idan yan kukan sunkama tayi abunta ta qoshi ta godewa Allah sannan tayi wanka tafito bawan da ze gane halin da take ciki amma yau tayi ganganci gashi kuma ankusa ranfota dan tasan tabbas sai yayanta ya tambayeta ko ba yauba dole tasan amsar da zata bashi,
Bakin ta ta bude cikin sauti a fili take cewa nashiga uku ni Azeema wai meyake shirin faruwa dani ne waddannan abubuwan suke faruwa dani tunda nake bantaba ganin inda aka taba yin hakaba daga ganin mutum ka kamu da matsananciyar soyayyar sa wace take shirin tarwatsa farin cikina gaba daya inazan saka raina yazanyi dashi araina taya zancire shi daga cikin zciyata me yasa zuciyata zata min haka meyasa bata da hankali bata san abun da yake daidai ba da wanda ba daidai ba hannu tadaga sama tafara jero addu'a
Ya Allah naroqeka badanni ba badan halina ba Allah ka cire min sonsa araina Allah ka kawomin mafita acikin ala mura na Allha ka kawo min dauki Allah ka taimake ni Allah kataimakebi bani da wanda zan gaya damuwata saikai kaikadai kasan halin da nake ciki Allah ka yaye minshi kabani abun da yake daidai arayuwata kacire min abun da ba daidai ba idan kuma jarrabawace wanna Allah kabani ikon cinyeta dan dakatawa tayi tanaci gaba da kuka sannan ta dora cewa , Allah ka kawo min dauki kacireni daga wannan haukan da nakeyi tana gama rufe bakin ta taji ance" Ameen Ameen"
Ahakace tajuyo tare kidimewa lokaci guda kuma taji zuciyar ta ta wani buga da qarfi waiwayowa tay danganin me amsa mata addu'ar da take yi idon tane sukayi mata tozali da abun da bata taba tsammani ba tsaba tsoron da taji ne yasata sumewa awajen ...........✍
(Tofa meke faruwane takwara wakika gani haka kuma wakike so)
who guess? kowaye wannan waze iya gaya min wanda tagani next page nashine nayi alqawri💃
Azumi fa yazo sai kunyi min uziri yanzu ba kullum zakuna samun posting ba sai sanda kuka gani kawai
Story and writing
by
xeemat love
[3/28, 10:52 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
by❤xeemat.....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
﷽
Bismillah........ ✍
Episode58-59
"""""""""""""""""""""""""""""""""
💋Spacial thanks to you all ❤wannan page din naku ne saboda ku nayi da wadanda suka canka daidai da wadanda basu canka bama duk ina miqo saqon gaisuwata gareku,
irinsu 👇
sabreena,
it'z hauwee,
halyma,
kirawa,
Gbemisola abdulrasheed💋💋💋
******************
__________________AZEEMA
bude idonta ta shiga yi ahankali dishi dishi tafara gani kafin ta qarasa ware su tar ganin inda takene yasata saurin tashi zaune tana murza idon ta dan tabbatar da inda take,
idon ta tasauke akan shettima dake gefen kujerar datake zaune ido ta zuba masa tana kallon sa shima itan yake kallo ko kiftawa basayi ita fafara janye idonta daga kansa sannan shima yajanye nasa yayi sai daga bisani kuma ya katse shirun nasu da cewa "ya jikin naki?
bata bashi amsa ba saima tunanin yanda akai tazo nan take shin to wai ina wanda tagani ne kode da gaske ne alajanine kamar yanda take zato,
to hakan na nufin aljani take crushing bata sani ba tabbas idon ta yagane mata wanda take son gani to amma kuma tunda ta ganshi bata qara sanin inda kanta yake ba sai yanzhaka0mta farka taganta anan to me yafaru da ita bayan ta ganshi din batasan lokacin da fili ta furta aljani ne kenan jin abun da tace ne yasa shettima juyowa shima da mamaki sannan ya maimaita abun da tace aljani kuma a ina?
juyowa tayi tace uhm alajani ne wlh aljani ne yace ke wai aljani a ina kasa amsa mishi tayi kawai sai ta fashe da kuka sosai ta tsoratar shi yakasa gane inda ta dosa kafadun ta yadafa yana dan jijjigata yana cewa ke malama ki nutsu me yake damun kine jikin yaji yadau bari na tsoro ganin hakanne kawai yasashi jawota jikin shi yasakata a faffadan kirjin shi ya rungumeta qama ajikinshi yana shafa bayanta alamar rarrashi sannan yace shiiii pls kidena kukan haka bawani alajani anan nine fa ,
cikin shashsheqar kuka tace wlh naganshi dazu aljanine tafada gaba daya tafita hayyacin jikin ta sai faman karkarwa yake qara riqeta yayi sosai dan ya lura a tsora ce take sai kuma yafara tunanin to kode aljanin ta gani dagaske tunda ayanayin da yaje yaganta bisa ga dukkan alamu dayagani kamar furgita ce tasata suman inba haka ba to meyasa ta suma awajen gashi kuma fuskar ta shabe shabe da hawaye to me yake damunta yatambayi kansa amma beda wanda ze bashi amsa tabbas akwai wani babban al amari da yake damunta amma ze bincika gurin yayanta yaji ko ta taba yin irin hakan ko kuma yanzune aljanun suka shafeta har suke bude mata ido,
cigaba yayi da rarrashinta har saida yaji tayi shiru ta dena kukan amma hakan besashi dagata daga jikin shiba ya rabu da ita ta tashi dan kanta saida suka dauki lokaci ahaka kafin ta yunqura ta raba jikinta da nashi saita qara komawa jikin kujerar ta jingina kanta da hannun kujerar tare da lumshe idon ta kamar meyin bacci
zuba mata ido yayi yana kallon ta kamar yasamu tv shi kansa yayi matuqar daure wa da lamarin yarinyar nan na farko tazo tanayin kuka taqi fadar abun da akayi mata na biyu kuma tace bazata zauna ba kuma ta tafi nanma kuma bata tafi ba ta tafi can wani waje alhalin tace ta tafi gida to me yakaita can wajen kuma me tagani da har yakaita ga sumewa hannun sa yazura a aljihu ya dauko wayar sa yafara daddan nawa ,
Adaidai lokacin ita kuma ta bude idon ta ganin abun da yake yi yasata saurin cewa in roqeka wani abu dakatawa yayi da abun da yakeyi tare da dagowa ya kalle ta sannan yace inajin ki saida ta danja dogon numfashi kafin tace dan Allah kar ka gayawa yayana abun da yafaru yace me yasa tace banason yasan komai saboda banaso hankalin sa ya tashi kuma idan yaji ze gayawa mamana itama zata shiga damuwa kuma zasu tambayeni dalilin damuwata ni kuma bazan iya gaya musuba dan haka nake roqonka dan Allah kar ka gaya masa kaji plsss ta qarasa maganar tana marairaice fuska,
sosai jikinshi yayi sanyi dan haka yace gaskiya kiyi hakuri bazan iyaba halin da kike ciki dole su sani domin a nema miki magani watakil aljanune suka shafeki suke bude miki ido yakamata susani sai a gaggauta nemo miki magani,
Murmushin takaici tasaki jin furucin dayake sannan tace hmmm baza ka gane bane amma ni bana tattare da shafar aljanu nide kawai alfarmar da nakeso kayi min kenan wannan yazama sirri tsakanina dakai, kallonta yayi sannan yace zan amince amma abisa sharadi kin amince?
daga masa kai tayi alamar eh ta yarda cigaba yayi da cewa sharadin shine zaki gaya min abun da yake damunki da kuma abun da kika gani da harkike tunanin aljani ne..
wani busashen yawu ta hadiye da ya tsaya mata a maqogaro sannan tafara girgiza mishi kai tana cewa kayi hakuri wannan sirrin zuciya ta ne nayi alkawari koda zan rasa rai nane babu wanda zan iya gayawa inde ba abunne ya tabbata ba bare ma nasan har abada baze tabbata dan haka zanci gaba da ajiyeshi acikin zuciyata daga nan harzuwa lokacin da ze zama ajalina dannasan shine ajalina sanadin sane zanbar duniyar nan wani irin kukane ya taho mata da yasa takasa qarasa maganar takeyi saida tayi me isarta sannan ta dora da cewa dan Allah naroqeka karka takura min akan sai kaji dalili na karabu dani kawai, yace to na rabudake amma kisani dole susan halin dakike ciki sai sudau mataki akai nida kaina zanje har gidan ku ingaya wa mamanki da abban ki ko so kike nasan halin da kike ciki inzuba miki ido har kimutu idan nayi haka ko agurin Allah ina da laifi gwara nagaya musu nafita sauran yarage nasa yana kaiwa nan ya miqe ze bar wajen da sauri itana ta miqe tare da shan gabansa ta hada hannuwan ta biyu waje daya fuskar ta kuma hawaye sai sintiri suke akan kumatun ta dan Allah fa nace baka da tausayi ne ya kakeso inyi da rayuwata ne da damuwar da take damuna ko da wacce kake son kunno min yanzu yace ai ke kika zaba duk ma abun da yafaru mafita daya ta rage miki zabi biyu nabaki ko kigaya min ko kuma in fada musu sai kigaya musu da kanki dafe kanta tayi sannan tace naji na zabi ingaya maka amma kamin uzuri ahalin yanzu da nake ciki bazan iya gaya maka ba kabari idan nasamu time zamaka magana sai muhadu ingaya maka kayarda kai yadaga mata sannan yace yanzu naji magana zan daga miki qafa amma fa na tsawon sati daya idan baki fada ba kuma kinsan sauran ina fatan kin gane,
Eh tace masa yace good girl yanzu ki share hawayenki ki muje nakai ki gida in kuma kinaso saleem yazo yaganki anan baki tafi ba ba ruwana dan yana tambaya zan gaya masa gaskiya da sauri ta goge harda kwakwalo murmushi ta aza akan fuskarta sannan tace nagode muje to duk abun da yasan ze dauka ya duba yadauka saboda idan yatafi yatafi kenan ba dawowa zeyi ba yana gamawa yace sutafi fita sukayi atare yaja office dinsa sannan ya nuna mata wata hanya yace mubi tanan yanda bazamu hadu dashi ba binshi tayi yana gaba tana baya har suka zagayo tabaya suka zo wajen parking space din da kansa ya bude mata gaban motar ta shiga sannan yace mata bari ya shiga yanzu ze fito ze dan leqa abokin sane inyanzu zai tafi su tafi tare in kuma ba yanzu ze tafi ba sai suyi sallama ok kawai tace dashi shikuma sai ya rufe mata qofar sannan ya koma ciki direct upstairs ya nufa wajen sam yana qara sawa bakin office din nasa sai ya kwankwasa yadan jira ko za abude amma shiru saida ya buga wajen sau uku amma ba abude ba hakan yasashi murda qofar sai yajita a kulle juyawa yayi ya koma,
wajen motar yakoma sannan yabude ya shiga da sallama amsa masa tayi ciki ciki kallon tayayi ganin idon ta arufe yake sai ya share ta kawai be cemata komai ba yayi wa motar key tare da yin reverse yajuyata suka fita daga cikin hospital din sai da ya hau kan titi sannan yadauko wayar sa yadan lallatsata ya lalubo number sa yadanna mata kira sai yakara wayar a kunnen sa yace ana dagawa yace hello Sam kana ina ne ko ka tafi naje office dinka ban ganka ba naji ma a kulle yake bansan amsar da akabashi ba kawai yace ok sai gobe to nima na wuce gida daga nan kuma yakashe wayar ya ajiyeta gefe batare da ya kalle ta ba yace wacce unguwar tace kurna wajen masallacin na kowa yace ok daga nan sukayi shiru tafiya kawai suke kowa da abun da yake saqawa aransa saida suka danyi nisa bazato ba tsammani taji yace kiyi hakuri dan Allah bude idon ta tayi tana kallon sa sannan tace sorry for what yace for everything tace like how kai da bakai kayi min laifiba meyasa zaka bani hakuri yace namiki mana haduwar mu ta farko da ta biyu nasan na bata miki rai amma kiyi hakuri dan Allah kiyafe min duk abun da nayi miki bakiji dadi ba,
dan murmushi tayi saboda taji dadin wannan maganar tasa dan haka kai tsaye tace bakomai wlh ai ni bankullace kaba kuma tuntuni na yafema nima kayi hakuri bisa rashin kunyar danayi maka sharrin zuciya ne ka yafemin tafada tana dan satar kallon sa aikwa karaf suka hada ido dashi da sauri ta kawar da kanta tare da basar wa bata jira yayi magana ba ta dora dacewa wai nikam in tambaye ka mana yace fadi kanki tsaye wani murmushin ta qara saki jin abun da yace sai kuma lokaci daya murmushin yabace saida tayi shiru na wasu lokutan kafin wai ya akai ka ganni awajen nan kuma aya ka ganni?
Juyowa yayi yadan kalleta sai kuma yamayar da dubansa kan titi sannan yace bayan fito warki da kikace kintafi gida nikuma da na koma office sai nake ganin kamar nine sanadin dayasa kika shiga damuwa kika qi sakin jikin ki saboda abun da nayi miki da kuma wanda nagaya miki awaya shiyasa naji bankyauta ba sai na biyo ki ko zan sameki a titi sai inbaki hakuri sai kuma da na fita na nemeki na rasa nazatama kin tafi shiyasa na dawo bayan nadawo kuma nayi parkin nafito har zan wuce sai idona yafada wajen wani lungu sai naga kamar hannun mutum awajen hakanne yasa ni qarasawa dan ganin waye sai kawai naganki kwance awajen nazata ma ko mutuwa kikayi saboda yanda jikin ki yasaki gaba daya saida nasaita kunnena sannan naji alamar kina numfashi sumane kawai sai kuma yayi shiru kallon sa tayi tace sai kuma me ya akai naganni a office din ka tana gama rufe baki yace daukar ki nayi mana nakai ki zaro ido tayi tace dauka ta kuma yace eh mana to me kikeso inyi miki ko sokike inta tashin ki tace a'a yace to ina kaiki na yayyafa miki ruwa amma still baki farfado ba sai da nasa bakina anaki na toshe miki hanci na hura miki iskar bakina sanna kika kawo numfashi danazo kuma cire bakina sai kika riqe kika qi sakar min saida kika gama abun da kikeso sannan kika saki dan kanki qarasa fada yayi tare da satar kallon ta ta gefe yana boye dariyar sa,
azabure ta juyo tana kallon tare da ware idanuwanta akansa tace dan Allah da gaske yace nataba yi miki wasane tace a'a amma wlh nide banyi ba gaskiya bani Wlh banyi ba Allah sharri kayi min ni me zanyi da bakin ka da har zan ruqe wama yace kasaka min baki bada a kwai abun busa iska ba me yasa baka busamin da shiba zaka busa min iskar baki me wari ni har kasa ma nafara jin amai tafada tana kakarin yin amai wani wawan burki yaja da saida ta buge da gaban motar da sauri ta juyo a tsorace tace so kake ka kashe nine zaka ja irin wannan burkin harara ya galla mata sannan yace waye me warin bakin tace nifa ba da kai nake ba yace ko to fitar min amota kije kishiga motar da ba me warin baki ba tace dan Allah yi hakuri da wasa fa nake katseta yayi da cewa wlh bazan qarasa dake ba intaimakeki kuma kishigo motata kiringa gaya min magana nine me warin baki ko to nagode fita yafada yana nuna mata qofa hakuri ta qara bashi tana yar dariya ciki ciki yanda duk taga yabi yayi wani kicin kicin da fuska shi adole yaji haushin maganar ta shi yamata abun da yace mata itama ramawa tayi daman ance ramuwar gayya tafi ta gayya zafi juyowa tayi tana dan magana dariya nason kwace mata tace haba doctor ya da fusata haka maida wuqar to da wasa nake ramawa nayi kaima kasan abun da kafada ba daidai ban shiyasa nima nayimaka haka kayi hakuri muje kaga har magariba tayi kar amin fada yace ayi miki mana ai bada muwata bace ni malama kifitar min intafi ina da abunyi agida kafada ta maqale masa tace Allah ba inda zanfita tunda ka dauko ni sai ka kaine gida yace haka kikace to muje zuwa zankaiki gidan mu wlh kuma idan nakaiki zancewa hajiya sona kike shiyasa kika nace wai sai kinzo ki gaisheta daga nan kuma zan qara wasu abubuwan dariya tayi sosai har haqoranta na fitowa tace lalle baka san wacece niba sharrina yafi naka kasan nifa macece kar kamanta mata qannan shaidan dan haka kabini ahankali tafada ta na nuna kanta tana qara yimasa dariya shiru yayi kawai ya zuba mata ido yana kallon ta har mamaki take bashi yanda tasake dashi lokaci daya kamar ba itace ta gama kuka dazu ba kamar bata da wata damuwa shikuma daman yanasane yake ta janta da hirar duk dan saboda tasake yamantar da ita damuwar da take ciki shiyasa yake tayi mata haka kuma zaici gaba dayi mata har sai yaga komai daidai sannan zai maida ita gida tsagaitawa tayi da dariyar ganin irin kallon da yake mata, gira daya ta daga masa tare da cewa yade ko ka tsorata ne shima girar ya daga mata budar bakin sa sai cemata yayi tunda hakane bari inyi abun da nasan zaki iya yimin sharrin dashi kinga sai kifada adaidai yanda zatafi yarda tsoro ne yakamata saboda tasan halinsa ba kunya ce dashi ba bata gama tunanin ba taji yasawa motar luck tare da matsowa kusa da ita dasauri taja baya tace nifa matsala ta dakai kenan yanzu fa kagama ban hakuri da neman yafiyata amma shine zaka qara aikata haramun to ni duk abun da nafada dawasa nake taqarasa maganar cike da jin tsoron sa dariya ya kwashe da ita sannan yakoma inda yake yace matsoraciya ashe baki cika qanwar shedan dinba ai da sai in nunamiki nine shedan din ke kuma qanwata itama dariyar tayi tace to naji nide dan Allah muje kawai kallon ta yayi yace ina zamuje tace gidan mu mana yace dawa tace da wanda nake magana yace ai nagaya miki bazan kaiki gidan kuba saide gidan mu kuma nagaya miki abun da zance idan naje marairaicewa tayi tare da yin qasa da murya tace plsss mana zan siyamaka alawa a shagon qofar gidan mu inada canjin goma agida jajjiga kansa yayi sannan yace me kika maidani ni yaro ne da zan sha alawa tace to da maye tafada ciki ciki yace me kikace tace