Author : Billyn Abdul Category : Love
kam dai yaima rayuwarshi, dana iyalanshi giɓi. Amman ya ɗaura ɗamarar zama adalin miji mai son haɗe kan mata da yaranshi. Ruwa Bilkisa ta kawo mishi da abinci ta ajjiye mishi a gabanshi.
"Bari in watsa ruwa tukunna, in yi sallar la'asar. In kina da maganin zazzaɓi ki kawo mun in ɗan haɗiya" Miƙewa yayi ya shige ciki ya watsa ruwa ya fito. Jallabiyya ya zura a jikinshi, ya rama sallah. Yana zaune jugum Bilkisa ta shigo da tiran abincin a hannunta. Magani ta ɓalla ta bashi ya watsa yabi da ruwa"
"Meke damunka ne na ganka sukuku haka, kuma ba'a mota kazo bane?"
"Isa ne ya saukeni ya wuce da motar Kaduna. Daga Kano nake wajen Shanono, yara sun koma hannunta " Kallon tuhuma ta cike shi dashi.
"Umman Sulaiman dama an san inda take, har yara sun koma hannunta? Kai amman na mata farin ciki wallahi." Kallonta yayi kawai, abincin ya ɗan taɓa kafin yace mata.
"Allah ya ƙaddari na saki Shamwila, zamanmu ya ƙare da'ita. Ina mai baki haƙuri a bisa ƙuntata miki da nayi na auri mai aikinki. Ada na kasance namiji makwaɗaici, mai kuma son mace ƴar ado da kwalliya gani da ruwan ido. Amman a yanzu in sha Allah daku zan ƙare rayuwata. Bilkisa kiyi haƙuri ki yafe mun duk kusakuran dana aikata miki." Kallonshi Bilkisa tayi da kyau tace.
"To batun yafiya na yafe maka. Batun ƙarewar aurenka da'ita wannan ba abu bane daya shafeni. Allah ya yafe mu baki ɗaya. Kaima kasan mai kuskurene, duk wani abu daya ɓullo a cikin gidanka kai ka bashi damar faruwa. Amman tunda ka gane kuskurenka ai shikenan."
"Nagode sosai. Ina roƙonki ki biyoni mu koma Kaduna da zama, domin inason in haɗe kawunanmu mu zama tsintsiya guda. Yarana inason su shaƙu dani, su kuma shaƙu da ƴan uwansu. Kiyi haƙuri karki ce a'a Bilkisa. A taimaka ayi hakan zaifi alkhairi, dama sabida Shamwila ne kika ce ba zaki zauna ba. To yanzu bata gidan."
"Aikina da gidana in yi Yaya dasu?" Ta jefo mishi tambaya.
"Aiki zan sama miki wani a Kaduna. Gidan ko haya sai ki saka. In kuma kinason in siya in caske miki kuɗinki zan siya, ni nasa hayar" A taƙaice dai Kaila yaci galabar shawo kan Bilkisa, dan Allah ya yi shi da iya tsara mace, da sarrafa harshe wajen lallashinta. ta amince zata dawo Kaduna. Amman sai ta samu aiki a Kaduna kafin ta baro Zaria, sannan gidanta da take ciki ya siya ya bata kuɗinta a haka suka rabu.
Shanono:.
Kai tsaye kotu na nufa, nayi shari'ar dake gabana, amman na kasa gabatar da sheduna dukka, na roƙi alfarma a zama na gaba zan gabatar dasu. Alƙali ya ɗage lokacin zaman zuwa wani lokacin. A girguje na shige motata na bar cikin kotun. Habiba Bala sai kiran wayata take ta faman yi. Fur naƙi ɗaga wayarta domin bansan me zance mata ba. Ina kuma tsoron ita me zata ce mun, daga ƙarshe ma wayar na kashe gabaki ɗaya. Ina shiga gidansu Inno na tarar da tulin kayan abinci kamar za'a buɗe shago. Yara suka taryoni da murnarsu, Sani da Dauda basa nan sun fita. Ige ce tai mun bayanin kayan da kuɗi da Kaila ya bayar na batun karatun yara. Karɓar kuɗin nayi kawai na shige cikin gida. Haka nadinga yin komai sukuku babu kuzari a jikina. Ga faɗuwar gaba da naita fama dashi. Tunani yaimun yawa, na rasa abinda ke mun daɗi sam. A daren wannan rana saina tsinci kaina da kasa bacci sam. Haka na wayi gari idanuna sunyi zuru_zuru. Takwas dai_dai na shiga office. Amman na kasa yin aikin kirki, sai in yi shiru ina tunani, haka naita faman yi. Ko Oga Rashid sai da yasa akai mishi kirana yake tambayata meke damuna. Nace mishi babu komai bana jin daɗine kawai.
"Muje in kai ki asibiti, ya zaki zauna da ciwo har kizo office kuma a haka, no muje asibiti daga nan sai in kai ki gida" Bani da zaɓi ni kaina nafi sha'awar in tafi gidan in ɗan kwanta, ga jiri da ciwon kai ya tasarmun, halamu Bp na ya hau. A motata muka tafi, shi ke tuƙawa ina zaune a ɓangaren me zaman banza, idona a lumshe. Wani asibitin kuɗi ya kaini suka dubani, gwajin farko suka faɗamun jinina ne ya hau ina buƙatar hutu, da dena yawanta tunani. Magunguna suka bani muka fito. Oga Rashid da kwatance ya kaini har ƙofar gida..
Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi "
"Babu komai. Dan Allah ki sha magungunanki ki kwanta kiyi bacci. Sannan in nazo da daddare kya bani labarin meye musabbabin wannan tashin hawan jinin. Allah yasa ba kalaman dana furta miki na asirin zuchiyata bane ya jefaki cikin wannan yanayin ba. In kuwa shine a shirye nake da in janye kalamina, muddin zaki zauna lafiya. Hakan yafi mun daidai, ki shiga gida " Godiya na kuma yi mishi, muka fito tare. Keyn motar ya miƙo mun, tare da yi mun sallama ya wuce. Ni kuma na buɗe gidana na shiga, ina jiyo surutun su Sani da su Inno. Ina shiga na wuce ciki na sha magani na kwanta. Amman na kasa bacci na kuma kasa dena tunani.
Yanzu shikenan JeGa ya zubar mun da mutumcina a idan iyayenshi, ƙila har a idanun Habiba Bala ma. Dan nayi imani wannan lamarin bazai taɓa yi ma Habiba Bala daɗi ba. Domin ita kanta hakan ka iya sawa ta fuskanci matsaloli a gidan auren nata. Wasu ma tunani zasu yi baki muka haɗa da Habiba Bala dukiyar gidan muke son handamewa. Wadannan abubbuwan su nake tunawa in ji hankalina yayi ƙololuwar tashi. Kiran sallar azahar ne yasa na tashi nayo alwala na gabatar da salla. Ina idarwa na koma gado na kwanta. Ba'a jima da idar da salla a masallaci ba. Na jiyo muryar Sani da Dauda a Falo suna kiran sunana. Izinin shigowa na basu.
"Umma lafiya kika dawo kika kwanta. Umma baki da lafiyane ko Babane? Dariya nayi nace.
Baba kuma, me Babanku zaiyi mun Sani? Aikine babu da yawa a office shi yasa na dawo. Amman da yamma akwai inda zani." Zama yayi a bakin gadon yace.
"Umma inason gobe zan koma makaranta. Baba yace zai yi ƙoƙari in samu tranpa karatuna ya dawo Kano. Kinga shikenan sai mu dinga tafiya shagon ɗinki da Yaya nima in koya. Nifa Umma kuɗi nake so inyi sabida ke kawai. In siya miki motoci, da gidaje, duk azumi ki je kiyi umara, in buɗe miki gidauniya. Kinga umma ai banci ta zama ba. Duk wata wahala umma sai ta rikiɗe ta koma arziki da izinin Allah. Waɗanda suka wulaƙantaki sai sunci arzikin abinda kika haifa." Wannan kalami na Sani ya sani farin ciki da samun kuzari sosai. Gaskiya Sani shi ɗin na dabanne a cikin yarana.
Nagode Sani. Allah yai ma albarka ya baku abinda kuke nema, ya cika muku burukanku da Alkhairi. Nagode sosai. Ina su Sulaiman suke ne?" Dauda yace.
"Suna can suna koyama su Indo karatun boko. Yanzu suka dawo makaranta. Su Amina kuma basu da aiki sai zaulayar Baffa. Muma muna son mu shiga gidan Umma ne mu gaisheta. Ɗazu ma ta kira da safe tana son yin magana dake, to lokacin kin tafi wajen aiki" Duk walwalar da nake ciki sai na nemeta na rasa, gashi ban isa ince kar suje ba zasu tuhumeni. Dole haka sukai mun sallama suka tafi. Misalin ƙarfe biyar da rabi na gama kintsawa tsab na fito. Sai da na kama hanyar Munjibir kana na buɗe wayata. Kamar ko jira yake yi sai ga kiranshi ya shigo wayar. Ɗagawa nayi na kara a kunnena.
"Hello ranki shi daɗe ina cikin Munjibir kamar yadda mu kai alƙawari. Ina fatan baki mance ba ko?" Numfashi naja.
Ina hanya nima"
"To shikenan Allah ya tsare miki hanya ya kawo mun ke lafiya"
Ameen" Na datse wayata na ci gaba da bin santsi har zuwa Munjibir. A wajen da aka tanada dan ajjiye motoci na ajjiye motata na suri jakata na fito. Takawa nake yi a hankali, ina ɗan ware idanuna ko zan hangoshi. Ga ƴan mata da samari wasu a zaune a kujeru farare, wasu a zaune a kafet, wasu ma a tsaye suke,yayin da wasu suke tafiya irina. Yanayin garin babu rana yayi lub, sai iska sassanya da take busowa gwanin ban sha'awa. JEGA na hango cikin shigar manyan maza. Baƙar shadda ce a jikinshi ɗinkin malum_malum, hularshi da takalminshi duk baƙaƙene, agogo da tabarau ɗin idanunshi kuma masu ruwan zaiba ya saka, kalar surrfanin dake jikin kayan nashi kenan. A gaskiya yayi kyau sosai, ƙasumbarshi tasha gyara Masha Allah. Tun daga nesa yake ƙaremun kallo, tare da yi mun murmushi har na iso inda yake a tsaye.
"Kinyi kyau marar musaltuwa. Ke ɗin kyakkyawace, uwa uba gaki da aji, da sanin daraja,, da kimar kai. Kar in cikaki da rashin kunya muje ga kafet na tanadar mana." Bayanshi nabi har zuwa kan kafet ɗin. Waje na samu na zauna muna fuskantar juna.
JEGA bari in baka asalin cikakken tarihin rayuwata tun daga farkon soma sanin kaina izuwa yau da nake gabanka a matsayin Barista. Wannan itace kaɗai hanyar da zai sa ka haƙura da neman aurena kabar zuchiyata ta samu salama. Rayuwata a cike take fal da tarin ƙalubale, da jarabawa wani kan wani. Labarina ya samo asaline daga cikin ƙaramar hukumar shanono dake nan jihar kano.
Cikakken labarin rayuwar shanono da irin jarabawar data samu a gidajen aurenta zai zo muku a ciki book 3 da izinin Allah wanda ni kaina bansan yaushe book 3 ɗin zan soma sakar muku shi ba.
Na ɗan samu matsalar ciwon idanu, kuma an ɗaurani a kan magani, da izinin Allah da zaran komai ya daidaita zaku jini da book 3. Ananne Shanono zata feɗe mana biri har wutsiya.
Shin ya halaƙar Jega da Shanono zata kasance, kuna ganin JEGA zai iya samun zuchiyar shanono kuwa?
Ko dai shanono gidan tsohon mijinta Kaila zata koma ne?
Ga Oga Rashid shima fa yana mutuwar son shanono da zafinshi yazo.
Duk zamu ji yadda zata kaya da izinin Allah.
Ki faɗi ra'ayinki dangane da littafinnan. Kai tsaye wanne irin darasi ke kika koya a cikin littafin? Ina jiran amsarki.
Masu karantawa a batu, kuma ina yinku sosai. Nagode da ƙauna. MRS BUKHARI taku ce a ko da yaushe.
Sai mun haɗu a book 3