SARKI SAMEER BOOK 1 Hausa Novels

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   39 / 49

114K to 117K   out of 145.7K words

yakeso yaje ya dawo da wuri,

adan qanqanen lokaci suka qaraso asibitin yana gama parking suka fito tare da nufar cikin asibitin wayar sa ya dauko yakira shettima yasanar dasu zuwansu shi kuma yayi masa kwatancen inda suke,

gurin da yakwatan ta mishi yanufa sukuma suna mara masa baya ahaka har suka qaraso bakin qofar dakin nocking yafara yi daga ciki shettima yace ku shigo mana tura qofar yayi ahankali yasaka kai yashiga ciki sannan suma suka shigo,
gaba dayansu mutuwar tsaye sukayi da ganinta dan zuwa yanzu har ta farfado tana zaune shettima nabata tea abaki..........
[4/2, 8:13 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode 66-67-68

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

shettima ne yacewa Ameesha da yaga bata kula dasu ba yayi mata nuni da hannu dagowa tayi ta dubi inda yake nuna matan akan bossay idon ta yafara sauka kuri tayi tana kallonsa kamar meson gano wani abun ko kiftawa batayi shima itan yake kallo sun qurawa junansu ido saidaga bisani ahankali yafara takawa zuwa inda take kuma be dauke idon sa akanta ba har yaqaraso bakin gadon sai kuma yaja burki yatsaya saida yagama qare mata kallo sannan yace baby meesha na da gaske kece ba gizo bane bata tanka masaba illa ido da ta zuba masa tana kallonsa dasauri yadan raunkwafa zeyi hugging din ta amma sai ta matsa baya dakata wa yayi sai yakuma qoqarin ruqo hannun ta amma sai ta qara janyewa jikinshi a sanyayye yace meesha nine fa tace nifa bansanka ba bazan bari ka taba niba kaidin waye suwaye ku dan Allah kufita wlh banason ganin ku taqarasa fada harda dan guntun hawayenta tana qara matsawa daga kusa dashi tsaye yayi ya kasa motsawa kamat mutum mutumi (gunki),

Dadda de suman tsaye tayi dan bata taba tsammanin ganin jikar tata ba ahalin yanzu dan ita zuciyarta bata takeyi tamutu kawai zasuzo suga gawarta ne kawai bossay na boyewa ne be gaya musuba sai kuma taga akasin haka bata san lokacin da kwalla ta fara zubo mata ba, ashede da rabon zata qara ganin gudan jinin ta jikar ta tilo aduniya,

faruq ne yaqarasa shigoa ciki tunda daman tunda suka shigo yana baya beganta kuma daman besantaba ganin de yarinya akan gado yasashi tabbatar wa akan itace Ameeshan da ake nufi bakin shi a washe har kana ganin fararen haqoran sa yace wannan ce Ameeshan taki dadda yatambaya yana kallon dadda datayi tsaye sai faman zubar da hawaye take rabuwa yayi da ita ganin bata da niyar bashi amsa, "sai kawai ya maida dubansa wajen Ameesha da itama zuwa yanzu ta maido dubanta garesa ganin hakan yasashi qara washe baki tare da qaraswa inda take hannu yadaga mata kana yace hy beauty girl dina yajiki kasake tayi tana kallonsa kallon da kana gani kasan kallon rashin sani take mishi batare da tace komai ba tacigaba da kallon su daya bayan daya,

Ammi ce ta katse musu shirun nasu da cewa dadda kiqarsa mana kin tsaya anan ko bakiyi  farin ciki da ganin jikar taki ba taho mutafi tafada tana ruqo hannun ta suka qarasa bakin gadon tsayawa sukayi agabanta

Dadda ce tabude bakin ta da qyar tace shalelena dagaske kece a zaune ba mafarkin da nasaba yi bane matsawa tayi kusa da ita tana niyar rungumota amma sai tajanye jikin da mamaki dadda ta tsaya tana kallon ta wasu hawayen nen suka qara tarar mata tace shalele nice fa daddar ki baki gane ni ba budar bakinta sai cewa tayi ni bansan kiba bantaba ganin ki ba kuma ni ba shalelan kibace tafada tare da murguda baki sannan ta karbi cup din shayin dake hannu shettima taci gaba da sha kamar ma bata san da halittar su agun ba sau biyu ta kurba sannan tace dan Allah kun isheni da kallo dan Allah kufita banason ganin ku anan,

gaba dayansu ba wanda beyi mamakin jin furucin ta ba musamman shettima da yanzu suka gama magana da ita take cemishi ya kira mata daddar ta shiyasa yayi mata wayo yace inbata sha tea din ba baze kira mata ita ba saboda jin hakan yasatake sha,
Amma kuma yanzu tace bata sansuba to kode kwakwal warta ta dan tabu wajen yin aikin jin sautin kuka ya katse masa tunanin sa,

dadda ce ta fashe musu da kuka tana cewa shikenan yanzu shikenan anrabani da jikata nashiga uku gudan jinina ta manta dani kunjifa me take cewa wai bata son ganin na tama ki yarda intaba ta dan Allah ku ganar da ita ko ni wacece wlh bazan iya rayuwa idan babu itaba kar ki gujeni dan Allah tafada tana kallon Ameesa da ta toshe kunnen ta bama jin surutun ta take ba bossay ne yashiga rarrashinta da shima kawai dauriya yake dan jinsa yake kamar ya fashe da kukan shima karde ace Ameesha tayi losing memory din ta idan kwa hakan yazasuyi gashi taki yarda da ko wannen su,

Ammi ce ta kallesu tace kunga dan Allah mubi komai a hankali wannan ai ba abun tashin hankali bane daman inde akace abu tashafi brain to dole za a iya samun irin wannan matsalar ko doctor tafada tana kallon shettima da yakasa magana daga mata kai yayi tace kayi musu bayani yanda zasu fahimta magana yagamsu da maganar ta shiyasa yafara yi musu bayani a nitse yake cewa yanzu daman ba lalle ta iya gane komai ba saboda yanayin matsalar ta tana iya taba kwakwalwa ta manta da wasu abubuwan amma in akai sa'a ana tuna mata da wasu abubuwan da kuma da kuma abun da tafiso naci ko nasha da komai de data ke rayuwa dashi da to zata iya tuna baya adan qanqanen lokaci batare da anja lokaci me tsawo ba kun fahimta,

cike da gamsuwa suka amsa masa itade dadda ba haka taso ba amma yazatayi tunda ahaka abun yazo,

Ammi ce ta zauna kusa da Ameesha tare da ruqo hannun ta yanzu bayi musuba kuma bata kwace hannun ta daga ruqon da Ammi tayi mata cikin nutsuwa Ammi tafara yimata bayani tace 'yata ki kwantar da hankalin ki munan da kika ganmu mune danginki tanuna kanta tace nice mahaifiyar ki ta nuna dadda tace wannan kuma sunanta dadda itace kakarki wadannan yayyankine tanuna bossay da faruq sannan tace kina dawasu yayan mata harma da qanne su suna gida munbarosu agida duk kinmata damune saka makon rashin lafiya da kikayi har aka kwantar dake anan kindade a kwance yau wajen satinki biyu akwance sai yau muka samu damar zuwa ganin ki kuma munzo da murnar gashi kinmanta damu amma dan Allah kide na furta bakya son ganin mu in baki san ganin mu to suwa zaki gani dole mune naki kinji 'yata ko kinaso kiga hawayen mahaifiyar ki kai ta girgiza mata alamar a'a tace to yanzu kin yarda zaki zauna damu tare,
kai ta daga mata sannan ammi tace yauwa yar albarka yanzu kibawa kakarki hakuri kice ta dena kuka kinga sai kuka take saboda duk cikin ku tafisonki shiyasa kiga tana zubar da hawaye akan abun da kikai mata bataji dadiba,

cikin sanyin murya tace dadda kiyi hakuri yanzu nasanki wani irin farin ciki dadda taji ya lullubeta jin shalelanta ta ambaci sunan ta hakan ba qaramin dadi yayi mataba batasan lokacin da ta saki murmushi ba tare da rungume ta tace ni daman banji komai ba kawai tashin hankalina kice bazaki zauna dani ba amma yanzu tunda kin amince shikenan hankalina yakwanta idan kina tare da mu zaki tuna komai zaki gane ko ni wacece zaki tunani ahankali taqarasa fada tare da raba jikin ta da nata kallon ta ta mayar kan bossay dataga ya kafeta da ido murmushi tasakar masa sannan tace kaine yayana ko kai yadaga mata sannan tace ya sunan ka da qyar ya iya cemata bossay jin jina kai tayi tare da nanata sunan kafin ta kuma duban faruq tace kaifa ya sunanka yace ni sunana Ameesha tace ashe sunan mu daya tunda nima haka naji suna kirana dashi yar dariya yayi dukansu saida suka dan murmusa jin shirmen da take yi ,
"dadda ce tace Allah sarki jikalle Allah yabaki lafiya wai yanzu dan Allah ita iya gaskiyarta ta zata sunan su daya batasan sunan namiji daban ba na mace ma daban Ammi ce tayi murmushi tace ai komai sai an nunamata an koya mata yanzu ba komai akanta duk abun da aka dorata ahaka zata taso dadda tace rayuwa kenan yau kaine yau ba kaibane gata de itadin ce komai nata amma kuma ba abun da tasani kamar 'yar qaramar yarinya Allah yaqara miki lafiya me amfani gabadayan su suka masa mata da ameen daga nan kuma faruq yace beauty girl ni ba sunana Ameesha ba da wasa nake miki wannan sunan mata ne ba a kiran namiji dashi nikuma sunana umar amma anace min faruq ke kuma yaya faruq zaki ringa cemin kinji kai ta daga masa kawai bossay ne ya doke mishi qeya yace bazata fada din ba ke faruqu zakina ce mishi inma kika ga dama kice mishi umaruru duk wanda kike so dan murmushi tayi sanan tace to zanringa ce mishi umaruru yama fi dadi,
Faruq hade rai yayi kamar zeye kuka dan ya tsani yaji ance mishi umaru bare kuma har aqara da wata ru din wai umaruru sai kace wani dan iska ko mafarauci dan caucau kallon dadda yayi yace dadda kinji shi ko to wlh kigaya mata ba sunan bane kar tasake ta qara kirana da haka inba haka ba kuma hmmm yafada yana hade bakinsa tare da watsa mata harara saura kadan tasaki dariya amma sai ta basar tunkan dadda tabashi amsa tace to nadena yaya faruq hakan yayi maka lokaci guda yasaki murmushi yace yauwa ko kefa haka akeso zamuje dake tunda kina jin maganata ya qarasa maganar yana wani bubbudewa shi adole ga babba nan hararar sa bossay yayi yace dalla malam meye hakan kake uban son girma ahaka ake neman girman yafada yaba watsa masa wata hararar tare da kai masa qozo akai yayi saurin gocewa ya samu iska abun da sukeyi ba qaramin burgeta sukayi ba sai faman sakin murmushi take duk abun da take akan idon shettima da yayi zaune be tofa musuba saboda abun na family ne gwara yayi shiru kar ya tsoma baki aciki kallon fa yakeyi kawai tare da dan karkata wayar sa yana mata videon duk abun da takeyi batare da tasani yanayi ba kuma suma saboda farin cikin da suka tsinci kansu ba wanda yakula da abun da yakeyi wasuma daga cikin su sunmanta dashi agun sundau tsawon lokaci ahaka suna ta nishadantar da junan su suna janta da hira saboda taqara sabawa dasu kafin sukoma gida, ganin hirar tasu ba qarewa zatayi ba yasa shettima dakatar dasu yace yakamata su dan bata guri ta huta saboda yanzu kwakwalwar tana bukatar taringa samun hutu akai akai basuyi musuba sukayi na'am da maganar sa sannan Ammi ta tambayeta me takeso su kawo mata tace musu ba komai basu takurata ba sukace de zasuje gida suyo mata wani abu su dawo anjima daga haka kuma sukayi sallama badan sunsoba suka hakura da ganin ta haka fita sukayi kowa da kewarta da kuma jin dadin kasancewa dasukayi tare adan wannan lokacin da qyar faruq yafita da cewa yayi shi anan ze zauna subarshi saida Ammi ta gargadeshi sannan ya yarda yabisu bayan tafiyar su ta gyara ta kwanta tare da lumshe idanuwanta shettima ne yace yakira sunanta bude ido tayi tana kallonsa tambayar da ya jefomata ne tasata tashi zaune tana muzure da manyan idanunta sannan tace me kace oh kina nufin bakiji me nace ba to bari in maimaita miki me yasa kika zabi yi musu qarya nasan kina cikin hayyacin ki sarai kinsan kowa kingane kowa bawani losing memory dakikayi amma inason sanin dalilin ki na boye musun dakikayi meye amfanin hakan.......??????
[4/3, 8:02 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍

Episode,69-71-72

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

zakuga kwana biyu ina hade page uku uku haka zanringa yi har inkai 100 pages Sabaoda inasone nan da kwana goma ingama hade book one kuma inaso numbobin su kasance guda dari shiyasa nahade su guda uku hakanne kawai zesa sukai pages 100 ina fatan kungane bayanina.

***********************
*shettima*
ina sauraronki meyasa kikayi hakan rarrau tayi da ido kamar zatai kuka sannan tace nifa bangane me kake magana akaiba yace kar ki rainamin hankali kinmanta yanda mukayi dake kafin suzo kenan amma yanzu kuma zaki canza min magana kedakanki kika ambaci sunansu kuma kince inkira maki su sunzo kuma kin maida mutane shashakai hawayene yafara zubowa daga idon ta sannan tace hakane gaskiya  kafada nasan su babu abun da na manta inasane duk nayi musu haka amma  dan Allah kayi min rai ka taimake ni kar kabari kowa yaji   dan Allah nima da farko badaniyar hakan nayi ba ina gwadasune kawai daga baya ince musu wasa nake to amma bayanin da naji Ammi tayi da kuma naka su suka canza min ra'ayi da nayi wani tunani sai naga gwata ma inbar abun ahaka abansan kowa din ba saboda ina da nawa dalilin shiyasa nake so muje ahaka ammafa kayi hakuri bazan iya cemaka komai ba akai saboda family issue ne be kamata kajiba dan haka kayi hakuri kawai kuma ina qara roqonka dan Allah kar kasanar da kowa zancen nan tafada tana hada hannuwanta biyu waje guda alamar roqo bata sanar dashi kan cewa sauran ba 'yan uwanta bane kawai tabarshi azin danginta ne kamar yanda Ammi ta sanar musu,

Shi abun ma mamaki yake bashi ace yarinya kamar wannan  yar qarama da ita taya ta iyayin irin wannan tunaninn haka to amma koma menene yasan baqaramin abubane katse masa tunanin sa tayi da cewa ya akai naji kayi shiru kallon ta yayi yace ai kin daure min kaine bansan me zance miki ba tace kawai inaso kamin alkawari ba wanda zeji halin da nake ciki baza ka gayawa kowa ba ta qarasa maganar tare da miqa mashi  hannu alamar yadafa yayi mata alqawari qin dafawa yayi yace gaskiya bazan miki alqawari ba saboda yanayi rayuwa amma de bazan gayawa kowaba kamar yanda kikeso saide bandau alqawariba kuma bazan matsa maki akan dole sai naji dalilin kiba amma de inaso nabaki shawara akan kafin ki yanke hukunci kiringa tunani sosai ko kuma kiringa neman shawarar nagaba dake tunda de ke yarinyace qarama kina da qarancin shekaru be kamata duk abun da yazo miki cikin zuciya kawai ki yanke hukunci ke kadai batare da kin nemi shawarar nagaba dakeba domin hakan ze iya jawo miki nadama da danasani kuma da nasani qeyace bata da amfani dan haka ki kiyaye nagaba,
Sosai maganganun sa suka shigeta kuma ta dauki shawarar sa amma hakan bazesa ta canza wanda ta riga da ta yanke kuma in sha Allah bata fatan zatayi da nasani awannan ammade zata kiyaye kuma zatai aiki da shawararsa nan gaba,

dagowa tayi suna fuskantar juna sannan tace naji duk abun da ka fada kuma in Allah ya yarda zankiyaye nagode sosai da sosai Allah yabaka abun da kake so duniya da lahira girgiza mata kai yayi kana yace ameen yanzu ki kwanta ki huta sai zuwa dare sai yazo yaqara dubaki nasan kuma yan gidan ku zasu dawo zuwa anjima ko da daddare yana kaiwa nan yamike yace bari naje zanturo nurse din dazata kula dake ko inkina buqatar wani abun sai kiyi mata magana ayi gaggawar sanar dani tace to shikenan nagode da kulawarka Allah yabiyaka da mafificin alkhairi, yaji dadin addu'ar ta cike da jin dadi ya amsa mata da Ameen Ameen nima nagode da addu'ar ki sai anjima ki kwanta dan Allah kisamu bacci kwakwal warki taqara yin fresh ko tace ok
batai mishi musuba saboda daman itama tana bukatar hutun dan jinta takeyi wani iri kwanciya tayi tare da jan aburufa saboda dan sanyin datakeji sallama sukayi ya fita yabarta yana fita ta lumshe idanunta aranta take cewa yanzu zamu fara sabuwar rayuwa kuma nasan ta hakane kawai zan cimma abun danakeso tahaka zan gano ko ni wacece inban gano komai ba bazan taba bari wani yasan ina cikin hankalina zantayin basaja harzuwa lokacin da naukar wa kaina wannan alqawarine na daukar wa kaina sai nasan suwaye mu idona akoda yaushe ze kasance akanki dadda,
dan bata manta da abun da yafaru da itaba ranar da abun yafaru da ita kuma ta danso ta fahimci wani abun tun aranar amma bata samu damar gane komai ba amma tana fatan yanzu zata gane saboda zatayi acting bata san komai ba saboda haka kuma tana da yakinin cewa dadda bazata ringa boye mata wasu abubuwan ba zataringa yin komai agabanta saboda tasan kotayi agabanta bazata gane ba saboda bata cikin hayyacinta bazatasan me take kullawa ba, da irin wadanan tunane tunane datakeyi ahaka har bacci yayi awon gaba da ita,
bata farka ba sai wajen qarfe tara tana bude idon ta taga su dadda agaban ta kamar de yanda sukazo dazu haka suka dawo yanzu ma sannu suka shiga yimata tana amsawa kafin daga nan kuma Ammi ta takura ta akan sai ta danci wani abun daga cikin abubuwan da suka kawo mata da qyar tayarda ta dan sha kunun gyada da daga nan kuma tace ba abun da zata qara hira suka dan taba kadan kafin suka tafi amma banda bossay da yace suje ze taho in anjima faruq ma yaso abarshi sai akace inyazauna waze maida su gida dole yazo yakaisu badan yaso

39 / 49