Author : Billyn Abdul Category : Love
bugawar da kaina yayi bansan safiya tayi ba, har sai da hayaniyar yara ta shiga kara kaina a kunnuwana. Alwala na je na ɗauro kaina kamar zai tarwatse da ciwo, wani ƙududun abu ya riƙe mun maƙoshina, bai wuce ba, bai fito ba, sai nake jin ina jan munfashi da taurin gaske. Bayan na idar da sallah, Yaya Use ta zauna a gabana.
"Me ake ciki, wanne hukunci kika yanke ma kanki. Mu je in mayar dake ɗakin ki asirinmu a rufe, ko kuwa kin haƙura da yaran naki?"
Na haƙura dasu, bana ma ƙaunar sanyasu a idanuna. Yaya Use ni zan tafi in da rabo zamu gana wata rana. Ki roƙa mun gafara a wajan Baffa da Inno. Zan neme ku bayan wasu shekaru in rayuwata bata tsaya ba. Yara ko da nake tare dasu, dani da su Allah ke riƙe damu. Ko babu ni zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru, ana shawo sai yayi wannan caran. Duk suna zuwa sana'a ko basu samu ilimi ba, zasu samu aikin hannu na dogaro da kai. Dauda in ya samu Habiba zata kwatanta mishi taimakon ƴan uwanshi. Zan tafi ko dan in kwatantama matan da suke zaman aure domin yaransu, daga ƙarshe ciwon zuchiya ko hawan jini yayi ajalinsu, yaran da basa son bari kinga a ƙarshe dole sun barsu" Ƙanƙameni Yaya Use tayi tana kuka.
"A'a Tani kar ki bar gaban iyaye da ƴan uwa. Kima Allah ki zauna anan gidan, zan barki ki ci gaba da karatunki." Fur naƙi, dole Yaya Use ta haƙura ta barni. Kai tsaye na nufi Bauchi wajan Habiba Bala. Ita ta kwantar mun da hankalina tasa nutsuwa ta saukar mun. Inna tuno yarana sai faɗuwar gaba, sai dai Alhamdulillah yanzu na iya addu'o'i da dama, duk wacce tazo bakina biyata nake yi. Nice harda wanka, da cin abinci. Amman dana rufe idanu yarana sai su shiga yi mun gizo a idanuna. Sai dai in share hawayen dake sunturi a idanuna kawai."
Kaila:
Jigum yayi a tsaye a tsakar ɗakin Shanono. Yana jiyo sautin kukan yaranta, ya kasa cewa komai, ya kasa fita a ɗakin ma. Zama yayi a kujera ya tusa yaran a gaba, tausayinsu na shigarshi. Sani na ganin haka ya kwashe ƙannenshi suka shige ɗaki abinsu harda rufo ƙofar ɗakin. Da idanu Kaila ya bi sani. Yafi awa ɗaya a ɗakin shanono yayi kurum ya rasa meke yi mai daɗi. Da ƙyar ya ja ƙafarshi ya fito babban falo. Hajiyayye ya tarar jaye da akwatuna ga uban ciki. Yana tsaye ta gama kwashe komatsen suturunta tsaf. Ta dure mishi yaranshi a gabanshi.
"Gasu Shamwila ta haɗa ta kula dasu baki ɗaya. Nima banci ta zama ba, kaga sai kuci amarci da kyau babu mai saka muku idanu. Baice komai ba ta gama fitsararta ta fice, hannun yaran ya kama ya musu nuni da su shiga ɗakin Shanono. Shi kuma ya wuce turakarshi. Amman me Kaila sai ya kasa tsaye ya kasa zaune. Daya rufe idanu Shanono kawai yake gani. Take ƙwaƙwalwarshi ta shiga aikin tariyo mishi irin so da yardar da Shanono ta damƙa mishi, da irin gudun fishinshi da take yi. Kab duniya sai yanzu ya gane Shanono bata da tamka a cikin duniyarshi. Hawayene masu zafi suka gangaro mishi a kumatunshi. Gabaki ɗaya yayi laushi, har yake jin tamkar wani ɓari na cikin jikinshi ne ya mace. Kaila baisan awowi nawa ya kwashe a tsaye goye da hannayenshi ba. A tsayen Shamwila ta sameshi, tana shigowa ya ƙura mata idanu, bai yi aune ba ta zame doguwar rigar data sako, daga ita sai fatarta fara tas. A wannan dare sun gurje juna sosai ita da Kaila, dan a turakarshi ma ta kwana. Duk da wannan lamari Kaila bai bar tunanin Shanono ba. A gurguje bayan misalin bakwai na safe ya sake wanka. Ya je ya samu Hindatu ya bata kuɗi yace tai ma yaran abincin kari zai je ya dawo. Kai tsaye wajan barar Baffa yaje ya sameshi a bakin masallaci.
"Kaila kaine da safe haka?"
"Wallahi nine Baffa nayi tunanin kana wajan bara ne shi yasa ma nazo nan kai tsaye." Baffa yace.
"Ai anan na kwana, Inno ma yanzu ta tafi masallacin ƴan taya wajan tata barar duk anan muka kwana. Ince dai lafiya ko?" Kaila yayi shiru, ya fahimci Shanono bata je gida ba, ko kuma su basu san tana gidan ba. Sadaka yaba Baffa a gurguje ya nufi gidansu Shanono. Wayam, kai tsaye ya nufi gidan Yaya Karime nan ma wayam. A gidan Yaya Use ya samu labarin a gidan ta kwana, amman ta tafi da safennan, kuma ba'asan inda ta nufa ba. Kaila gabaki ɗaya ya ruɗe sosai. Yana hanyar komawa gida mahaifin Ɗanyan gwal ya kirayi wayarshi akan yazo suna da zama dashi a Zaria. Yana shiga gida, ya shiga falon ya tarar da Salis sai kuka yake yi Sani da Amina na rarrashinshi. Sameera ma ɗiyar Hajiyayye hawaye take matsewa, gashi duk sun zubar da taliya a kan kafet, manja duk ya ɓata wajen. Wayarshi ce ta ci gaba da ruri. Mahaifin Hajiyayye ne, yana ɗauka yaji zancan irin na mahaifin Ɗanyan gwal ne. Take zazzaɓi ya rufe Kaila yama rasa inda zai dafa ya samu sassauci.
Gidansu Hajiyayyen na soma zuwa, nan ya tarar da mahaifinta, da kishiyoyin mahaifiyarta, da Yaya Tabizaro, da Anas, sai Hajiyayye a zaune a gabansu kamar mai roƙon gafara, sai kuka take shirga. Kaila ya nemi waje ya zauna, a kan kujera, bai gaishe da kowa ba haka zalika bai nemi izinin zama a wajan kowa ba. Mahaifin Hajiyayye yace.
"Kiyi ma mutane shiru, yau ga mutuniyar banza, bini bini sai ki kwaso kaya ki dawo gida ko kunya bakya ji, duk rufin asirin da kike ciki, kece da ƙaton shago harda motar hawa. Uwar me akeci a gidan da kike son dawowa? Wallahi daga yau sai yau muddin kika kuma fitowa daga ɗakin ki, sai kin sha mamakina mutuniyar banza, dukan da kika sha ba komai bane akan wanda zaki sha in kika dawo." Ya dawo wajan Kaila.
"Na dawo gareka Kaila. Ka sake haƙuri da wannan sakarar yarinyar, shirme ne yake damunta kasan mata hankali bai ishesu ba. Amman in ta kuma zuwa kai kan ka sai ka tausaya ma halin da zata shiga. Ka ɗauki matarka ku tafi gida" Da sauri Hajiyayye tace.
"Baba ƴar aikin kishiyata fa yake shirin aure, dukkansu matan gidan ko wacce ma ta kama gabanta, sai ni ce zan koma?" Ai ƙarshe a guje Hajiyayye ta fita har ƙofar gida, kakafab_kakafab Mahaifinta ya shiga dukanta ga ciki, Kaila da Anas ne sukai ta bashi haƙuri. Babu shiri Hajiyayye ta shige motar Kaila suka koma gida. Amman sai zazzageshi take yi suna tafe, shi kuwa ba ita bace a gabanshi tunani yake yi ya za'ayi ya ga Shanono? Shine abinda ke gabanshi. A ƙofar gida ya sauketa har ya juya ya kirayi sunanta.
"Ki yi girki harda su Sani, a basu su ci su ƙoshi kar a sake a takura musu" Wani banzan kallo ta watsa mishi, ta ja dogon tsaki ta yi shigewarta ciki. Ya jima a ƙofar gidan ma, ya rasa ina zai dosa, Isa abokinshi ya nema suna tafe a hanyar Zaria ne yake sanar mishi abinda ke faruwa a gidan nashi.
"Ka tabka babban kuskure wallahi Kaila. Ai rabuwa da uwar ƴaƴa tashin hankali ne, ballantana Tani da ta ɗago da darajarka kayi suna. Jibeka a yau, jibi motar da kake hawa, kaya okutenti kake sawa, kana da biranj kusan a garuruwa biyar yanzu. Ga gidan ka mallaka, ga tabkeken fili da kake ginin gidan sama. Kuma ka sani duk wannan ɗaukakar ka sameta ne silar Tani. Ni Isa bazan mance lokacin da Shanono take zuwa har garejinmu ta bamu kuɗin abinci ba. Lokuta da dama a bakin kwata take samun mu, rana da ƙishin ruwa na cinmu. Muna hangota muke ajjiyar zuchiya. Kaila Tani mutum ce harda ɓari, ka yaudareta ka cutar mata da rayuwarta ka ɓata mata lokaci a banza da wofi, da kasan sakinta zaka yi, da ka shina ka saketa tuni ai. Wallahil ƙudrat da zan ga Tani aureta zanyi in wanketa fes mu yi zaman mu" Wani mugun kallo Kaila ya watsa mishi, ba shiri ya haɗiye maganar, dan dama suɓutar bakine. Kaila idanuwanshi suka kaɗa su kai jawur, hawaye suka cika guraben idanun tab, daya tuno da soyayyar da Tani ta nuna mishi da irin sadaukarwar da tayi mishi, taƙi ɗan uwanta sabida shi. Yau ga abinda yayi mata a matsayin sakayya. Hawayene suka gangaro a kumatunshi, bai san sanda ya fashe da kuka ba. Ba shiri ya sauka daga titi, ya haɗe kanshi da sitiyari ya dinga rera kuka kamar majnun. Isa ne ya amshi tuƙin zuwa Zari'a, anan Zaria sun ga wulaƙanci sosai, dan mahaifin Bilkisa kafewa yayi akan sai Kaila ya sakar mishi ƴa. Isa sai haƙuri yake bayarwa. Tas mahaifin Bilkisa ya dinga zagin kwaɗayi da rashin ta'idon Kaila. Hakan duk bai isheshi ba yace su fice mai a gida sai ya sake nemanshi tukunna. Sun so ganin Fatima, ko uwar Fatiman amman basu samu damar hakan ba. Rana zafi inuwa ƙuna. Kaila duk in da yasan zai samu Shanono ya karaɗe, shine har gidan Habiba Bala, amman babu labari. Ko bacci baya iya samu ishasshe sam. Yaran Shanono kuwa wani irin ji dasu yake yi, dan kullum sai sun yi rikici da Hajiyayye a kansu, baya son ko ƙula ya taɓa yaran, wani irin so yake musu marar musaltuwa, har mamakin kanshi yake yi, Sani kuwa daya ga shigowar uban yake haɗe kan ƙannenshi su koma ɗaki sum_sum, hakan ba ƙaramin dafa Kaila yake yi ba. Daga ƙarshe da Hajiyayye ta ƙi kulawa dasu sai ya ɗaukar musu ƴar aiki mai kula mai dasu, yaci gaba da ɗaukar nauyin dake rataye a wuyanshi nasu. Yaran fur basa ƙaunar ganinshi. Dan ko dariya suke yi, yana shigowa zasu gimtse barin ma Sani da yake ji kamar ya kashe uban nasu, Kaila kuwa kullum a cikin siyo musu sabbin suturu yake ko zasu ji sanyi. Rayuwa kenan Allah me yin yanda yaso. Ana cikin wannan yanayi aka ɗaura auren Kaila da Shamwila an yi shagali ba ɗan kaɗan ba. Sai dai babu zumuɗin angwaye tattare da Kaila. Ranar da Amarya ta tare a sabon ɓarayinta ma, kulle kanshi yayi a turaka, ya kasa zaune ya kasa tsaye. Lamarin Shanono yana giirgizashi ainun.....
GAWURTATTU UKU 👠👠👠
1 _KWAI A BAKA_
*(UMMU AFFAN)*
2 _ZULFA_
*(UMMU MAHEER MISS GREEN)*
3 _NA FAƊO DAGA BENE..._
_NA ZARCE RIJIYA_
*(BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI)*
_Littafi ɗaya; 400_
_Littafi biyu; 800_
_Littafi uku; 1000_
Ga masu son turo kuɗinsu ta account sai su tura a wannan account ɗin 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
0037219728
Fatima Rabi'u Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ku tura da shaidar biya ta wannan number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
08104335144
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan number 👇🏻
08104335144
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANNIN SHAFINMU NA Facebook, whatApp, telegram, YouTube, groups, status, zamu tallata muku ne a kan farashi mai rahusa 10k ne kacal sai ku tuntuɓi numbobinmu kamar haka 👇🏻
08104335144
07068606171
08179523215
Domin tallata muku hajojinku a cikin na sati guda ya kama👇🏻
2k kacal
Sati biyu
3k ne
Idan kuma kanason har mu gama book mu dinga ɗaura maka ya kama
10k kacal.
Muna godiya da zaɓar GAWURTATTU UKU ako da yaushe. Siyan nagari mai da ƙudi 🙏🏻..NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU
Assalamu alaikum masoyana, ina mai godiya q gareku, jikina da sauƙi babu laifi. Amman kuimun afuwa kunsan sha'ani na ido sai ana yi ana lallaɓawa. Ba lallai bane in ringa posting kullum ba, kuimun afuwa, idon ya matsa mun sosai.
LAMBA TA 6
Har zuwa wannan lokacin Bilkisa tana Zaria tace ita fa ba zata dawo ba. Bata ga kuma wanda zai sa ta dawo ba. Ya aiko mata takaddarta ta gaji da auren ita ba zata yi kishi da ƴar aikinta ba. Shi kuma Kaila yace taci ƙarya ta kwana da yinwa. Ya faɗa mata bazai sake karambanin sakin mace ba a rayuwarshi.
Haka dai lamarin gidan Kaila al'mura suke ta gudana. Sani, da Sulaiman da Shafi'i ya turasu makarantar kwana a Kano MAI TAMA SULE SAYENS SCHOOL GAYA" su kuma matan suka ci gaba da karatu a gabanshi, kuma iya bakin ƙoƙarinshi yana kulawa dasu, dan mai aikin daya ɗaukar musu su kaɗai take yi ma Hidima. Amman har zuwa wannan lokacin basu sake dashi ba. Ko ziyara ya kaima su Sani a makaranta basa ko farin cikin ganinshi. Dariyarsu ma daya gani a wani ziyara da ya kai musu dan sunga Yaya Karime ne, sai su kai farin ciki, tare da kukan takaicin rashin Ummansu da babu ko ɗuriyarta, a wannan rana hankalin Kaila ya kuma tashi ainun. Sabira da Abban Mustapha suna kaima su Sani ziyara, haka ma Habiba Bala da Dauda suna zuwa dubasu. Sai dai fa Dauda da kuka kullum suke rabuwa da ƙannen nashi. Dauda an girma yanzu yana ATBU anan yake karatu ɓangaren ilimin injiniyanci. Kuma yana da shagon ɗinkin kayan maza ɗinkin zamani, duk sanda zasu je Gaya kai ma su Sani ziyara kayan provision cikin Ghana most go yake dire musu. Duk abinda ya samu tanadi yake ma ƴan uwan nashi, domin yana gani shi suke kallo a makwafin uwa da uba. Su Sani kuwa ko sun yi hutu basa ƙaunar zaman gidan mahaifinsu, sabida takura da hantarar da suke fuskanta a wajan Shamwila a hakanma ba ƙaramin taka mata birki Kaila yake yi ba, Su kansu su Amina cikin matsatsi suke, Hajiyayye kanta bata da damar shan ruwa cikin salama, mulkar kowa Shamwila take yi a cikin gidan. Sai abunda ta zana dashi ake aiki dole. Kaila ba mazauni bane, hatta kuɗin kayan abinci ya dawo hannun Shamwila, keyn store a hannunta yake amman banda kuɗin abincin su Sani, Hajiyayye sai ta jaye jikinta ta koma gefe tabi sahun Shanono ada, taci gaba da ɗaukar nauyin kanta dana yaranta. Motar da take hawa Shamwila ba tai sati ba a gidan tasa Kaila ya kwace motat. Hatta shagon da take gadara dashi, ba ko da yaushe Kaila ke barinta fita ba. Kuma duk munafurcin Shamwila ne. Hajiyayye dai tana zaune ne a gidan dan babu yanda zata yi, kuma ko ta koma gida mahaifinta bazai amsheta ba. Sannan al'ummar Hausawa ba zasu karɓeta hannu bibbiyu a matsayin bazawaraba. Wannan dalilin yasa dole take zaune, gashi sai kwatso yara take yi, kafin ta yaye ta haihu, sai ga Hajiyayye na fama da zarnin fitsari, da ƙiriniyar yara. Hidimar yara yasa ta zama kamar mahaukaciya kawai. Hindatu kuwa nata ido ne, dan ko ga maciji basa yi da Hajiyayye. Lokacin da Hajiyayye ludayinta yake kan dawo, babu irin wulaƙancin da ba tai ma Hindatu ba har goranta mata take yi, wai Amadudu yaƙi yin zuchiya shima ya gina musu nasu gidan. Tunda aka aureta a cin alfarma suke. Ranar dambe su kai a tsakar gidannan babu wanda ya raba su, sai da suka gaji suka bari. Tun wannan lokacin suka dena magana. Da duniya ta saki Hajiyayye taso su dawo halaƙa da Hindatu, ita kuma ta nuna mata babu wannan ƙofar.
Ta ɓangaren su Inno kuwa, sai da akafi wata da sakin Shanono sannan ranar Inno ta tutsiye Yaya Use a wajan bara tace.
"Use wato dake za'a haɗa baki a rufe mu bai_ bai ko? Ashe mitsiyaciyar yarinyar nan kashe auren nata tayi ta zaɓi karatun banza akan tai ma Baffa biyayya? Sani ya sanar dani wata guda kenan Tani bata gidan mijinta. Bama asan inda take ba. Shi kanshi Kailan ya yi sunturin nemanta bama asan inda ta tafi ba"
Yaya Use tayi tsilli_tsilli, cikin rawar murya taso labarta ma Inno abunda ya faru. Nan ta hauta da zagi harda yi mata dundu a gadon bayanta.
"Ai shikenan ta faru ta ƙare Tani ta kashe aurenta na biyar, ta watsar ta yara tabi uwa Duniya. Baffa kuma ya kwashe ma rayuwarta albarka, abinda na guda kenan. Ranar ko rintsawa na kasa yi wallahi, sabida irin tsinuwar da Baffa ya dinga narka ma Tani bazai bari taga Haske ba. Amman ai ita ta jama kanta, Allah ya kyauta, ni ban yi mata baki ba na yi mata uzuri, wata rana Tani zata neme mu." Dole haka Use ta ja bakinta ta tsuke ta bar su Inno akan tunaninsu. Dan tayi imani watarana zasu so ganin Tani, ko muryarta sai sun so ji.
BAYAN WASU SHEKARU MASU DAMA.
BARISTA SHANONO:
Ƙwas_ƙwas_ƙwas_ƙwas kawai kake jin ƙaran takalmina mai tsini daga cikin kotu. Sanye nake cikin ɓaƙaƙen kaya irin na lauyoyi. Farar riga mai kwalace a jikina, sai baƙin sitiret skirt ɗina irin na ƴan gayu, kaina saye da ɗan ƙaramin hijabi gayu fari, sai hular lauyoyi dake kan nawa, kafaduna sagale da rigar shari'a wacce take iyakar cinyata. Takalmi da jakata fararene sol masu dan banzan tsada, ga takalmin da tsinin gaske, sai kwas_ƙwas kake ji duk inda na wuce, sai busa ƙamshin ni'imtacciyar Humra nake yi ta asalin matan Kanuri wanda nake siya a wajan Mrs Bukhari gidan ƙamshi
Duk wanda ya shaƙi ƙamshina yasan turaren na manyan mata ne irinmu, shi yasa bana wasa da wannan haɗi na musamman, tsadarshi bata mun tsada sam, domin ƙamshinshi da riƙe fata da kaya ya kai a bata lambar yabo. ( Ga masu buƙata su tuntuɓeni) . Alhamdulillah ayau na kawo ƙarshen kes ɗin Dattijon da yaima yarinya ƴar kimanin shekara goma fyaɗe. Na tsaya tsaiwar daka cikin ƙwarewar aiki da sanin makamar bincike, har sai da nakai lauyan wannan Dattijo ƙasa. A yau kotu ta yanke mishi hukuncin zaman gidan kaso na wasu shekaru, tare da cin shi tarar kuɗaɗe masu yawa, wanda za aci gaba da kulawa da lafiyar yarinyar. Iska na fesar daga bakina, ina tafe ɗas_ɗas kamar ɗawisu har zuwa bakin titi domin taran abun hawa zuwa chamba. Hannu na sa ma mai ɗan sahun ya tsaya.
Kabuga zaka kaini malam" Shiga nayi na zauna, idanuna da suke saye cikin farin tabarau mai mugun kyau, sai kallon titi nake yi, zuchiyata fal tunani da kewar yarana. Wayata na zaro,