Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Love

Chapter   2 / 14

3K to 6K   out of 40.7K words

damben, dan ita tai ta zagin yaya Use. Sannan Yaya Use bata daki Hajiyayye a ciki ba, kuma bata zauneta ba. Hindatu ƙarya take yi ma kotu bata faɗi gaskiya ba. Sannan Tani ita ƙoƙarin raba faɗan ta dinga yi ita da Hindatu. Kuma ita ta fita tayi kururuwa jama'a suka shigo. Iyakar abinda na sani kenan." Alƙali bayan ya gama nazari yace.
"Lauyan masu ƙara yana da abinda zai tambayi Bilkisa?" Lauyan su Hajiyayye ya miƙe yace.
"Bubu ya mai Shari'a. Amman ina roƙon wannan kotu mai alfarma da tai gaggawar yanke hukunci. Domin likitoci sun tabbatar da cewar buguwace tasa yaron Hajiyayye ya mutu." Alƙali yace.
"Barista Suwiɗi kana da wata shaidar ko iyakarsu kenan"
"Akwai my lord. Inason kotu ta bani dama in gabatar da shedata ta ƙarshe."
"Kotu ta baka dama" Cewar alƙali.
"Inason Dr Ruƙayya ta fito gaban kotu" Wata mata ce fara ta fito tana sanye da fararen kaya na likitanci. Lauyanmu yace.
"Dr ki gabatar ma da kotu sunanki, da halaƙarki da wannan shari'ar" Tace.
"Sunana Dr Ruƙayya. Kuma nice na ciro mataccen jaririn dake cikin Hajiyayye" Lauyanmu yace.
"To ko zaki faɗa mana abinda ya kashe wannan yaron a ciki, kuma ai ku likitocine ina tunanin zaku iya sanin kwanan jaririn nawa da mutuwa ko?"
"Tabbas kuwa. Jaririn a ƙalla zai kai kwana uku da mutuwa a ranar da aka ciroshi, bincikenmu ya nuna mana buguwace tasa jaririn mutuwa, dan har jikinshi ya soma yin yellow, da saɓulewa. Tabbacin kwananshi uku zuwa huɗu da mutuwa a cikin. Kuma Hajiyayye bata zuwa awon ciki balle likitoci su dinga duba lafiyar jaririn. Iyakar abinda zan iya cewa kenan." Murmushi ne ɗaure a kan fuskar iyayena,ƴan uwana, da Aminaina. Alƙali yace.
"Kina nufin mutuwar yaron bata da alaƙa da dukan da su Use su ka yi mata, wanda yai sanadiyyar zuban jininta, sannan ance zanga_zanga aka kawota asibitin, kuma sabida laushin da tayi ne yasa akayi mata aiki. Shi aikin yana da halaƙa da dukan da su ka yi mata ne?" Dr Ruƙayya tace.
"Tiyata bata da alaƙa da dukan da Hajiyayye tasha. Tana da alaƙane da mutuwar yaron a cikinta. Tunda yaron a mace yake, naƙudar za ta yi mata wani iri, ba kamar in yaro yana da ranshi ba. Wasu yaran ma basu cika fitowa ta hanyar mace tayi naƙuda ba in dai sun mace a ciki. Shi yasa muka zaɓi yi mata tiyata mu cire yaron, ba tare da ita uwar jaririn ta sha wahala ba. Wannan shine dalili" Alƙali yace
"Dr Ruƙayya kin tabbatar gaskiyane duk abinda kika faɗa ma kotu? Kotu ba zata barki ba muddin tayi bincike ta gano kin mata ƙarya, ko shaci faɗi" Cikin ƙwarin guiwa Dr Ruƙayya tace.
"Abinda nake faɗa gaskiya ne. Ko da wasa bazan yi ƙarya ba ko dan kare martabar aikina da asibitinmu MATANMI"
"Lauyan masu ƙara yana da tambayar da zaima Dr Ruƙayya?" Alƙali ya jefo tambaya. Lauyansu Hajiyayye ya miƙe jiki ba laka yace.
"Babu ya mai shari'a" Alƙali ya ba Dr Ruƙayya izinin tafiya. Raina fal farin ciki, ta wani ɓangaren fal takaici. Alƙali yace.
"Akwai sauran hujjoji ko babu in yanke hukunci?" Kotu ta ɗau shiru halamar ba wani sauran hujjoji. Hajiyayye sai sauke kanta ƙasa tayi, suma ƴan uwanta su kai ɗib.........✍🏻



_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_

_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_

*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*


*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S

*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224

*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*

*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*

*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*

*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*

*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*

sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*

KAMARSU👇🏻👇🏻

*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*

DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻



https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lmhttps://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm

NA FAƊO DAGA BENE......
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU





LAMBA TA 2.




Alƙali kawai kowa yake jira domin jin hukuncin da zai zartar.
"Wannan kotu mai Alfarma, bayan sauraren ƙara, da kuma yin nazari game da hujjojin da aka gabatar mata, da gamsuwarta akan lamarin. Kotu taci tarar Hajiyayye da Hindatu nera dubu ɗari biyar , wanda za'a ba Use da Tani, a bisa ɓata musu suna da su ka yi. Sannan za su yi zaman gidan kaso na kwana ashirin da aiki mai wuya a sakamakon cin zarafin Use, da Tani da su ka yi, su ka sa aka kullesu a gidan kaso ba tare da sun aikata laifin komai ba. Kotu ta wanke Tani, Use a bisa tuhumar kisan kai da ake musu. Dan haka Tani da Use zasu iya komawa cikin iyalinsu. Kotu zata karɓo musu kuɗinsu daga hannun Hajiyayye da Hindatu, tare da danƙa musu a hannunsu, Kuna da damar ɗaukaka ƙara matsawar hukuncin da aka yanke muku bai muku ba." Guduma alƙali ya buga duk muka miƙe. Hawayen godiya ga Allah nayi, tare da jero kirari ga Allah mamallakin raina. Su Hajiyayye ido ya raina fata, Kaila sai zazzare idanu yake yi, tsoro yake kar kotu ta yanke mishi nashi hukuncin shima. Tuni aka tasa ƙeyarsu zuwa waje. Kotu ta karaɗe da hayaniya da kukan ƴan uwan Hajiyayye. Hindu kuwa dama ita kaɗai tazo kotun, ba ƴan uwa take dashi a garin ba. Muna fitowa Baffa yace.
"Allah ya soki Use Wallahi da ace yaronnan ya saki Tani da tsine miki zanyi kibi uwa duniya. Ke kuma Tani muddin na kuma jin wata fitina wallahi ranki in yai dubu sai ya ɓaci. Inno wuce mu tafi wajan bara. Use ta bi mijinta su tafi gida, Karime ta raka Tani gida."
Baffa ga Habiba Bala kui mata godiya, ita da Sabira sun taimaka mana sosai. Habiba itace ta ɗauki Dauda yana hannunta" Da jin haka su ka washe baki su ka shiga runtuma godiya. Baffa yace.
"Wayyo yarinya Allah ya saka miki da Alkhairi mun gode sosai" Habiba Bala tace.
"Babu komai Baffa." Sallama su kai mana suna tafe suna faɗa, Yaya Use ma Baban yara ya tafi dasu gida. Ni dai wasai nake jin kaina. Motar firzin ta fice a guje dasu Hindatu, ƴan uwansu kuma suka nufi ofishin alƙali dan ganawa dashi. Barista Suwiɗi ma ya tafi ofishin yanzu.
Habiba Bala, Sabira nagode muku. Allah ya barmu har gaban abada" Cikin zolaya Habiba Bala tace.
"Wa zai gane mun idon shanono a cikin firzin. Kin haɗu da kuɗin cizo kuwa" Sabira ta tuntsure da dariya tace.
"Kuɗin cizon gidan yari bazai bata tsoro ba. Tsohuwar katifarsu in kika ɗagata zaki ga kuɗin cizo yafi ɗari suna yawo fa" Murmushi nayi musu kawai, dole su zolayeni mana. Amman ni yanzu ai naji faɗansu, za su ga canji a zahiri. Ba ma su kaɗai ba, duk waɗanda suke tare dani zasu ga canji. Bilkisa ce ta ƙaraso muka gaisa, nayi mata godiya, su Sabira suka taya ni yi mata godiyar suma. Sallama tayi mana muna gani ta shige motarta ta figa ta bar Kaila da Baba Rammai a tsaye. Baba Rammai ta riƙe haɓarta. Bayan na karɓi Salis na je wajan Baba Rammai na gaisheta, wani harara ta watso mun. A tunaninta zanci gaba da tsaiwane har sai ta gama mulkinta. Sai kawai nima na yi ficewata na bi su Habiba Bala. Ko ta tafasa ko ta ƙone a shirye nake da kowa." A lifan Kaila ya Goya Baba Rammai suka fita. Barista ne ya fito yake shaida mana duk sanda kuɗin da aka yanke ma su Hajiyayye suka biya ta hannun lauyanmu zai zo. Nan muka ɗunguma sai gida. Da shigata yara suka tare ni da murna da ihu. Bilkisa ta tare mu da liyafar abinci mai garɗi, Ina shiga cikin ɗakina na fashe da kukan murna kamar wata ƙaramar yarinya. Naita musu godiya ina shi ma zuriyarsu da albarka. Wuni su ka yi cur. Habiba Bala ce ta soma tafiya. Kafin ta tafi sai da tai mun albishin zata riƙe mun Dauda, zata mayar dashi makaranta ta sashi a wajan sana'a kuma. Ta bani nera dubu tamanin a lokacin kuɗin ma da daraja. Wannan kuɗin ƴan ajinmu ne su ka haɗamun dan in ja jari.
Wannan shine silar soma kasuwancina na sai da kayan miya. Cikin yardar ubangiji cikin ƙanƙanin lokaci aka sanni a kan sana'ata. Domin na faɗa muku filin sukuwa unguwace mai zurfi. Kuma duk tsukukun naci sa'a nice kaɗai mai siyar da kayan miya. Duk da dai mu muna ta can ciki ne, inda gidajen yaku bayi sukafi yawa. Unguwar ta hamshaƙan masu kuɗine sosai. Cikin ikon Allah komai yana tafiya dai_dai har na koma bakin karatuna. Ɗakina da jikina babu yabo babu fallasa, gaskiya na ɗauki shawarwarin masoyana, na gyara ba irin shanonon da kuka sani bace yanzu, mai shafe miya a kai, mai dangwalar yawu ta kama kuɗin cizo. Fita a cikin sabgar Kaila da kowa ma, da kuma dogaro da kai, da karatu, da cuɗanya cikin mata iri iri, yasa mun nutsuwa da kamewa, ni kaina in ance in yi abinda nayi a baya na ƙazanta bazan yi ba. Kwanansu Hajiyayye ashirin cib a gidan ɗan kande, wata rana da yamma sai gasu sun shigo bisa jagorancin ƴan uwa, duk ta rame ta yi duhu, tun daga ranar suke kiyayemun dukkansu. . Ni uban gayyar ma ban sake saka shi a idanuna ba. Sai wata ranar juma'a na fito ina sauri zani islamiyya. Da ɗan madaidaicin hijabina wanda ya wuce guiwa, sai doguwar rigata irin yadin hijabin. Harda ɗan niƙab ɗina na ɗaura. Ina fitowa muka haɗu da Kaila. Gabana ya faɗi, shi kuwa galala yake kallona, bai ce mun ba, nima ban ce mishi ba nasa kai na fice. A wajan Bilkisa nake jin wai sati biyu yake yi a Fatakwal, sati biyu a Jos. Ciniki ya kankama dan naga ya ɗebo gini harda ƴar motarshi ya siya yana murza kwalta gayu da kayan gayu yaci uban nada, lifan ɗin ya bar ma Amadudu. Tunda su Hajiyayye suka dawo ita da Hindatu babu wanda ya sake kallona daga cikinsu, balle ya takaleni da faɗa ko habaici, banyi wata ƙaxanta ba balle su tozartani. Amman fa kafin jikina ya saba da wanka kullum na ɗan ci wuya, da nayi wanka jikina zai shiga ƙaiƙayin jaraba, sabida rashin sabo da yi kullum, kitso kuwa duk sati in nayi sai nayi jinyar ciwon kai na kwana biyu sabida rashin sabo. Sai na yi kamar in watsar sai Sabira ta tallafeni, a haka har ya zame mun jiki, kullum zan yi wanka, yara zasu yi, zan gyara ɗakina in sa tsintsiyar ƙamshin viji, ko in kunna turaren kajiji wanda nake siya a wajan Mrs Bukhari. Tun Hajiyayye na mun kallon mamaki ni da yara har dai ta watsar. Da ina gaishe da Hajiyayye da Hindatu in mun haɗu, sai suke wani fuskewa, daga baya nima na watsar, su wuce in wuce. Kaila kuwa tun wannan dubu ukun da yaba Sani ya ajjiyemun ƙwandala bata sake shiga tsakanina dashi ba. Ni kuma na lashi takobin bazan tambayeshi ba. Rabon kwanane banaso, yaje can ya riƙe abarsa, bana zuwa, yaƙin na Bilkisa da Hajiyayye ne. Duk da ma na ga Bilkisa ta kanta take yi, cikinta ya fito titsitsi, Hajiyayye ma har ta sake amsar wani, ga Hindatu itama da ciki. Ni kuwa sai karatuna nake yi kawai, da sana'a. Barister Suwiɗi ya turo mana da kuɗinmu dubu ɗari biyu da hamsin _hamsin, wanda aka haɗa da ƙyar da siɗin goshi. Kuma dulmiyasu nayi a kasuwanci. Na soma ɗauko manja, mangyaɗa, maggi. Sani shi ke siyar mun da kaya in na tafi islamiya.


Bayan wani lokaci:
Kwanci tashi asarar mai rai, wai yau gamu a fagen zana jarabawar game sakandare, wanda yayi daidai da shigarmu S S 1 A islamiyya. Alhamdulillah na gama karatuna, amman fa harna kammala ban iya turanci ba. Ina dai jin komai, amman bana iya mayarwa, larabci kam mune gurayen aji Alhamdulillah, na fi mayar da hankali a fannin harshen larabcin. A wannan shekaru ukun abubbuwa da yawa sun faffaru, marasa daɗin faɗe, nayi rama, na komaɗe na zube sosai, ko bacci bana samu cikakke. Akwai raɗaɗi ace kana aure, wanda kake zamanshi ya saka a kwandon shara. A baya ana ganin ƙazantace tasa Kaila sani a gefe. A wannan ɗan shekarun na fahimci ko agwagwa zan zama dan wanka, in zama ɗawisu dan ado, Kaila bana gabanshi, bazan kasance a gabanshi ba. Wani irin raini ne mai ƙarfin gaske Kaila yake yi mini. Kuma yana tunanin ya wuce ajina yayi gaba ya barni a baya. Tunda yasa ƙafa ya shure baya. Haka naci gaba da kasancewa a gefe ni da Yarana. Da ni zasu yi wasa su yi dariya, nice uwar, nice uban, nice ƙawar duka yarana. Ina sake godema Allah subhanahu wata'ala da ya bani damar tarbiyyantar da yarana, na jure ƙunci dominsu, ina fatan wata rana su maisheni wata aba, uwa irinta kwatance a gari.
Bilkisa tana goyon ƴarta me Suna Fatima, Hajiyayye tana goyon Anas, Hindu tana goyon mai sunan Kaila. Ni kuma tuni na yaye Salis jira nake ya shekara huɗu in danƙarashi a makaranta. Yara kuma na cire su a makarantar gwammati, na mayar dasu ta kuɗi, nice cinsu, nice shansu, suturarsu, jigilar lafiyarsu. Sai in yi wata cur ban sa Kaila a idanuna ba, ko yazo gari baya nema na, ya fiye mun dan na mugun tsanarshi, ina zaune ne kawai sabida yarana, da kuma tsoron bakin Baffa. Amman ko iyakar hana Yaya Use zuwa gidana da Kaila yayi ai ya cutar dani. Yaya Use ta aurar da ƴan matan ta du biyun. Sanda za'ayi bikin satinmu guda a gidan ni da yaran Bilkisa ma ta zo mana kamu da mu ka yi a mufiz Garden."
Haka na sake kammale karatun islamiyyata cikin farin ciki, tare da haɗa gagarumar walimar data samu baƙuncin masoyana, da ƴan makarantarmu ta kwana , da kuma makarantar matan aure dana kammala. Mata matan layinmu ma sun zazzo sosai, sabida an sanni sosai a unguwar, nayi fice ta fannin sana'ata, har niƙaƙƙen garin tuwo nake siyarwa, da albo, da dakakken yaji, wani zubin harda fulawa da shinkafar tuwo. Bayan na kammala karatuna, sai na mayar da hankali na a kan kasuwanci na. Duk abinda na samu akan su Inno da Yarana nake ƙararwa, Dauda kuwa yana Bauchi makarantar kwana yake yi, ya ma fi su Sani gata dan Habiba Bala ta mayar dashi tamkar ɗan data tsugunna ta haifa da cikinta, yaro yayi tsawo, yayi haske kamar ba shi ba. Ga taron ƴan makaranta duk babbar sallah sai mun gabatar dashi, duk in da zani kai tsaye nake zuwa, ba makwaɓi. Gidan Kailan ma naga duk ya wargaje, da halama matan nashi duk zaman haƙuri suke yi, naga Hajiyayye ta dawo rakiyarshi dan kullum a cikin yaji take. Sanda Bilkisa ta haihu ma da ta tafi wankan gida, sai da ta yi wata tara cur, auren dai kamar zai ƙare, daga baya kuma sai ta dawo ɗakinta. Alh Kaila girma nata kamashi, gashi Allah ya sa mishi Nasibi cikin harkar kasuwancin shi, ya sake buɗe gidan gashi a Abuja, ya gangara Bauchi. Kuɗi sosai sun zauna a wajanshi, naga ma ya bar ma Hajiyayye motarshi, ya sai wata sabuwa. Ranar naga falli a tsakar gida, ina tsugunne ina ba yara tumaturi ya bata keyn motar. Ta wani rungumeshi ta ɗafe jikinshi, shi kuwa yayi lib a jikinta. Kaina na kaɗa kawai nayi shigewata ciki, Hajiya Hajiyayye an samu duniya, cikin ƙanƙanin lokaci ta zama wata hamshaƙiya, sutura kuwa ita da Bilkisa wannan na wane wannan ne, dan a yanzu Hajiyayye ta kamo Bilkisa ado da kwalliya, dan har shagon koyon kwalliya Kaila ya sata, yanzu ana biyota har gida taima mutane make up. Ina ji tana faɗa ma Hindatu ta samu shago a wajajen Salisu Adamu, ta buɗe shagon kwalliya, da lalle. Shikenan gidan sai na zama mai gadi da jiran yara, na ɗan waye ɗin ma ban tsira ba, tsabtarnan ina kamantawa, duk da banayi ɗari bisa ɗari, amman a ganina bani da wani aibu da zai sa Kaila ya kasa jerani da matanshi. Ni dai nasan na fi Hajiyayye kyau na fita haske, duk da itama da kyanta, kuma fararce, bilkisa kuma duk ta fimu kyau ita kuma, wata rana haka kaila ya sasu gaba su ka tafi bikin abokinshi a Abuja, ni duk suka zube ma yaran, ko wacce ta wanke ƙafa tabi miji. Ko banyi niyyar kuka ba dole ina ware lokaci in yi kukana mai isata, ganin yarana da rayuwar Dauda ta tayi kyau ne kaɗai ke sanyaya mun raina. Kuma fa har gobe Baffa bai daina ja mun kunne da gargaɗin kar in yi sake aurena ya mutu a karo na biyar ba. Su fa abun faɗe kawai suke gudu iyayenmu, Inno ta riga tasan zaman haƙuri kawai nake yi, ƴan uwana duka sun san ni nake riƙe da kaina da yarana, kaila mafaka kawai ya bamu. Gasuwa ruhina yake yi sosai, har fatan mutuwa na dinga yi ma kaina, daga baya na tsiri wuni cur a uwar ɗaki a kwance.
Kamar da wasa Habiba Bala tai mun tayin me zai hana na zana jam, in ci gaba da karatun jami'ata. Ai tana faɗin haka naji na gamsu ɗari bisa ɗari. Kamar wasa na zana jam tare da cike kos ɗin da zanyi nazari akai. An yi harna mance kwatsam na samu gurbin karatun jami'a a Jami'ar Bayero unibasiti dake jihar Kano, a fannin ilimin low. Murna babu irin wanda banyi ba, nan

2 / 14