Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Love

Chapter   12 / 14

33K to 36K   out of 40.7K words

taran dare. Yana dawowa Hajiyayye ta tarbeshi.
"Barka da dawowa Kaila. Salima an dawo?" Hararar Hajiyayye tayi ta yi shigewarta ciki. Hajiyayye ta kalli kanta da koɗaɗɗen zanin dake ɗaure a jikinta tayi murmushi tace.
"Salima kenan. Da kinsan sha'anin maza da baki ɗauki duniya da zafi haka ba. Ballema da kikai dace da samun irin su Kaila " A fusace yace da ita.
"Me kike nufi Hajiyayye?"
"Ina nufin kai azzalumine Kaila. Ni kam gidanmu zan tafi, zan bar maka yaranka ka kula dasu. Sannan ina mai maka albishir, Shanono ta kwashe yaranta sun koma hannunta. Sun zo sun kwashe komai da yake mallakinsu sun ma matan gida sallama. Dan haka nima banci ta zama ba, bazan zauna zaman ƴaƴa ya sa in rasa rayuwata ba. Jibi yanda ka mayar damu bola ni da Shamwila, ka mayar damu ababen tausayi. Duk da dai mu muka jama kanmu. Mu mata in namiji ya fifitamu, mu kuma sai mui amfani da wannan damar ta hanyar cusgunama mata ƴan uwanmu. Babu da irin makirci, da bita da ƙullin da banyi ma Umman Sulaiman ba. Dan kawai ka fifitani samanta. Kuna zaman zamanku na mutunci na shigo rayuwarku, sanadiyyata wulaƙanci da tozarci wannena bata gani ba? Nima kuma ai naga iyakata tun zamanin Bilkisa. Shamwila tazo ta rama ma umman Sulaiman duk abinda nayi mata harda riba. Salima itama tazo ta rama mun abinda Shamwila tai mun. Haka gidanka da rayuwarka zata ci gaba Kaila muddin baka gyara ba wallahi" Kuka ta fashe mishi dashi mai tsuma zuchiya, shi kuma yayi shiru kamar ruwa ya cinyeshi. Duk jijiyoyin jikinshi sun ɗaɗɗaure. Hajiyayye taci gaba da cewa.
"Sani da ƙannenshi basa ƙaunar buɗe idanu su ganka a cikin gidannan. Yaron bai sake walwalaba har sai da yaji labarin mahaifiyarshi. Ga Samira can bata son ma in dangantata da kai. Haka suma kakeso su taso ko? To ni na gaji ka sakeni ko in kai ƙararka kotu bazan iyaba Kaila ya isa haka, ai nayi ibada." Tana kaiwa nan ta wuce fuu zata nufi BQ inda take rayuwa. Sai kallonta yake yi yanda ta zama ƙazama kamar ba Hajiyayye gwanar kwalliya ba. Ita kanta Shamwila ta fice a hayyacinta kamar bama ita bace. Sai yau ne Kaila ya gane ashe shi yake lalata matanshi na gida, sai yaga sun tsufa, shi kuma sai ya fice ya sake nemo wata. Yanzu ya gane rashin kula da mace shike sawa ta lalace ta fice a hayyacinta. Take nadama gami da dana sani ta saukar mishi. Bazai yi gigin rabuwa da Hajiyayye ba, domin duk da tayi abubbuwa, amman daga baya ya zalunceta. In ma akwai wacce ta dace ta bar gidan to Shamwila ce ya dace ya saki. Lokaci yayi daya dace ya haɗe kan yaranshi da matanshi waje guda." Wayarshi ya zaro ya kira Sani yana mishi sababi akan me zasu bar gida ba tare da an sanarma kowa ba, kuma wani babba bai zo ya mishi magana ba. Ana cikin haka ya jiyo muryar Shanono tana bashi bayani. Ƙwaƙwalwarshi kusan juyewa tayi dan mamaki wai yau shi Shanono take sanarma su haɗu a kotu. A sanyaye ya zare wayar a kunnenshi, ya nufi ɗakin Hajiyayye ya sameta sai harhaɗa kaya take yi. Carab ya cabki boron kayan nata. Ta juyo suka haɗa idanu, hawaye suka ci gaba da tsiyaya a kumatunta.
"Hajiyayye ki yi haquri kar ki tafi ko ina. Zan gyara duk abinda na ɓata da kaina. Kuma zan tattare kan yarana in kula dasu yanda ya dace, in koya musu zumunci da son junansu. Kiyi haƙuri na san na zalunceki ki yafe mun ki zauna a ɗakin ki. Gobe zan tafi Kano in dawo da su Amina. Zan gyara miki waje a cikin gida in da zaki zauna. Shamwila kuma zan sallameta ta kama gabanta, domin bana ko ƙaunar in buɗe idanu in ganta a gefena. Bazan iya ci gaba da zama da'ita ina mai cike da zarginta ba" Hajiyayye tace.
"Zargi wanne iri, ashe nima cike kake da zargina duk tsawon shekarunnan? Tunda dai na yi kuskuren baka jikina tun a waje." Kai ya girgiza yace.
"Ko ɗaya wallahi. Ai ke nayi imani bayan ni babu wanda ya sanki. Domin ni na yage tantaninki. Itako Shamwila muna bara muna karuwa ce, babu hotel ɗin ba bata sanshi ba a cikin garinnan. Idonane ya rufe shi yasa har na aureta. Dan haka zan rabu da'ita in je in dawo da Umman Fatima daga Zaria ta dawo kuci gaba da zama. Tunda na auri Shamwila ta juya mun baya, har yau da nake gabanki Ɗanyan gwal fishi take yi dani shekara nawa." Haka dai Kaila ya rarrashi Hajiyayye tare da yi mata alkawarin komai zai daidaita, dama shi ya ɓata, zai kuma gyara. Fitowarshi ke da wuya ya nufi ɗakin Shamwila da zummar sallamarta. Sai yaji tana waya tana faɗin.
"To shikenan zan zo zuwa anjima ka turo mun lambar ɗakin naka " Ganin Kaila a tsaye a kanta ne yasa ta saki wayar ta faɗi. Sai ta sau kuka kawai. Shima wasu hawayene suka shiga yi mishi zarya a kumatunshi. Tunani ya sureshi. Ita dama zina yaɗuwa take yi ta kewaye zuriya. Tunda shima ya aikata zinar nan da yaran wasu, shima gashi ana neman danne mishi tashi matar.
"Kaicona da son zuchiya yasa na kasa iya faɗama kaina gaskiya na bi son zuchiya na auri marar tarbiya. Shamwila bazan dakeki ba, bazan zageki ba, abinda na shuka ne nake girba. Kije na sakeki saki uku, kar ki sake in dawo in sameki. Yarana sun raba gardama domin da yayyensu suke kama. Dan haka ki miƙa mun su wajen Hajiyayye " Juyawa yayi ya haye sama ya kulle kanshi sai tunanika ne suke dawo mishi. Kaila ya shiga tashin hankali mai yawan gaske a wannan dare. Sallar isha a ɗaki ya yi ta. Bai ci komai ba tun karin kumallon safe. Ga zazzaɓi kau a jikinshi. Wayarshi ya ɗaga ya kira Alh Isa.
"Kaila ya kana gari kenan?" Ya ambayeshi. Cike da kasala yace.
"Isa kai mun rakiya gobe zuwa Kano gidan Shanono, ta kwashe mun yara inason in dawo dasu ne. Yaran su nake buɗe ido in gani in ji sanyi Isa." Ajjiyar zuchiya isa ya sauke yace.
"Tanin dama an san inda take ashe Kaila?"
"Ba'a jima da jin labarin nata ba. Dan kwanakin baya can yaran suka zo mun da labarinta. Har ma suka tattare suka je mata ziyara, da akai hutu ma suka je mata. To yaune tasa Sani yazo ya kwashe mata kayan yaran dama suna tare da'ita a Bauchi sun je biki. To wai har ni Shanono take cema yara sun koma hannunta, in ina ganin kuma mu haɗu a kotu ne to" Da Alh Isa ya lura a cikin damuwa Kaila yake, sai ya rarrasheshi akan gobe da safe zai zo ya ɗaukeshi su tafi Kanon, a haka suka rabu. Kwana Kaila yayi yana juyi a kan gado ya rasa me ke yi mishi daɗi. Wannan dare yayi mishi nisa sosai da ƙyar garin ya waye. Alwala ya ɗaura ya fito zashi masallaci yaci karo da Salima. Harararshi tayi ta ja tsaki ta yi shigewarta ɓarayinta. Kai ya girgiza kawai ya wuce abinshi. Yana dawowa daga masallaci yayi wanka ya kece ado na daukar hankali matuƙa gaya, burinshi ya burge Shanono, yana fatan ta sanadiyyar yara ƙila auren nasu ya dawo, kuma yanzu ga gurbi ya nema mata na zama, duk ba da niyya yayi hakan ba. Ɓarayin Salima ya shiga, ko sallamarshi ta kasa amsawa.
"Zan tafi Kano, daga can zan shiga Zaria. Inaso ke da Hajiyayye ku gyara wancan shashen Umman su Fatima zata dawo kuci gaba da zama. Itama Hajiyayye zata dawo ɗayan shashen?" Buɗar bakin Salima tace.
"Ita kuma Shanono turakarka zaka bata ko, tunda ka saki Shamwila ka koreta dan uwar ƴaƴanka ta samu gurbi" Murmushi yayi mata yace.
"Dukka gidannan gurbin Shanono ne, dani da dukiyata duk mallakin yaran Shanono ne, kinga kuwa a tafin hannunta nake. Ko bata dawo gidana ba, ai tafi ƙarfinki sai dai ki kalleta." Ficewarshi yayi. Yaje su ka gaisa da Hajiyayye ya jaddada mata abinda yace ma Salima, na game da komawarta ciki, da kuma gyaran ɓarayin Bilkisa. Godiya tayi mishi tare da yi mishi adda'ar dawowa lafiya. Fita yayi daga BQ ɗin ya samu Alh Isa a cikin mota, suma sun jima da dawowa Kaduna da iyalanshi. Sai da suka kama hanyar Kano Kaila ya samu salama."





Barrister Shanono:.
Tun sassafe na shirya tsab cikin shigar aiki, yau ina da sabuwar shari'a mai zafin gaske. Sani ne ya dafa mana tea ya soya mana wainar ƙwai. A gurguje naci, nai musu sallama na fita. Sai da na shiga gidan su Inno muka gaisa kafin na nufi chamba. Ina shiga na tarar ana shirye_shiryen meeting. Misalin ƙarfe takwas na safe duk muka hallara a meeting holl, duk muka doka wayoyinmu a silent dan gudun kar a kira ana tsakiyar tattaunawa. Oga Rashid ya soma magana.
"Am maƙasudin wannan taron, na taraku ne domin mu tattauna akan wasu matsaloli da suka shigo mana wannan Chamba. Tun farko dana buɗe Chambata, na buɗetane domin in tallafi ƙananun baristoci da suka gama karatunsu na low suna yawon neman aiki. Gaskiya dokin ƙarfe na kafata ne domin gaskiya da gaskiya. A cikin baristocin da ni nake dasu, an samu waɗanda ake haɗa baki dasu ana murɗe ma masu hakki hakkinsu, akan abun duniyar da bai taka kara ya karyaba. Ni tsohon lauyane nasan yanda harkar take, nasan yanda ake mana tayin kudi, nasan yanda ake mana barazana da ranmu. Akwai wara shari'a dana gabatar shekaru talatin baya, wallahi sanadiyyar wannan shari'ar har makaranta akabi mai ɗakina aka saceta, tun duniyarma na kwance. Akace in ban ƙaryata duk hujjojin dana kafa ba wallahi sai sun kasheta. A lokacin na shiga tsaka mai wuyar fita, gashi ɓangaren dana riƙa rauni garesu ni suka riƙe a matsayin sandar jagoransu. Da dabara dai aka sako mun matata, nai musu alƙawarin zan ƙaryata kaina. Bayan sun sakota aka gama shari'ar ba tare da na yi abinda su suke so ba. Amman har biyoni su kai a titi suka harbeni a hannu. Banda motoci, ko gida da za'aima tayinsu. In muka ce zamu ruɗu da irin wannan tayin wallahi zamu cutar da kanmu ne. Sannan kun rage ƙwazo da himma akan aiyukanku. Barista Shanono, da Barister mai Hula ne suka fi kowa mayar da hankali akan aiyukansu. Kuma in suka nace ma kes sai sun yi nasara. Sannan suna da hanyayo da salon bincike sosai, ina bibiyar aiyukan kowa. Wannan shine maƙasudin taron namu. Kuma akwai sammaci da muka yanka ma mutum 6, zan rarraba muku aikin in sha Allah. In da me magana sai yayi" Mun fi awa uku muna abu ɗaya, daga bisani ya Sallamemu taron ya watse. Da zan fita Oga Rashid yace in na rarrage ayyukana in zo in sameshi zamu yi magana. Ina zama a teburina wayata ta shiga haske dake a silent take. Sabuwar number na gani. Ɗagawa nayi na kara a kunnena. Sai naji muryar mijin Habiba Bala.
"Barista shine jiya kika gudu ko sallama babu ko?" Ajjiyar zuchiya na sauke da naji muryar tashi washar da'ita. Na yi tunanin Jega ya kira mun ruwane.
Ango da kanshi, barka da safiya ya kwanan Amaryar?" Da dariya yace.
"Gata ita tace in kirawoki ma" Miƙa mata wayar Yayi.
"Shine kika gudu ko Shanono dan wulaƙanci, su Sabira sai nemanki suke yi."
Yi hakuri kira na samu na gaggawa ƙawata kuma nasan in dai nace miki zan tafi ba lallai ki amince ba. Ya kin tashi lafiya?" Dariya kawai tayi mun tace.
"Zaki zo ne in kin baro office akwai labari fa" Nima dariyar na mayar mata nace.
To zan yi kokarin hakan. Yaranki fa sun dawo hannuna, jiya ma Kaila ya kira ta inda yake shiga ba tanan yake shiga ba. In nazo ma zaɓa musu makarantar da kika ga ta dace dasu, sai nazo, Sabira sun koma ne?"
"Tun yaushe, taje ma gida ta dubo su Inno. Tasan kin tara aiki a office ne shi yasa ma bata bi ta kanki ba, sun kusa shiga Jos ma ai yanzu" Sallama nayi mata, ina sauke wayar kiran Sani ya shigo.
Sani ya akayi?"
"Umma su Babane suka zo, suna cikin gidan su Inno, Baffa ne yace in kira ki, in ba wani abun kike yi ki zo yanzu." Gabana ya yanke ya faɗi ras a sanyaye nace.
To ganinan zuwa yanzu Sani. Har zan kashe wayar yace.
"Umman kin mun alƙawarin ba zaki koma hannun Babanmu ba, kar ki manta da wannan. Ni bazan taɓa yarda ki koma mishi ba umma" murmushi nayi dan in kwantar mishi da hankali.
Babu ma wannan zancan Sani, kaji ko kasha kuruminka ganinan zuwa" Wayar na kashe Mai Hula ta kalleni tace.
"Wata matsalarce?"
E yarane nasa aka kwaso mun suka dawo hannuna, shine Babansu ya biyo sahu. Baffa ne yace yanason ganina. Bari in je sai na dawo" Fita nayi zuwa ofishin Oga Rashid. Kwankwasawa nayi ya bani izinin shiga.
Ƙwas_ƙwas_kwas na shiga, kujera ya nuna mini yana murmushi.
Nagode sosai Sir.
"Ai ya zame mun wajibi in baki waje zama ni fa na gayyaceki" Katseshi nayi.
Dama a gidane mahaifina yake nemana akwai abun da ya taso ne, shine nake neman izininka" Da mamaki ya kalleni yace.
"Dama tare kike da mahaifanki a garinnan?"
A'a dawowa dai su ka yi, da Bama tare sir" Murmushi yayi yace.
"Allah sarki, to a gurguje nima bari in yi amfani da wannan damar domin in fallasa miki asirin zuchiyata, tunda kin ƙi ki fahimci inda na dosa sam. Kaina nayi sauri na sunkuyar gabana ya shiga harbawa Fat_fat_fat.........


Team Kaila #
Team JEGA #
Team Oga Rashid #
Ku futo. A ganinku wa ya fi cancanta Shanono ta miƙa ma zuchiyarta a karo na shida ?.....NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU


LAMBA TA 14



"Barista na jima sosai ina rainon jaririn sonki a zuchiyata har yayi girman da nake kasa mallakar kaina. A mafiya yawan lokuta, zagaye da nake yi zuwa ofishoshin ma'aikata, ina yine domin in ganki in ji sanyi. Ina sonki Shanono, Allah yasa babu wanda ya rigani, dan ni tun ina matashi bana iya haɗa soyayyar mata biyu. In kuma naje wajen mace na ganta tana kula wani saurayin to jaye jikina nake yi. Dan ni in inaso ban iya so ba, haka in abu ya fitar mun akai ma haka nake. Da fatan zaki bani lokaci in zo in sameki a gida mu ƙarashe maganar?" Ni dai tunda ya soma jawabi gabana ke aikin bugawa, abun wani iri nake jinshi, duk da nasan Oga Rashid ya jima yana tattalin sona, amman ni fa ba auren da zanyi magana ta gaskiya"
Nagode Sir, inaso ka bani lokaci zanyi nazari akai" Da murmushi ya dubeni yana wani numshe idanu yace.
"Zuwa yaushe kenan? Kar ki sakani cikin zulumin tare da taraddadin me zai fito bakin ki. Domin rashin amincewarki zai iya jefa ni cikin wani hali mawuyaci. Na daɗe ina rainon sanki, yayi girman da rasaki zai iya kassara kuzarina" Ruɗani na shiga mai girman gaske, nama rasa bakin magana, bance komai ba har ya sake magana.
"Zuwa yaushe zan jira amsar taki Barista, ba zaki tausaya mun zuwa ko gobe bane in zo gida in sameki mu tattauna ba? Ai mun wannan alfarmar, ban taɓa neman alfarmarki ba, yau ɗaya na roƙa aimun dan Allah " Ɗaureni da jijiyoyin jikina yayi tamau, Oga Rashid tabbas mutumin kirki ne, lokacin da nazo neman aiki, ma'aikata sun cika Chambarshi, amman da yaga macece ni mai rauni, a hakan ya nema mun ofishin da zan zauna, ya ɗaukeni aiki. Tunda dai ya nemi alfarma ya kamata in mishi. Amman bazai iya samun soyayya ba, dan in na faɗa mishi ina sonshi na zalunceshi, na zalunci kaina. Babu wani wanda daɗin bakinshi zai sa in iya sonshi sam an riga da an sha ni na warke.
To shikenan Sir Allah ya kaimu gobe." Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya miƙo mun wayarshi.
"Saka mun number wayarki da hatimin amincewa in kira wayar a ko da yaushe." Karɓar wayar nayi nasa mishi number, kana nace.
Baka samu hatimin amincewa da kira ko yaushe ba. Kira in ya wuce taran dare wayata ma bata kunne, domin kullum ina zama in yi karatu domin nazari"
"To shikenan sai yanda kikace ai. Muje in taka miki" Nayi nayi dashi ya barshi, amman fur yaƙi, sai da ya kaini har bakin mota.
"Kina da shari'a yaune?"
E inada ita, a kotun bayan gidan sarki, ƙarfe huɗu zamu yi zaman. Ƙila daga gida can zan wuce" Murmushi yayi kawai baice mun komai ba, naja motata na tafi na barshi a wajen. Ina tuƙi sambatun Oga Rashid suna yawo a kaina. Wayata ce tayi ruri, da sauri na duba ko Sani ne. Amman sai naga sabuwar number. Ɗagawa nayi na saka a kunnena.
"Amincin Allah ya tabbata a gareki Amaryar Jega da fatan kin tashi cikin ƙoshin lafiya, yaya gajiyar biki?" Saida kaina ya sara mun, ƙit na kashe wayar ma baki ɗayanta, hawaye ya soma zuba a idona. Mahaukaciya ma suke shirin mayar dani na lura, soyayya dai_ soyayya dai a aureka daka kwana biyu kashi ya fika daraja. Ina bazan iya bama kowa damar shiga rayuwata ba sam." Da wannan surutan na isa gida. Ina shiga gidan na hango takalman maza biyu a ƙofar ɗakinmu. Yaran duk suna tsakar gida, Sani na ganina ya kamo hannayena muka shiga ciki tare. Idanu muka haɗa da Kaila. Ya zuba mun idanu yana kallona. Nima shi nake kallo, ina hango murmushin muguntar da yayi mun sanda zamu je zaman firzin. Ige ce tace.
"Shigo Tani. Kai kuma Sani shikata ka koma ka jira waje." Kallon Sani nayi nace.
Ka jirani, ku tafi can gidan bazan daɗe ba kaji Sani na?" Jayayya yaso ni na hanashi, yana hawaye ya fita, ni kuma na shiga na nemi waje na zauna. Sai ƙaremun kallo Kaila yake yi. Ban yi yinƙurin gaishe da kowa ba, Baffa yace.
"Tani, Kaila ne yazo tafiya da yara. Yace shi bai yarda yaranshi su zauna a hannunki ba. Yanason haɗe kan iyalanshi waje guda. Dan haka ke

12 / 14