Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Love

Chapter   7 / 14

18K to 21K   out of 40.7K words

shiga Sabira ta kirawo wayata.
Ƙawata Sabira, kinsan tunaninki nake yi yanzu sai ga kiranki?"
"Babu wani nan lauya zance dai irin naku na lauloyi. Gani a Kano ni da Baban Mustapha shine dai nace bari in ji in kina gida sai ya saukeni a gidanki." Baki na washe nace.
Yanzu dawowata gidan kenan. Sai kun ƙaraso." Sallama mu ka yi. Na ajjiye wayar, a gurguje na watsa ruwa, na saka doguwar rigar atampa. Sai na shiga kitchen, ruwan shinkafa na ɗaura, muna da stew dinmu da Rahama tayi mana cike da naman kaji. Ruwan ko tafasa bai yi ba na jiyo muryar Sabira a tsakar gidan. Da sauri na fito na taryota muka shigo ciki. Sai dariya muke yi.
"Shanono Allah ya yarda kinga yadda kika dawo kuwa? Babu mai cewa uwar takwas ce wannan. Rayuwa ta yi kyau. Naji daɗin ganinki Shanono" Zaunar da'ita nayi a kujera, rabonmu da juna shekara biyu kenan. Baban Mustapha duk sanda zai shigo Kano tana biyoshi tazo wajena, mu yi hirar zumunci, mu yi dariya da nishaɗi. Ruwa da lemo na kawo mata na dure a gabanta
Sha lemo, kinsan Kano akwai zafi ba irin Jos ba. Malama ya ɗalibai?" Malama ce Sabira a Al bayan tana koyar da matan aure ilimin hadisi. Sai da ta shanye lemon kafin tace.
"Ɗalibai munata fama dasu. Ya kotu ƙawata?"
Muna ta fafatawa, Yaya Use ma tana hanya. Ƙila daga nan ta wuce Kaduna dubo yaran nata" Zama Sabira ta gyara, nasan magana take son yi, sai na bata hankalina"
"Tani wai sai yaushe zaki bari yaranki su saki a idanunsu ne? Ni ina ganin lokaci yayi daya dace ace kin kaima yaranki ziyara. Ko dan hankalinsu ya kwanta. Kullum fa Sani a cikin tunaninki da ba Mustapha labarinki yake. Bana faɗa miki ajinsu ɗaya a jami'a ba. Yaran suna cikin raɗaɗin rashinki. Duk da fa uban na ƙoƙarinshi a kansu, ƙarfinshi kawai akafi. Su Amina har yanzu Shamwila bata sarara musu ba, damba sun girma kuma sune manya a gidan. Ni na kwana biyu ma ban kira wayarsu ba. Zan kira Amina anjima ki ji muryar su, hankalinki ya Kwanta. Ko su Inno a yanzu yana da kyau su san inda kike ai ko, ko dan halin mutuwa.?"
Hakane Sabira. Akwai abunda nake jirane shi yasa kika ga banje dubo yara ba. Kuma inajin labarinsu a wajenku, duk da banso barinsu Jos ba dan nasan kuna yawan kai musu ziyara. Batun su Inno kuma kinga na sai musu ƙaramin gida anan garin, na zuba musu kayan katako, inaso nima in je in tawo dasu, amman tunanin yanda zan tunkari Baffa nake yi Sabira. Da ciwon rashin yaran nake kwana in tashi." Sabira ta dubeni tace.
"Yanzu ba da bane. Nayi imana su kansu su inno zasu yi farin cikin ganinki a wannan yanayin. Ina kuma ga kice musu kin siya musu gida su biki ku tawo, kinsan da gudu Baffa zai yafe miki, girma ya kuma sakko mishi baki ganshi ba. Yarannan ki duba lamarinsu Shanono." Murmushi nayi na kawar da zancan ta hanyar tambayarta maƙotanmu na layinmu na da, dan bana ƙaunar abunda zai sa in dinga tuno Kaila" Dariya tayi mun. Misalin shiddan yamma sai ga Yaya Use ta shigo, Sani na biye da'ita. Idanu muka zuba ma juna ni da Sani. Hawaye yaron yake zubarwa sosai, ya kasa furta komai. Ji nake kamar in je in kamoshi in rarrashi abuna, amman sai naji ƙafata na rawa kamar wacce tayi ƙarya.
"Sani ga Tani nan ka ganta. Na cika maka alƙawarinka. Tani Sani tun bayan fitanki gidansu yake cikin ƙunci da damuwa, ko walwala sam bayayi. Yarannan ya kamata ki bayyana kan ki su ganki Tani. Dama ance mai haƙuri bai iya fishi ba" Hannu na miƙo ma Sani, da gudu yazo inda nake maimakon ya rungumeni sai ya tsigunna a gabana ya kama mun ƙafafuwana ya sake sakin kuka. Sai na tuno ranar dana tafi na barsu a tsugunne a gaban Kaila suna bashi haƙuri akan karya barni in tafi. Hawayena na share cikin nuna dakiya nasa hannu na rikoshi, na ɗan tallafoshi zuwa kafaɗata, ina dukan bayanshi halamar rarrashi.
Yi shiru Sani na. Ba gashi ka ganni ba? Ban gujeku dan bana sonku ba, na barku ne dan bani da yanda zanyi Sani" Yaya Use tace.
"To ku zauna kukan dai ya isa haka Yaron Tani" Murmushi yayi kawai ya sauke kanshi ƙasa. Girman ɗan mutum babu wuya, jibi Sani yanda ya zama babba, da ganin suturarshi kasan ɗan masu kuɗine, ga sumar fulani lub_lub a kanshi. Sabira tace.
"Yaya Use kin kyauta. Kinsan Allah maganar Sani nake yi mata yanzu muka jiyo sallamarku. To Alhamdulillah naji daɗi da kika tawo da Sani ya ga mahaifiyarshi, a ƙalla ya tsayar da zuchiyarshi yayi karatunshi." Abinci na zubo mana a tiran silver dukkanmu, muka gyara zama, kowa ya soma ci. Sani daya kalleni sai murmushi. Duk duniya babu abinda nake so sama da ƴaƴana, na ji daɗin ganin Sani cikin shigar kamala.
Ya su Shafi'i da Sulaiman, da su Salis duka?"
"Suna Kaduna Umma. Ni kaɗaine a jos nake karatu Sulaiman yana karatu a Bauchi, duk sati Yaya Dauda yana zuwa wajena a makatanta. Har Kaduna yake zuwa ya kaima su Amina kayan sawa" Farin ciki ya sake ziyartar zuchiyata, nayi dariyar da na jima banyi ma irinta ba. Ana cikin haka sai ga Rahama ta shigo. Sani ne kawai bata taɓa gani ido da ido ba. Amman ta sanshi a waya. Cikin sakin fuska ta marabcesu, dan Rahama akwai kirki sosai. Bayan mun idar da sallar isha ne Yaya Use ta jamu ɗakina ni da Sabira, mu ka bar Sani a falo yana kallo hankalinshi kwance.
"To ni dai abunda ke tafe dani abu biyu ne Tani. Ki ma Allah ki bayyana kan ki yaranki su ganki, ko ba gaskiya ba Sabira? Nayi magana da Habiba Bala ashe bata ƙasar ma wai taje wani kos, ita ma tace in ta dawo zaku zauna ku tattauna. To Sani da kike gani yana da ƙulafaci da bin diddigi har sai da ya gano nasan inda kike. Da kuka yazo mun, babu shiri na kawo shi gashinnan. To Habiba Bala tace shi kanshi Dauda abun na taɓa mishi aikin shi Tani, dan ma shi yana da uwa madadinki. Ki yi haquri Tani." Suka hadu su kaita daddanneni har sai da na amince week end zan shiga Kadunan in ga yaran. Sannan suka ƙyaleni.
"Magana ta biyu akan su Inno ne Tani. Saudiya fa suke son tafiya yawon bara Inno da su Indo da Habu. Wata almajirace tai musu hanya. Baffa yana kwance kwana biyu ba lafiya. Mun je ni da Karime mun yi ma Inno roƙon duniya kar ta tafi taƙi. Shikenan rayuwarsu su a yawon bara zata ƙare, baki ga Baffa yanda ya tsofe bane, ina laifin ma su koma shanono su zauna tunda suna da ɗaki acan. Banga amfanin wannan barar da suke yawon yinta ba. Tun muna yara ake abu ɗaya har zuwa girmanmu ni na rasa ina zan sa kaina Tani. Daga ni har Yaya Use hawaye muke zubarwa, iyayenmu a wannan bakar rayuwar ta yawon bara muka taso muka tsinci kanmu tare dasu, ta sanadiyyar bara babu abinda bamu yi ba, babu abunda bamu gani ba. Rayuwar mabarata da ƴan jagora cike take da ƙalubale mai tarin yawa. Ina roƙon Allah ya kawo mana shugaban ƙasan da zai haramta bara a Najeriya baki ɗaya kowa ya huta. Sabira cike da tausaya mana mu duka tace.
"Tani tun wuri ki je ki kwaso Inno da Baffa, su Indo su samu su shiga makaranta. Ko rayuwarsu zata yi haske. Nasan duk wannan aikin da kike ci tuƙuru sabida su Inno kike yi. Baffa jikinshi akwai rauni sosai."
In sha Allah, jibi babu aiki a gabana zan kama hanyar Jos, kafinnan an gama yi mun plate number na sabuwar mota dana siya ban faɗa muku bane da naso sai an gama komai. Suma yaran zanje su ganni zukatanmu suyi sanyi" Yaya Use tace dani.
"Amman Tani kina shan magungunan hawan jininki dai ko, sannan ki dinga kiyaye duk abinda zai tashi hankalinki. Oh Tani nayi miki murna da rayuwarki ta samu canji sosai." Mun daɗe sosai muna tattaunawa, ko da na leƙo falo Sani har yayi baccinshi akan doguwar kujera. Na jima a kanshi nayi tsaye ina jin wani irin san shi na motsa mun raina. Sani tun yana yaro daban yake shi a cikin yarana. Da Dauda ya shigo rayuwata saina kasa iya tantance wa yafi ƙulafacina a cikinsu. Allah sarki Allah yai musu albarka, da ɗaukacin yaran musulmai baki ɗaya. Rabuwa da yara kana da rai yafi duk wani abun misali zafi da ciwo. Ta sanadiyyar damuwar rashin yarana ne hawan jini ya kamani, domin har kasa barci nake yi, ko inta firgita. Komawa nayi ɗakin Rahama acan na kwanta. Yaya Use da Sabira suka kwana ɗakina. Washe gari tun wurwuri na shirya tsab, yau shigar baƙaƙen kaya nayi daga sama har ƙasa, ƙaramin hijabinane kaɗai fari, hannuna na dama sagale da jaka, na hagun kuma sagale da rigar lauyoyi. A kurguje na kurɓi shayin dake hannun Sani, nayi musu sallama na fice a guje. Harna fita na jiyo muryar Sani a bayana.
"Umma" Da sauri na juyo na zuba mishi ido, shima ni yake kallo.
"Umma kinyi kyau sosai, kin fi ko wacce mace a duniyarnan kyau. Allah ya tsare Barista Tani Shanono Naroro" Murmushi nayi tare da lumshe idanuna. Haƙiƙa nayi kewar yarana sosai.
Sani nagode sosai, ina alfahari da samunku. In na dawo daga office zamu zauna ka ban labarin ƴan uwanka kaji ko? Sai na dawo" Sani bai gushe a tsaye ba har sai da Ɗan sahunmu ya ɓace mishi. Ina ganin hannunshi ta mudubin gaban ɗan sahu yana mun adabo ( by by).......✍🏻[17/10, 1:23 p.m.] +234 803 831 1474: NA FADO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU


LAMBA TA 9


Motar mu ta tsaya a daidai ƙofar gidan dana siya ma su Baffa. Yaya Use tana riƙe gam da hannun Baffa suka fito a mota, Inno, da Yaya karime suma suka fito, sai nima na fito. Na buɗe gidan muka shiga. Inno sai washe bakinta take yi, na buɗe ƙofar falon nasu muka shiga baki ɗaya.
Inno Baffa ku zauna ga kujerunan. Yaya Use kinga gidan yayi ko?" Sai da ta zaunar da Baffa tukunna tace.
"Masha Allah Tubarkallah. Gida yayi kyau Tani Allah ya saka miki da aikhairi. Kamar yanda kiketa ƙoƙari a kanmu Tani Allah yasa ƴaƴanki su zame miki ni'ima a rayuwarki. Inno, Baffa wannan gidane da Tani ta daɗe tana yin asusu dan ganin ta siya musamman domin ku. Allah yau ya cika mata burinta gaku a gidan da Tani ta siya muku." Tana kaiwa nan ai sai dukkanmu kowa ya soma sharar ƙwalla, harda Baffa da Inno wanda mamaki, ko farin ciki suka hana su cewa uffan. Yaya Karime tace.
"Gaskiya Tani kinyi namijij ƙoƙari sosai. Ji rayuwa kamar ba zata kai miki ba, amman ji beki yanzu kin zama tauraruwa a cikin dangi. Allah yai ma zuriya albarka.' Baffa ne ya amsa da cewa.
"Tani Ubangiji Allah yai ma rayuwarki da rayuwar iyalanki albarka. Yau Tani kece kika ciremu a ƙangin da muka tsinci kanmu. Kinga uwarku gata saudiyya take son tafiya ta barni yawon bara. Dan taga ƙarfina ya ƙare. Ni da duk inda zani nake riƙe hannunta muje, amman ita tsallakewa zata yi ta barni. Yawon bara har kwatano munje, a can akai cikin Karime, lokacin Use na hannu." Inno ta doka mishi harara tace.
"Ana zancen farin ciki zaka dagula mana zukata Baffa. Tani mun gode Allah yai miki albarka. Kiyi haƙuri da tsangwamarki, da ƙyamatarki da muka dingayi a baya, lokacin da gidan aure yaki yi miki dadi. Ɓatanki ya taɓa mu ainun, ni dai dashi nake kwana nake tashi. Da tafiya naga tanata tafiya na fidda rai da ganawarmu na zaci sai a darussalam"
Babu komai Inno. Wannan abunda nayi muku shine kaɗai abinda zan iya muku hankalina ya kwanta. Bana ƙaunar ganinku a kwararo, cikin zafi, ruwa, da iska kuna bara. Lokaci yayi da zaku zauna ku nutsu waje guda ku bautama Allah yanda ya dace. Zan ɗaukar muku malama da zata dinga zuwa tana koyar daku addini har gida. Dan akwai gyara a alwalarku, sallarku, da karatun sallar kanshi. A irin wannan shekarun hutu kuke buƙata ba wata wahala ba. Inno babu maganar zuwa saudiyya bara." Dariya mu ka yi dukkanmu.
"Sai abinda kika ce yarinyar kirki" Dariya muka sake kwashewa dashi. Muna cikin haka sai muka jiyo sallamar su Goggo Ige, su Goggo marka, Goggo mai riga, Da su kawu Junaidu. Da ƴan uwan Inno, su Goggo Azumi, da su Kawu Mati. Bus guda su ka yo. Ni na fita na sallami mai Bus ɗin. Kuma munyi dashi da yamma zai dawo ya mayar dasu. Yaya Use ce ta yi musu bayanin na siya ma su Inno gida ne. Kai Alhamdulillah Wallahi ranar an shi mun arbarka fiye da tunanin masu karatu. Ige tace.
"Naroro bara ya ƙare. Muma in Shanono ta ɗau zafi sai mu zo mu huta anan." Inno tace.
"Ke da ba miji ba Ige dama zamanmu mu ka yi na samu abokiyar taɗi ai ko?" Nan fa kowa ya ɗauka da cewa.
"Kuma wallahi hakan yayi" Kawu mati yace.
"Gaskiya Tani kinyi kokari sosai, Allah kaɗai yasan irin ladan da kika samu. Kinga su Yusuf kai tsaye sun san inda Baffa yake a matsayinshi na babba. Duk wata matsala za'a kawo mishi gabanshi. Allah yayi albarka. Su Inno yawo ya ƙare, har aka gama yawon bara banga wani abun da kuka tara ba. Mu kuma ana ce mana mabarata kuɗine dasu." Baffa cikin karfin murya irin na makafi yace.
"Wata gigitacciyar sata akayi mana a wata anguwa a legas mai suna agege unguwace ta hausawa. A funfata sai da ɓarayinnan suka samu million biyar. Inno kuma million uku ne cib a lalitarta cikin leda, duk suka yashemu. Wadannan kuɗaɗe mun daɗe muna tarasu amman ɓarayinnan suka durƙusar damu" Baffa sai kuka shi da Inno. Duk lokacin da suka tuno da wannan satar to fa sai sun zubar da hawayensu, nima rana ce da bazan manta da'ita ba abadan. Ana cikin rarrashin su Inno wayata tayi kuka, Sani ne yake kira ƙila sun shigo Kano ne. Ina ɗagawa kuwa ya sanar dani shigowarsu Kano kenan. Da tambaya ana nuna musu hanya har suka iso ƙofar gida. Ina tsakiyar dangina yarana suka shigo da sallama. Cike tab idanuna yake da hawaye na kura musu idanuna. Amina da su Shafi'i sai murna da ihu. Hauwana da Salis ɗina kuwa basu gane ni ba sam. Dauda gefe ya koma ya fashe da kuka. Ya zama saurayi sosai harda ƙasumba ya ajjiye. Kyawun yarana ya fito sosai, kowa ya girma gasu cikin kyawun shiga da kamala. Bani kaɗai naji sha'awar wannan yara ba. Kab falon babu wanda bai yaba dasu ba. Dauda kuwa sukaita mamakin girmanshi ya zama babban mutum. Gefena duk suka zauna, na ɗaura Salis a kafata. Dauda sai kallona yake yi. In suka haɗa ido da Sani sai inga ya banka mishi harara. Rahama tayi ma masu abinci jaroranci suka shiga shigo da abinci. Masa nasa akayi, da jallof ɗin shinkafa wacce taji kayan lambu da tsokar nama, sai abun sha, da ruwa. A wannan rana zukata cike suke da farin ciki marar yankewa. Sai yamma lis mai Bus ɗin daya kawo su Kawu yazo ya kwashesu, bayan na bibbi kowa da dubu biyar biyar, na rakasu har bakin motar ni da Sani da Dauda da suka maƙale mun.
"Tani tunda Dauda gashi a Kano, ki daure ki rakashi ya duba dangin mahaifinshi su ganshi shima. A daure ai komai ya wuce, kune a sama kin yi ma Narani tazara mai yawa. Yanzu kam aurenki ai sai wanda ya shirya. Murmushi nayi nace.
"To Goggo Ige in na ɗan rarrage aiyukana zan je in sha Allah in rakashi ya gaishesu. Amman ba wannan zuwan ba, sabida jigilar asibitin Baffa ban je aiki ba, aiki ya tarumun a office " A haka muka rabu dasu kamar ba zamu rabu ba. Hannun yarana na ja muka koma ciki, ina zama yaran duk suka dawo kusa dani.
Yaya Use kinga Salis, da Hauwa sun mance dani fa" Sulaiman yace.
"Da Salis da Hauwa kullum sai sun yi kukanki Ummanmu. Gaskiya ummanmu muna sonki, duk munyi kewarki. Babanmu yace in mun zo mu gaisheki sosai." Amina tayi zaraf tace.
"Ya ba da sako ma yace in baki hannu da hannu Umma. Umma mu fa ba zamu koma ba, dake zamu zauna" Ni dan tsantsar farin ciki ma duk wanda na kalla sai inji kamar nafi son shi. Su Baffa sai nan nan suke da su Sulaiman. Abun gwanin ban ƙawa. A gidan dai muka kwana baki ɗaya, washe gari kuma ya kasance asabar ne, in monday tayi sati na biyu rabona da wajan aiki, komai nawa ya tsaya cak. Da sassafe sai ga Rahama tazo ganin yara, Mai hula ma Rahama bata jima da shigowa ba sai gata.
Kai wannan sammako haka, sai kace kun tashi dani a mafarkinku?" Da zolaya nake maganar. Mai Hula tace.
"Ni tun daren jiya da kika faɗa mun yaranki sunzo ganinki, ba da ban mai gidan bazai barni in fito ba wallahi da a daren zaki ganni. Ga yara Tubarakalla, kyawawa dasu, ashe kina da samari manya ma, Shanono ke fa ba ta yau bace kyan jikine dake." Dariya nayi mata kawai.
Kajita yarane fa tsayin dai kafane dasu. Rahama ta harareni tace.
"Wadannan samarin da zasu iya ma mace ciki kike kira da yara Shanono? A gaisheki, gaskiya kin kyauta da kika dawo da iyayenki kusa dake, gida yayi kyau sosai." Yaya Use ce ta fito musu da abincin karyawar da nasa su Dauda suka fita suka siyo mana.
"Shanono wannan itace Yaya Use ko, me yawan kiranki in kina office?" Dariya muka saka ni da Rahama.
"Itace, ai Yaya Use akwaita da kiran waya." Itama Yaya Usen dariya tayi kawai ta koma ciki. Su Mai Hula suna tafiya muka fita cefane, ni da Yaya Use da Yaya Karime, da Sani da Dauda.

7 / 14