iyayin komai da wayar idan sukaganta nande muka shiga zilimin yanda za muyi muna cikin haka matar ta dawo dauke da wata yar qaramar akwati ashe duk taji tattaunawar mu tace ku kwantar da hankalin ku zanyi qoqarin dauko maka wayar ka zansa a bincika dakin kafin su ankare da wayar awajen ina ka jefar yace wlh ni kaina bansan ina bane kawaide adakin da aka kwantar da ita tace me no.dakin yace ni wallah bansani malam yace nide naga ansaka biyar ajiki qofar dakin watakil ko itace number matashiyar budurwa tace ok ba damuwa za aganta yanzu da kamata mushiga da ita can dakin dan tana bukatar taimakon gaggawa naga tana cikin wani hali watakil sun tosheta shiyasa bazata taba haihuwa ba har sai abun cikin ta ya mutu da sauri suka kamata dan zuwa lokacin ma tanade kwance kawai itakadai tasan abun da take ji saboda da azabar datakeji tafi qarfin kanta suna shiga ta dakin aka kwantar da ita akan wani gado me kama dana asibiti qoqarin fita yayi amma sai nadeeya ta ruqe hannun sa tace ka tsaya dan Allah ka yafemun duk abun da nayi maka nima na yafe maka kace wa su ummi ma su yafe min bana jin zan qara wata rayuwa tare daku nasan qarshena yazo hannu yasa ya rufe mata baki yace kidena fadar haka dan Allah in sha Allah ba abun da ze sameki baza ki mutuba zaki tashi muci gaba da rayuwar mu mamar da tare da danmu 'yarmu kinji bata bashi amsaba sai kawai hawaye dake zubowa daga idon ta tare da cize baki sakamakon dubatan da matar take sosai matar ta shiga bata taimako amma ba wani canji ganin hakan yasa kawai ta yanke shawarar tayi mata cs amma bata faraba duk saida ta tambayi yardar mu gaba daya muka ce munyi yarda tayi mata haka ta shiga shirya kayan bukata dake babbar likitace babu abun da bata dashi acikin gidan saboda tana duba mata da yawa aciki ba komai take zuwa asibiti tayi ba wani abun agida take yi saboda yafi mata sauki cikin qanqanen lokaci tayi tahada komai da zata bukata sanna tacewa sameer ya fito ya bata waje bayan da ya iya haka yafito ya barota aciki tana kuka tana kiranshi ya tsaya ayi komai agabansa amma matar tace aa tayi hakuri baze yiyu ayi agabansa tayi hakuri ana gama mata sai yadawo nande ta hakura ita kuma ta fara aikin ta yanda yakamata mukuma muna tsaye abakin qofar dakin muna jiran fito warta muna yi mata addu'a,
Munkai wajen awa awajen muna jira sannan daga baya muka fara jiyo kukan jariri gaba dayan muka daga hannu munayiwa Allah godiya saida tagama shirya babyn tare da nadeey ta canza mata kaya komai de ta gyare gurin kamar ma ba haihuwa akayi ba sannan tace mana mushigo da saurin mu muka shiga ciki har muna 'yar rige rige muna shiga muka ga nadeeya kwance kan gadon amma idon ta biyu kuma yana kan mu kamar ba wacce ta haihuwa ba matar kuma tana riqe da jaririyar a hannun ta qarasawa mukayi kusa da ita muna kallon jaririyar me kama da ubanta dan batayo kamannin mahaifiyar ta ba kwata kwata hannu nasa sannan ta miko mana yar tubarkallah da ita dan alokacin da kibar ta kamar ma bada ga ciki ta fito ba bul bul gata fara sol kamar zabiya daman kuma mahaifinta shima farine sosai sai ta dauko har farin mahaifin nata babu inda ta barsa kamar su daya sak,
mu muna ta murnar ganin yarinya amma shi yana can wajen matarsa ko takan yar ma bebi ba yana can yanayi mata sannu ita kuma inbanda kuka ba abun da takeyi rarrashin duniya yayi mata taqi yin shiru sai da qyar da saka bakin mu sannan tadan tsagaita da kukan yarinyar muka mika mata ta kalleta sannan tabawa sameer ya karbeta yana qare mata kallo sannan tace kayi mata huduba kasaka mata sunan da kake so alokacin yayi mata yace yasaka mata sunana KHADIJA sannan yace za aringa kiranta da sunan da kika cemin kinaso yama sunan dan dariyar qarfin hali tayi sannan tace Ameesha inason sunan saide kuma bazan rayu da itaba bare har inkirata dashi saide ku kuringa kiranta dashi ina ta girma kuce ina sonta taqarasa fada tare da share hawayen da suke zubomaya hakuri muka shiga bata muna cewa tadena fadar irin wadannan abubuwan in Allah yayarda zata rayu da 'yarta kamar yamda take so,
Sai kawai ta girgiza mana kai sannan bazan taba rayuwa da itaba tafada tana kallon yarinyar tare da cemana banyi niyar gaya muku ba amma yakama ta kusani kafin intafi inbarku dan Allah ku kula min 'yata gashi nan na baku amanar ta ku kula min da ita tana da makiya tun tana ciki batazo suniya ba ma akeso akasheta saboda sunce basa san zuwanta duniya sunaso ta mutu tun acikina sai kuma gashi Allah beyi ba gashi tazo duniyar kuma in Allah ya yarda zata rayu ko suna so ko basa so sannan muyi saurin barin garin nan soboda suna tare dakai makiyan ka suna jikin ka kayi saurin raba kowa dakai kar kasake kowa yaqara sanin wani sirrin naka ta hakanne suka gano ko kai waye kuma baza subarka da ranka muddin suka samu abun da suke so awajen ka daga baya kuma zasu rabaka da duniya anna take gaya mana ashe itama wani mutum yaje mata lokacin da baya nan sun gargadeta sannan sukace mata wannan abun bada gashi bane abun ya faro tushe ne daga mahaifiya sa taga ya masa kuma duk wanda ya rabeshi shima zai rasa ransa ba a ason ya rayu daga shi har mahaifiyar sa harma wannan dan dake cikin ta da kuma wanda ya shiga cikin rayuwar su saida mukace meyasa bata gaya mana tun farko ba tace saboda sunce kar nafada kuma bataso mushiga wani tashin hankalin shiyasa ta roqe abun ta ita kadai bata san kuma muma sun gaya mana sanna ta dora dacewa yanzu naga ya muka dan kuqara kula da duk wanda zakuyi mu'amala ni yanzu tawa ta qare muka ce tadena fada in Allah ya yarda zata rayu kamar yanda yarta zata rayu sai kawai tayi mana mumushin qarfin sannan tace kunsan me yasa nace muku dole in mutu maka ce aa tace saboda sunyi min allura tun lokacin da kuka kaini asibitin agaban idona suka hada alluarar da poison ina roqon su kar suyi min amma saida sukayi min kuma allurar idan akayi ta ba alokacin mutum yake mutuwa ba tana iya kaiwa awanni masu tsawo ajikin mutum kafin daga baya tafara aiki ajiki haka naji sunce shiyasa nake gaya muku haka dan bantaba ma tunani zan kawo iyanzu ba araye tana gaya mana tana kuka mun qara shiga wani tashin hankalin dajin wannan batun nata da bamusan dashi ba bayama da tace sunriga sunyi mata allura shima anasa bangaren ba qaramin tashin hankali ya shiga ba tambayar matar yayi ko da akai abun da za ayi allurar ta tsaya tace wlh tunda sun riga da sun dade da yimata be baza a iyayin komai ba saboda qa idar allurar ma bata wuce awanni biyar bata fara aiki ba gashi ita har tafi awa gomama ajikin ta kafin ace za aje wani asibitin ma zata iya qarasawa saide kawai muyi mata addu'a duk da haka be yarda ba yace yaji kawai mushirya muje inda tasan za a iya yi mata maganin ta qara tabbatar masa ko sunje babu abun da zasu iyayi akai amma yace shifa be yarda kawai muje itama nadeeya tace ya barshi dan Allah basai sunje ko ina ba itama yace mata aa gaba dayan mu babu wanda becemasa ya hakura ba amma yace shifa sai yaje in baza mu taimaka masaba sai yatafi shi kadai jin hakan yasa muka amince gaba dayan ma ya daukota muka fito waje amotar ta muka qara shiga gaba dayan kuma har zuwa wannan lokacin yarinyar tana hannun daga uwar har uban ba wanda ya nemi da yaganta kowa da abun da yake damunsa haka muka nifi wani asibitin da saida mukayi tafiya me nisa danni kaina bansan ina muke nufa ba saida mukai wajen awa daya muna tafiya sannan muka iso wani asubiti dan lokacin ma wajen qarfe biyar na dare ana daf da kiran sallar asuba muka qarasa muna zuwa aka karbeta saide kuma kamar yanda mukayi tunani hakan ce ta faru muna zuwa rai yayi halinsa tun kan a shiga da ita dakin haka mukayi sallah muka dawo da ita amma abun mamaki sai ta nufi wani gidan damu daban bade mu tambayeta muka bita gidan nan made babu kowa sai ita kadai wajen qarfe goma na safe akayi jana'izar ta ba mutane da yawa sai 'yan tsiraru da shima malam ne yayi qarfin gayawa wasu mutanen aka dan hadu akayi mata sallah akaita gidan gaskiyar ta kwanan mu wajen uku agidan tare da mata kwatsam kuma sai muka wayi gari babu wannan matar da har zuwa lokacin bamu taba tambayar ko ita wacece ba qarewa ma ko sunan ta bamu taba tsayawa mun tambayeta ba saboda bama cikin kwanciyar hankali haka muka cigaba da zaman mu mukadai sai kuma muka fara tunani barin gidan dan bamusan ko wani abun ta shirya mana ba tunda batayi mana sallama ba kuma gashi yau wajen kwanan mu biyu amma bata dawo ba hakan yasa muka fara shirin barin garin da bamu san sunan garin ba ma gashi babu kudi agurina zuwa yanzu kudin da na fito dashi duk yaqare akan siyawa jaririya madara saboda akanta muka dorata inda Allah ya taimake mu gidan a kwai komai babu abun da zamu bukata murasa bangaren abinci akwai komai a kitchen tunda amma duk da haka bamu da kwanciyar hankali saboda shi kansa sameer munkasa gane kansa tun bayan rasuwar sa bashida aiki sai kuka sai kuma yadau 'yarsa ya rungume yana sambatu ganin hakan yasa muka fara shirye shiryen barin gidan aranar da zamu tafi munfito daga gidan kenan kawai saiga jiniyar motar 'yan sanda tsayawa mukayi muna kallon su da mamaki suna zuwa sukace u are under arrest mr.sameer zaro ido yayi yana kallon su yace me nayi kuma sukace idan munje can zakayi bayani ina kuka na shiga roqonsu dan Allah suyi hakuri su fada mana abun da ya aikata da suke son tafiya dashi dayane daga cikin su yace hajiya daga banki ne aka turo mu sakamakon hakin din makuden kudaden da yayi yakwashe su batare da saninsu ba ya diba ne amatsayin sata kuma ya gudu tun kwana biyu da suka wuce ake nemansa ba asame shi gaba dayan muka shiga basu hakuri da nusar dasu cewa wallahi bashi bane har labarin abun da yafaru damu da rasuwar matarsa da dalilin abun da yakawo mu nan amma duk sukace su basu san zance ba idan munje can mayi bayani haka muna ji munagani suka sakashi a mota suka tafi dashi mukuma muka hau motar haya tare da bin bayansu muna zuwa aka shiga dashi nande aka fara bincike inda har yakaimu ga shiga koto duk wata hanya da zamubi dan ganin mun karesa agane shine me gaskiya sunfi sun tosheta bamu da wata sheda tunda hashi qiriri annuna da wayar sa akayi aikin duk wata alama da za ta nuna shine sun bayyanata inda aka gano da number wayar sa akayi komai aka shiga asusun banki akayi danyan aikin nan dan haka dole yabiya duk yanda aka yanka masa sannan abiya kudin belin dinsa ko kuma za a kullesa a prison tsawon shekaru a ashirin kanaji kasan shirya masa hakan a kai da abun da suka shirya yi sannan akace muje mudebo duk wani abu da muka san yatara ya ajiye mukawo su da har zamuyi hakan sai kuma muka tuna da maganar nadeeya sunce dak sun rabasa da komai kafin su kashe shi tuna hakan yasa muka ji gwara ma kawai muyi shiru tunda ko mun basun hakan bazesa su rabu dashi ba dan haka kawai mukace musu mu bamu san inda koman sa yake ba duk da haka basu yarda tun alokacin suka sukace muje gidan a bincika muna farga ba mukaje gidan suka shiga bincika lungu da sako na gidan basuyi nasarar samun komai ba hakan sukace zasu daga gidan su siyar bamu da yanda zamuyi saboda bamu da wata shaida dazesa su yarda damu kwana biyu suka bamu muyi duk abun da zamuyi mubar gidan hakanne yasa muka yanke shawarar kawai mu kwashe koman mu kafin sudawo mubar garin idan mukaje muka ajiye sai mudawo mu fuskan ce su tun aranar muka kwashe duk wani abu da ya kwatanta mana cikin dare nafita nabar gidan naje na boye su sai washe gari na dawo gidan tun abakin hanyar shigowa nake jin muryoyin mutane acikin gidan nazata wadancan mutanenne suka dawo amma jin irin maganr da sukeyi nagane basu bane dan leqawa nayi tare da buya inda bazasu ganni ba,
wasu mutane nagani suna gaban malam kagaya mana inda suke malam yace wallahi gaskiya nagaya muku yanzu haka yana can sun qulleshi kuma sunce in ba abiya suba sai nan da shekara ashirin ze fito idan kuma baku yarda ba kuje zaku gani da kanku kudi kuma ni bansan inda komansa yake ba matar sa kuma da yadauka ta mutu ita da 'yar gaba dayansu sunrasu yau wajen sati daya kenan da mutuwar su gabadayan su iya abun da nasani kenan yanzu hakama gidan nan bana mu bane sunce zasu daga su siyar dashi bamu da komai wani ne ya kwada masa wani abu yace bakason ranka kenan muzaka gayawa maganar banza kana tsoho dakai zaka yi mana qarya waya ya zaro yayi kira bansan me akace masa ba naji yace bata nan sannan yagaya masa abun da malam yace masa bayan yayi shiru kuma yaqara cewa mutaho dashi to shikenan amma itafa matar bamu ganta ba da ita da jaririyar amma zamu qara bincikawa gidan ko zamu samu wani abun daganan sai aqona gidan gaba daya inma tana ciki ta mutu kawai shiru yayi sai kuma yace a gafarce ni oga subutar bakine hakan bazata faruba sai mun tabbatar basa ciki kafin muqona shi inyaso sai susiyar da filin gidan bayan nan sukayi sallama ya kashe wayar sannan ya kalli sauran mutum biyun dasuka zuba masa ido suna jiran suji me zaice sai yace oga yace mutafi dashi can kar aka sheshi har sai yafadi gaskiya zamuje mita azabtar dashi sukuma muci gaba da binciken inda suke mu nemosu duk inda suka shiga gidan kuma da sukace za a siyar a qonashi dayane daga cikin su yace kasan nayi mamakin guduwar mutanen nan duk yanda akai fa watakil dasa hannun su akan wannan matsalar bankin da tafaru su suka ahirya komai dayan yace nima su nake tunani amma nasan ai oga yana sane dasu zai binciko sune duk inda suke lokacin malam asume yake tunda suka buga masa abu be qara motsawa ba danni a tunani nama ko sun kasheshi bande saniba ahiga cikin gidan sukayi suka fara bincike ko ina amma basu ga komai ba saide sunga alamar inda na bude na kwashe abubuwan ciki hakan yaqara tabbatar musu da cewa dole mun kwashe wani abu agun dan haka suka fito suna cewa dole mu nemota komai yana wajen ta daya yace ku dauko sa muwuce jin zasufara fitowa yasa nayi saurin lallabawa nafice daga gurin ina fitowa Ameesha tasaki wani kuka da tashinta kenan daga bacci saboda tana bayana agoye sauri nayi naqarasa fitadaga gidan gaba daya can nesa da gidan naje na boye inda zan iya ganin fitowar su sauketa nayi na shiga rarrashinta nabata ruwa sannan tayi shiru cigaba nayi da tsayawa agurin ina jiran fitowar su,
Inaganin su suka fita da malam dan rashin mutunci ma aqasa sukajawo sa suka bude boot suka jefasa suka qulle sannan suka ja motar suka bar qofar gidan a tunani na ko sun fasa qona gidan dan har ina tunani komawa ciki sai kawai naga hayaqi na tasowa taciki ashe kafin su tafi saida suka bude silindar gas tare da kunna gas din sannan suka fita da sauri,
akan idona gidan nam yakama ci da wuta banbar wajen ba har saida naga yabkusa qonewa inaganin mutanen ana ta qoqarin kashe wutar amma taqi mutuwa bangama ganiba naja qafata nabar wajen wata unguwa nasamu ina tunani kuma yanzu ta ina zan fara wane irin taimako zanwa wadancan bayin Allahn mijina da kuma dana dake hannun su wazan fara taimakawa dan sai a lokacin nagane tabbas ba bakinsu daya ba masu yimasa wannan abun na harkar banki daban suma masu naiman sa daban dan bawan da yasan da zaman wasu kowa nasa harin yakai masa ba mutum daya bane yame farautar sa,
da qyar nasamu wata qasan bishiya da ba wanda zai ganni anan nake kwana wajen kwana na biyu agurin ba ci ba sha damuwa babu wacce ban shiga ba ga Ameesha kullum cikin kuka take min dan 'yar madarar da nake batama ta kusa qarewa kadan kadan nake bata saboda idan ta qare bansan a inda zan samo mata wata ba daman ba ruwa take shaba ahaka mukayi rayuwa tsawon kwana biyu da wuni gida danaga de ina niyar halaka kaina sabida yjnwar da nake ji ta gama kamani dan da qyar ma nake iya daga qafata nake tafiya idanuna kwa har rurrufewa suke yi saboda rashin bacci da yunwa haka nafito daga cikin dan dajin ga Ameesha abayana sai kuka take min ahaka nazo bakin titi amma sai na dan rufe fuskata da gefen mayafina saboda kar aganeni......,
***********************
*Azeema*
Tunda safe tagama shirin ta tsafa cikin matattun kaya da kana ganinta zaka san tana bukatar taimako saide idan kallon ta kayi sosai shine zaka ga jikinta ba na neman tai mako bane saide akayane kawai zaka fahimci haka sosai mama tayi mata fada akan ta kula sosai tare da yimata fatan nasara da addu'o'i ahaka sukayi sallama harda dan guntin