Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Love

Chapter   8 / 14

21K to 24K   out of 40.7K words

Kayan masarufi muka siyo ma su Inno da duk abinda nasan zasu buƙata, hatta tukwane sababbi na sai musu dal. Bamu muka shigo ba sai bayan la'asar, a tsakar gida muka samu su Baffa da yaran. Amina na bashi magungunanshi, Sulaiman na rike da kofin kunun Baffa, dan da kunu yake iya haɗiyar maganin. Bayan mun yi sallah kuma muka shiga jera musu abinci da kayan aiki a kitchen, dan naga su Amina sun gyare gidan tas, ko ina fes.
"Tani amman zamu koma Jos ɗebo kayanmu ko? Dan inada ajjiyar kuɗaɗe a cikin tsummokarai" Cewar Inno kenan, Yaya Karime tace.
"Ni da Yaya Use zamu tattare muku duk abinda ya dace Inno, Yaya Use zata zo ta kawo muku kayanku, kuɗaɗenku ba za su yi ciwon kai ba" Da yamma na ɗebi yarana muka je gidana dan mu keɓe in basu lokaci sosai. Na shiga kitchen nayi musu girki mai daɗi, na shige tsakiyarsu muka ci tare muna suturu gwanin daɗi. Bayan sallar Isha muna zaune a falo ni da su Dauda yana bani labarin damuwar da suka shiga bayan rashina, da yanda ya kammala karatunshi, da garin da yaje bautar ƙasa, sai ga Amina da wata ƴar ƙaramar jakar kwali fara sol ta miƙo mun.
"Umma ga saƙon da Baba yace a Baki, da muka je mishi sallama" Sani ya fisge jakar a hannun Amina yana mata muzurai, harda mikewa kamar zai daketa wai dan me yasa ta karɓo daya bata. Sai da Dauda yace ya zauna kana ya zauna. Ita kuwa duk ta firgita da Sani. Turarene a cikin jakar, da wata wasiƙa. Kekketa wasiƙar yayi, turaren ya sa a aljihun jallabiyarshi.
"Sabida me kayi haka Sani, ba Baba bane ya aikota ba, daka sani ka ba Innata ta karanta ai" Ni kuma abinda Sani yayi shine daidai, dan koni dana karɓa kakketa takaddar zanyi shi kuma turaren in raɗashi da ƙasa. Meye zai fito daga hannun Kaila in ji ina sha'awar karɓa, babu shi."
"Ni banaso ta karantane Yaya Dauda kar umma taxo taji tanason komawa ɗakinta. Ni kuma wallahi in dai ina numfashi ko mutuwa Baba zaiyi sai dai ya mutu akan ya sake mallakar Ummanmu. Nifa ina zaune dashine kawai dan bani da yanda zanyi, a yanzu banga wanda zai rabani da uwata ba. Me yasa dan ubanta da suka je mishi sallama ma ta sanar dashi inda zamu tawo?" Kawai sai ya fashe da kuka harda haɗiɗiyar zuchiya, ɗakina ya shige da gudu. Ƴan uwanshi suka bishi da idanu jikinsu a mace. Maganganun sani sun fama mun mikin dake ƙarƙashin zuchiyata. Hawayena na share na yi murmushi nace.
Babu komai ai. Bayaso in koma hannun Babansu ne. Je ka rarrashi ɗan uwanka Dauda ka faɗa mishi babu abunda zai mayar dani hannun mahaifinsu" Da sauri Dauda ya bi bayan ɗan uwanshi, Amina jiki. Mace tace.
"Umma dan Allah kiyi haƙuri bansan karɓo saƙon zai sa Yaya kuka ba. Umma muma bama so ki koma Allah, ko da ya bani saƙon yace in kawo miki ni na karɓane dan kar ya hana mu zuwa muganki.
Murmishin ƙarfin hali nayi mata kawai nace.
Baki da laifin komai. Ai ubanku ne, kuma aikoki yayi. Nan gaba dai in ya baki saƙo ki kawo mun, karma ki nuna mun. Koma meye saƙon kuyi amfani dashi, in takaddace ki yayyageta ki watsar, kinjini ko? Ku zo mu je mu kwanta ku mata. Ku kuma Sulaiman a falo zaku kwanta, Sani zai fito muku da fululluka." Ina yinƙurin tashi sai ga Dauda da Sani sun fito suna dariya kamar ba Sani bane yanzu yake kukan fitar rai. Murmushi nayi musu haƙiƙa haɗin kansu ya burgeni, gabaki ɗaya sun zamema kawunansu abokan juna, kuma na lura suna matuƙar girmama Dauda a matsayinshi na babban wa uba garemu baki ɗaya. Bamu muka kwanta ba sai wajajen ƙarfe biyun dare, ni da tani za'abi kwanan zaune ma zamu yi wallahi. Matan na kwashe muka shige ciki. Mazan kuma Rahama tace su kwanta a nata ɗakin, zata kwanta ita a falon tunda baƙine su. Su Amina nabi da idanu sunata sheƙar baccinsu, ko wacce da ɗan nono a ƙirjinta. Kamar jiya nake ganinsu a kwance a bayana a katifa, suna bacci cikin fitsari, mu wayi gari katifarmu na yararin fitsari. Dariyace ta kwace mun kawai, dana tuno irin ƙazantar dana dama. Babu abunda yafi bani wahala kamar sanda na kwana goma a firzin babu wanka, ga jinin biki daya mammane mun, na sha ɗan karen azaba. Dan sai da ruwan zafi bawo guda ya ƙare kafin wajen ya sake, amman saida ya kumbura ya zamemun ciwo gagarumi. Nifa bacci ɓarawone ya kwasheni harga Allah. Sai naji na kwaɗaitu da zama da yarana, zanso hakan ta kasance. Amman bari in yi ƙoƙarin siyan mana gida tukunna, sai in tattaro kan yarana mu yi zamanmu, domin sune sanyin rayuwata, dan banji daɗin yanda Salis da Hauwa suka mance dani ba, duk da daga baya sun sake, kamar suna son tunoni.
Washe gari duk kuɗaɗen dana tara sai da na kashema iyalaina kab a ShopRite, kama daga kan suturu, takalma, kwalam da makulashe iri_iri. Daga ƙarshe muka ya da zango a gidansu Inno. Mun samu Yaya Use tana tuƙa musu tuwon semovita, harta kammala miyar ma. Sai da mu ka ci tuwon dare muka ɗau azamar tafiya. Yaya Use da Yaya Karime na sallamesu da kuɗin mota, jibi zasu koma
Na ba Baffa da Inno ɗan na kashewa. Yara su kai musu sallama dan gobe zasu kama hanyar Kaduna. Bayan na idar da sallah, ina ninke daddamu Sani da Dauda suna falo, su Sulaiman kuma muna tare a ɗaki. Sai ga Amina da gudu da waya a kunnenta.
"Umma, Babane yake son zaku gaisa dan Allah" Ita da wayar nabi da kallo. Bansan sanda na ɗauketa ta mari ba tsabar takaici. Na wuce na barta tana kuka, ɗakin Rahama na shige na kulle kaina dan baƙin ciki sai na sau kuka. Yaran hankalinsu ya tashi matuka barin ma Amina wacce take ta magiya a bakin ƙofar. Yayyenta sai hantararta suke yi. Da ƙyar na yarda Rahama ta buɗe ƙofar ɗakin duk suka shigo. Da kyau na dubeta, sai naji ta ban tausayi, amman hakan baisa na saki fuskaba.
Daga yau kar wanda ya sake kiran sunan ubanshi a gabana, ni bazan rabaku da ubanku ba. Amman ban yarda wani ko wata ya sake dangantani dashi ba. Nan gaba kaɗan sai dai ya kira yaji muryarku, dan kwasheku zanyi nima a hannunshi, in gani ko zai hanani yin hakan ne, in buga shari'a dashi" Kowa sai ya shiga taitayinshi, dan ina maganar ne muryata na tsitssinkewa.
Allah yayi dare gari ya waye. Yau yara suka shirya tsab suka kama hanyar garinsu, tare da mun alƙawarin da zaran anyi hutu duk zasu tawo muyi hutu tare. Sani kuwa shi da Dauda cemun su ka yi sunga hanya ai. A tsaye suka tafi suka barni cike da kewarsu mai tarin yawa. A gidan su Inno na wuni sai dare muka tawo tare da su Yaya karime, Ige ta kwaso kayanta ita da su Indo da Habu sun dawo gida. Washe Gari su Yaya Use suka kama hanyar Jos ni kuma na koma bakin aikina. Kullum muna waya da duk yarana, mukan daɗe akan waya suna mun labari ni kuma ina jin daɗi. Dana taso aiki gidansu inno nake zarcewa, sai ɗaiɗaikun ranaku da nake wucewa gida, musamman in inason inyi nazari. Gaga_gaga dai haka rayuwar tai ta shurawa, su Baffa basu da aiki sai batun aure, ni kuwa duk wani wanda zai nuna mun so jaye jikina nake yi. Waɗanda suka tunkareni kuwa da batun kai tsaye nake basu haƙuri. Ni a ganina soyayya bata dace dani ba, yanzu burina abu biyune. Buɗe gidauniya domin taimakon nakasassu da koya musu sana'a. Na biyu kuma dawo da yarana hannuna. Duk da anayin hutu Sani ya tarkato kansu yazo ya dure mun su ya koma. Yana gama jarabawa ya biyosu shima. Dauda kuwa duk juma'a a Kano take yi mishi, nayi faɗan harma na gaji. Habiba Bala tace in rabu dashi. Bayan shekara guda

Alhamdulillah na samu wani gida kusa da maƙotan su Inno, katangarsu ma ɗaya. Me gidanne ya rasu shine yaranshi suka sa gidan a kasuwa. Kamar wasa Baffa yace in sayi gidan in ina da hali yaji Inno tana yabon kyawun gidan. Abu in ya tsaga rabonka ne sai ka sameshi. Ranar Dauda yazo daga Bauchi ya kawo mun ankon bikin Mamanshi Habiba Bala, sai yanzu Allah ya nufa zata sake yin wani auren. Komai lokacine. To tare dashi da Ige muka zaga ganin gidan da yamma. Akaima gida kuɗi million biyu, ni kuma a lokacin kuɗin dake asusuna bai shige million ɗaya ba. Dauda yace.
"Inna in kina son gidan, sai in cika miki, ina da million ɗaya da rabi dana jima ina tarawa, dama gida naso in gina miki dashi." Allah mai iko, cikin kwana biyu muka tattaro kan kuɗi da shedu muka biya, aka sauya takaddu da sunana, akayi komai gida ya zama mallakina. Ragowar kuɗaɗen daya rage a hannuna kuma dasu na soma gyaran gidan a hankali. Cikin ƙudurar ubangiji a cikin sati biyu naci larfin gyaran gidan sosai ƙarewar kuɗine ya dakatar dani da gyaran. Bikin Habiba Bala yanata matsowa, yau sauran sati biyu. Duk wani shirye_shirye tare muke gabatarwa a waya komai da komai dai. Ana biki saura kwana Hudu Dauda ya tuƙa motata muka wuce Bauchi. Sani kuma munyi dashi zai tawo da su Amina daga Kaduna, Yaya Use su kuma sai ranar ɗaurin auren zasu tawo itada yaya Karime.Biki Habiba Bala ta shirya sosai na manyan mata. Ƴan uwanta da danginta cike da gidanta danƙam, anata harkar girma. Masu suyan naman sa nayi, masu suyan kaji nayi. Uwar ɗakinta na ƙule da akwatina. Anan na tarar da Sabira da likitoci ƙawayenta, ko wacce ka ganta babbace sosai. Sai kallon kayan akwati suke yi suna yabawa da kayan da aka danƙara mata babban abin da yafi mun daɗi shine Habiba Bala a Kano zata zauna, dan angon namu bakanone, zumuncinmu ya ƙara matsowa kusa.....✍🏻
[17/10, 1:23 p.m.] +234 803 831 1474: NA FAƊO DAGA BENE......
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU

LAMBA TA 8



KAILA:
Ta ɓangaren Kaila kuma. Bayan fitar shanono daga rayuwarshi sai Allah ya jarabceshi da ƙaunar buɗe idanu ya ga yaranta suna yawatawa yana kallonsu. Ya katange duk ƙofar da za'a ci zalin yaranshi. Tunda mai aikinsu ita yake ba ma kuɗin hidima dasu. Duk da Shamwila tana hana abubbuwa da yawa, amman ta kasa hana Kaila dena jawo yaran shanono a jiki. Musamman Salis da Hauwa tunda sune ƙanana, Kaila na matuƙar ji dasu. Sani kuwa baya ko son ganin mahaifinsu, shi kanshi kailan ya sani sarai. Da Sani ya soma girma ko sallama yayi sai gabanshi ya faɗi, tsoron yaron yake ji ko kunyarshi ya rasa ɗaya daga ciki, amman yana jin shakkar haɗe girar yaron. Shamwila ta takura musu ainun. Hajiyayye sai dai ido, dan Tani ta fita daraja da kima a idanun Kaila. Kullum a cikin yi mata gorin yawan tarin yara yake. Sai dai ta shige ɗaki tayi kukanta. Ko komawarsu Kaduna a ranar da zasu tafi Kaila yake sanar mata ta shirya zasu koma can gabaki ɗaya da zama. Ƴan uwanta ma sai daga baya suka zo suka dubata. Ita a BQ ma yace ta zauna da ƙazaman yaranta. Shamwila da su Amina a asalin cikin gida suke su kuma, duk da shanono bata gidan, fasali ɗaya ya ba yaranta suke ciki dana Shamwila, duk da Shamwila tayi ma Kaila tas akan hakan haƙuri kawai ya bata, sai ɗakin su Sani a tsakar gidan. Hatta makatantar da Kaila yasa su Amina ba irinta su Sameera suke zuwa ba. Hajiyayye dai ta yi na'am ta karɓi ƙaddararta dan tasan ta zalunci Tani a zaman da su ka yi a baya ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya. Da ba dan yaranta ba da tsallakewa zata yi ta bar gidan. Duk da in taje gidan ma ba daɗi bane. Dan yanzu shagon gwanjon ma mahaifinsu bashi dashi, sai tarin tulin yara cunkushe a gida ga mata huɗu reras. Iyayenta mata ma ko wacce yaranta ke ciyar da'ita. Waɗanda yaranta basu kawo ƙarfi ba kuma sai ta nemi abun yi. Kwatsam wata rana Hajiyayye na tsakar gida ta ji yiriri_yiriri an shige ma da Kaila Amarya, dariya tayi haɗi da shewa, tace.
"Ai ko bunsuru ya shafa ma Kaila, sai dai su yi kunnen doki da Ayu."
Daga zuwan amarya komai ya ɗauki saiti, dan ta saisaita ma kowa kai a gidan. Shamwila itama tana ji tana gani ta zama ƴar kallo. Amarya ta kafe gwamnatinta, shine har Hajiyayye ta samu iskar ƴanci ta ɗan soma shaƙa, ita da yaranta. Bilkisa fa tana Zaria mahaifinta ya siya mata gida, taci gaba da aikin asibiti a asibitin Shika. Duk randa Kaila yazo ya dubata ita da yaranta biyu miji. Duk randa ya tsallake ƙafa ya koma aboki, a haka Bilkisa ta ajjiye Kaila. Dan ba zaman soyayya take yi dashi ba, tuni ya gama fice mata a rai. Kullum a cikin yaɓa mishi gori take. Tunda ya auri Shamwila basu sake haɗuwa da Bilkisa ba, amarya ma daya auro Bilkisa bata santa ba. Harkokinta da kula da yaranta kawai ta saka a gaba, ta sake Haihuwar namiji.
KAILA kuma a kullum da shanono yake kwana yake tashi, gurbinta yana nan a zuchiyarshi baya jin akwai macen da zata iya cike gurbin Shanono a zuchiyarshi, sanadiyyar tunanin Shanono har hawan jini sai da ya kama kaila. Duk wannan daular da yake ciki baya jin daɗinta sam, domin wacce ta zama silar arzikin ta fice a rayuwarshi. In ya tuno da butulcin da yayi mata, sai ya sake kyautatama yaranta. Ya saima Sani mota in yana gari shike kai ƙannenshi makaranta, sai dai in baya nan direba ya kaisu, tunda shi Kaila ba zama yake da'iman a Kaduna ba. Burin Kaila yayi tozali da shanono ya roƙi gafararta ko Allah zai sa ta yafe mishi ta kuma koma kan yaranta. Dan ji yake shanono kamar mahaɗin rayuwarshi ce. Yayi ma kanshi alƙawari zai yi amfani da iya kalaminshi, da yaudara, ya sake siyan zuchiyar shanono a karo na biyu. Ya yarda itace rayuwarshi, zai karɓeta ko da kashi take wanka kullum.



SHANONO:
Kafin in dawo daga aiki, Sabira da Abban Mustapha har sun kama hanyar Jos. Yaya Use da Sani kawai na tarar a gidan suna kallon tashar Arewa 24. Sani na jin sallamata ya taso ya karɓi ledar dake hannuna da jakata.
Wash Allah sannunku da gida Yaya Use, kuna zaune shiru sai dai kallo. Yaya Use tace.
"Ke dai bari kunne gashi ya saba da haya hayar yara, danma yanzu kowa ya girma ya kama gabanshi." Sani ya zauna a kusa dani yace.
"Umma yau ni nayi mana girki a gidannan. Ni fa umma nan gidan zan dawo da zaran munyi hutun makaranta. Ni gaskiya bazan koma gidan Baba ba. Baba ya auro wata ƙaramar yarinya sai rashin kunya."
Kul Sani" nayi saurin kwaɓa mishi.
Kar ka zagi matar Babanku ban baku wannan tarbiyyar ba. Bazan hanaka in anyi hutu kana son zuwa wajena ka kwana biyu ba. Amman ba zaka bar gidanku ba duka, kaine fa uba a gidan, su Amina in baka nan suyi yaya kuma?" Yaya Use tace.
"Gaskiya ne, kai suke kallo makwafin uwarku. Tunda a yanzu da kai suka fi shaƙuwa. Hauwa da Salis ma ba zasu gane Tani ba sai dai nan gaba. Tashi ka zubo mana abincin muci ni yunwa nake ji." Taliya Sani ya dafa mana mai romo irin wacce nake yi musu in baje mana a faranti muyi ta ci. Sai dai ita wannan banbancinsu shine taji haɗi ga kifi zuƙu zuƙu. Gaskiya Sani ya iya girki sosai, ni harma ya fini iya girki tunda mu ba iya girki mu ka yi ba. Inaci ina santi har na ƙoshi. Sai murmushi yake yi dan ya sake sani farin ciki. Bayan sallar magriba na samu zama da Sani mukaita tattauna zantuka yana bani labarin bayan rabuwa, da irin gashin da mahaifinsu yake amsa a hannun mace. Ai dama ni nasan jarabawar Kaila ta mata ce, duk wuyar da suke bashi bai dena ruwan idanu ba, gashi har yaranshi sun girma sun san a wanne irin layi mahaifinsu yake.
"Umma tunda kika fita a cikin rayuwar Baba duk ya lalace, baki ganshi ba ya rame sosai. Wataran in ya sa su Balaraba a gaba kamar zai haɗiyesu, harfa ƙwalla yake fitarwa." Murmushi nayi kawai nace.
Adda'ata ta karɓu, dama burina mahaifinku yasan mahimmancinku, da darajarku. Da yau na tawo daku ba lallai bane Babanku ya sake neman mu a rayuwa ba. Duk abinda ke faruwa a gidanku na sani Sani. Kuma nasan irin son da mahaifinku ya ɗaura a ranshi bayan tafiyata. Yanzu dai tunda kai ka biyo ni zanje in ga ƙannen naka."
"A'a Umma ni fa wallahi Allah ba zaki je gidannan ba. In kin yarda Yaya Dauda zai kawomu dukkanmu mu zo mu ganki. Amman ban yarda ƙafarki ta taka gidanmu ba. Umma duk wulaƙancin da Baba yayi miki fa ban mance ko ɗaya ba. Umma kin tuna wani duka da yayi miki akan umman Samira ta muku sharri ke da Goggo Use, lokacin kin je Shanono kin tawo da Yaya Dauda a halin ciwo? Umma abun yana ɗamfare a raina har in koma ga mahaliccina bazan mance ba, kuma bazan daina ganin baikenshi ba" Kuka yaronnan ya fashe dashi, nima kukan nake yi, rungumata yayi tsam yana mun magiyar shi bazan je gidansu ba. Yaya Use a haka ta fito daga ɗakina ta same mu muna kuka mai raɗaɗi. Kaila ya cuceni yasa ma zukatanmu wani miki wanda dashi zamu koma.
"Iko sai Allah. Sani, Tani to kuyi haƙuri kukan ya ƙare haka mana. Cikin rauni nace.
Nima bana ƙaunar in buɗe idanuna in ga Kaila, dan kun tursasamunne shi yasa nace zanje, kuma nasan sabida yaranne. Sani yace bazani ba. Yaya Use bazan je ba, Dauda ya tuƙo mota ya kawo mun yara in gansu kawai.

8 / 14