Author : Billyn Abdul Category : Love
zuchiya.
Wai me yaronnan yake nufi da nine, so yake in je in sameshi, ko kuma dai me yake nufi?" Kaina nake yima tambayar, kamar yasan me nace a cikin zuchiyata sai ya soma tattakowa a hankali har zuwa dab dani. Ina jin tururin numfashinshi, wanda ya cakuɗe da ƙamshin turarenshi mai suna cool brize. Da sauri na matsa, jin motsin kamar za'a fito ne yasa na yi hanyar waje, dan bana fatan a ganni tsaye da JEGA. Biyo bayana yayi muka dawo bakin get.
Jega ina fatan lafiya dai ko?"
"Lafiya lau laifine dan masoyi ya zo wajan masoyiyarshi? Ni a tunanina babu laifi a ciki. Ba da wasa nazo ba wallahi, kuma ba yaudara bace ta kawo ni wajenki ba. Asalima nasan taƙaitaccen tarihinki da lambobin aurenki. Wannan dalilin shi ya kawo ni wajenki, ki yarda dani ba cutarki nazo yi ba, ina miki zalla marar algus a cikinshi" Ido kawai na kafa mishi, ni mamaki yaron yake bani, baya ko jin kunya, kuma na fuskanci da gasken gaske yake yi. Shi yasa na nutsu zan yi mishi bayani da kyau yanda zai fahimta, na tabbatar yarinta ke ɗibarshi.
JEGA kai yarone matashi mai jini a jika. Bazawara mai yara takwas bata dace da kai ba sam, bazawararma mai aure biyar. Yarana manya ne, zasu iya yin fito na fito da kai, abun bazai yi maka kyau ba. Ina da halaƙar mutunci kyakkyawa tsakanina da mahaifinka. Mahaifiyarka kishiyar Aminiyata ce, mahaifinka mijin aminiyata ne. Taya zaka zo mun da wannan lamarin a matsayinka na yaro ƙarami. JEGA baka da budurwane?" Na tambayeshi ina mai tsattsareshi da ido.
"Ina da mata dai ba budurwa ba. Ina da yarana biyu mace da Namiji. Kinga magidancine ni ba yaro yanda kike tunani ba. Batun mahaifiyata, da mahaifina da kike kawowa kuma. Ni banga wata matsala ba dan na tunkaresu kai tsaye da wannan maganar ba. Nine fa nace inaso, kuma zan iya. Ko tunani kike bazan iya bi dake yanda ya dace bane uhm?" Duk wata tsiga ta jikina sai da suka tashi, gashin jikina su kai tsaye, a sakamakon furucin da JEGA ya feso mun. Kunyace ta lulluɓeni, kamar yanda shima kunyar ta dabaibayeshi har yana runtse idanu. Wajen ya ɗauki shiru na wasu lokuta kafin yayi ƙarfin halin cewa.
"Kiyi haƙuri da furucina, ke kike ingizani in kika kirani da yaro, ni ba yaro bane, zan iya sawa ki mance da tunaninki. Kije ki kwanta dare yayi, sai nazo taɗi in sha Allah, Allah yasa kiyi mafarkin munyi aure harda tagomashin fita yawon buɗe idanu. Ƙila shi zai kasance na farko a rayuwarki, dan ban tamman ƴan ƙauyan da kika aura a baya sun san yawon buɗe ido ba" Yana kaiwa nan ya fice. Hawaye masu zafi suka zubo mun a kan kumatuna. Zawarci babu daɗi, yanzu in banda Zawarci taya JEGA zai zo wajena a matsayin mai neman aurena, har yana furta kalaman sakin layi. Lallai Bazawara kina ganin rayuwa, Allah sarki zawarawan Arewa shanono ta yi kuka da kukanku. Na fi minti goma a tsaye ina tubka da warwara, kafin na shiga ciki na samu jama'ar biki. Wasu na zube a falo anata sheƙar bacci. Ɗakin Habiba Bala kuwa sai hira ke tashi harma da shewa. Babu walwala na shiga ɗakin da sallama. Banɗaki nayi saurin shigewa dan ma kar Habiba Bala ta ganni a cikin damuwa ta damu kanta itama. Ga Sabira ma muna haɗa ido zata gane me nake ciki. Wanka nayo na dole, na fito ɗaure da tawul da kayan dana cire a hannuna. Sukuku nake komai, amman da yake cikin hira suke, babu wanda ya kula dani ma. Ina sa kayan bacci na nemi waje a ƙasa nayi kwanciyata. Ido kawai na rufe zuchiyata na suya, tun inajin tashin muryoyin masu hira, da masu waye_waye har naji shiru, halamun sun yi bacci kenan. Idanuna na buɗe sunyi jawur sun kuma kumbura, hawaye sai tsiyaya suke ta gefen Idanuna. Silin na ƙurama idanu ina tunanin irin yanda maza suka ƙware wajen yaudara, ni babu irin yaudarar da ban gani ba, babu daɗin bakin da maza ba sui mun ba, maƙaryata masu son kansu da yawa. Ji yaro ƙarami suna zaman zamanshi da ƴar matarshi da yaranshi, yana neman ya jajiɓo ma iyalanshi wani al'amari. Yanzu in mahaifiyarshi ta Sani dan Allah me zata ɗauka, goɗai_goɗai dani sai in auri yaron mijin ƙawata abu ba ko fasali" bansan iya daɗewar da nayi ina karanta wasiƙar jaki ba. Ni dai bansan baccin awa nawa na samu ba.
"Shanono tashi lokacin Sallah yayi, da wuri zamu wuce, kuma a gidansu Mama za'a ɗaukeni kinsan" Cewar Habiba Bala kenan. A hankali na buɗe idanuna da suka kumbura su kai suntum. Habiba Bala ta kalleni tace"
"Kuka kika raba dare kina faman yi kenan ko? To me ya same ki Shanono, ni ai nayi tunanin kukanki ya ƙare tunda Allah ya cicciɓeki kina kan babban matsayi mai daraja. Jibi yaranki fa gwanin sha'awa, nifa nawa yaran bani da sabo dasu sam mahaifinsu ya daƙile hakan. To wacce damuwace zata dameki?" Shiru nayi mata kawai, bana iya ɓoye ma Habiba Bala komai. Amman lamarin JEGA na zaɓi in ɓoye mata shi. Sai nace mata.
Bari in yi salla in zo zaki ji dalilin kukan nawa." Sai da na shirya tsab cikin ado da kwalliya da suka zame mun jiki, na bi jama'a muka gaggaisa. A wajen su Yaya karime na zauna, Sabira da su Amina ma acan na tarar dasu. Na shiga cikinsu muka karya baki ɗaya.
"To Tani mu kam yau zamu gudu. Sai kuma mun zo Kano ganin Amarya. Shikenan Aminiya ta dawo kusa dake ko?" Dariya nayi ma Yaya Use nace.
Hakane kam ai ina farin cikin hakan. Dauda ma ya samu canjin wajen aiki, shima Kanon zai koma Habiba Bala tace dashi zata tafi." Yaya Karime tace.
"Gaskiya Habiba Bala na ƙaunarmu da yawa, yanzu da wannan tiƙeƙen saurayin zata tafi gidan auren? Iko sai Allah, batun shagon ɗinkinshi kuma fa?" Nace musu.
E zasu koma da aikin nasu Kano da yaran shagon duka, in da zasu dinga kwana bazai gagaraba. Kano akwai arziki a cikinta, ko ɗinkin kaɗai zai iya isarsu ma. Yaran kuma nace suje dasu su kwaso kayansu a kai mun su Kano, zanci gaba da kulawa da yarana. Shi kuma yaci gaba da kulawa da sauran yaran nashi da matanshi." Sabira tace.
"Kuma kina ganin hakan bazai zama wata matsala ba? Tani ke da muke miki fatan Aure shine zaki ɗebi yara ki mayar dasu hannunki, ki yi haquri ki bar yarannan a gidan ubansu, tunda kinga ga Dauda zai koma kusa dake. Ai uban yana ƙoƙarinshi a kansu"
Wallahi Sabira ku baza ku gane bane. Sabida tare da yaranku kuke yin rayuwarku hankalinku kwance, baku san raɗaɗi da zafin ranuwa da yara bane. Sanadiyyar yarannan na kamu da lalurar hawan jini, sabida tunaninsu da nake yi babu dare babu rana. A halin yanzu bazan iya zama suna wata uwa duniya nima ina wata uwa duniya ba. Ku barni dan Allah kar ku hanani" Jikkunansu yayi sanyi sosai da sosai. Yaya Use tace.
"Allah yasa hakan shine mafi alkairi Tani. Shikenan bamu isa mun rabaki da yaranki ba, yara tarbiyyarsu a hannun mahaifiyarsu yafi ai" Da haka zancan ya mutu dai, su Yaya Use suna yin wanka su ka hau azamar komawa Jos. Ko da su ka je yima Habiba Bala sallama sai da ta basu kuɗi, bayan cincin dasu alkaki data basu hilimi guda. Ƙin karɓa su ka yi fur. Tafiyarsu Yaya Use da kaɗan kuma sai ga su Sani sun shigo da shirinsu na tafiya Kaduna. A motar Sani suka ɗura ƙannen nasu suka tafi, Dauda kuma ya miƙo mun Key ɗin motata. Mu kuma. Da su Sabira muka kama hanyar gidansu Habiba Bala, wanda ta gyara musu ya dawo kamar ma ba shi bane. Sha ɗayan rana muka kama hanyar Kano.
Gaga_gaga awanmu huɗu cib a hanya kafin muka shiga garin Kano ta dabo tumbin giwa. Kai tsaye zuwa Hotoro. Wani tabkeken gidan sama babba muka shiga, family house ne babba, ga motocinan jejjere. Ga canopys an kakkafa a tsakar gidan, da kayan kiɗa jibge a gefe guda. Da dukkan halamu wani sabon bidirin za'ayi a gidan ma. Muna fitowa dangin ango da dangin uwar gidan sukai mana tarbar arziki. Angwaye kuma suka wuce nasu ɓangaren daban. Da jagorancin Dangin Alh Nura muka samu damar ɗanewa sama ɓarayin Amarya wanda ya sha gyara matuƙa gaya. Babu wani hayaniyar kaya a ɓarayin. Ni babban abida yafi tafiya dani wata durowa na hango a kusa da Tv cike da turarukan wuta da humra, kwalaben ma abun kallone, dan ƴan Dubai ne ba ma ƴan ƙasata Najeriya ba. Abin mamaki sai naga sticer a jikin durowar mai ɗauke da tambari da sunan Mrs Bukhari gidan ƙamshi. Lallai matarnan ta shahara, wato har durowa suke zuwa su kafe ma amarya a ɗaki, aikin ki yana kyau Mrs Bukhari. Ciki muka shige kowa na ta faɗin masha Allah_ masha Allah. Bayan mun zauna mun huta kuma sai aka gabatar mana mana da abinci. Ɗaya daga cikin matan da suka shigo mana da abincin tace.
"Hajiya tace mu sanar muku akwai biki data shirya na tarbar Amarya. Misalin ƙarfe huɗu za'a yi a cikin harabar gidannan."
To shikenan Allah ya nuna mana lokacin, kuma a isar mana da godiya, kafin muzo da kanmu." Na ari bakin kowa da kowa na bata amsa. Bayan mun cicci abinci, an yi ramuwar sallah, sai muka soma yin wanka domin soma shiri. Mai Hula na kira a waya na mata kwatancen inda muke nace ta turo mun ƙanwarta mai make up tazo tai ma Amarya. Duk da bamu zo da shirin yin taro ba, ya kamata Amarya a kalleta a kuma, tunda ita uwar gidan bamu san irin shigar da zata yi, bamu da masaniya akan shirinta. Habiba Bala da Sabira na ja wani ɗaki daban.
Habiba kina da wasu kaya da zaki yi amfani dasu na kece raini, ko kuma muje mu siyo miki ɗinkakku? Ko ba Gaskiya ba Sabira, uwar gidan bamu san shirin ta ba ko ya kuka gani?" Habiba Bala tace.
"Ina da laces, da material, da atampa ɗinkin dubai irin mai stone dubu ɗinnan. Sannan ina da lafaya mai stone, da bakin lace. Mu je ku gani." Komawa mu ka yi uwar ɗakin Habiba Bala ta nuna mana. Atampar Aura ce, kuma ɗinkin ya dace da atampar sosai, gashi stone sai walwalin kashe idanu suke yi.
To inaga abinda zamu siyo takalmi da ƴar jaka ne ko, sai ashoke na ɗaurawa akai. Sabira muje, lafin a gama make up ɗin mun dawo da izinin Allah." Sallama mu ka yi musu muka fito. A falon ƙasa muka haɗu da JEGA riƙe da hannun wata ƴar yarinya mai gashi. Yana ganina ya sakar mun murmushi. Ni ko na ɗauke kaina kamar ban ma sanshi ba. Bamu muka shigo gidan ba sai wajajen ƙarfe huɗu da rabi na yamma. Har zuwa wannan lokacin ba'a soma taron ba, an dai soma shirya kujeru da tebura. Masu kiɗa ma sun soma harhaɗa kawunansu. Kiɗanma kamar irin giɗan duma ne. Unguji suka kira daga Kaduna za'a saki duma. Na lura uwar gida ta shirya ma wannan biki tsab. Muna shiga muka tarar da Amarya an gama yi mata make up ta fito shar da'ita. Ɗaurin ashoke akayi mata, ta fito sai sheƙi take yi. Ta sa ɗankunne da sarƙa, da zobe da awarwaro na gwal seti ne guda mai kyau sosai. Sha'anin bikinnan ba'a soma ba sai da mu kai sallar magriba, kafin muka soma jiyo sautin kiɗan duma. Uwar gida Hajiya Kilishi da kanta ta shigo ɓarayin Amarya bisa jagorancin aminiyarta. Tako ci uwa da uban ado, ko iyakar gwai data damɓara a wuyanta abun a kalla ne. Lashi jikinta wanda akaima ɗinkin bubu kuɗin shi zai ɗara dubu ɗari biyu. Dake ba mai ƙiba bace, sai girma bai nuna a fuskarta ba, babu wanda zai ce ita ta haifi JEGA, dan da kaɗan ta wuce tsararmu, a idona dai nasan ba zata wuce shekarun Yaya Karime ba. Hannun Habiba Bala ta riƙe tana fara'a muka fita zuwa tsakar gidan. Kafin mu fita wajen ya karaɗe da guɗa ga hasken fitulo tamkar rana. Ina gefen hannun hagun Hajiya Kilishi. Har muka isa inda aka tanadar domin Amarya da danginta. Hidima gagaruma akayi a wannan dare, Unguji ya gwangwajemu da kiɗan duma, mun sa amarya a tsakiya mu ka ɗan rausaya ba mai yawa ba. Muna cikin filin rawar ne Hajiya Kilishi ta yafito wata kyakkyawar budurwa, tana isowa ta kama hannunta tace da Habiba.
"Amarya ga matar Babban Ɗanki Jega Khadija sunanta. Itace surukata ta farko. Sai na tsinci kaina da ƙarema Khadija kallo da kyau. Baka ce kyakkyawar gaske, gata da fararen idanu da cikar gashin gira. Ɗagowar da nayi na hango JEGA a can gefe yana yi mana video da camara a hannunshi. Numfashi na ja..........✍🏻
[19/10, 5:04 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA 13
Ba shiri na zame daga cikin filin na je kusa da Sabira na zauna nima na zama ƴar kallo. Duk inda Khadija ta wulga idona a kanta. Har zuwa wajen JEGA da tayi ina kallonta. Oh maza kenan, jibi matarshi kyakkyawa amman ya kasa runtse idanunshi da kallona. Dududu yaranshi biyu, amman yana neman ƙarin aure da Bazawara mai yara takwas Aure biyar. Wayata ce naga tana wuta Sani ne yake kirana a waya. Sai na nufi bayan gidan can inda babu kiɗan sosai na ɗaga wayar.
"Umma gamu mun shigo Kano, muna cikin gidansu Inno ma." Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Alhamdulillah, barkan ku da isowa lafiya. Zan dawo gida zuwa anjima in sha Allah. Akwai event ne da akeyi bazan iya tahowa ba tare da an gama ba. Amman dai zan dawo da zaran an kammala, kaji ko?"
"To Umma Allah ya dawo mana dake lafiya ummanmu." Murmushi nayi mishi nace.
Ameen yaron Ummanshi." Mu kai sallama na sauke wayar a kunnena. Juyowar da zanyi naga JEGA yayi tsaye a bayana ya shagaltu da kallona. Sauke kaina ƙasa nayi bance komai ba. Domin al'amarin nashi ya soma isata hakanan. Ina jin kaifin idanunshi yana yawo a jikina. Ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace.
"Wallahi Allah ba yaudararki zanyi ba. Aurenki nake son yi dan mu raya sunnar ma'aiki Arrasul Sallallahu alaihi Wasallama. Ban shiga rayuwarki domin in cutar ko in tozarta shekarunki ba. Kar ki mance nima fa ɗane ai bazan so a tozarta mun uwa ba, taya zan tozartaki Barista? Sama da shekara guda na jarabtu da sonki mai zafin gaske. Na soma saninki ne ta dalilin yanar gizo, na kasance mai bibiyar rubuce_rubucenki da kike yi akan harkar abinda ya shafi hakkin mata. Dana nan na gane ke ƴar gwagwarmaya ce. Barista in fa baki bani dama mun fahimci juna ba, to magana ta gaskiya zan tunkari Umma Habiba da batun neman aurenki, kuma ina sa ran zata shige mun gaba har zuwa wajan mahaifina." Da sauri na ɗago muka haɗa idanu waje guda, sai naga JEGA ya saka fuskar tausayi sosai. Ni ba yarinya bace, na san so, na san yanda zafin so yake sosai. Tabbas Jega yana sona ainun, ina iya karanta zuchiyarshi a fuskarshi. Matsalar itace Shanono ba Aure zata yi ba, baya gabanta, a ma ture batun yarinta a gefe. Shirin wuceshi nake yi, JEGA yayi ƙarfin halin riƙe mun hannuna. Naji wani zum, kallon dana watso mai ne yasa babu shiri ya saki hannuna.
In ka sake tunanin furta mun kalmar so zanyi maganinka Samari. Kar ka sake tare mun hanya na faɗa ma kenan, sakarai kawai yara kun tusa Kallon indiya a gaba, soyayya na son ta ɓata muku tunaninku" Ina kaiwa ƙarshe na ja tsaki na barshi a tsaye ya kasa ko motsawa. Ni ko dan haushi ina fitowa na haura sama ta ɗakko jakata na sulale na nufo gida abuna. Ina shiga gidan na tarar da wata sabuwar dirama. Kaila ya kira a waya yana zazzaga ma yara ruwan faɗa. Zare wayar a hannun Amina nayi na kanga a kunnena.
Nice na ce a ɗakko mun su. Ko yaranka ne kai kaɗai ka yi yinƙurin naƙudarsu ne? Yara dai sun dawo hannuna shine magana, kuma ina da ikon karɓar yarana, in baka yarda ba mu haɗu a kotu Allah ya ba mai rabo sa'a" Ban bashi zarafin cewa komai ba, na datse wayar. Inno dake tsaye ita da Ige tace.
"Iko sai Allah. Tani ai da kin bar mishi yaranshi ko dan gudun fitina yazo yana tayar mana da hankali a banza" Baffa daya fito daga ɗaki yace.
"A'a Inno mu bar yarinya tayi abinda ya dace. A baya mun tauye mata hakkinta. Kada mu sake yanzu ma mu tauye mata wani hakki. Tani Allah ya taya ki riƙon yaran. Su mazan sai mu zauna dasu anan, matan dai kwa zauna tare kafin ki ƙarashe gyaran gidan naki, Allah yayi miki albarka." Ajjiyar zuchiya na sauke na farin ciki. Kaila kuma in dai yace hankali zai ɗaga mun to kotu zamu je alƙali yai mana iyaka dashi, shine maganar gaskiya. Tare da yaran duka muka ɗunguma gidana dake manne dana su Inno. So nake in yi gyara sosai a haɗe gidanma ya sake yin faɗi, in mishi gyara mai kyau. Sabida in dangi sun zo su samu damar hutawa. Su Sani ana falo an baje kolin hira da dariya. Ni kuma hankalina da tunanina baya ma jikina. Shin ko Habiba Bala zan sanarma batun JeGa ne ko ba komai ta sanar ma mahaifinshi dan a ja mar kunne. Kar in zo in yi mishi abunda sam bazai ji daɗi ba."
Kaila:.
Ko da suka kwana a Bauchi da sassafe ya shiga kiran wayar Amina dan ta kwatanta mishi gidan da Shanono take. Amman Amina fur taƙi ɗaukar wayarshi. Ya kira Sulaiman kiran duniya shima bai ɗauka ba. Take zazzaɓi ya lulluɓeshi mai zafi. Dan a cikin tunanin shanono ya kwana. Sai biyun rana suka bar garin Bauchi. Sun ɗanyi tsaye_tsaye a hanya, gaishe_gaishen ƴan uwan Salima. basu suka shiga gida ba sai wajajen