Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Love

Chapter   3 / 14

6K to 9K   out of 40.7K words

na kikkira su Yaya Use nake sanar dasu na samu gurbin karatun jami'a, Sabira ina kiranta ta nufo gidana. A lokacin tana karanta islamic studys a jami'ar Jos tana aji na biyu.
"Na ta ya ki murna Tani. Oh rayuwa, yanzu dubeki yanda rayuwarki tayi kyau, yara sun dena amalala, babu ƙwarƙwata, babu kuɗin cizo, babu konika. Ɗakin ki tsab, gidanki sai ƙamshin turaren kajiji yake yi. Ga ilimi, ga sana'a masha Allah, na yi farin cikin maganar karatunnan. Amman Abban Sulaiman ya san zancan?" Tana faɗin haka raina ya ɓaci. Sai kuma jikina yayi mugun yin laushin.
Sabira ba lallai bane Kaila ya hanani tafiya ba. Sabida ai bai damu dani ba, yasan zaman yarana nake yi, kuma naga matanshi duk suna fita aiki, sai nice zai hana zuwa karatu? kuma kinga karatunnan dana kammala, harna gama bai ce mun komai ba, idanu kawai ya zuba mun. Kuma yara bana jinsu, abinda yasa nace Haka. Zan iya sa Shamwila ta dinga kularmun dasu, ina biyanta a wata, duk Sati zan dinga shigowa, kamar juma'a da safe, lahadi in kama hanya. Ina buƙatar karatunne Sabira. So nake in gyara rayuwata da rayuwarsu Inno, bana ƙaunar barar nan da suke yi. Amman zan je anjima in samu Inno mu yi magana in ji me zata ce" Sabira tace.
"Ki soma tuntuɓar Abban Sulaiman da batun tukunna. Amincewarshi ai itace amincewar su Inno. Amman Tani kar ki sake ya tauye miki hakkin ki, wannan damace wacce ba kowa take iya samu ba. Wa yayi tunanin zaki taka irin wannan matsayin a rayuwa? Jibeki fa masha Allah, har wani kashe ido kike yi tsabar fari." Dariya mu ka yi. Ta jima tana bani shawarwari daga ƙarshe ta koma gidanta, dama daga makatanta take. Ina zaune jigum har su Sani su ka shigo. Binsu nayi da idanu, jibi yanda suka girma, Sani da Sulaiman suna sakandare, Shafi'i yana ajin ƙarshe a firamare, Amina da balaraba suna aji biyar, Hauwa na tana firamare 2, Salis na Nosiri 2. Wallahi ban zaci zamu kai ba, daga ni har su ban tamman zamu zama haka ba.
"Umma sannu da gidan. In ji Sani dan duk cikin yaran yafi ƙulaficina sosai. Kuma ya fisu tausayina ko dan shine Babba yasan abubbuwa da dama ne oho.
Yauwa Yaya an dawo, ita kuma waccan cuno bakin me take yi?" Na tambayi Sani. Shafi'i ne yace.
"Abba mu kai ma sannu, yana tsaye da Shamwila shine ya doketa sai da ta faɗi ƙasa" Raina ya sosu sosai. Kaila ya tsiro da sarar ko tsakar gida yarana suka fita muddin yana gari, to kwa jishi yana hantararsu yana koromun su. Na rasa gane wai tsanatace yasa yaran da suka fito daga tsatsonshi baya son ganin sun raɓeshi? Sai yaran Hajiyayye wanda a yanzu yaranta uku, da Yaron Bilkisa, ita bata kuma haihuwa ba tun daga Fatima. Family planning ma take yi, a babban falo suka sha rikici lokacin da ya gano tana shan ƙwayoyin hana haihuwa. Buɗar bakinta tace.
"Ni bazan sake jiki inta haihuwar maka yara, daga baya ka barni da wahalarsu ba, ka samu a kwandon shara kamar yadda kasa umman Sulaiman ba" Maganar tayi mun zugi sosai a ruhi, ta soso mun wani gyambo da yafi shekara goma a ƙirjina, abinda Bilkisa ta faɗa gaskiya ne, ta farkar dani daga wani bacci, amman farkawar babu amfanin da zata yi mun, abinda ya faru ya riga da ya faru, sai dai kiyaye gaba. Bilkisa ba ƙaramin zubar ma da Kaila gwandon rashin mutunci take yi ba. Sawa take yi kanshi yayi jaji har ya batse. Kuma daga gidansu ma a kirashi anason jin ba'asin abinda yayi mata, ta kai ƙara wajan iyayenta ( yana daga cikin illolin talaka ya auri ƴar masu kuɗi, ko ya auri matar da take ganin ta wuce ajinshi, musamman in iyayenta sun san dan dukiyarsu ya auri ɗiyarsu).
Zo Hauwa na, tawo" Tana zuwa ta saki kuka har tana shessheƙa kamar zata shiɗe mun. Raina ya sake ɓaci. Hannayena na ɗaura a bayanta na shiga rarrashinta. Ƴan uwan nata kuma suka shige ciki sake kayan makaranta. Da unifom ɗin da suka cire Sani ya fito a bokiti, da ɗan omonshi. Ya dubi Hauwa yace.
"Hauwa zo ki cire kayanki, ki hado mun dana Salis in wanke mana tunda yau babu islamiyya. Da wata iriyar siga mai raunata zuchiya yayi maganar, gabana ya yanke ya faɗi, sai kawai nake tunanin ko dai mutuwa zanyi ne. Take zazzaɓi ya rufe ni sosai" Salis shima ya faɗo jikina sabida kishin yaga Hauwa a cinya. Duk na haɗe na rungumesu wani abu na mun motsi a zuchiyata......

Shanono tana gaisheku. Ku faɗi ra'ayinku, in Kaila ya hana Shanono tafiya jami'a wanne matakin a ganinku ya dace ta ɗauka?NA FADO DAGA BENE......
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU

LAMBA TA 3


Sun jima a jikina kafin na sake yin ajjiyar zuchiya na ciresu a jikina
Amina zo ki cire ma Auta kayanshi, ki kaima Yaya. Hauwa kema ki cire naki sai ku yi tsifa. Zaku je gidan Yabi ta wanke muku kai, tai muku sitirecin. Gobe kuma sai ku je ayi muku kitso. Ni gobe Bauchi zanje, zamu je ganin Yayanku Dauda a makaranta. Balaraba tayi carab tace.
"Umma dan Allah zamu je, kinji ummanmu, munason muje muma mu ganshi." Take zuchiyata tayi na'am da in tafi da matan, mazan sa zauna a gida. Sani babu abinda bai iya dafawaba, har tuwo ina bar mishi yayi mana, in ina makaranta, ko kuma ina farar gada sarin kayan miya.
To shikenan, ku yi sauri ku tsefe kan naku, kuje a wanke muku. Ayi muku kitson in muka dawo daga Bauchin." Nan ɗaki ya kacame da murna. Amina ta cire ma Auta da Hauwa kaya. Shafi'i ya tafi kaiwa, Sulaiman ya zaunar da Hauwa ya soma tsefe mata kanta, Amina da Balaraba kowacce tana tsefe nata.
"Umma sai yaushe Baba zai sai miki mota, kece kaɗai ba ki da mota a gidannan?" Murmushi nayi mishi nace.
In Allah ya hore maka sai ka sai mun ai Sulaiman ko? Su Inno kuma ka sai musu gidan da zasu zauna su dena yawon bara, da yawan bin gidan haya"
"Umma ke ma zan sai miki ƙaton gida da ƙatuwar mota, direba ne ma zai dinga kai ki anguwa" Amina tace.
"Uhm wa yaga Umma a bayan mota a hakince" Dariya mu ka yi dukkanmu, sai zuchiyata tayi wasai ina cikin yara muna nishaɗi. Sani na gama wankin sai ya zubo mana abinci a tire shinkafa da wake da latas na yi mana. Tare muka zauna mu ka ci abincin. Sai mu kai sallar azahar. Amina ta kama ƙannenta zuwa gidan wanke kai. Sani kuma ya kama ƙannenshi maza zuwa shagon aski. Ni kuma a maimakon in tashi in yi kaye_kaye. Sai na yi linkib a saman kujera na nutsa cikin tunani da fargabar abinda kaje kazo dangane da makomar karatuna, Allah ya sani inason karatu ko dan nima in sake samun canjin rayuwa. Gashi wannan zamanin da muke ciki maza sun fi son wayayyun mata masu ilimin arabi da boko, ƴan ƙwalisa. Kuma nima Bilkisa da su Habiba Bala sun sake kwaɗaitamun sha'awar aiki. Ina son in yi karatu mai zurfi in samu aiki mai kyau. Domin in tallafi ƴan uwana da iyayena. Ina fatan in zama haske kuma fitila a cikin dangina. Ada sunana yayi fice ta fannin ƙin zaman aure. A yanzu inason in zama jajirtacciyar ƴar gwagwarmayar ƙwato ma mata da zawarawa hakkinsu. Dan a Arewa ne zaka ga bazawara a cikin gidan ubanta Almarijin gidansu me ɗebo musu ruwa yana da kwanon abinci amman ita bata dashi. Akwai ƙarancin wayewar ilimin addini tattare da iyayenmu maza da mata. Domin a da iyayenmu ba su yi karatuba sai ɗaiɗaiku, hakan yasa suka fi fifita al'ada fiye da addini, face ɗaiɗaiku daga cikinsu. Inason in zama mudibi abun dubawar zawara da matan gida, wanda wahala da takaici ɗa namiji suka linkime rayukansu. Mata har yanzu a baya muke, duniya tana ta samun ci gaba, amman mazajenmu sun ki su tallafemu ko da da ilimine. Ya Allah kaga abinda na saka a gaba. Da abubbuwan da sukaita kawo min cikas cikin rayuwata, kama daga ranar da aka haifeni a ƙasan gada har izuwa yau da nake a matsayin uwar takwas. Allah kayi mun zaɓi abunda yake mafi alkairi "
Washe gari da wuri muka shirya, yaran fes dasu gwanin sha'awa, ko wacce saye da hijabinta har ƙasa, dan yanzu Shanono malamace, nasan abu mai kyau da mara kyau. Nasan mahimmancin lulluɓe jiki, mace ta suturce kanta umarnin Allah ne, ba umarnin wanin Allah ba. Shi yasa nake son yin ƙoƙari in ɗaura yarana bisa tsanin ƙarfe wanda nake da yaƙinin sari bazai cishi ba. Kuma na tsaya tsaiwar daka akan karatunsu, musamman ɓangaren muhammadiyya. Ibini Abbas suke zuwa islamiyya Makarantar Amayar sheik khalid Aliyu Babansu Umaima da Abdulwahit, sirikin gidan Garba na Garba. Kuma tana daga cikin makarantun islamiyya manya a garin jos. makarantar tana kan titin SALISU ADAMU, KUSA DA NEW MARKET ƳAN TIFA. Har zamu fita daga ɗakin Sani yace.
"Umma ba dan masu zuwa sayen kaya ba da nace kije damu. Kuma banason fa ciniki ya wuce ki ummanmu" Turus nayi a dokin ƙofar na kalli yaron.
Ku tawo mu tafin kawai tunda dai a shirye kuke, dan dai yau ɗaya ai babu komai mu yi haƙuri da cinikin. Shima wan naku duk santa mu ka je mishi bistin sai ya ce me yasa ba'azo daku ba." Ɗakina na kulle ruf, na nufi ɓarayin Bilkisa, su kuma nace su fice zan biyo bayansu. Sallama nayi ma Bilkisa akan zanje Bauchi dubo wan su Sani. Ai kuwa a cikin irin biskit da cakulet da Kaila ke siya ma ƴar lelen ƴarta ta ciro katan na biskit ta zura a ƙatuwar farar laida, ta ciko hannu da cakulet ta watsa, ta kuma cikowa ta watsa.
"Gashi ki kai mishi kice in ji mamanshi. Ba za'a bar mun dadi a gida ba Umman Sulaiman?" Dariya nayi nace.
Angode sosai. Babanki sarkin rigima ba, yana hannun Sani nace su yi gaba." Sallama nayi mata na fito. Bayan yaran na dinga bi ina kallonsu, yanzu cikin ƙudurar ubangiji wadannan yaran duk ni nayi naƙudarsu nai silar wanzuwarsu? Wannan ma kaɗai arzikine, dan suturar da aure tai mun kenan, banda yara dana samu da sai in ce babu abinda na tsinta a zaman aure. Sani yana reƙe da bakko babba wanda na shaƙe ma Dauda da kayan makaranta. Irin su biskit, siga, madara, confilakes na awo, da garin rogo da dakakken ƙuli, sai man ƙuli dana cika mishi goro, da maggi dunƙule. Haka nake yi mishi gwargwadon ƙarfina ba dan Habiba Bala ta gaza ba, dan ta ɗaukema Dauda dukkannin raɗaɗi, yaron ma ya fi saninta fiye dani, dan ni babu sabo tsakaninmu, ni inai mishi kunyar ɗan fari, shi yana mun kunya irin ta gadon fulani. Motar kuɗin baya na biya dukka, sit ɗin mutum uku, sai mutum ɗaya a gaba Yaya Use ce, a tasha muka haɗu da'ita, a taƙaice mu kaɗai ne a motar. Muka zauna a sake babu laifi, yara sai hayaniya suke yi, murnace fal ransu. Haka mu ka ci hanya, cikin awa guda da rabi sai gamu cikin falon Habiba Bala. Murnarta a wannan rana bata misaltuba. Tayi mana liyafar ban girma. Kafin muka nufi F J C Bauchi. Yau ranace da iyaye ke kaima yaransu ziyara. Da iyaye da yaran a wannan ranar sukan shiga cikin farin ciki marar misaltuwa. Duk yaron da iyayenshi basu samu zarafin zuwa ba kuwa, haƙiƙa wannan yaro an ɓata mishi ranar, bazai kasance da walwalaba. Akan yi girke_girken abinci masu kyau, a tawo da taburma ko dadduma a zauna. Kuga ɗanku, ɗanku ya ganku, ku bashi provision ɗinshi, in yamma tayi kuma ku tafi.
Muma hakane ta kasance, mun samu damar shiga cikin makarantar, sai dai fa babu masaka tsinke, sai yaro yayi da gaske zai iya gano ahalinshi. Amman abun mamaki sai ji nayi an riƙe mun hannuna. A zabure na juyo mu kai ido huɗu da yarona Dauda. Farin cikin maƙil a zuchiyata, bakin na washe mishi. Shima bakin ya washe mini.
"Innata sannunku da zuwa. Mummy ina wuni?" Yace da Habiba Bala. Hannu ta miƙa mishi, sai ya sakeni ya kama hannun nata. Allah sarki Habiba Bala a gaskiya Habiba Bala mutum ce guda gar da ɓari. Waje muka samu muka shinfiɗa ƙatuwar dadduma, muka baje plate da kulilin abincinmu, daga gefe kuma ga siyayyar da mu ka tawo mishi dashi. Abokanshi sai zuwa gaishe da Iyayen Dauda Naroro Shanono suke yi. Da sunan Baffana yake amfani kamar yadda nima sunana yake Tani Naroro Shanono. Masu karatu ina fatan baku mance ba Narani yace in Dauda ya haɗa sunanshi da nashi bai yafe ba? In kun man ce Shanono bata mance ba. Ada Da sunana yake Amfani Dauda Tani Naroro Shanono. To malamansu ne suka cire mai Tanin, dan a lokacin da aka cire sunana a cikin sunanshi, sai da yayi ciwon da dole makaranta ta dawo dashi gida, aka kula da lafiyarshi. Sai da nai ta rarrashinshi kana ya kwantar da hankalinshi, tare da mun alƙawarin komai daren daɗewa sai ya amsa wannan sunan. A ɗan zamana da fahimtar da nayi ma Dauda, yarone haziƙi mai nacin tsiya akan abinda yasa a gaba. Hakanne yasa ya zama tamkar zakara a makaranta, yana ƙoƙari sosai. Kuma yana da ƙulafacina, ko ince yana da kishina ainun, shi da Sani abun nasu tamkar gasa haka yake tafiya, ko dan su manya ne oho. Yaya Use tace.
"Dauda anata girma, har ka kamo uwar taka a tsayi" Dariya yayi ya sosa kanshi kawai. Habiba Bala tace
"Shanono yaronnan murmushinku iri ɗaya wallahi. Kinga can wajan Shanono zaki iya tuno ranar da muka daku a wajan lokacin muna makaranta? Lokacin kina kan karagar ƙwarƙwata." Dariya mu kai ta yi, harda ƙyaƙyatawa na dubi Habiba Bala nace.
Allah ya isa Habiba Bala. Sai kace wani sarauta wai karaga" Itama tana Dariya tace.
"To ai dukan akan mun shafa ma Siniya Zainab Abola ƙwarƙwatane fa. Kin tuna tana bacci muka je har ɗakinsu muka saka mata akai. Khadija Bakari kuma ta tona mana asiri. Shi kuma Malam Tanu kuɗin cizo muka tara guda shida, Halima Bawa ta je ta bayanshi kamar zata wuce ta saka mishi a rigarshi. Kai rayuwa kenan, Allah kar yayi abinda ba zai wuce ba" Abinci yaya Use ta zuba ma kowa, anaci ana nishaɗi.
Dauda na samu gurbin karatu a jami'ar Bayero unibasiti. Ka taya ni da adda'a zanje in karanta fannin shari'a, ya soma burgenine sanadiyyar shari'ar da muka gabza da Hajiyayye " Dauda yace.
"Ina miki fatan Alkhairi Innata. Allah yasa ki zama barister me ƙwato ma talakawa hakkinsu. Ki share hawayen marasa gata irinmu." Ɗib wajan yayi, na kasa cewa ameen, sha'anin Dauda na tsoratar dani. Shi ba yawan shekaru ba, shi ba wayewa ba sai hikima da tsarin zance kamar Kaila ne ya haifeshi. Habiba Bala ce ta kawar da zancan ta hanyar cewa.
"Ni kuwa Hajiyayye tana nan abunta iya rigima kenan, yanzu dai an mayar da kai wajan tarbiyan yara.
Ai fa, rigimarta ta koma kan Bilkisa gasa sosai take yi da'ita. Suna nan suna fama." Yaya Use tace.
"Kaila ya game ginin da kika ce yanayi kuwa a gidan?" Nace.
"Ya gama, wannan gini yaci kuɗi sosai yafi ko wanne ɓarayi cin kuɗi. Da halama amarya zaiyi ya sakata a ciki. Muna nan daku zaku ji" Mun jima muna fira, yaran ma Dauda ya kwashesu sun ɗan zaga.
"Shanono. Ni shawarar da zan baki itace kar ki bari Kaila ya tauyeki ta hanyar dakushe miki burinki. Kinsan irin zaman da kike yi a gidan Kaila, yanzu duk matanshi mota suke murzawa banda ke. Hajiyayye ya buɗe mata shago tana caskar kuɗinta. Bilkisa dama da aikinta ya kwasota. Kar ki sake ki biye mishi, kije ki yi karatunki ki game fes, ki samu aiki kema ki shiga daga cikin sahun mata masu daukar albashi. Kinga sai dai ki haɗa kai da Bilkisa ba dai Hajiyayye ba. Kune zaku fi ajin Kaila. Wannan kallon da yake miki na ƙazama mabaraciya, marar galihu duk sai kiga ya kau. Ke Kaila da kanshi zai kawo kanshi gareki a lokacin da zai ganki hasken ilimi na haskawa a rayuwarki kin zama lauya. Karatun lauya ai karatune na manya. Domin lauyoyi karatu baya isarku, kullum a cikin bincike kuke da sanin dabarun makamar aikinku. Na kuma ji daɗi da kika amshi tayina. Zan biya miki komai da komai, tun daga kan rijistiretion, har zuwa kama miki ɗaki, da ɗan abincinki da sauransu. Akwai ƙawata a bayaron take, ƙila ku zauna ɗaki ɗaya, in dai ita kaɗaice a ɗakin sai ku zauna tare." Maganganun Habiba Bala sai suka sake zaburar dani har nake ganin babu gudu babu ja da baya akan maganar karatuna. Sai da la'asar tayi muka kama hanyar gida. Kai tsaye ma tasha Habiba Bala ta kaimu. Ita ta biya kuɗin motar, banda alkhairi da tayi ma Yaya Use da yaran. Ita dai bata gajiya da tallafata, Allah sarki masoyiya Habiba.
Gaga_gaga sautin garawar rayuwa, rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya. Na gama hidimar rijistiretion, Habiba Bala ta nema mun ɗakin ƙawarta dake wajan makaranta, zamu zauna tare, bazawarace itama mai aure uku. Inata shirin makaranta, nice harda dinke _ɗinke, shopping da duk abinda zan buƙata a makaranta na tanadarma kaina. Ana jibi zan tafi na je gida domin yin sallama da su Inno. Duk wannan budurin fa Kaila baisan me nake ciki ba, jiya da daddare ya diro garin, ya dai kirawo Sani ya bashi manja ya kawo mana, iyakacin kyautar kenan itanma Bilkisa ce ta dameshi da ƙorafi. Yara na tafiya makatanta na nufi gida, Baffa kam bai kwana a gidan ba, shi da Habu. Innon ma a bakin ƙofa muka haɗu.
"Ince dai lafiya ko? Dan duk randa na ganki a sanyaye sai gabana ya faɗi. Menene ba dai auren bane ya ƙare ko Tani? Ki rufa mana asiri ki yi zaman aure Tani. Jibi yanda kika canja, da ganinki kina

3 / 14