abun da nakeso dakai shine yi sauri kagaya min wannan ce kawai damar da muke da ita tunda ya riga da yaganmu kuma nasan baze dawo ba saide kira yazo garemu fadamin yanzu kawai baba da kallon tausayi yabi yaron sai yaji qaunarsa har cikin ransa ahankali yace yaro baka jin tsoro kawai ina ganin mu hakura Allah ya kawo mana wani taimakon ta bangaren da bamuyi zato ba saboda bana so ta sanadina kashiga wata matsalar hamza yace ba komai kar kadamu ba matsalar da zanshiga yace to Allah yasa sai kuma yayi shiru saida hamza yaqara cewa loqacin fa ya wuce wa baba kayi sauri kafada kar suzo suriske mu anan still baba beyi magana ba sai da ga bisani sannan yadan nufasa numfasawa yace a unguwar kurna nake wajen masallacin na kowa idan kaje zakabi barin hannuka dakke tafiya bayan ka wuce masallacin da kadan sai kayi kwana hagu layi na uku zaka shiga kana shiga zaka ga wasu gida iri daya to basu ba nagabansu zaka ganshi me farin fanti da baqar qofa to nanne gida na hamza yace shikenan angama zan sanar da wani abokina in Allah ya yarda zaije har gidan yasanar dasu ka kwantar da hankalinka zantabbatar da iyalinka sun san halin da kake ciki koda zan rasa raina ne zanfita da kaina zanmaka wannan aikin da yardar Allah saboda tsabar jin dadi baba har yar qwalla ce ta tarar masa a ido sannan yace yaro Allah yayi maka albarka Allah ya albarkarci rayuwar ka yanda ka taimake ni kaima Allah ya taimake ka aduk halin da ka tsinci kanka Allah baka abun da kakeso duniya da lahira
da ameen hamza ya amsa shima yaji dadin addu'ar da yayi mishi tunda yake betaba samun wanda ze mishi irin wannan addu'ar ba sabo da amaraya yataso shikadai ne aduniyar nan bashi da kowa besan kowaba shiyasa tunda yaga baba yaji ya bashi tausayi kuma yadauke alqawarin taimaka masa domin bayaso 'ya'yan sa sutaso a haka basu da uba rayuwa ba iyaye baqaramar matsala kake fuskanta ba a rayuwa baba ne yakatse masa tunanin sa yace yaro naji kayi shiru tunanin me kake haka girgiza masa kai yayi yace bakomai ni zantafi sai anjima yafada yana juyawa tare da barin wajen baba binsa da ido yayi yana qara jin son yaron aransa yadade yana tunanin abubuwa kafin daga bisani kuma yajuya ya koma dan qarasa aikin da yake yi yana cikin yi yama kusa gamawa
Kamar daga sama yaji anshaqo shi tabaya tare da miqar dashi tsaye juyo dashi akayi kafin yayi wani yunquri yaji an kifa masa mari begama tantancewa ba yaji qarin wani marin da mamaki yadago yana kallon wanda yake marinsa ganin wannan bafaden da yayi mishi bulala tun ranar da yazo yasa beyi mammaki ba yasan zeyi fiye da wannan ma saboda ba imani ne dashi mutumin da ya mareshi bece mishi komai ba kawai yafara janshi kuma dan mugunta ta baya yake janshi ga shi ya matse masa wuya ana jawoshi ba fada akayi dashi ba part din fulani aka nufa dashi ana zuwa bakin qofar falon ya jefashi ciki kamar kayan wanki aikwa ba qaramar buguwa baba yayi ba dan da kyar ya iya dagowa sannan yadaidai ta kansa yazauna da qyar saboda dauriyace kawai irin tashi amma da ko tashi baze iya yiba yana zama aka shigo da hamza shima jefishi din akai amma dake shi da kwarinshi be kai ga faduwa ba yade yi tangal tangal ze fadi sai kuma ya dake ya tsaya da qafafunsa sannan ya tsugunna tare da sada kansa qasa saboda bama yaso su hada ido da baba shiyasa ya kawar da kansa
fulani ce dake hakimce a kujerarta ta dora qafa dayakan daya tana girgizata ta zuba musu ido tana yi musu wani matsiyacin kallo yayin da gefenta kuma shugabane agurfane fulani tace ina sauraronka fadi abun da kaji suna cewa
saida ya juya yayi musu wani irin kallo me nuni dacewa kunshigo hannu zakuce ubanku saida yasakar musu murmushi batare da sanin fulani ba sannan yace Allah ja daranki ranki yadade uwar masarauta tun zuwan wannan tsohon naga yanayin take taken shi na rashin gaskiya kamar ma da wata manufa yazo gidan nan ko kuma turoshi akayi domin tarwatsa farin cikin masarauta tunda naga haka sai naked bibiyar shi batare da saninshi ahaka nagano bakinsu daya da hamza kullum suna tare wani lokacin ma adaki daya suke kwana banta ba jin tattaunawar suba sai yau nazo wucewa naga shigarshi bangare dokuna shiyasa nayi saurin binsa abaya ina shiga kunnena yajiyo min abun da saida na kusan faduwa jinai wannan tsohon yana cewa kai tunda kazo ka kasa tabuka komai shekarar ka nawa amma ba abun da kayi nan da sati daya ni zangama dashi in koma inda nafito inje aban kudade na kai kuma kana nan ana wulakanta ka to ni bazan iya wanna bata lokacin ba dan inagama ko sati dayan bazan ba zan kammala abun da yakawo ni inwuce in barka inkaga dama ka taho inkuma anan zakai tazama saikayi
sai shi kuma hamza yace mishi ai shima yana gab da kammala nasa watakil ma yariga shi gamawa daga nan baqarasa jin maganar tasu ba najuyo saboda bana so sun ankara dani su cutar dani tunda mugayen muta nene su da harzanje ingaywa me martaba sai naga gwara nafara sanar dake ayi gaggawar daukan mataki akansu kafin su cimma mugun nufinsu yaqara sa fada harda dan guntun munafikin hawayen qarya.....
Fulani bata son lokacin da ta miqe tsaye ba tana takawa ahankali cike da qasaita ta qaraso gabansu tsabar yanda takejin zuciyarta nayi mata quna dan tazo wuya qiris take jira dan zata iya kashesu da hannun ta kafin su sukashe su gwara ita tafara kashesu amma bahalin yin hakan ayanzu saboda tanaso sufara fada mata wanda ya turo su zaga yasu ta shiga yi batare da ta tanka musuba saboda da tana tunanin wane irin hukunci zatayi musu
Allah sarki bayin Allah sunyi tsuru tsuru da su suna mamakin irin wannan sharrin da yayi musu musamman baba be taba tunani irin wannan sharrin ze musuba shikam hamza beyi mamaki ba sosai saboda daman yasan halinsa tun ba yauba yasaba yiwa mutane sharri amma kuma betaba gani yayi irin wannanba daga kai yayi sai suka hada ido da shugaba wani murmushi yasakar masa tare da kashe mishi ido daya kawar dakai hamza yayi tare da ayyana abubuwan dazeyi wa wannan mutumin idan angama yankewa musu hukunci sai yaji ya qara tsanar mutumin nan ko ganinshi ma baya sonyi kallon sa yamayar ga baba dake ta faman rawar jiki ga zufa da take zubo masa duk yabi ya fita hayya cinsa yana tunanin irin hukun cin da za ayi masa san ba qaramin tsure wa yayi ba dan yasan babu wanda ze yarda dasu kowa in yaji hakan baze yi tunanin suna da gaskiya ba saboda ba wanda ze tsaya yaji ta bakinsu akan zancen haka yake ko ba haka bane
Fulani ce ta data gama binsu da kallon tsana sannan ta koma kan kujerarta ta hakimce sanan tacewa wani bafade da suke kira da me doruna shine wanda yaje yataho da baba har ya mareshi kumafa ba asashiba kawai zallar mugunta ce irin tashi.......
kiranshi fulani tayi ya qaraso kusa da ita da hanzarinsa yace gani yake uwar masarautar nan umarnin ki kawai nake jira za arabasu da ransune yanzu ko sai anjima....daga mishi hannu tayi sannan tace mishi afara hora min su yanzu kafin suyi bayanin wanda ya aiko su tana gama fada yace yanzu kuwa kamar anyi angama yana gama fadar haka ya miqe tare da zaro wata narkekiyar zabgegiyar makadediyar zugegiyar shambareriyar 😂bulala ga wani tsayi da kauri da duk kallon kurillar ka baka isa ka gano da me akayita ba dan ko doki kaga andakeshi da ita sai yabaka tausayi bare kuma bil adama wanda ganinta ma kadai ya isa sa mutum shiga taitayinsa komai yake sai ya nutsu dan qaniyarsa......
yana zuwa ya daddage iya qarfinsa yadaga ta shimfidawa hamza a gadon baya aikwa ta shigeshi runtse idonsa yayi qam begama tantance zafin ba aka qara dora mishi wata jiyayi kamar yasaki kuka amma bazeyi ba saboda taurin rai irin nasa yanaji kuma ko motsi beyiba kuma be bude idon saba saida yaji antsaya da dukansa sannan ya bude idonsa da duk sun canza kala daga fari zuwa jajawur kamar gauta sai fuskarshi da ya hade kamar anyi mishi albishir da gidan wuta daga su yayi ya sauke su akan me dukan nashi da yaga ya tsaya akansa qeqam yaqi matsawa harara ya watsa mishi sannan ya kawar da kansa shima harar yayi mishi tare da matsawa daga gurin shi sannan ya nufi wajen baba da niyar shima ya bashi tashi alawar me zaki
Allah sarki bawan Allah baba ai tunda yaga bulalar ya tsure dan lokacin da akayi mishi ta farko bada irin wannan bace wannan ba qaramin tayar mishi da hankali tayi ba ga jikinshi sai faman kyarma yake ido yayi zuru zuru sai faman hadiyar yawu kake da qyar dan shima neman barin ma kogaronsa yake da yaga andaga ta kwa ansauke ta ajikin hamza ai tuni yasaki futsari awajen dan ji yayi kamar ajikin shi ta sauka😂 (Allah sarki baba daga dukan wani sai sakin futsari to ina ga kai aka daka watakil kuma sai kasakar musu tutu ka lalata musu falon da hamami)
Yana gani andaga ta za asauke mishi ita abaya yayi saurin runtse ido yana addu'ar Allah yasa yacika da imani dan yasan wannan bulalar idan ta sauak ajikin shi ai sai yatafi barzahu da mamakin sa sai yaji dif yadauka yatafi barzahu ma'ana yayi bunga yabar duniya sai kuma yaji wata irin murya da besan taba agun kuma yakasa tantance wa ko tawa ce ji yay ance kai me yasa baka da imani ne wallahi ka sauketa ajikin shi ko taba shi tayi sai nayi maka dari da ita kaji inda dadi mugu kawai marar tausayi kai in wanan mutumin fa a haife ya haife ka fa kai in aka daki babanka zakaji dadi to wlh baza ka dakeshi ba saide duk abun da ze faru ya faru
ahankali baba ya shiga bude idon sa amma yana gama budewa da mamaki bega baquwar fuska agun ba idon sane yasauka akan abun da yafi sashi mamaki da kuma daga hankali ba komai bane yasashi mamakin sai tozali da yayi da bulalar nan a hannun hamza ashe duk wanna zantukan shi yakeyi baba miqewa tsaye yayi yana kallon su ba shikadai ba duk ilahiran mutanen wajen ko saida yayi mamaki da ganin abun da hamza yayi anya yana cikin hayyacin sa yayi bawani abun ya shaba irin wannan katsalan dan din agaban fulani mayake damun sa to kode jinnu ne suka shafeshi kowade da kalar nasa tunanin dan ba wanda yayi tunanin acikin hayyacin shi yake irin wadannan maganganun.....
Wanda suke kira da shugaba ne yayo kansa a harzuqe ze kaimasa duka fulani ce ta da katar dashi da tare da cewa rabu dashi watakil aljanune ajikin shi je kakira malam baba yazo yayi masa ruqiya shugaba ya juya yana kallonta yace ranki ya dade bawani aljanu kawai ranine kibarni in ladaf tar dashi ya shiga hankalin sa bata kula shiba ta taso daga inda take ta zo gaban hamza da har yanzu be saki bulalar ba yayi tsaye kuma ba alamar tsoro a tattare da shi..
fulani da ta tsaya agabansa ta kasa magana tana kallon sa shi kuma ganin tsare shin da tayi da ido sai yasashi sunkuyar da nasa idondan baze iya hada ido da itaba data ga haka sai tace yanzu nagane na tabbatar da kana cikin hankalin ka to kasani ka tafka babban kuskure arayuwar ka kai har ka isa kahana ayi hukuncin da nasa kuma agabana zaka yimin katsalandan acikin abun da nazartar kai waye kasqantan bawa marar galihu marar gata marar asali kamanta lokacin da aka tsinto ka aka kawo ka gidan nan acikin bola kamanta atunamaka tana cikin maganar wata baiwa tashigo jikin ta na rawa tazo ta zube aqasa tace agafarce ni na katse ku daman wata matace tace ai mata iso dake tana nan wajen falon tana jira cike da jin haushi fulani tace taahi kifitar min kar nasake ganin qafar kowa anan kuma koma wace tazo ace mata ta koma bani da lokacin ta yanzu
jiki na rawa baiwarnan ta miqe ta nufi hanyar fita saide kuma bata kai ga fitar ba bakuwar dake tsaye awaje ta shigo ciki kanta tsaye tunda duk taji abun da fulanin tace sakamakon daga muryar da fulani tayi shiyasa tajiyo ta..
fulani dake niyar cigaba daga inda ta tsaya sai kuma ta zabura tare da juyowa dan tabbatar da muryar wadda taji da gaske ne kokuma gizo ne aikwa ta tabbatar ba mafar ki bane sakamakon murmushin da taga matar nayi mata tsayawa tayi tare da juyowa sosai tana fuskan tarta sannan ta qaqaro murmushin dole ta aza afuskarta tana cewa ashe babbar bakuwace ai bansan ke bace lale marhaban shigo tana fadar haka tajuya ga sauran tace ku fita gaba dayan ku zanne ne ku sannan kuma aje a qullesu dakin qasa kafin nagama zan nemeku duk mikewa suka yi gaba dayan su me dorina ya shaqo baba yamiqar dashi shugaba kuma yajawo hamza suka fara jansu za su fita faga falon kawai sukaji bakuwar nan tace WHAT!!!!!! da qarfi tare da sakin jakar hannunta tafadi qasa gaba dayansu dakatawa sukayi tare da kallon ta dan ganin me takeyiwa wannan ihun haka fulani ce tace Hajiya sara meke faruwa ne haka me yabaki mamaki kasa magana tayi sai can kuma tayi saurin daidaita nutsuwarta tare dacewa ba komai fa wannan bulalar ce ta tsorata ni amma de ba mutum ake duka da itaba jin hakan yasa fulani kallon su cike da tsawa tace uban me kuka tsayayi ku bacen dagani da sauri suka fita daga ciki
Bayan fitar su fulani ta naida hankalinta ga hajiya sara tace amma kinban mamaki sai kace yau kika fara zuwa masarautar nan kuma nasan bayau kika fara ganinta ba gaya min nasande da abun da kika gani amma ba wai bulala ba daukar jakarata da tafadi qasa tayi sannan ta koma kan kujera ta zauna itama fulani zama tayi akusa da ita tace ina sauraron ki gaya min hajiya sara tace a ina kuka samo wannan tsohon?
Fulani tace sarki ne ya samoshi yanzu kuma yazama bawanmu karkada kai hajiya sara tayi sannan tace babbar magana ana wata ga wata lokaci zeyi rana zatai halinta daman ance rana bata qarya saide uwar diya taji kunya Fulani da batasan inda maganrta ta dosa ba kuma takasa fahimtar me take nufi tace ke nifa kinsan aduhu kimin baya ni mana yanda zan gane kinzo kina tawasu maganganu daban gane kansuba kin sanshi ne ?
Hajiya sara girgiza kai tayi tace yau nafara ganinsa ma amma shawarar da zan baki shine ki gaggauta korarsa aginda nan yabar gidan nan tun kan lokacin ya qure miki
Fulani tace kamar ya kince bakisan shiba amma kuma kinace wa inkoreshi daga nan to me like nufi da hakan
Haji ya sara tadan yi shiru tana tunanin kuma wace qaryar zatai mata dabaze sa tagano da wani abun ba aqasa dan numfasawa tayi sannan tace hakan nan nace miki ki koreshi danni kallo daya nayi mishi nagane ba mutumin kirki bane daga ni wani abunne ya kawoshi shiyasa nace ki koreshi amma bawai dan nasan shiba
taqarasa fada tana kallonta danjin me zatace
fulani jin abunda tace sai ta sauke ajiyar zuciya a boye sannan tace ai mungano shi yanzu ma hukuncin ake yankewa kika shigo bakiji nace musu akulle suba zan nenesu ai tuni shugabansu yagano min shi shiuasa nake son aiki da wannan bawan yana min aiki yanda ya kamata baya wasa agun aikinshi...
Hajiya sara tace aini nasani kinga nima baki gaya minba amma nagane hakan saboda kina kallon idonshi zaki gane hakan kinsan halina da saurin fahimtar mutum.....
Fulabice ta saki wani qayataccen murmushi sanna tace ai nasan halinki kwa bari insa akawo miki abun taba sai muyi maganar data kawoki dan nasan halinki baza kizo nan hakannan ba dole saida dalili
Hajiya sara tace wlh a'a hakannan nazo mugaisa yanzu ma zantafi ana jirana a mota ta qarasa maganar tare da niqewa fulani tace wai da gaske tafiya zakiyi tace wlh tafiya zanyi jirana akeyi amota fulani tace to shikenan ai nagode ai nazata maganar dakika saba ce ta kawoki amma tunda kince haka to ki gaida gida tace gida zeji sai ankon biyu kuma fulani tace saide naganki kawai zakice ko kuma sai bukatar ki ta taso murmushi kawai hajiya sara tayi sannan tace naji koma me zakice ni kinga tafita tana kaiwa nan tasakai tafice bata jira cewar fulani ba dan ta matsu tabar gidan tunda taga wannan tsohon hankalinta yatashi zaman da tayima jinta take kamar akan qaya tana fita tace tabb nida qara dawowa masarautar nan ai har abada abun da yakawoni ma nafasa aikwa asatin nan ma zan bar qasar nan ma gaba daya bazaki qara ganin qeyataba tana tafiya said faman sauri take kamar zata tashi sama.........✍🏿
(haba hajiya sara yazaki barmu cikin duhu baki gaya mana komai bafa gaskiya kar kitafi😭)
_______________®_______________
*ANNOUNCING*
Hello readars Pls wait and read this
Nakusa dena posting akowane group zan ringayi a group biyu kawai 👌
Yan Facebook kuyi sarching din group din sarki SAMEER sannan kuyi join anan zanringa yin posting
Yan group din wasu WhatsApp din kuma ga number ta duk meso yayi min magana insakashi a group din WhatsApp 08124226526
_______________®_______________
#comment
#share
#likes
#vote
""""""""""""""""""""""""""""
[3/8, 10:26 AM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER.....💅
by❤xeemat.....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹