SARKI SAMEER BOOK 1 Hausa Novels

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   38 / 49

111K to 114K   out of 145.7K words

kula saba saleem yacewa shettima sir 'yan uwanta sun sani kuwa naga ba wanda yazo shettima yace masa a'a wlh inaso inyi musu surprise ne sonake sai tadawo nml tana magana tana tafiya tukunna ince suzo insuka zo sai suganta kawai to amma kuma kaga har yanzu shiru yanzu zuwan sam kawai nake jira yaqaraso sai yaqara dubata muji a inda matsalar take jinjina kai saleem yayi sannan yace hakan ma yayi zasuji dadi idan sukazo suka ganta lafiya lau hakan sai yafimusu akan suzo suganta a wannan halin gwara abari din tasamu lafiya sosai duk da nagama alamar kamar ba wani abu da yake damunta kawaide rashin maganar ne haka suka cigaba da tattaunawa acikin dakin kuma duk tana jinsu kuma tanaso tayi maganar amma sai ta daga bakin ta da niyar yin magana sai taji yayi mata nauyi, sunkai wajen minti arba'in agurin kafin sam yaqaraso asibitin yana shigowa be fito daga motar ba yakira shettima yace masa ya iso gashinan shigowa suna wane room shettima mane yace masa bari yazo ya shigar dashi daga nan suka katse wayar yana katse wayar yafito daga dakin yazo yasameshi a parking space tare suka jera gwanin birgewa suka shiga ciki dakin suka qarasa tare da sa kai suka shiga cikin dakin suna shiga saleem yashiga gaida sam hannu kawai yadaga masa tare da matsawa kusa da ita dan tattabata yayi kafin yace ke tashi bude idonta tayi aikwa sai tayi saurin rufewa tare da kamkamesu kamar taga dodo mamaki ne yakama shi ganin abun da tayi amma hakan be damesaba matsawa yayi daga kusa da ita sannan yadan kalli shettima yace kace bata jin magana gashi kuma nace ta tashi ta tashi yace eh tanaji amma bata iyayin magana yace daman ai bazeyiyu tayi magana koda yaushe ba   saboda bakin ta zeyi mata nauyi sai ahankali zata dawo daidai hakan ba wata matsala bane juyawa ya kumayi gurinta sai yaga tana matsi da hannun ta alamar tana son wani abun fahimtar hakan da yayi yasa shi qarasa kusa da ita sosai tare da dagata cak dinta ya zaunar da ita rumtse idon ta taqara yi jin yatabata harda dagata zamawa taqara yi da niyar komawa ta kwanta yasa hannunsa ya ruqota tare da cewa kar ki kwanta ki zauna zaman tayi bata qara komawa ba amma kuma bata bude idon taba haryanzu ganin hakan yasa shettima cewa baby kibude idon ki mana dubaki zeyi sai yanzu sukaga ta girgiza kai alamar baza ta bude ba sam ne yace ke bude idonki karkibata min lokaci ina da abun yi danshi harga Allah abun da takeyi ta bashi haushi hakan nan yake jin haushin ta daga ganinshi ta wani rufe ido saikace taga dodo banza yar kauye kawai mtsw yaja tsaki da harsaida yafito kuma kowannen su yaji saide ba wanda ya iya tanka masa bude idon ta tashiga yi a hankali ta sauke su akansa ga mamakin su sai suka ga ta maka mishi wata qatuwar harara tare kawar da kanta gefe waro manyan idanun sa yayi yana kallonta dukan su da mamaki suke kallon ta ganin hararar da datayi bare kuma wanda tayiwa mamaki begama kashe suba saida sukaji abun da basu taba zato ba budar bakin ta sai cewa tayi aikin banza kawai tare da zuro qafafun ta da niyar sauka daga kan gadon saide kuma abun da bata saniba shine qafafun ta baza su iya daukar taba dole saida taimakon wani aikwa tana takawa tasaki wata razananiyar qara tare da tafiya luuuuu zata fadi dan har tagama bayarwa tafadin saide bata kai ga faduwar ba dukan su sukayi kanta zasu taro ta saide shikadai ne yafisu zafin naman da yayi nasarar tarota shima kuma garin sauri be ankara ba yana tarota suka fada kan gadon atare tana rungume a kirjin sa haduwar qirjinsa da nata hakan ya haddasa musu wata irin mummunar faduwar gaba gabadayan su bawanda beyi mamakin jin irin wannan faduwar gaban ba wanda har kowa na iya jiyo bugawar ta dan uwansa saboda tsurewa da tayi ne yasa ta qara cukuikuye shi tare da kwantar da kanta a gefen fuskar sa batare da tasan me takeyi ba saboda ba a cikin hayyacin ta take ba..........,
[4/1, 10:45 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode 64-65

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

Ganin tayi lamo ajikinsa sai abun yaqara bashi haushi janye fuskar shi yayi da ta dora kanta sannan yasa hannu biyu ze janyeta sai yaga ta qara riqeshi tsaki yayi tare da cewa useless girl ita kadai tajishi amma bawanda kuma hakan besa tasakeshi ba shettima mane yakai hannun sa da niyar yajanyeta ganin yanda tabi ta rurriqeshi  amma sai sam yadaga masa hannu alamar ya barta kar yataba dakatawa yayi sannan yace baby uhm tace mishi shi kuma sai yace mata  kitashi mana ko bazaki iyaba ahankali muryarta cike da shagwaba kamar zatayi kuka tace kainane yake juyamin idan natashi ze iya fashewa wayyo dadda ta taqarasa fada da dan qarfi sakamakon jin kannata yaqara sara mata hannu wanta tasa duka biyun  tariqe kan nata dan dagaske ciwo yake mata hankalin shettima ba qaramin tashi yaayi ba jin abun da take cewa bashi kadai bama har saleem yaji tausayin ta shettima mane akaro nabiyu yaqara kai hadubatapa ze riqe mata kan saide yanzu ma kamar dazun sam yadakatar dashi aqufale yake kallon sa sannan yace kanajin fa abun da take cewa kar azo wata babbar matsalar takara faruwa yakamata ka qara dubata fa da kyau wani irin kallo ya watsa masa da yasashi jan bakinshi yayi shiru dan yasan halin abokin nasa kamar yunwar cikin sa saboda haka yasan ma'anar kallon da yayi mishi hannu yadaga tare da nuna musu qofa alamar su fita subashi guri saleem ne yafara fita amma shettima sai ya tsaya yaqi ko motsawa kawai kallon su yake dan shi hakan da sukayi beyi mashi dadi ba ya matsu yaga yasake ta sunraba jikin su hakanna yake jin zuciyarsa nayi masa quna da be san dalilin jin hakanba (Allah sarki to kode kishi kakeyi ne bamusani ba)  sam ne yaqara kollon sa irin kallon baka ji me nace bane dauke kansa yayi daga garesa duk da yaga kallon da yake mishi kuma yagane abun da yake nufi amma hakan besa shi fitar ba saima juyar da kansa yayi gefe ganin hakan yasa sam kufula cikin farajin haushin shi yace wai bacewa nayi kafita bane ko innabarka da ita zaka iya duba tane duk wanna shirmen naku dakuke yi ku da ita ba dole kanta yayi ciwo ba idan kukace gabama nan gaba fashewa zeyi ya tarwatse bashike nan ba jin an ambaci kanta ze fashe yasata fashewa da kuka tare da cewa wayyo Allah na dadda kizo zan mutu wayyo wayyo kaina yar tsawa yadaka mata saboda ya tsani kuka gashi kuma tanayi masa a saitin kunnen sa dan ji yake da lafiyar ta qalau ba abun da ze hanashi ya canza mata kamanni da maruka dan abun da yafitsana kenan kaf rayuwar sa shiru tayi tana dan shashsheqar kukan tare da fara qoqarin tashi daga kansa saide kuma yasa hannun da ya dakatar da ita shettima da yagama cika famm kamaer ya fashe yasashi barin dakin a kufale ya fita tare da janyo qofar da qarfi da har saida Ameesha ta dan zabura dan ta tsorata da jin qarar girgiza kai sam yayi yanajin haushin abun da abokin nasa yakeyi da be gane kansa ba miqewa yayi tare da ita ajikinsa sai ya riqeta sosai yanda bazataji zafin kannata ba sosai kwantar da yayi akan gadon yana ajiyeta ta qara dafe kannata da hannuwanta shima sai ya dora nasa hannun akan nata sai daga baya kuma yajanye nata hannun ya dora iya nasa addu'a yashiga yi mata yana tofawa lokaci guda kuwa tafara jin sassauci haka yaci gaba da yimata harsaida ya tabbatar da yadena yimata ciwon sannan yajen ye hannun sa yana qoqarin meqewa budar bakin ta sai kawai tasaki dan qaramin tsaki tare da cewa kawai anzo an tofe mutum da yawu sai kazo ka goge min duk kabata min fuska da shi kamata ma yayi inyi wanka wallahi asukwane yajiyo jin abun da take cewa ga mamakinsa kuma sai yaga bakin ta a rufe idonta ma a rufe kamar ma ba ita tayi maganar ba jiyayi kamar ya kwasheta da maruka Allah yatai maketa a gadon asibiti take akwance kuma idan yatabata za a iya samun matsala shiyasa kawai yake daga mata qafa amma badan hakaba tun harararsa datayi tun farko da tuni yayi maganinta  ta kusa bakuntar lahira,
yana mamakin qarfin hali irin nata watakon ita duk halin datake ciki bakinta baya mutuwa bata da kunya ko kadan yanda ya karanceta a iya haduwar sa da ita yagane tana da tsiwa batajin magana aikwa da rabon kagi tabar asibitin nan sai ya gyara mata halayen ta saboda shi baya daukan irin wadannan shirmen,

bude idon datayine ya katse masa tunanin da yakeyi wata hararar taqara yimasa lokacin da suka hada ido tunani me zeyi mata kawai yake,

aikwa tana rufe ido taji saukar abu akan fusakarta  me dan dumi bude idon ta tayi tana kallon sa da tabbatar da abun da take zargi bata gama tunanin ba taqara jin ya tofa mata wani yawun a fuska zaro manyan idanuwanta tayi takaici ya isheta watakon de da gaske yawu ya tofa mata a fuska dan tsabar wulakancin da rashin sanin darajar dan adam kuka tafashe dashi kawai sai kuma ta yunqura da niyar tashi ta rama dan bazata hakura ba wlh saide kuma tana tashi taqara jin wani ciwon saurin komawa tayi ta kwanta tare da ruqe kan wani kallon ya watsa mata ganin abun da tayi niyar yi da yatsa ya nunata tare da cewa da kwa kin tafka babban kuskure a rayuwar ki dan sai nasakaki kinyi nadama ganin tana ta qara bata mishi rai da kuma lokaci yasashi dauko allaurar baccin da yazo da ita tofa anan akeyinta domin arayuwar ta ta tsani allura tana tsoron ta sosai tuni ido ya raina fata girgiza kai ta shigayi tanacewa dan Allah karkamin allura wlh na tsani ta dan Allah na roqeka dan darajar iyayen ka karkamin karkamin wlh idan kamin mutuwa zanyi kar ka kasheni da allura duk wannan surutan da takeyi be kulata ba cigaba yayi da hada ta aranshi kwa haka yake cewa ashe rashin kunyar ta ban zace, bakya da tsoran  mutane amma kina tsoron allura  mtswww ya kuma jan wani tsakin a bangaren ta kuma sai Allah yasa take jera mishi tunkan yayi mata ma allurar saida yagama hadawa tsaf ya nufuto ganin de da gaske inta zauna sai ya tsira mata yasa ta tashi da sauri tana niyar sauka daga kan gadon mayar da ita yayi da hannunsa kana yace mata juya qin juyawa tayi tare da make mashi kafada ido kawai ya zuba mata yana kallon ikon Allah wannan yarinyar yar qarama da ita amma tana neman saka mishi ciwon kai yana ganin qarfin halinta dan a iya kiyasin shi yasan su Hamna zasu girme mata amma sai faman wahalar dashi take akan abun da be taka kara yakarya ba sa'ar ta daya bata da lafiya amma da shikadai yasan kalar hukun cin da zemata,

yunqurawa ta qara yi zata tashi yasa hannu yadagata tare da zama akan gadon yajawota ya hada ta da jikinshi yariqeta gam yanda bazata iya kwacewa ba sannan yadaga rigarta ya saita daidai bombom dinta inda ake allura ya tsiramata yana tsikara mata kwa tasaki wata qara adaidai kunnen sa lokaci guda kuma sai ta dauke wuta dufff jin hakan yasashi dagota ya kwantar da ita ganin yayi bata motsi jikin ta ya mutu da alamade sumewa tayi saboda zafin allura, tashi yayi ya gyara mata kwanciyar tare da rufar ta a hankali ya furta marar kunya kawai idan kingama suman kin farfado sai ki koma bacci ko ruwa da yake gefe a gora yadauko ya shafa mata ta farfado saide dishi dishi take gani idonta har rufewa sukeyi saboda allurar da tafara yimata aiki,
kallonta yayi kana yace  allura kawai tasa kin suma amma kin iya yiwa mutane rashin mutunci maganin me tsiwa kenan anjima ma kika tashi kiyima wani rashin kunya sai namiki goma oho ita bata masan yanayi ba dan tuni bacci yayi awan gaba da ita saida yadan qara duddubata ahaka sannan yafice daga dakin yana fita yatarar da shettima abakin qofar sai safa da marwa yake yaqi zaune yaqi tsaye harde hannunwansa yayi yana kallonsa shima shi yake kallo sai yace malam lafiya kake kallona sam yace bansani ba wai meye matsalar kane da yarinyar nan naga duk kabi ka damu kanka akanta harar wasa ya watsa masa sannan yace ina ruwanka da ni kawai kazo zaka tsorata yar mutane gaya min me kayi mata nasan baka da imani wlh yanzu baza ka duba rashin lafiyarta ba zaka iyayi mata duk abun da yazo ranka kallonsa yayi yace dake ga mahaukaci ko to zaneta nayi kamar yanda kake tunani nafasa mata baki ma yanzu haka ta suma zaka iya zuwa kabata taimakon gaggawa kar tarasa ranta inkuma ta rasa saika bita ku tafi tare yana kaiwa nan yabashi hanya tare da nuna masa qofar da hannun sa sannan yawuce yabarsa agun, kamar mutum mutumi haka ya tsaya agun yakasa ko motsawa dan duk atunanin sa dagaske yake saboda yasan kadan daga cikin halayen sa kenan tsaf ze aikata abun da yace din sai can kuma kamar an tsikare sa da sauri yabude dakin yashiga har yana hadawa da dan gudu gudu yana zuwa kuma yaja burki ya tsaya ganin bawata alamar wahala atattare da ita dan dubata yaqara yi tare da sauke ajiyar zuciya,  a fili yace dan rainin hankali ashe qarya kake hmm da kwa yau kagane waye ni saina nuna maka bacin raina akan yarinyar nan wallahi saide komai ze faru ya faru abun rufarta ya gyara nata sannan yafita daga dakin zuwa office din sameer yana zuwa ya tarar dashi zaune kan kujerar sa yana duba wani file ko sallama beyi ba ya shiga ciki yaji shigowar mutum amma bedago yakallesaba saboda yasan ba wanda ze mishi haka inba shettima man ba shiyasa ya shareshi zama yayi akan kujera yana fuskantar shi sannan yace Allah yataimake ka wlh naganta lafiya qalau amma badan haka ba ko hmmm sai yanzu ya dago ya kalleshi sannan yace badan haka ba me zefaru zaka rama matane yace what ever de yanzu de duk ba wannan ba me yake damun ta yanzu wani irin kallon banza ya watsa masa sannan yaci gaba da aikin gabansa batare da ya bashi amsa ba duk nacinsa nason ya kulashi kin kulashi yayi daga qarshe ma sai yatashi yabashi waje yayi shigewar sa ciki zama yayi agun yana mamakin wannan halin na abokin shi yanzu inde yanaso yaji halin da take ciki dole saide yabishi ta lallami da limana sannan inyaga dama yagaya masa beyi qasa agwiwa ba yaqara tashi yabishi cikin cikin lallami yashiga roqonsa saida yaga dama sannan yagaya masa duk yanda sukayi da ita kuma ya dora masa da cewa ya gargadeta idan ta farka karta kuskura taqara yimasa wani abun makamancin haka inkuma bahaka ze riqeta ne har sai tasamu lafiya sosai ya hukuntata sannan ze sallame ta shide kawai to yake cewa bashida bakin ja inja dashi tundade yanzu masalaha yake nema gwara yabishi a hankali su rabu lfy,
tambayar sa yayi zuwa yaushe zata farka yace masa nan da awa biyu ma zata iya farkawa saboda bame qarfi yayi mata ba godiya yayi masa kawai ya tashi yafita yana fita yakira number bossay bayan sungama gaisawa yasanar dashi suzo anjima amma kar yagaya musu cike dajin dadi da haryana jiyo irin farin cikin dayakeyi sai faman godiya yake zabga masa kamar yayi mishi albishir da aljanna sallama sukayi sannan yakashe wayar ya nufi dakin da takede dan baya gajiya da kallon ta beqi ace kullum yana gabanta yana kallonta ba...........,


*Bossay*
fadawa yayi kan gadon sa tare yana tafaman sakin murmushi yaji dadin wannan albishir din daman fitowar sa daga wanka kennan dan haka yatashi da sauri yashiga shafa mayika tare da feshe jikin sa da turaruka wajen jerin kayansa yaje ya tsaya yana binkayan da kallo yarasa wanda ze saka kayan da yasaka ranar da zeje dauko ta yaje saikuma Allah beyiba zata gani dan haka da sauri yazarosu yasaka shaf shaf yashirya yafito har yana hada step bibbiyu gurin saukowa daga benen bakowa afalon dakin dadda yafara nufa yana zuwa bewani tsaya tabashi izinin shiga ba kawai yadanna kai ya shiga yana shiga yatarar da ita akan gado jin anbanko qofa yasa ta saurin boye abun da takeyi kallo daya zakai mata gane bata da gaskiya amma saboda halin farin cikin da yake ciki besa yagane hakan ba qarasawa yayi inda take yace tsohiwa kishrya zamuje asibiti muji ya ake ciki kinga tun ranar da sukace zasu kira har yanzu basu jiraba yakamata muje muji ko lfy tana gurin azaune takasa motsawa kawai sai kai datake daga masa alamar to be tsaya bitakanta ba yanufi dakin Ammi dan yanzu shi bakomai bane agabansa face yaje yaganta dan ji yake kamar yayi tsuntsu yangashi agabanta itana Ammi yanda yagayawa dadda itama haka yace mata sannan yace suyi sauri ba bata lokaci kuwa kowannen su yashirya suka fito falo suna shirin fita saiga faruq tanbayar inda zasu yayi dadda ce ta bashi amsa dan haka shima yace sai yaje bawanda ya hanasa gabadayansu suka fita amota daya suka hau bossay da faruq agaba say dadda da Ammi abaya gudu kawai yake da saida kowa yayi mamakin irin gudun da yakeyi saboda ba halinsa bane inde bawani abu bane emergency yataso baya gudu a mota da suka tambayeshi dalilin gudun sai yace musu anajiran sane agurin aiki shiyasa

38 / 49