace. Ni dai sai Alhamdulillah kawai nake furtawa, bani da wata adda'a dana iya, sai godiya da nake ma Allah. Na yi imani tsananin son da Ubangijina yake yi munne yasa nake faɗawa kwatami iri_iri. Tun kafin in kai haka nake fuskantar ƙalubalen gidan aure kashi kashi. Jiya na kasance a cell, gashi yau zan kwana a kurkuku, oh ni shanono, wai ni Hajiyayye zata raɗa ma sharri, abun tambayar akan me take yin duk wannan abun, akan Kaila? A'a ba haka bane tunda tasan ko kallo ban ishi Kaila ba. To akan me take yi ne ku bani amsa in kun sani?. Kaina yayi zafi sosai. A haka muka iso gidan yarin. Gandirobobi suka tasa ƙeyarmu izuwa wani dogon falo. In da anan zaka faɗi sunanka da laifin da yasa aka kawo ka. Bayan duk mun faɗi sai aka ajjiyemu a ɗakin jiran shari'a wato ( waiting room? Duk wani wanda ba'a gama zartar mishi da hukunci ba, ana kotu ana gumurzu, to wannan ɗakin shine wajan zamansa. In an yanke maka zaman gidan yari, na wasu wa'adi, ko ɗaurin rai da rai irin na Su Hauwan Aminu diya ga marne ƴa ga Sada ( UNGULU DA KAN ZABO) to wannan wani abune da ban. Za'a shigar da mutum cikin yadi. Bayan an tasa ƙeyarmu zuwa cikin wannan ɗakin jira. Sai lokacin na saki kuka dana yi tozali da matan dake cikin ɗakin, harda waɗanda suka manyanta. Dama mata su na yin laifin da har ake kawosu gidan yari kenan. Iko sai Allah. Kwananmu na farko tamkar a cikin kabarina na kwana haka naji. Ashe akwai ɓirɓishin rahama da salama a cikin gidan Kaila. Duk lalacewar Kaila ya fi gidan yari gaskiya. Allah sarki yarana. Abincin gidan yari bala'i ne. Har maggi wasu suke barbaɗawa, suna da kuɗi a kanta, gandirobobi ke siyo musu. A kwana na biyu Sabira ce ta kawo mana abinci, amman bamu samu ganawa ba. Ta dai kawo mun aidigar mata, da ɗan dires sababbi guda takwas. Nonuwana sun suntuma sunyi tauri tamkar dutse, hakan ya haifarmun da zazzaɓi mai zafin gaske. A ranar ne Habiba Bala da lauyanmu su ka kawo mana ziyara, domin sake jin ta bakinmu. Halin da suka tarar dani ya kidimasu, da taimakonsu aka kaini ɗakin shan magani dake cikin gidan yarin aka harhado mun magunguna.
"Shanono kiyi haƙuri. Muna kan bincike kuma akwai danshin nasara. Yaronki yana hannun Sabira tana bashi madarar yara. Makarantar islamiyyarku Sabira ta sanar musu wata tafiya ce ta taso miki, haka ma bokon an sanar musu. Yaranki suna cikin ƙoshin lafiya. Kaila ya je har gidan Sabira ya tasa ƙeyarsu ya mayar dasu gabanshi. Amman kiyi haƙuri gidansu ne ai. In ma kashesu zai bari Hajiyayye tayi ai sai ya bari. Yaya Use kema na je gidanki ni na sanar ma mijinki duk abinda ake ciki. Jiya yazo ba'a bashi damar ganinki bane."
"To lokacin ku ya cika" Cewar wani gandiroba daya katse ma Habiba Bala hanzarinta. Haka dai rayuwar mu taci gaba da gudana a cikin gidan yarinnan. A cikin ƙanƙanin lokaci duk mun rame, bamu sake ganin kowa ba, basa bari a ganmu. Har Baffa da Inno suma sun zo bisa jagorancin Yaya Karime. Suna dai sanar mana sunayen masu kawo ziyarar amman ba'a basu damar ganinmu, in ba dai lauyanmu ba. A cikin sunayen banji sunan Kaila ko sau ɗaya ba. Sai da na kwana goma cib a gidan yarinnan banyi wanka ba. A cikin kwana na sha ɗaya ne na watsa ruwan sanyi, nayi wari har sai da bokan zamana suka ishemu da ƙorafi, gabana duk ya ɗaɗe, sabida ina jini, kuma baya samun ruwa, duk jinin biki ya bubbushemun, ya manne a gashin wajen, sai ciwo yake yi mun. Wuni nayi da zazzaɓi mai zafi a jikina a ranar. Bazan iya fasalta muku irin rayuwar gidan yari ba. Amman ko maƙiyina bazan so a kawo shi wannan wurin ba. Amman zaman gidan ya sake farkar dani, gami da zaburar da ni akan al'amuran rayuwa. Kwanci tashi asarar mai rai. Cikin hukuncin Allah yau yayi dai _dai da ranar laraba ashirin ga sabon wata. Wanda yayi dai_ dai da ranar da zamu yi zaman kotu na ƙarshe. A daren ranar ni da Yaya Use haɗe kai mu ka yi, mu kai ta kuka. Babban tashin hankalin mu shine ace dawo damu za'ayi wannan baƙin gidan. Cike da damuwa da taraddadi gari ya waye.
Kaila:
Tun bayan da Bilkisa ta dawo aiki ta ga yaran Tani a falo a takure suna kuka. Ɓarayinta ta ja su, ta basu abinci. Suna cikin ci kan baka kan ƙwarya, Kaila ya shigo, Bilkisa tayi tagumi tana kallonsu cike da tausayinsu, a zahirin gaskiya tana tausayin uwarsu sosai."
"Su kuma waɗannan yaran me su ke yi a falonnan kalan su tsuttsula fitsari. Ku tashi ku fice ƴan iska" Jikinsu na rawa, Sani ya sasu a gaba suka fice daga ɗakin. Bilkisa ta kalli Kaila tace.
"Wata rana na tabbatar yarana za ka yi ma wannan koran wulaƙancin. Tunda ai kana son Tani ne shi yasa tun farko ka aurota. Kuma duk ƙazantarta da kake kafa hujja dashi, gashi ɗanyan goyo ne da'ita. Sannan hausawa sun ce matar so ita ke yin konika. Kaila ni fa na gaji da aurenka. Na roƙeka dan Allah ka sake ni in koma garinmu" Zabura Kaila yayi, ya kafeta da idanunshi domin yasan suna da tasiri akan duk matanshi, ba ma su kaɗai ba akan duk macen daya zuba mata su, suna da tasirin kashe jiki. Saurin ɗauke kanta tayi. Shi kuma cikin sigar yaudara yace.
"Tani na sota irin son da ban yi muku ba duk ku biyun. Amman shekararta uku a gidana naji duk duniya babu wacce na tsana sama da ita. Tantiriyar ƙazama ce. Bilkisa ki mun uziri ko mu'amular aure zanyi da Tani sai na sa tayi wanka fin sau uku, ki yarda dani, sai na toshe hancina nake iya kusantarta sabida irin warin dake fita a gabanta......"
"Ya isa nace. Ka dena tona mata asiri haka. Akwai wani mataki daka ɗauka akan hakan ne, ka sani ko lalura ta gamu dashi, ko ka taɓa faɗa mata, ko asibiti ka kaitane, shin ko maganin gargajiya kake bata?" Zum yayi domun Bilkisa shirin ɗaureshi da jijiyoshinshi tayi. Yasan baiyi duk abinda ta lissafoba. Face cin zarafin Shanono da zaginta, da kiranta ƙazama ballazaga samodara. Hakanne yasa ya ja numfashi cikin kaurara murya irin ta cikar mazantaka yace.
"Ɗanyan gwal. Kina ganin kamar bana yi ma Shanono adalci ne? A ƙarƙashin inuwar aurena fa take, kuma bana hanata abinci da yaranta. Sannan ai..
"Ya'isa yanzu ina taje naga yaran su kaɗai a babban falo, su da gidan ubansu amman duk sun takure?"
"Tana firzin ita da yarta, alƙali yace a ɗauresu akan kashe yaron dake cikin Hajiyayye da suka yi. Zuwa ashirin ga sabon wata mai kamawa za'a sake zaman kotu" Cikin ɗaurewar kai tace.
"Kotu akan Hajiyayyen, bayan ita ta cakali yar umman Sulaiman da faɗa, da cin zarafin iyaye? Ai ni banga ta yanda za'ayi su kashe mata ɗa a ciki ba. Domin babu wanda ya taɓa cikinta. Sannan ai ba da Umman Sulaiman akayi rikicin ba. Kai kuma wanne hukunci kake shirin ɗauka akan lamarin, Dady kuma yana ina?"
"Dady yana hannun ƙawarta Sabira. Ɗanyan gwal wanne hukunci kuwa zan ɗauka. Ai kes na gaban alƙali sai abinda ya zartar"
Tun daga wannan rana, Kaila bai sake samun kan Bilkisa ba sam. Ajjiyeshi tayi a kwandon shara, ta banza ajiyarsa hakkinshi ma da figi da yagi yake karɓa. Yaran Tani kuma ita ke kula dasu, ita take basu abinci. Ta ɓangaren Shamwila kuma sai tambaɗewa suke ita da Kaila. Tana ta yashe mishi aljihu. A cikin kwanakinnnan Kaila ya tafi Port Harcourt, ya buɗe ƙaton wajen gashin naman kaza harma da balango. Amadudu, da wani yaron aikinshi ne suka koma Port Harcourt ɗin suna kula da wajan. Sati biyu da kulle Tani Sabira da, Habiba Bala, da Yaya Karime su ka zo suka gyare ma Tani ɗakinta, aka zuba mata saitin kujeru, harda kafet na tsakiyar ɗaki. Wanda Sabira ta sai mata suka baje mata a uwar ɗakinta, doguwar kujerar da Sabira ma ta bata uwar ɗakin aka kai mata. Suka sa mata ƙarfen, da sababbin labule. Su Sani sai tsallen murna suke yi. Yara sunyi fes dasu har haske suka ƙara sabida kullum Bilkisa na sa Shamwila tai musu wanka, ta wanke musu kayan da suka cire. Yaya Karime ta saɓa Hauwa a baya da zasu tafi ta tafi da'ita dama tare suka zo. Hajiyayye tana babban falo sai ƙwafa take yi, tana mamakin yadda akayi Tani ta samu irin kujerun da taga an wuce dasu. Gogan kuma yana Port Harcourt ya koma ya ɗan riƙa ma su Amadudu aikin. Dan ba ƙaramin ciniki suke kwankwatsawa ba, kunsan mutanen kudu akwai su da son suya."
Ɓangaren su Baffa kuwa. Bayan sun dawo suka ji abinda ya faru a bakin Baban yara mijin Yaya Use. Sun shiga tashin hankali marar misaltuwa. Su gani suke yi ma su Tani sun tafi kenan. Barin ma da Habiba Bala tai musu jagora zuwa firizin ɗin aka ƙi bari su gansu. Hankula ya kuma tashi. Yaya Karime ce tai ta aikin rarrashi. Nan kuma Baffa ya buɗe fitina da faɗan me ya kai Use gidan Tani salesalin ta turguɗe mata ɗan auren da suke lallaɓawa ta zauna. Sawunsu biyu wajan tukubar Kaila basa samunshi. Inno ce ta yi dubarar zuwa gidan iyayen Hajiyayye domin ta basu haƙuri. Su kai mata cin kashi da gori marar daɗin saurare. Haka ta fito, ba tai zuchiya ba ta je gidan Tani wajan Hajiyayye ta dinga bata baki. In kun tanka Hajiyayye ta tanka. Inno dole data gaji da zaman jiran amsar Hajiyayye ta fita jiki a mace, bayan ta shiga ta dubo yaran.
*RANAR ZAMAN KOTU*
A motar gidan yari aka shigo damu kotun. Da Inno da Baffa na soma yin tozali. Sai su Habiba Bala, Sabira, Yaya Karime, Baban Yara, da Hajara ƴar Yaya Use da take aure a can garin su Baban yara. Hawayene suka shiga suntiri a kumatuna. Yaya Use kuma ta saki kuka mai sauti. Gefe da gefen mu gandirobobine mata suke tsare damu. Cikin kotun muka shiga, Su Inno suka mara mana baya. Zama mu ka yi a wajan zama. Da Kaila na haɗa idanu yana cikin ƴan uwan Hajiyayye. Bilkisa tana ganina ta taso, ta dawo ɓarayin da su Inno suke. Hindatu ta kalleni ta watsar, naga kotun an cika sosai, har da ƴan kallo a wannan karon. Bayan shigowar alƙali da mintuna aka soma karanto ƙara.
"A yau Ashirin ga sabon wata. Wannan kotu mai alfarma zata ci gaba da sauraren shari'ar Hajiyayye, da Tani,da Use." Alƙali yayi gyaran murya tare da cewa.
"Laiyoyin ɓangare biyun in sun hallara zasu iya soma ba da shaidarsu" Zuruf lauyanmu ya riga lauyan su Hajiyayye tashi.
"Na gode mai lord sunana Barister Suwiɗi, nine lauyan dake kare waɗanda ake ƙara. Ya mai girma mai shari'a. Ranar biyar ɗin babbar sallah data wuce. Malama Tani tana ɗakinta mijinta Kaila ya je ya sameta har ɗakinta. Ya ce ta ɗakko atampar da tasa ranar ukun sallah, tazo ta same shi a ɗakin kishiyarta. Haka Tani ta ɗakko kayan ta bi Kaila ɗakin Hajiyayye ta bashi. A gabanta ya ɗauki kayan ya miƙa ma Hajiyayye har yana tambayarta.
Rigimar ta ƙare ko?" Alhalin ba Kaila bane ya sai ma Tani wannan kaya ba. Asalima rabon da Kaila yai ma Tani sutura shekara huɗu kenan. Ya kasance marar adalci, kuma azzalumi akan matarshi..."
"Ina da ja ya mai shari'a lauya mai kare waɗanda ake ƙara yana shirin sauka daga kan doron abinda ya tara mu. Shari'ar Hajiyayye da su Use akeyi, ba wai tuhumar Kaila ba. Nagode my lord" Alƙali yace.
"Ƙorafi ya karɓu. Dan haka barister Suwiɗi ka kiyaye" Barrister Suwiɗi yace.
"Nagode my lord. Akan wannan kaya da aka kwace ma Tani ta hanyar fin ƙarfi shine. Yaya Use taje ta karɓo ma Tani kayanta. Wanda a ranar da abin zai faru kayan Hajiyayye ta saka, ta fito tsakar gida tana homa. Use ba da tashin hankali ta je ma Hajiyayye ba. Itace ta cakaleta, ta hanyar zagin iyayensu. Daga nan dambe ya ɓalle a tsakaninsu. Kuma ba Use bace ta kashe ma Hajiyayye yaron dake cikin ta ba. Yaron ya mutu tun kafin wannan faɗan."
"Ina da ja ya mai shari'a. Wannan ƙirƙirarren labari kawai Barista Suwiɗi yake ba kotu." Lauyanmu yayi murmushi yace.
"Ya mai girma mai shari'a iyakar abinda zance kenan. Kafin in soma gabatar da hujjojina. Nagode my lord " Zama Barister Suwiɗi yayi, yana share zufa. Ni a wannan karon ko gezau bana ji a zuchiyata. Kuma da zan samu dama a cikin kotunnan zan kashe Kaila uban kowa ya rasa. Muryar makirin lauyan su Hajiyayye ne ya dawo dani daga duniyar tunani.
"Ina neman wannan kotu mai alfarma ta bani dama in gayyaci Hindu Facalar su Hajiyayye wacce a idanta faɗan ya wakana. Asalima da ita aka ɗauki Hajiyayye ranga_ranga zuwa asibitin matanmi."
"Kotu tana neman Hindatu" Ƙur na ƙura mata idanu. Ta tawo sai harɗewa take yi, ta tsaya a cikin ɗan akwaku. Alƙali yace da'ita.
"Gabatarma da kotu sunanki"
"Sunana Hindatu Madaki." Lauya ya tsaya a gabanta yace.
"Hindatu zan so ki bani labarin abinda ya faru a ranar talata, wanda yayi daidai da bakwai ga wata na bature, da misalin ƙarfe shida da minti goma na yamma"
"Ni dai ina tsakar gida ina aikina. Sai naga Use akan Hajiyayyen tana cewa su je ciki su yi magana. To Hajiyayye dai ta nuna mata ba zasu shiga ciki ba. Shine Use ta rufe Hajiyayye da duka, Tani na tayata. Haka su ka zauna a cikinta Use na kokawar sai ta yi mata tsirara, dan harta yayyage mata rigar jikinta, daga ita sai gwado. A haka jini ya ɓalle mata. Ko da mu ka kaita asibiti likitoci suka ce tiyata za'ayi mata, sakamakon dukan cikinta da akayi yaro ya mutu mata. Iyakar abinda na sani kenan." Murmushi nayi kawai, Hindatu zata aika ai. Tunda ta taɓa kuzama Balarabana ruwan zafi tana rarrafe, ɗuwaiwanta sai da ya sale. Yaya Use kuma kuka ta rushe dashi.
"Ko lauya me kare waɗanda ake tuhuma yana da tambaya da zai yi ma Hindatu" Cikin ƙarfin guiwa yace.
"Ina da shi my lord " Ƙwaf_ƙwaf_ƙwaf ya isa bakin ɗan akwakun yace .
"Malama Hindatu. Shin dama Tani ta saba rigima da Hajiyayye ne, ko wannan shine karo na farko?" Hindatu tayi tsiri, daga baya tace.
"Basu taɓa yin faɗa ba gaskiya."
"In na fahimceki zaman lafiya suke yi kenan, babu komai a tsakaninsu"
"Ina da ja my lord. Lauya na son ɗaura ma Hindatu fargaba. Wannan shine tsaiwarta a kotu na farko, bata saba ba" Alƙali yace.
"Ƙorafi bai karɓu ba, dole Hindatu ta amsa wannan tambayar. Barista Suwiɗi ci gaba da tambayarka"
"Nagode my lord. Hindatu kotu na saurarenki" Hindatu ta nisa, kana tace.
"Zaman doya da manja suke yi. Amman basa yin faɗa, Tani bata fiye shiga harkar Hajiyayye ba gaskiya" Kai ya gyaɗa yace.
"Zaki iya tafiya" Sum_sum ta fito. Lauyanmu yace.
"Ina neman alfarmar wannan kotu da ta bani damar gabatar da shaidata ta farko" Bayan rubuce_rubuce da alƙali yayi yace.
"Kotu ta baka dama"
"Ina son Bilkisa Ɗanyan gwal ta fito gaban kotu"" Bani kaɗai ba naga hatta Kaila, da Hajiyayye, dama Hindatu sai da su ka kaɗu. Ƙwas_ƙwas_ƙwas ƙwas take tafiya takalminta na fitar da sauti. Cikin ɗan akwakun ta shiga. Kaila sai zazzare mata idanu yake yi, ita kuwa tayi biris ."
"Bilkisa kotu na son jin sunanki daga bakin ki"
"Sunana Bilkisa Salis Sabo"
"Ko zaki iya sanarma da kotu gaskiyar abinda kika sani?" Bilkisa ta gyara tsaiwarta tace.
"A kan idanuna komai ya faru. Tun daga zuwan Yaya Use wajan Hajiyayye har fitar da'ita da akayi a gidan tana zubar da jini. Yaya Use bata je gun Hajiyayye da fitina ba, asalima Hajiyyen ce ta nemi ayi