ganye hararar sa tayi tace naga alamar kafara shaye shaye ni wuce mutafi gaba yayi tana binshi ahaka har suka shiga cikin gidan suna zuwa falo suka tarar da Ammi nafaman yiwa bossay fada wai tana yi mishi magana yayi mata banza ya shigo gida ko sallama babu sai faman hade rai yakeyi shigowar sune yadaka tar da ita da sauri ta qarasa kusa da dadda tare da rungume ta tana cewa faruq a ina kasamo ta dadda ina kika shiga duk kintayar mana da hankali tafada tana raba jikinta da nata tana jiran amsar ta dadda ta dan saki murmushi tace ayya kuyi hakuri dan Allah wlh gidan wata qawata naje lokacin da na fito kuma kina bacci shiyasa kawai na tafi ban sanar dake ba gashi kuma hira tayi dadi bansam lokaci yaja haka tana gama fada ta samu kan kujera ta zauna Ammi binta tayi da kallo amma bawai dan ta yarda da abun da tafada mata ba kawai de zata rabu da ita tunda de bataso ta fadi gaskiya to sai su rabu da ita dan haka kawai saitace to ai shikenan tunda kindawo lafiya amma daga yanzu duk sanda kikaji kina son zuwa guri kisanr dani tuk lokacin fitar taki tayi sai faruq yakaiki ko kuma Aliyu ko basa nan ma ai aysher zata iya kaiki amma dan Allah karki qara fita bada sanin kowa ba tafada ayayin da take nufar kitchen dadda to kawai tace mata sannan ta ja bakinta tayi shiru faruq ne yace mata to kinji de dan haka sai kiringa fada ni kuma kullum zankaiki ai kece kedin ta dabance dole ko me nakeyi inbarsa inzo inkai amarya ta ko ina takeso amma wlh kidena fita ke kadai dan a unguwar nan akwai 'yan yankan kai zasu daukeki suje subawa aljanun su ke shikenan kin tafi kenan yafada yana qumahe dariyar sa dan yasan yanzu zata fara yi mishi bala'i ........
Ilai kuwa yana gama fadar haka ta haushi da duka waikai dan Allah yaushe zaka dena jawa mutane bala'i suna zaman lafiyar su baka da zance kullum sai yiwa wani mummunan fata to koma mekake yi ya koma kanka sannan tace kaini dan Allah ma daga yau karka qara zuwa inda nake tunda baka da halin kirki dan kaga ina wasa dakai shiyasa ka rainani to zan dena ka kusa dena ganin dariyata suna cikin wannan abun nasu,
su Ammi suka fara fito da abinci ita da sannan suka jere akan dinning faruq ne yafara miqewa sannan yamikawa dadda hannu wai ta tariqe ya tasheta amma sai taqi harda juya masa kai irin gayawa qeya dankwali yabaka amsa dariya yayi yace kinsan de daukar ki ba wahala zata minba dan haka gwara kitaso inkuma ba hakaba hmmm kinsan sauran tana jin hakan tasan kuma bata ido ce dashiba tsaf ze iya aikata hakan dan haka ta miqe tace kaide wlh kafiya takura jan hannunta yayi yace naji koma me zakice saida yaja mata kujera sannan yasake ta ta zauna bajimawa sauran yan matan gidan ma duk suka fita kowade ya hallara "amma banda bossay da tun shigowar su da yaganta ya yashi daga wajen yatafi part dinshi dan acewar sa yana son kasancewa shikadai san yasamu damar tunani dayawa ko ze gano wani abun"
Ammece tace wa mimi zekikira yayanku yafito shi muke jira da gudun ta kwa ta tashi ta nufi hanyar dakin shi bata dade ba ta dawo tace yace wai yaqoshi baya jin yunwa "ok"Ammi tace sannan furairah ta fara yin sarving dinsu nande kowa yafara cin nasa bamai magana acikin gurin yayi shiru sai qarar cokula kawai daya bayan daya suka fara tashi daga nan wasu suka wuce domin su kwanta wasu kuma suka zauna a falo suma kuma bayan wani dan lokaci kowa yatafi ya kwanta,......
"Washe gari bayan sun kammala breakfast suna falo dukan su dadda tacewa faruq to dan albarka qyande alqawari cikawa sai kazo mutafi ko kallonta yayi sannan yace to je kishirya kifito nutafi Ammi ce tace ina kuma zaku yace asibiti zankaita ance yau doctor din ze dawo shiyasa tace inkaita ta gani,
Ammi tace to kuna da tabbacin ayu ze dawo kuma ayau zefara yi mata aikin ni inaganin da kun hakura da zuwan nan kubarwa gobe koma jibi lokacin komai yafara daidaita kinga sai kije hankali kwance ko yakika ce ai hakan yafi ko tafada tana kallon ta dan jin abunda za tace dadda hade rai tayi tace nifa komai zaki fada sai de kifada dan koda 'assayada dita sai naje Ammi shiru tayi sannan tace to Allah ya kiyaye hanya Allah yabata lfy sai kundawo faruq idan akwai wata matsala sai kayi gaggawar sanar damu yace to Ammi yana fada yace to ai sai kitashi mutafi ko tashi tayi ta gyara mayafinta da ta ruqoahi ahannu tun lokacin data fito daga daki tana gama gyarawa faruq yace bari indauko mukulkin motar tace to sannan ya haura sama da gudu yana shiga ba jimawa yadawo riqe da mukullin motar "ba bata lokaci suka fice daga falon suna fita suka shiga mota faruq ya tayar da motar sannan yajata da gudu suka bar gidan gudu yafara yi kamar yanda yasaba saida dadda ta dakatar dashi sanan yadan rage gudun yana tafiya daidai shi ba guduba shi ba ahankali ba ahaka har suka qarasa.....
tundaga baking gate suka ga anata share share daza sushiga kwa saida aka tsaidasu aka bincika su sannan suka shiga ciki kuwa jama'ane ta ko ina kowa da abun da yakeyi ana ta gyare gyare sude sunga ikon Allah basu san neyake faruwa ba komai za ayi oho basu da me basu amsa parking yayi sannan suka fito suka nufi ciki bayan sun shiga kuma sai suka rasa inda zasu dosa da qyar de suka iya kai kansu wajen da suka tsaya ranar nan dadda tace to kaje kakira mana shi mana muji ya ake ciki ko shiru yayi sannan yace nifa dadda wlh ba inda nasani kawai mu tsaya anan idan Allah ya kawo mana wani sai mu tambaye shi tace in kuma bawanda yazo fa sai muyi ta zama kenan yace in Allah ya yarda ma baza murasa ba "yana gama rufe baki kwa sai ga dr.shettima kamar anjefoshi sai faman sauri yake harze gotasu ze wuce dadda tayi saurin dakatar dashi tace bawan Allah dan Allah tambaya muke ganin ita tsohuwace yasa shi dakatawa duk da irin saurin da yakeyi ahankali yace inajinki tace dan Allah daman mune wadanda muka kawo wata yarinya da za ayi mata aiki akace sai babban likita yadawo kuma ance yau ze dawo shine muka zo muji ko ya akciki dan dawowa yayi kusa da ita sannan yace ok to kujira yanzu haka ma da kuka ganni sauri nake zanje na dauko shi a airport dan ko gida ma basu san da saukar shiba yace nan ze fara zuwa idan ya dubata sai yaje gida dan haka ku kwantar da hanjalinku yanzu zamu dawo tare kujirani hamdallah dadda tayi sannan tace to shikenan Allah ya dawo daku lfy gsky naji dadi sosai kayi sauri kaje dan Allah dan na matsu inga anyi mata aikin nan tadawo gareni jinjina kai yayi sannan yajuya ya fita yana fita ya afka mota yajata a sukwane yayi waje yana zuwa ya doka horn da sauri gate man ya wangale mishi gate din shikuma yadanna hancin motar ya kwasheta a guje ya fice gudu kawai yake ba qaqqautawa cikin yan mintina kadan ya qaraso airport ✈yana zuwa kwa yaci sa'a be makaraba domin lokacin da yazo lokacin jirgin yagama sauka Hamdalah yayi dan duk azatonsa idan yazo ze tadda shi yana jiran sa shiyasa yake ta gudu saigashi kuma yazo akan lokaci fita yayi daga motar ya tsaya agaban motar yana jiran fitowar sa sabda already jirgin yagama sauka dan har wasuma sun fara fitowa saida yadade agun dan yana tunanin ma mutanen ciki sungama fitowa gaba daya amma begansa ba to kode be tahoba sai kuma yatuna ai baya magana biyu tunda harya kira yace yataho yadauke sa to kwa yasan dole yataho din kuma watakil abun nasane ya motsa yanzu haka yana cikin jirgin sai yaga damar fitowa sannan ze fito gajiya yayi da jiransa dan haka yafara takawa zuwa gaban jirgin da niyar ya leqa yaga ko yana nan din dagaske tunkan yaqarasa ma yaga ansako qafa daya dakatawa yayi saboda yana da tabbacin shine dayar qafar aka sako ahankali kamar ba a so ake ajiyeta sannan yafara saukowa gaba dayansa har ganganr jikin sa ta bayyana tundaga qasa nafara kallonsa har zuwa sama bansan lokacin da na sume ba na dawo saboda tsabar tsorata danayi bazan iya kwatan ta muku abun da nagani ba yanzu dole sai nabari na kwakwalo jarumta zuwa gobe sai in bayyana muku........✍
*tode daga yau nagama posting kamar yanda nagaya muku sai a group biyu kacal zan ringa yi saide kuma ko wani ze iya yin share to another group*
Follow me all👇
wattpad@xeemat
Arewabooks@Azeemadahiru
Facebook @Azeemadahiru(xee
Whatsapp@~~~~~writer~~~~~
My WhatsApp number is 08124226526
💅SARKI SAMEER....💅
by❤xeemat.....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
﷽
Bismillah........ ✍
Episode42-43
""""""""""""""""""""""""""""""""""
tundaga qasa nafara binsa da kallo har zuwa sama masha Allah dogone amma bacan ba sosai yana da dan budewa da faffadan qirji gashi da cikar haiba kallo daya zakai mishi kagane wannan ba irin sauran maza bane shidin na dabanne ya shabam bam da sauran danni tunda nake bantaba ganin mutum me irin zubin halittar shi ba domin abar kallo ce koda ita kadai akabarka akace kai ta kallo kar ka kalli fuskar shi to hakan ma ba qaramin dadi zemaka ba domin zakai ta kallane batare da kagaji ba tunda nayi mishi kallo daya jiya haryau bandawo daidai ba sai tunanin shi nake jikin shi sanye yake da jens ne yellow sai rigar ma yellow ce sai wacce ya dora akai kamar ta sanya me gashi gashi ita kuma baqace kuma ta sauko mishi qasa har wajen gwiwa kuma tana da huciki mma besaka hular ba ahankali nafara bin fuskar shi da kallo fari ne sosai har wani jaja yake kamar idan kasa yatsa katabashi jini ne ze fito tundaga kan lips dinshi nafara bi da kallo dana kasa gane wane irin kalane ko kuma abun yashafa oho ammade gashi nan kamar red kamar pink kalar tayi kyau sosai kuma ba babba bane dan qarami ne amma ba sosaiba sai dogon hancin shi sai idanun sa dara dara gasu farare tas dasu sannan sexy ne sai eyelashes din sa dogaye ga cika kamar na mata sai eye brown dinsa da ta wani fidda shap kamar anyi shaving dinta asaite take gata baqa kamar ansaka mata kwali sai gashin kansa da yake akwance luf yasha gyara dan harya zubo kan goshin anyi masa wata kanan nada yayi kamar macaroni sai Bluetooth da ya maqala akunnen shi guda daya hannunshi daya a cikin aljihun rigar jikin shi dayan kuma yana ruqe da trolley ahankali yake tafiya kamar bayaso da sauri dr.shettima yaqarasa gurin sa tare da yin hugging dinshi tare da cewa you are well come my man I'm so happy to see you I wanna miss You too much duk wannan abun da yake besamu arzikin anyi mishi magana ba kuma yana tsaye ko motsi beyi ba bare kuma yamayar masa da hugging din dayayi masa saida yagaji dan kansa sannan yataba jikin shi danashi yana ta faman sakin murmushi da gaske de yaji dadin dawowar tasa kuma qin kulasan dayayi be damesa ba hannu yasa yakarbi trolley din hannun sa sanna ya ruqe hannun sa suka fara tafiya har suka qarasa wajen motar sannan ya bude mishi ya shiga sai ya bude back seat yasaka trolley din sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver yazauna tare da yiwa motar key tare da yin reverse yasai ta kan mota sannan yafara tafiya a tsanake dan juyawa yayi ya kalle sa saiga ya kwanatar da kansa jikin hannun kujera ya lunshe idon sa kamar me bacci ganin hakan yasa shi yin shiru shima dan yasan tunda yaganshi haka to ko meze ce mishi ba amsa ze samu ba dan haka gwara kawai yayi shiru shima,,
ahaka bawanda yayi magana har suka qaraso hospital din yana gama parking yaqara kallonshi tare da kiran sunan shi yace SAM muqaraso fa shiru ba amsa kuma har yanzu be bude idonsa ba saida yagama shan qamshin shi sannan ya bude idon sa yadan kallishi batate da yace komai ba kuma yabude motar yafita da shima budewa yayi ya fito yarufe qofar yazagayo ya koma kusa dashi yace ka tsaya ko sai na dauke kane sai yanzu ya bashi amsa shima ba bude baki yayi ba kwai uhm yace mishi dr. shettima sai yadanyi murmushi yace ai zan iyane kar ka ganka wani qato dakai ba wahalar dauka zakamin ba jinjina mishi kai yayi sannan yafara tafiya ba tare da yabashi amsa shima bayansa yabi dake kowa yasan da dawowar sa yasa ba kowa awaje kowa yakama aikin gabansa gudun jawa kai matsala any mistake game over qaramin abu zakayi yayi firing dinka dan haka kowa yake taka tsantsan idan yazo dan surabu lafiya tunda ba dadewa yakeyi ba idan yazo,
yana tafiya yana kallon asibitin har suka shiga ciki nanma kalla yaringayi office dinshi asama yake dan haka direct suka nufi sama saide suna dab da fara hawa benen saiga dadda tsudum abayansu tan cewa to yaza kutafi bayan kasan tundazu muke jiran ku tsayawa dr.Shettima yayi saboda yagane muryarta amma banda dayan dan har ya qarawa motarsa mai be tsaya sauraron taba duk da yasan dasu ake magana dr.shettima ne yace kiyi hakuri baiwar Allah yanzu yadawo kinga dole sai yadan huta tukunna ze samu damar fitowa kuqara hakuri tunda saboda aikin nata nema yazo nan da baze zo bama kujira kinji baba jiki asanyaye dadda tace to aishikenan yafito lafiya munade jiransa yace to karkidamu bawani dadewa zamuyi ba yana fada ya wuce shima dadda komawa tayi kusa da faruq, faruq na ganinta yace dadda yanaganki haka me ya sukace miki tace bansani ba din ni wlh banma san neye amfanin ka ba kazo kayi zaune nida nake mace ni nake qoqrin jin ba asi kaide anyi malalacin namiji ni kakiramin wancan yaron duk wulakancin shi yafika wayewa da shine da tuni yayi abun da yadace amma kai sai wani noqewa kakeyi saikace dan qauye kwata kwata baka wayeba sai iya shiganta ka anan kafi kauri dariya yayi sosai yace lalle dadda yanzu nidin ne ban waye ba ki kallenifa kina ganina kinga wayayye dan zamani yafada yana wani kada kai harda juya ido saikace mace kasake dadda tayi tana kallonsa tace ikon Allah kai abun naka kullum gaba yake ji yanda kake abu saikace mace wannan ce wayewar da ancuci wayewa wlh da ka waye ai baza ka tsaya anan ba ni wlh nama yi danasinin tahowa dakai daman wancan yaron na lallaba muka taho yace au yanzu dadda hakan ma danayi miki bazaki gode min ba saide ki ta kusheni kina yabon wani to bari intafi gida sai kikirashi yazo din yana gama fada ya tashi yana niyar fita daga wajen da sauri dadda tace la ai da wasa nake dan albarka tsokanar ka fa nake dawo muzauna ai yanzu komai yayi daidai tunda na tambayo kuma yanzu zasu fito tafada tana danyi murmushi kwabe fuska yayi yace Allah kisake ni intafi bazan zauna ba kuma daga yau bani bake munkunce tace haba dan albarka ai nasan baza muyi haka da kaiba ko baka so inbaka jikar tawa inde kanaso dole kazauna dani inkuma bakaso shikenan na yarda mukunce din kuma in munkunce baza mu sake daurawa ba tafada tana mika mishi hannu alamar sukunce din sai yamaqe kafada yaqi mika nashin yazata da gaske take dariya tayi sannan tace ja'iri ai nazata zaka yarda din ashe baza ka iyaba banza yayi mata ya koma inda yatashi yazauna tare da juya mata baya wai shi adole yayi fushi da ita itama kusa dashi ta dawo ta zauna tana dan dariya qasa qasa saboda kar yajita,
dr.shettima yana zuwa bakin qofar yadan kwankwasa sannan shiru ba amsa saida yadanyi jiran kamar 1 minutes sannan ya bude ya shiga ciki be wow aljannar duniya office iya office ya hadu iya hasuwa kamar ma ba office ba abubun ciki komai farine gashi yasha gyara tunkan zuwan shi daman kullum sai anshiga an gyara duk da bayana table din farine sai abubun kaine kawi suka kasan ce black sai kujeru guda biyu na zaman wan inya shigo ze zauna sai fridge shima fari saide shi sai fulawoyi da akayi ado dasu sai wani tamfatsetsan hoton shi da ke maqale da bango kana shigowa dashi zaka fara cin karo saboda yana facing din qofar shigowa suka dai ne aciki sai qofofi biyu danake da tabbacin daya kitchen ne dayar qofar kuma bedroom ne,......,
dr.shettima yana shiga ciki sai yaga baya nan dan haka sai kawai ya nufi bedroom din dayake da tabbacin yana ciki nan ma saida yayi nocking sanna yadan qara bashi lokaci idan ma wani abun yake ya gyara saboda yasan ba lalle yayi mishi magana ba kai tsaye ya tura qofar yashiga ciki da mamakin sa yana shiga yaganshi a baje akan bed ko takalmi be cire ba qarasawa yayi gabanshi ahankali yakira sunan shi amma shiru ba amsa saida ya kalleshi sosai sannan ya fahimci ashe har bacci yayi awon gaba dashi adan kankanen lokaci ysugunnawa yayi yacire masa takalmin qafar sa sannan yagyara masa kwanciyar sa yafito daga dakin har ze fita kuma sai dadda ta fado mishi tana can tana jiranshi gashi kuma me kankat din ya kwanta bacci besan kuma lokacin tashin shiba dan ze iya daukar lokaci yanayi gashi kuma qaidar shice idan yana bacci ba a tashinshi sai yaga damar tashi dan kansa fita da har yazauna a office din Nada sai kuma ya miqe yafita