Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Love

Chapter   10 / 14

27K to 30K   out of 40.7K words

kenan, duk dakon wannan ranar da nake yi a haka ashe zata same ni? Banyi zato ko tunanin haka daga wajan mace mai girman daraja da karamci kamarki ba. Ni fa na ɗauka masoyi duk ƙanƙantarshi, ko girmanshi abun a daki ƙirjine a nuna shi. Cikakkiyar soyayya ta gaskiya babu ruwanta da girman ma'abotanta, ko ƙanƙantarsu. Dan da tana la'akari da hakan. Da yara ƙanƙana basu isa saninta ba. Amman so bai ware kowa ba. Shanono ki ma ɗan jaririn da yake neman tallafin uwar goyanshi duban tausayi, zuchiyata jaririyar zuchiyace tarairaya take buƙata" Ƙur na zuba mishi idanu, cike da kallo mai ɗauke da fassarar baka da hankali. Na rasa me zance ma wannan yaron, na kuma kasa ɗauke idanuna a kanshi, shima ni ya zuba ma idanu. Na lura jikinshi har rawa yake yi kaɗan.
Buɗe mun ƙofa in fita Samari." Iyakar abinda na furta kenan. Baice uffan ba ya zare sakatar data rufe motar. Na buɗe motar na fito abuna. Ido huɗu nayi da kaila yana tsaye suna gaisawa da wani dattijo.
Yaci uban ado na kece raini, ga wata mata saye da lafaya a gefenshi a tsaye. Dinkin malum_malum na Ami green shaddace dakakkiyar gaske a jikin kaila, hular kanshi iri ɗaya da design ɗin dake gaban rigar tashi. Sai takalminshi mai rufaffen gaba irin na maza ƴan ƙwalisa. Idanunshi saye da farin tabarau mai ɗan girma, agogonshi da zabban hannayenshi kuma masu ruwan silver. Kunsan Kaila gwanine na iya wanka, duk da na yarda a jinin ƴan jos iya wanka yake. Kawar da kaina nayi, gabana ya tattake ya faɗi, daurewa nayi na soma tawowa ƙwas_ƙwas_ƙwas_ƙwas_ƙwas tsinin takalmina sai ba da sauti yake yi."


Kaila:
Mutuwar tsaye Kaila yayi ya ƙame kamar status. Tabarau ɗin dake manne a fuskarshi ya kawar, dan gani yake kamar tabarau ɗinne yake yi mishi gizo.
"Ina wannan ba Shanono bace, gizo kawai Idanuna yake yi mun, shanono ba zata zama haka ba" Ya furta a zuchiyarshi tare da girgiza kai a zahiri. Salima Amarya ta dubi Kaila, ta dubi Hajiyar da yake ma wannan mayen kallon. Ta zo har wuya, take taji kamar tayi bindiga ta fashe dam. Kaila kuwa baisan ma me Amaryarshi Salima take ciki ba, kuma ita yai ma rakiya wajan bikin. Shanono tana gibtawa, ni'imtaccen sihirtaccen ƙamshinta mai kaɗa ruwan ƙwaƙwalwa ya sauka a salansar hancin Kaila. Baisan sanda idanuwanshi suka lumshe da kansu ba tsabar daɗin kamshin. Tunda yake bai taɓa jin makamancin ƙamshi irin wannan ba, wannan ya ya kasance na musamman ne. Da yaga turaren Shanono na shirin shagaltar dashi ya rasa kanshi, sai kawai ya tsinci kanshi da furta kalmar.
"Shanonooooooooo"



Shanono:
Cak na tsaya da naji Kaila ya ambaci sunana. Ji nayi kamar ya watsa ma jikina ruwan dalma. Hawayen daya ciko Idanuna ne suka gangaro sirara. Ina jiyo takun tawowar kaila ta bayana.
Ƙwab_ƙwab_ƙwab_ƙwab_ƙwab Hannu nasa na goge hawayen fuskata, na juyo. Da Jega muka haɗa idanu, yana tsaye a jikin motarshi ya harɗe hannu yana kallona. Sani da Dauda ne suka nufoni. Tare da Kaila suka iso inda nake a tare. Sani ya kalli Kaila ya kalleni.
"Shiga ciki umma. Taro yayi taro a matsayinki na babbar ƙawar Amarya ke ake jira. Kowa jakarki ummana" Jakar hannuna Sani ya karɓa ya riƙo mun hannu muka juya mu ukun muka bar kaila a tsaye........✍🏻NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU

LAMBA TA 11




A tsakiya suka tusani har sai da suka nema mun waje kusa da Yaya Use, kana suka juya Dauda hannunshi sagale a kafaɗun Sani, sunyi anko irin na abokan ango suma. Gabaki ɗaya sai na ji hankalina ya kasa kwanciya sam, jina nake kamar wata marar lafiya. Miki biyu ne suka haɗu suke neman kaini ƙasa. Na farko mikin da Jega ya fama mun a zuchiyata na ƙoƙarin shigar da kanshi zuchiyata, ko ince rayuwata yana ɗan yaro dashi. Ina daga cikin matan da suke ƙalubalantar manyan mata masu yin wuff da samari ƙanana sa'annin yaransu, wasu ma sa'annin jikokinsu. Ai da ace su Sani zasu san me Jega ke shirin yi musu na yi imani a wuyanshi Sani zai dira. Dan yaron zuchiya gareshi, ji dai yanda yayi fito na fito da ubanshi ma. Miki na biyu shine haɗuwata da Kaila, ya rarakemun babban ramin mikin daya tona mun a cikin rayuwata. Ko ɗar banji daɗin ganin Kaila ba, asalima da nasan zan haɗu da azal ɗin haɗuwa da Kaila, da Jega da ban yarda na tako garin Bauchi ba. Amman raina yayi fari fat dana iya gigita nutsuwa da tunanin Kaila, ai nasan Kaila akwai macewa akan mata masu aji. Na kuma yi farin ciki da abinda Sani yayi mishi, hakan ƙila ya zame mishi izna."
"Tani Habiba Bala sai yafitoki take yi, hankalinki a ina yake ne?" Na jiyo sautin muryar Yaya Karime a kunnuwana. Kallon inda Amarya da ango suke nayi, naga ni Habiba Bala take kira. A hankali na miƙe jikina babu laka sam. Ina zuwa tsakiyar filin naci karo da Jega, da wani irin mayen kallo mai wuyar fassarawa ya bini. Harara na daddage na dalla mishi, shi kuma ya sakar mun murmushi"




KAILA:
Mutuwar tsaye yayi kawai. Ya bi Shanono da yaranta da kallo, yabi takun da shanono take yi cikin tsari da gogewa irin ta manyan mata, wayayyu waɗanda suka san ciwukan kansu. Murmushi ya saki.
"Wacece wannan Apple da har ta ɗauke maka tunaninka ka mance kanka, a gabana kake ma mace mayen kallo haka, wai dama haka kake? To da kake kallonta sakin ɗaya daga cikin matanka zaka yi ka maye gurbi da ita ko yaya? Gashi naga har Sani ma ya santa, meke faruwane?" A jejjere take tuhumarshi tare da kafeshi da idanuwanta da suka koma jawur dan haushi. Shi kuma Kaila cikin rashin mallakar kai yace.
"Gyatumar su Sani ce, uwar ƴaƴanace Shanono" Ya bata amsa tare da soma tafiya, ƙamshin shanono yananan daram a hanyar data wuce yana gauraye da iskar da Kaila yake shaƙa, sai lumshe idanu yake yi. Salima kuma mamakine ya cikata da ganin Shanono ita a tunaninta ba haka zata ga shanono ba, domin taji jita_jitar ance iyayenta mabaratane, amman dai bata da wani labari dangane da ƙazantar da aka dama. Jikin Salima yayi sanyi, dan da a tunaninta tafi ko wacce mace a idanun Kaila, ganin Shanono ya ture mata wannan tunanin kuma ta miƙa wuya cewar Shanono ta fita nesa ba kusa ba, kuma har wayewar da take taƙama dashi Shanono ta kere mata. Uwa uba yanda take fitar da wani irin fitnannan ƙamshi mai sa nutsuwar zuchiya, dan har zuwa lokacin hancinta cike yake da ƙamshin turaren da Shanono ta bar musu a matsayin abinda zai ta buga musu kawunansu. Da jan ƙafa Kaila da Salima suka shiga cikin holl ɗin, tare da samun wani teburi suka zauna. Ashe teburin dake kusa da su Sulaiman ne da su Amina. Sai ji Kaila yayi Balaraba tace.
"Baba" Da sauri ya juya, ido huɗu yayi da Sani, yaga yaron na mishi wani irin kwarjini, da sauri ya ɗauke idanunshi akan nashi yana harararshi. Ya yafito Balaraba da hannunshi. Miƙewa tayi tazo kusa dashi.
"Kina da number ummanki?" A kunne yake tambayarta, gyaɗa mishi kai tayi halamar e tana dashi.
"To shikenan zan karɓi number a wajenki, amman kar ki sake ki faɗama kowa. Inaso in dawo muku da ummanku ne, kuma ku zauna a wajan mamanku" Sani idanunshi a kansu yake, yana ƙissima yanda zai ma Balaraba. Saketa yayi ta koma wajan zamanta, Salima ta harareshi, yayi tsam yana kallonta yama mance da shakkarta da yake ji yau sam. Juyawar da zai yi ya hango Shanono tana sakkowa daga inda Ango da Amarya suke, sai dariya take yi. Ganinshi yayi a tsaye kamar soja yana ƙarema takun Shanono kallo. Sai da Salima ta finciko hannunshi ta dangwarar dashi a kujera, ta nuna shi da ɗan yatsa.
"Bari kaji nafi ƙarfin kai mun wulaƙanci wallahi, me akayi akayi ka? Namiji sai shegen kallon matan tsiya kamar wani bunsuru. Ji yanda kake kallonta ka mance da ni a zaune a gefenka. Ina zaka sata to in ta amince ma zata dawo kan yaranta?" Harara ya sakar mata.
"Lallai Tanjirin. Baki san waye Shanono a cikin rayuwata bane. Baki san a yanda shanono ta tsinceni mu kai aurenmu na rufin asiri bane. Wanda nayi imani da kece zaki tsinceni a irin yanayin da shanono ta tsinceni ba zaki ma yarda ki saurareni ba. Kuma bance miki dan wani abun nake kallonta ba. So nake mu gaisa a matsayina na wanda mu kai rayuwa tare a baya, yaranmu bakwai tare da ita. Ai kuwa ta riga ta zama ni, na zama ita" Kallonshi ta yi ta sake mayawa. Kana Tace.
"Zaka ga buyagin da zanyi maka wallahil azeem. Bari in je wajan su Yaya Hama, in ka ga dama sai kaxo ku gaisa"


Sani:
Balaraba na komawa yace mata.
"Baba zai dawo mana da ummanmu ko? Nafi kowa farin cikin hakan" Ya faɗi hakanne domin ya nuna mata gaba yake da ita, dukan cikinta yayi. Abinka da yarinta nan ta hau ɓarin zance ta kwashe yanda su ka yi kab da Kaila ta faɗi ma yayyenta. Amina ta harareta tace.
"Wawuya kinaso ummanmu ta dawo kenan Baba yaci gaba da dukanta yana zaginta a gabanmu ko?" Sani yayi carab yace.
"Umma da fa ɗauke ku zata yi a hannun matan Babanmu, ta mayar daku Kano wajenta cikin sabon gidanta. Hankalinmu a kwance. In Umma taji labarin ke kika ba Baba number ta ya kirata. To a Kaduna zata barki wajan Umman Musa, mu kuma mu koma can. Duk sai Balaraba tabi ta ruɗe. Dauda ya harari Sani yace.
"Wai me yasa kake yin duk wannan abunne? Ka ba Innata dama ta kwaci kanta a wajen Baba mana, ni ina ganin wannan faɗan nasu ne. Akwai gaɓar da zamu iya shigar mata ko ya kace?" Sani ɗan duniya dan yafi Dauda gogewa sosai yace..
"Ba za ka gane bane. Ai barinsu su yi doguwar magana ka iya rushe mun ƙudurina. Wallahi Allah in har sai Umma ta dawo hannun Baba misali zai ci gaba da numfashi. Tsaiwar numfashinshi yafi mun aikhairi ni. Umma taci wuya fa Yaya. Ta wulaƙanta ta ƙasƙanta sosai" Take hawaye ya soma gudu a kumatunshi, baya ƙaunar abinda zai tuno mishi da rayuwar ummanshi a hannun mahaifinsu.



Shanono:.
Anata sha'anin biki, kiɗe_kiɗe sai tashi suke yi, Amarya da ango suna zaune sai liƙi ake yi musu. Ƙawayenmu an haɗe kai seti_seti sai hira da shewa irin da duniya tai daɗinnan su ke yi. Ni kuma gabaƙi ɗaya maganganun Jega sai nuƙurƙusar ƙasan raina take yi. Ni ba'a taɓa rainani irin na yau ba. Ni yaro ƙarami haka zai nemi tsarani, ta ya yayi sake zuchiyarshi tayi wasa da tunaninshi? Yaro yarone ko da kuwa ɗan giwa ne. Ta wani bangaren in na tuno da irin ruɗewar da Kaila yayi a kaina sai inji wani farin ciki. Ko banza ina da abinda zan iya ma Kaila ƙwalele dashi, ƙwalele irin na har abadan kuwa. Dan kuwa nasan Kaila babu shi babu runtsawa a daren yau ɗinnan. Haka taro yaci gaba da gudana cikin farin ciki da nishaɗi. Anci ansha an goge wuya abun ba'a cewa komai. Mun yi rabon kasko da tureren wuta, harda ashana, wanda Sabira tai mana odarsu a wajan Mrs Bukhari gidan ƙamshi. Kowa ya samu, har sai da aka koma da rogowar kayan rabon, tsabaragen munyi komai a wadace sosai. Bayan taro ya tashi Sani shi da kanshi ya zo ya fito dani daga taron, ya sani a cikin motarshi, Kaila yana tsaye yana ƙare mana kallo, amaryarshi kuma tana gaisawa da ƙawayenta ne ko ƴan uwanta ne ohon mata dai. A gidan baya na zauna ina sauke ajjiyar zuchiya. Kaila ne ya kirayi Sani yace yaje. Su Amina kuma suka shiga motatata su da Yayansu Dauda. Bansan dai mai Kaila yake cema Sani ba, amman koma meye nasan yana da nasaba da abinda ya faru ɗazu, dan naga sai faɗa yake yi kamar zai daki Sanin. Ya dai gama borin kunyarshi Sani yazo muka bar wajen, ina ganin Kaila yanda yake bina da wani mayen kallo, naga har haɗiɗiyar yawu yake kamsr wani tsohon maye. Sani baice mun komai ba tunda ya shiga motar, sai gudu yake shararawa dani, ni kuma jin shi shiru sai hakan ya taɓani, ya saba da zolayata da kuma yi mun hira dan ya faranta mun. Bansan Sani kuka yake yi ba har sai da muka iso ƙofar gidan su Habiba Bala bayan na fito. Idanunshi sun kaɗa sun yi jawur dasu, hawaye sai zuba yake yi a kumatunshi. Take hankalina ya tashi ainun.
Sani kukan me kake yi haka, me Kailan ya faɗa maka?" Na tambayeshi a jere, dai_dai shigowar motar su Dauda.
Ka share hawayenka kar ka ɗaga ma ƴan uwanka hankali. Sani bazan taɓa iya bama Kaila dama ko wacce iri bace. Ba kaila kaɗai ba, ni ɗinnan da ka ganni babu batun aure sam a gabana, ina da tarin burika masu girma da nake son ganin na gabatar. Yanzu haka inason in ware office a cikin gidana na sauraren koken Zawarawa, da matan da suke shan wahala a gidan mazajensu. Dan haka kama dena damun kan ka kaji ko?" Murmushi yayi mun yace.
"Nagode ummata ina alfahari da kasantuwata a matsayin ɗanki. Ina kishinki umma." Dariya mu ka yi dukkanmu. Dauda da ƙannenshi suka ƙaraso.
"Wai Innata shi wannan yaron nunawa yake yi yafi kowa sonki ne? Nifa ban yarda ba wallahi duk bugun zuchiyata da sonki yake bugawa Innata. Sani naga yana shirin ture mun matsayina." Su Amina suma su ka ce ai suma basu yarda ba. Tuni yarana ababen alfaharina suka ɗebe mun damuwar dana shiga. Ina dariya nace.
Dukkanku Umma tana sanku. Kune farin cikinta kuma, Dauda kai da Sani zaku je Jos gobe su Amina su harhaɗo kayansu, ku kawo mun su Kano. Zan ci gaba da riƙesu" Tsantsar murna da farin cikin da na gani a idanunsu bazai musaltuba sam. A guje su Amina da su Sulaiman suka shige cikin gidan. Dauda kuma ya ja Sani zuwa gidan abokinshi a maƙota, acan zasu kwana. Na juya zan shiga ciki kenan na ji an ambaci sunana.
"Barista Shanono" Cak na tsaya ni ban shiga ba, ni kuma ban juyo ba"



Kaila:.


Tunda suka shiga ɗakin hotel Salima take huhhura hanci, ƙiris take jira kaila yayi mata magana ta sauke mishi kwandon ruwan masifa da bala'inta. Tunda ba raga mishi take yi ba. Tun a mota take sa ran soma bata haƙuri gami da rarrashinta amman abun mamakin bai ce da'ita komai ba har zuwa yanzu. Nutsuwarshi da tunaninshi ma baya tare dashi. Sakkowa tayi daga kan gado ta ja dogon tsaki ta shige banɗaki. Da idanu ya bita cike da karantar yanayinta. Ajjiyar zuchiya ya sauke mai nauyi tare da lumshe idanunshi, ji yake yi tamkar yau ne ya soma shiga sabuwar soyayyar Shanono. Ko a mafarke_mafarken Shanono da ya saba yi baiyi tunanin ganin shanono a haka ba. Ta rikirkita mishi lissafi, ya rasa gane kanshi gami da kasa mallakar kai. Shanono ta zama babbar mai aji wacce ta wuce tunani da hasashe. Takunta, da ƙamshinta yau su suka fi komai ɗimautashi. Daren farkonshi da shanono yake hangowa, da irin alƙawarurrukan daya ɗaukar mata na mallaka mata kanshi, da bata farin cikin da zai mantar da'ita ƙuncin da take ciki. Tunaninshi ya dawo baya wata rana ya dawo daga gajeri jikinshi duk baƙin mai ya shigo ya iske shanono a zaune a bakin murhu tana girki, shi dai yasan bai kawo abinci ba, bai kuma ɗauki sisi ya bata da zai fita ba. Tana fama da tsohon cikin Sani da ƙyar take turawa.
"Shanono ina kika samu kuɗi har kike yin girki?" Tambayar daya jefeta dashi kenan. Ita kuma Shanono bata bashi amsa ba, ta ɗakko tire ta zuba musu jallof ɗin taliya, suka shiga daga ciki, wayam yaga babu ko katifa a ɗakin sai ledar tsakar ɗaki, duk kayan ɗakin babu su babu dalilinsu. Kallon tuhuma yai ma Shanono wacce take miƙo mishi damin kuɗi.
Tsakin da Salima ta doka ne yasa kaila ɗagowa da sauri ya dubeta.
"Wai in tambayeka me kake nufi ne, sakin wata daga cikinmu zaka yi ka dawo da uwar ƴaƴanka koko Yaya, ya ma akayi har ka saketa yanzu kuma kake son yin zawarcinta?" Ta jero mishi tambayoyin cike da tsiwa har tana fitar da ƙwalla. Tsuru Kaila yayi yana kallonta, yana ji kamar son Shanono zai iya sanadinshi kafin wayewar gari.
"Tanjirin ya kamata ki shiga taitayinki, ki kuma san waye a gabanki, dan na fuskanci kishi na shirin sanyaki a cikin uku. Kar ki ce zaki tsolma kanki cikin sha'anina da Shanono, zai fi miki tsayawa a iyakar matsayin da kike a wajena. Zancen dawo da Shanono, ko sakin wata mace kuma wannan duk a hannuna yake. Ke baki isa kin hanani abinda nayi ra'ayi ba" Ai Salima sai ta dira a wuyan Kaila, cikin ihu da tafi ta shiga yayyarfo mishi munanan maganganu marasa daɗin ji. Shi kuma yana zaune yana kallonta yama rasa me zai ce mata. Da dai yaga kuka take yi sosai, babu shiri ya shiga aikin rarrashinta, da ƙyar tayi bacci kanta na saman ƙirjin Kaila. Shi kuma sake dulmiya kanshi yayi a tunani. Yana son keɓewa da shanono domin su tattauna kafin ya bar garin Bauchi. Amman Sani na son hanashi rawar gaban hantsi, ya jima da sanin yaron kishin shi yayi yawa, kuma zai iya yin fito na fito dashi akan uwarshi. Shima kuma ganin Shanono yasa yana jin babu abunda zai iya gibtawa ya sake rabashi da farin cikinshi, koma waye, balle Sani ɗan cikinshi ƙaramin alhaki.........✍🏻[19/10, 8:54 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU


LAMBA TA 12



SHANONO:.
Shiru banji halamar taku ba, kuma banji halamar motsin rai ba. Da sauri na juyo nayi tozali da JEGA a tsaye ya harɗe hannayenshi a ƙirjinshi yana ƙaremun kallo. Wani tuƙuƙin bakin cikine ya turniƙe mun

10 / 14