Author : Billyn Abdul Category : Love
na kutsa cikin ma'ajjiyar hotuna, na shiga kallon yarana ɗaya bayan ɗaya. Take farin ciki ya kamani, na shiga murmushi idanuna cike tab da ruwan Hawaye. Wannan tunanin shine abincina tsawon wannan lokaci, ban taɓa dena tunaninsu ba, zuchiyata tana bugawane tare da sansu da kewarsu tsantsa. A dai_dai Kabuga na sauka, na biya mai ɗan sahu kuɗinshi na shiga cikin chamba.
"Barister Shanono wanka, kina sauka a abun hawa Nafi'u ya gyara zama wai zai kashe ƙwarƙwatar idonshi. Murmushi nayi na manyan mata gogaggun da suka san jiya da yau. Bance dasu komai ba na kutsa cikin office ɗinmu, mai ɗauke da tebura huɗu na baristoci, mu biyu mata, biyu maza. Khadija mai hula ta ɗago ta kalleni tace.
"Barister Shanono har kin kammala shari'ar taki, aina ɗauka zai ɗauke ki tsawon lokaci sosai." Sai da na zauna a kujerata na ajjiye farar designar jakata kana nace.
"Ke dai bari Mai hula, na gaji tulus, gashi ƙarfe huɗun yamma ma ina da wata shari'ar, yanzu nazari ma zan ɗan kuma yi. Littattafan dana ce ki tawo mun dasu kin kawo mun kuwa?" Na tambayi Mai Hula cikin kafeta da idanu. Tace mun.
"E na tawo miki dashi, yana mota bari Aisha in ta shigo zan bata key ta ɗakko miki. Ɗazu wasu mata suka shigar da ƙara, akan wai mijin ita ɗayar ta siya musu gida suna zaune, mahaifinta daya rasu ta harhaɗe kan gadonta ta bashi ya ja jari. Katsaham sai ya jijjigo aure kinji dalilin shigar da ƙaran." Idanu na lumshe ina nazari tare da ƙalubalantar mazan wannan zamani, da rashin amana yai ƙaranci ga dayawa a cikinsu. Kafin ince wani abun Oga Rashid ya turo office ɗinmu, ya doge a bakin ƙofar ya kalleni.
"Barista Shanono "
Sir ( Yallaɓai) Shine kaɗai abinda nace mishi cikin girmamawa.
"Ki same ni a office zamu yi magana yanzu, dan ina da shari'a nan da awa guda" Yana kai aya ya rufe ƙofar. Numfashi na ja, cikin ƙarfin guiwa na miƙe na fita ƙwas_ƙwas zuwa office ɗin Barista Rashid. Office ɗin babbane sosai, ga kayan more rayuwa a ciki, dangin Tv, firji, dispensa, da doguwar kujera babba daga gefe, ga kafet malala a office ɗin. Waje ya nuna mini na zauna.
"Akwai wata mata da ɗazu ta shigar da ƙaran mijinta, har na yankar musu sammaci ta tafi dashi. Inason ki jagoranci kes ɗin. Nan da kwana talatin za'ayi zaman farko." Takadda ya miƙo mun mai ɗauke da cikakken sunan matar, da number waya, harda adireshi.
"In kin samu lokaci sai ki neme ta ki soma binciken daya dace. Abu na gaba ina yabawa da ƙoƙarinki, jajircewarki tana burgeni. Na tura miki frend request a shafinki na facebook, ance kina faɗakarwa sosai, amman baki aseptin ɗina ba, ko me yasa?" Ya ƙarashe zancen da zolaya. Basarwa nayi nace.
Za'ayi aseptin Sir ( Yallaɓai), ban samu zarafin hawa bane kwana biyu sakamakon aiyuka da suka sha mun kai. Asabe kuma zan nemeta ni da ita mu tattauna kafin zuwan shiga kotun. Nagode akwai littattafan da zanyi nazarinsu yanzu Yallaɓai, zan iya komawa bakin aikina?" Dariya yayi mun yanata daddana komfutarshi.
"Zaki iya komawa Barista Shanono" Da sauri na miƙe na fice. Office ɗinmu na koma, na samu waje na zauna. Aisha mai mana goge_goge tace.
"Anty Shanono zanje siyo abinci akwai abinda kike son ci?" Ido na lumshe, sai lokacin na tuno ruwan shayi kawai na kurkurɓa da safe a gurguje shima.
E Aisha, a siyo mun amada, da miyan ewedu da ganda" dubu ɗaya da ɗari biyar ne plate. Sai na zaro dubu biyu na bata.
Ki riƙe canji, ko abinci kya siya kema" Tana godiya ta fita. Ban ɗakin cikin ofishinmu na shiga na ɗauro alwalar azahar. Daddumata na shinfiɗa, na buɗe durowata na ciro ƙaton hijabina na ta da kabbarar Sallah. Ina idarwa wayata ta shiga kuka Yaya Use ce take kirana. Sai da na yi addu'o'in da kullum su nake maimaitawa, yarana nake roƙama ni kam Alhamdulillah duk abinda nake buri na samu, harda wanda ma ban roƙo ba Allah ya dubabe ba dan cancanta ba ya bani. Kullum dai a cikin ƙara gode mishi nake a bisa ni'imar da yayi mun nake. Ina zaune a daddumar ina jan jarbi Aisha ta dawo daga aiken da akayi mata. Nawa ta ajjiye mun a gabana da ruwa leda ɗaya. Ta ajjiyema kowa abincinshi akan teburinshi. Haidar ne ya shigo da sauri, kot ɗin jikinshi ya zame, ya zauna akan kujerarshi yana faɗin.
"Barister Shanono ina neman agajinki, wallahi wata shari'ace mai rikitarwa nasa a gaba ko runtsawa bana iyayi. Yau da mu ka yi zamannan sai nake ganin kamar abokin aikina zai yi galaba a kaina." Dariya kawai nayi mishi, na buɗe takeaway din gabana kafun nace.
"Ba zai kai ka ƙasa ba muddin ɓangaren daka riƙe me ƙwarine, sannan kune kake tunanin masu gaskiya, ba murɗa_murɗa irin na yawancin ƴan uwanmu lauyoyi ba? Amman duk da ina da shari'a ƙarfe huɗu kuma zanyi nazari. Zan saurareka bari in samu in sa wani abun a cikina." Abincina nasa a gaba inaci a hankali, harna kammala tas. Na shiga kewaye na wanke bakina da hannayena tas da sabulun ƙamshi. Ina fitowa Khadija mai Hula na shigowa. Teburina na koma na zauna na buɗe ɗaya daga cikin littattafan da Mai Hula ta ajjiye mun. Nazari na yi na awa guda, kafin na rufe, na saurari Haidar kuma. Ƙarfe uku dot na miƙe.
To da Alkhairi, daga kotu sai gida kuma. Sai gobenku" Sallama nayi musu na fice a nutse zuwa kotun da nake da shari'a. Ƙarfe huɗu muka shiga kotu, awa guda mu ka yi ana fafatawa kafin muka tashi, sai ƙarshen wata mai kamawa za'a sake sabon zama. Ban samu damar kiran Yaya Use ba har zuwa wannan lokacin. Key na zaro a jakata na buɗe ɗan madaidaicin gidanmu da muke Zaune ni da Rahama, wannan bazawara mai Aure uku da na zauna a ɗakinta lokacin ina karatu. Har zuwa yanzu tare muke zama, kowa in gari ya waye ya fita wajan aikinshi. Da sallama na shiga tsararren falon namu duk da nasan babu kowa. Gidan karamine sosai, falonmu 3sitter kawai muka saka ƙatuwa mai kyau. Sai kafet da muka malala a falon, sai kayan kallo, da dispenser, sai wajan cin abinci, sai primes da muka ƙawata falon dashi. Ko ina tas, to mu ba yara ba kuma mu ba mazauna ba ma. Ɗakina na tura na shiga dake hannun dama, na Rahama yana hannun hagu. Katiface sumbuƙa a ƙasa tasha lallausan farin zanin gado, da fululluka ƙananu har guda takwas, masu kala_kala. Daga gefen gadon durowar littattafainane shaƙe da manyan littattafai irin namu lauyoyi, sai teburi da kujerar karatuna, da laptop ɗina a kai. Daga kusa da inda wadrope yake kuma anan katakon sagale jakunnuna na suke, da abun jera takalma. Abunda zai baku sha'awa takalman duk yawansu kala biyu ne tak, fari, baƙi. Hakama jakunkunan suke, dan tsabar gaye ko wanne takalmi tare da jakarshi nake siyanshi, bana iya siyan wari da wari. Jakata da na shigo da'ita yanzu na sagale a inda sauran suke, takalmina ma na cire na mayar dashi gurbinshi. Na cire kayana tsab na yo wanka, su kuma kayan dana cire na dulmiyasu a ƙaramin injin wanki dake kewayena, na zuba ruwa da omo inji ya shiga aikinshi na wanki. Ni kuma na zura doguwar riga marar nauyi, na tada kabbarar sallar la'asar, na jima a kan sallayarnan ina roƙama yarana arzikin duniya dana lahira. Abu na gaba sai na kira Yaya Use a waya ringin biyu zuwa uku ta ɗauki wayata.
"Tani barka da yamma. Ai tunda na kira naga baki ɗaga ba nasan aikine yayi miki yawa. Kuma kinga yanzu Sani ya bar gidannan, ka kawo mun cefane wallahi" Murmushi nayi na farin ciki nace.
Masha Allah Yaya Use, wallahi aikine ya sha kaina kinga sai yanzu ma nayi sallar la'asar. Kuma a hakanma wani sabon aikin zan shiga fa. Ya iyalin, ya Baban yara?" Dariya tayi tace.
"Lafiya duka muke, dama inaso in sanar miki gobe inason zan shigo kanon, wallahi Tani Jos taci wuta talauci da rashin aikin yi na neman durƙusar damu. To kinga dai Baban yara yama dena gashin balangon yanzu, babu jari. Ni jarukan da kikaita bani a kai duk muka ta'allaƙa dole aita cinyewa. Ni kunyar roƙonki kuɗi ma nake yi wallahi. Ga su Inno maganar barannan wallahi sunƙi denawa duk kuɗin da kike turowa kuma wallahi ina kai musu, in sai kayan abinci in jibge musu. Ke Inno siyar da kayan abincin ma take yi. Indo ce ɗazu ta kawo mun wani zance, amman ki bari in na shigo kanon ma tattauna" Ajjiyar zuchiya na sauke na dafe kaina, hawaye suka zubo mun. Wai me yasa mabarata su basa son dena barane, shin sun fi son ganin rayuwarsu a wulaƙance kenan ko yaya? Duk abinda na tara akan su Inno da yara nake ƙararwa, duk da basu san kuɗin daga gareni bane. Yaya Use ce kaɗai ta sani, sai Habiba Bala, da Sabira, ko Yaya Karime bata san cewar Yaya Use ta san inda nake ba. Kowa akan haka yake. Yarana ina jin labarin duk halin da suke ciki, na kuka in yi musu, na jin daɗi kuma in taya su farin ciki.
To Yaya Use shikenan babu damuwa Allah ya kawoki lafiya. Ki aika yara wajan mai P O S ɗin bakin unguwarku su karɓo miki dubu ashirin zan tura mishi yanzu. Sai kiyi kuɗin mota, ki ɗan ajjiyema yara abinci. Bari in ɗan taɓa aikin, sai goben." Godiya Yaya Use ta dinga ragargazo mini. Ni kuma sai murmushi kawai nake yi mata. Alhamdulillah duk sanda na taimaki iyayena da ƴan uwana, da yarana sai inji farin ciki sosai, ko da kuwa ace ni bani da ko sisi a jikina. Dadduma na naɗe na adanata. Wayata da labtop ɗina na ɗauka na fito falo. Ruwan zafi na tara a kofi a dispenser, na zuba milo da madara, kana na zauna. Labtop ɗina na buɗe, a hankali.....NA FAƊO DAGA BENE...
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU
SAKON GAISUWA GA ƊAUKACIN MEMBERS NA GIDAN NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA. INA JINJINA MUKU. ƳAN V I P BAN BARKU A BAYA BA.
LAMBA TA 7
Facebook na shiga kai tsaye zuwa shafin Ƴancinmu wanda ni ke jagorantar shafin. Ina amsa tambaoyin mata. A rana ina amsa tambayar mata mabanbanta sin goma. Saƙonnin tambaya a rana ina cin karo da fin ɗari. Kuma duk zancan matanmu na Arewa baya wuce akan, cin zarafin maza, Zawarci, A'a miji ya sakoni da yara, iyayena sun koreni nike biyan haya nake kula da yarana. Iri iren matsalolin kenan. Wannan matsalar ta jefa Arewa a cikin gararin zina, maɗigo, luwaɗi. Mace dan miji ya saketa sai iyaye su hanata saƙat, dole ta fita ta kama haya dan ta dinga ciyar da yaranta. Iyayenta suna da rai amman kowa wahalar yake gudu. Daga haka wasu suke afkawa karuwanci,maɗigo. Duk dan su rufa ma kansu asiri, kuma sun samu damar hakanne a sakamakon gazawar iyaye. Bazawara a ƙasar Hausa bata da daraja balle kima. Wannan dalilin ne fa ya jefa mata da ƙananun yara cikin garari. Hawaye na share a guraben idanuna. Na soma amsa tambayoyi kamar yadda na saba, tare da ba da shawarwari. Wacce naji matsalarta babbace sai in nemeta in bata izinin zuwa gidana ta same ni. Wasu da kaina nasa suka shigar da kes kotu, na tsaya musu Alhamdulillah sun samu nasara, sun dawo suna rayuwar cikin sassauci. Akwai wata baiwar Allah Fatima, da miji ya saketa da yara goma, ya koresu har yaran. Tana zuwa gida raɓe_raɓe da kuka mahaifinta yace sai dai ta kama haya shi bashi da in da zai ajjiyeta da bataliyar yaranta. Hmm jikokin nashi yake kira da bataliya, a madadin manya su shiga lamarin Fatima, sai suka bar Fatima na ta yawon haya, da yawan wanke wanke gidan masu kuɗi, dan ta ciyar da yaranta. Da Fatima taga muddin da wannan sana'a zata dogara to tabbas yaranta ba zasu samu karatuba. Fatima sai ta faɗa zina, motoci na zuwa ɗaukarta short time, ko kwanan gida. Sanadiyyar shiga rayuwar Fatima da nayi ne da taimakon Allah na cireta a wannan ƙangi. Muka doka mijin Fatima a kotu, alƙali ya nuna mishi kurenshi, yanzu mijin Fatima kullum yana kai mata cefanen da zata ciyar da yara, shike biyan kuɗin hayanta, shi ke biyan karatun yara. Fatima ita kuma na tallafeta ta koma makaranta. Da wannan nake kira ga mata, mu yi ilimi, mu kuma riƙe sana'a. In mace tayi ilimi tana da sana'a kuma tafi ƙarfin wulaƙancin kowa. Dan wannan rayuwar ta sauya hatta iyaye sun fi ji da yaron da yake da tagomashi a cikin ƴaƴansu. Murmushi nayi dana tuno da irin rayuwar ƙasƙanci da wulaƙancin da nayi a gidajen aurena na baya. Babu mijin da bai sa hannunshi ya jibgeni ba. Kowa da irin wahalar daya bani. Amman na kan yi farin ciki in na tuno da yarana ababen alfaharina, da irin tarbiyyar dana ɗaurasu a kai. Rahama ce ta shigo tana tsaki. Hawayena na share na dubeta.
Yaya dai kika shigo babu ko sallama, sai tsaki?" Zama tayi a ƙasa ta yar da mayafi da jakarta a fusace tace.
"Ke dai bari. Ni gani dangina suke yi kamar wasu maɗuɗun kuɗi na tara ne. Duk matsala in ta taso sai a kirani. Sun manta korar karen da su kai mun. Dan sun ga iyayena basa raye. Wallahi Shanono da gudu ba ko takalmi na fito daga ƙauyenmu." Kuka ta rushe dashi, nima hawayen nawa nake ƙoƙarin mayarwa, amman ina sai daya ɓalle. Mun fi minti biyar muna rera kuka babu mai rarrashin kowa. Da ƙyar na yi shiru, na tuntsure da dariya dan in rage mana raɗaɗi nace.
Ya'isa haka Rahama. Mu dena kokarin tunowa da baya. Mu fuskanci abinda ke gabanmu. Mu gode ma Allah, matan cikin gida kuka, zawarawa kuka, ƴan matan ma fa a wannan zamanin kukan suke yi. Rahma mu gode ma Allah da yai mana ni'ima muke zaune ko wacce tana neman na kanta. Bama shashanci, bama zuwa inda za'a ganmu mutuncin yaranmu ya zube. Ki share hawayenki ki faɗa mun meye matsalar, nima ban daɗe da sauraren matsalolin iyayena daga bakin Yaya Use ba. Gobe ma tace akwai maganar da take son tazo mu tattauna."
"Nagode Shanono. Ina jin daɗin zama dake sosai. Tun muna wajen makaranta lokacin muna karatu, zuwanki yasa hankalina ya sake kwanciya. Ada gani nake yi kamar ni kaɗai na taɓa aure uku. Sai da na ganki ke mai Aure biyar. Yaya Hamisu ne ya kirani wai ɗiyarshi zata yi aure, shi kuma bashi da kuɗin kayan ɗaki. Shine Kawunmu yace mishi ya sanar mun. Ke ki ji fa Shanono, ni sanda nake buƙatar taimako wa ya saurari kokena? Kullum su kenan a cikin faɗamun matsala. Dubu ɗari uku ne kacal a aljihuna, kaya duk na dunƙule na saro kaya, ƴan office ɗinmu sun kwashe bashi. Dazu ina tsaka da aiki. Raliya babbar ɗiyata ta aro waya a maƙota wai Amir ƙaninta bashi da lafiya kwana uku yana kwance Baban bai kaishi asibiti ba fa, sai ni na tura musu da kuɗin asibitinshi" Rarrashinta dai na dinga yi, dan na fahimci yau a hasale take, da ƙyar na shawo kanta. Bayan mun yi sallar magriba sai na doka wayar Asabe.
"Assalamu alaikum wake magana?" Cewar Asabe, bayan na amsa mata sallamarta, sai na gabatar mata da kaina, tare da ɗaurawa da cewa.
Misalin ƙarfe goman safe gobe ki same ni a office inaso zamu tattauna, domin mu san yanda zamu ɓulloma lamarin ko Asabe."
"To Barista zaki ganni in sha Allah. Ai na ma san sunanki a facebook" murmushi nayi mata mu kai sallama. Rahama tana zaune sai lissafi da cike_ciken takaddu take. Aiki take a ma'aikatar shinkafa.
Uwar lissafi, me ake lissafawa ne haka. Ga wayarki tana ta ƙara" Rahama ta ɗago tace.
"Oganane Wallahi, nifa tunda yace yana sona sai na dena ma ganin girmanshi sam. Shanono ni fa tunda dai aure ba dole bane, ni kam na haƙura. Zan iya riƙe kaina in ci gaba da kulawa da rayuwata. Ina jin daɗin kasuwancina, da aikina sosai." Zancan Rahama hakane. Nima duk yanda mu ka kai da mutunci, muddin aka furta mun kalmar so, to zame jikina nake yi. Ni gani nake yi ma ai nafi ƙarfin wata soyayya a yanzu haka da girma na. Kula da rayuwar su Inno shine kawai a gabana." Bani na kwanta bacci ba sai wajajen ɗayan dare, ina kan labtop ina nazari. Washe gari kuma bakwai da rabi na fice. Yau saye nake da farar riga, da skirt na kanti, nayi zanzaro, saina ɗaura baƙar sut, da baƙin hijabi gayuna, farin takalmi da jaka. Sai ƙamshi nake busawa fatata ta wani murje tana sheƙi, gashina dake yana shan gyara, yayi wani irin tsawo sosai, sai yanzu kyauna ya sake bayyana, kasancewar bani da ƙiba kuma ni ba ramammiya bace sai shekaruna suka ɓuya. Kuma bana wasa da cin kayan itatuwa, domin Allah shine shaida banason in tsufa da wuri. Ƙarfe takwas dot ɗan sahuna ya saukeni a daidai chambar mu, isowar Mai Hula kenan itama. Tare muka ɗunguma ciki. Kowa ya kama aikinshi yana ta faman yi. Ƙarfe goma dot a chamba taima Asabe, mun samu keɓewa da'ita tayi mun duk bayanin da zan riƙa a kotu wajan ganin hakkinta ya fito.
Shikenan Asabe, in ina da buƙatar jin wasu jawaban daga gareki zan sake nemanki. Sannan kar ki sake kulashi kuyi wata rigima tunda kinsan kotu zata kwato miki dukiyarki." Godiya sosai asabe tayi mun, ta kama hanya ta koma ɗakinta. Ni kuma na koma bakin aikina. Ban jima da zama ba Oga Rashid ya leƙo, ya daɗe yana kallona ta ƙasan idanunshi. Sarai ina ganinshi, na daɗe da sanin manufarshi. Ina kiyaye mai zubewar mutuncinshi, dan yana furta mun kaimar so, naga zai takura mun, to zan iya barin aiki in sake chamba. Meeting ya sanar mana muna dashi gobe misalin takwas da rabi na safe, ya mayar da ƙofar ya rufe. Karfe hudu na baro office zuwa gida. Ina