SARKI SAMEER BOOK 1 Hausa Novels

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   42 / 49

123K to 126K   out of 145.7K words

yaga daya harta wuce amma hakan be hanasa lalubo number shettima ba kiransa ya shigayi amma ba amsa beyi qasa agwaiwa ba yaqara kiransa dan atunanin sa ko yayi bacci amma yanzuma ba amsa saida yakira sa har saubiyar sannan ya hakura yabarwa gobe tare da yin cilli da wayar gefe ya kifa kansa qasa yana taso yayi bacci amma yakasa ahaka bashi yayi bacciba sai wajen uku bacci ya dauke shi,
washe gari da gudu ya shiga wani daki akidime yace tana ina yarinyar tana ina tanbayar ka fa nake kamin shiru kagaya min inda take be gama rufe baki ba yaga anturo ta akan gadon asibiti za asaka ta a mota bisa ga dukkan alamu kuma bata nufashi da da gudu yayi kanta azafafe shettima yayi saurin da katar dashi idonsa duk ya canza kala kamar ma kuka yayi da kyar ya iya bude bakin shi yace yanzu burinka ya cika ka kasheta ko to kasani baka ta mutu abanza ba dan sai na bimata hakkin ta nima da hannuna zankasheka yanda kazama sanadin mutuwar ta to nima nine sanadin rabaka da duniya yana gama fadar haka yayi kukan kura ya cakumo shi yashiga naushinshin ta ko ina tare da shaqe mishi wuya hannu yasa yana qoqarin kwace kansa amma yakasa saboda irin ruqon da shettima yayi masa bana wasaba ne tun yana gani har ganinsa yafara daukew kuma yana taso yaay magana amma maganar ta makale taki fitowa hannu yasa suka fara kiciniya shi yanaso ya kwace shikuma ya riqeshi gam ya hana sa damar yin hakan tafiya yayi luuu zefadi da sauri ya bude idon sa tare da miqewa zaune yana tattaba wuyan sa ko zeji hannun mutum saide ba komai ajiyar zuciya yasauke tare da katanto addu'a idan mutum yayi mummunan mafarki ashe tunda yatashi yayi sallar asuba ya koma kuma sai yafara wannan mafarkin dan shi duk atunanin sa gaskiya ne agogo ya duba yaga har goma ta kusa wayar sa yadauko akan bed side drower kiran shettima yashiga yi amma ba adaga daga qarshe ma sai yaji wayar sweach up akansheta gaba daya ta kaicine ya cika shi yanzu yanaji yana kiransa amma ya kashe wayar yana sane lalle akwai matsala kenan betaba tunanin haka daga garesa ba ya dauka duk cika baki hake ashede ze iyadin text ya dan tafa ya tura masa sannan ya ajiye wayar yaje yayo wanka yafito ya shirya sannan ya baro part din be je ko inaba agidan kawai ya nufi inda motar shi take yanazuwa driver ya bude masa ya shiga sanan yace masa nasarawa zasu tunda yaji haka yasan inda zasu dan haka yadauki hanyar gidan su shettima ,

Shettima kwa jiya yana barin asibiti da ita a tunanin sa yatafi da ita abuja sai kuma ya tuna wani abu da sauri ya zaro wayar sa wata number naga yasaka ana dagawa bayan sun gaisa yake cewa yake cewa ya kashigo nan ne naji kace zaka shigo tun wancan satin daga can najiyo wata murya ance na shigo mana gobe na zan koma ai yace ok yanzu kana gida yace yace to dan Allah zankawo ma patien ka duba min ita ko zakazo gidan mu ka dubata kawai yace ok ba matsala bari inzo din kawai amma meyake damun ta adan takaice de yayi masa bayani yanda ze gane sannan sukayi sallama yaji dadi sosai wanda yakira wani abokin shine da suka hadu acan iyayensa duk yan nan ne amma sun koma can da zama gaba daya karewa ma shi acan aka haifeshi shiyasa komai nasa irin nacanne ba abun da yake irin na 'yan Nigeria shima kuma duk fannin yake karanta shi haryanzu be gama ba tasanadin shi yasaba da Nigeria har yake shigowa hakannan yadan huta sai yakoma wataran ma idan yazo ba lalle bane su hadu saboda shi abun da yake kawoshi daban yana zuwa ne yayi holewar sa da 'yan mata yakoma saboda yana jin dadin rayuwa da 'yan matan nan qasar,
hankali yake tuqin dan yanzu hankalinsa ba qaramin kwancuya yayu ba yasan beda matsala tinda ya hadu da makel sunansa Abbas amma yan can kowa da haka yake kiran shi babansane kawai yake cemasa abbas saboda shi yarada masa kuma yana son sunan,
yasan be da wata damuwa zeyi masa duk abun da yakeso ahaka har yaqarasa gidan yana gama parkin ya fito ya dauko ta ya nufi cikin gidan da ita dakin hajiyar sa ya nufa da ita yana zuwa taganshi da yarinya akidime take tambayar sa a ina yasamo ta ko bigeta yayi ne ce mata komai ba saida ya kwantar da ita akan gadonta sanan ya shiga yi mata bayani sosai taji tausayin yarinyar ya shigeta sannan tace gaskiya banji dadin abun da sam yayi ba ko ba komai ai ya tasaya mata saboda rashin lafiyar ta amma yanzu ka tabbata wanda zezodin ze iya yace eh hajiya shimafa kwararren likita ne yagama kwarewa kuma har yanzu bedana neman ilimin ba yana aikin sa kuma yana qara neman wani ilimin kinsa su sunfison kimai sai sunyi zurfi sosai aciki suke hakura tace to masha Allah daman Allah inya hanaka ta wani wajen saikaga ya buda maka tawani wajen suna ta tattaunawa de akan matsalar har wayar sa tayi qara dubawa yayi yaga makel ne ke kira da sauri yadaga tare da cewa ya ka iso me yace masa yaece ok gani nan fitowa yana katse wayar yace hajiya bari inje in shigo dashi tace to maza bayan fitarsa ba dadewa suka dawo ciki tare ya ruqo masa yar jakar da yataho da ita bayan ya gaida hajiya yafara dubata yace ai doguwar suma kawai tayi sakamakon kukan da tayi ne har yataba mata kanta sanadin hakan kuma komanta ya tsaya saboda ba adade da yi mata aiki ba kuma daman irin hakan na faruwa shiyasa akafiso mutum idan anyi masa anaso yasamu nutsuwa sosai karya ringa shiga damuwa ko ana yawan yi mishi hayaniya duk hakan ze iya jawo watamatsalar sun gamsu da bayanin sa sannan sukace in Allah ya yarda za akiyaye cigaba yayi da aikin sa yasaka mata wani abu abaki bata dade ba kwa ta sauke wani wahalallan numfashi hamdalah suka shigayi suna yimata sannu saida ya dubata sosai sannan yabasu magungunan da za sudorata akai da kuma hanyoyin da zasubi wajen ganin hakan bata sake faruwa yace inde anyi haka to da wuya ma takai sati bata dawo normal ba adan kwanaki zata dawo yanda take kamar da sunji dadin bayaninsa sosai musamman shettima da har dan murmushi yake saki sannan ya shiga yimasa godiya hajiya ma tayi masa tata sannan yaqara yi mata allurar bacci dan tasamu isashen bacci yace musu kuma ko zuwa gobe zata tashi rass kawai de bazata dawo kamar yanda take ba sai ahankali sannan adan ringa gwada mata tafiya saboda dadewar da tayi a kwance shima sai ahankali qafafunta zasu ware sosai yayi musu bayani dalla dalla bayanin dashi ogan ma beyi musuba shikwa komai yasanar dasu daga haka kuma sukayi sallama shettima ya rakasa har motar sa ya shiga leqawa yayi ya hango wata mace fara tas kana gani kuma kasan ta hada da bleaching kallon da yayi yace kai ko har yanzu bazakadena kwashe kwashen nan ba ko dan murmushi yayi yace zan dena amma ba yanzu ba sai nagama more rayuwata tukun badan irin sudin ba me ze kawoni qasarku dariya sannan yace su naku nacan me sukayi da said anzo tamu akeyi yace can ai kasan dalili saboda tsaro in bahaka ba old man kasan halinsa ya saka min ido da yawa shiyasa na fiso inzo nafi sakewa kuma yan nan sunfi dandano yafada tare da daga masa gira daya yace hamm Allah ya gyaraka ni wuce ko kunyata ma bakaji ko tafi kar kasa kunnuwana sude na ji zama dakai said wanda yashirya tayar da motarsa yayi sannan yace kaima bakagane bane shiyasa kake tazama ahaka ga ba aure ga baka dan hutawa kana qoqari danni wlh bazan iya jurewa ba ko kwana daya nayi banjini cikin mace ba akwai matsala shiyasa kullum muna manne yace to Allah yashirye ka to waya hanaka auren yace aure ba yanzu ba gwara na waje de shettima yace aikwa in bakai wasaba sai nakai qarar ka gurin old man dinka tunda shikadai kake tsoro ko Allah baka tsoro sai shiko dan tabe baki yayi yace kaga ni zan wuce ka ajiye surutan ka kayi su wani lokacin yana gama fada yatayar da motar tare da daga masa hannu sanan suka tafi shikuma ya koma ciki yana jinjina irin wanna halin na abokin shi da baya jin tsoron Allah kamar ba dan musulmai ba idan katabo masa Allah ma yanzu zai barmaka gurin da tunanin sa ya shiga ciki dakin yaqara komawa ganin ta akwance cikin kwanciyar hakali yasa shi jin wani farin ciki ya lullubesa shikenan yana fatan daga yanzu qarshen wahalar ta yazo kenan tunda yashigo hajiya take kallon sa ganin gaba daya hankalin sa yana kanta tadan yi masa gyaran murya tace kallon fa dan sosa qeya yayi sannan yace hajiya wlh ina tausayawa rayuwar ta ne hakan nan tun haduwata da ita ta farko naji tana ban tausayi tace Allah sarki Allah yabata lafiya yace amin daga nan suka dan taba hira sannan tace yake ya kwanta tundade ba farkawa zatayi ba sai zuwa gobe ita zata kula da ita da qyar ya hakura ya tafi dakin sa bayan ya shiga ne yagama duk abun da zeyi ya kwanta har baccima yadan fara daukar sa yaji wayarsa na qara da ya duba yagani yayi mamakin ganin me kiran yagani har ta tsinke wani yasake shigowa shima kin dauka yayi da yaga ba dena kiran zeyiba kawai sai yasa wayar a silent yakifata saboda idan ma yadaga besan me zece masa ba kuma besan me zejiba yana ganin watakila ma yakiraahine kawai ya kuma gaya masa wata maganar banzar shiyasa yaqi dagawa ahaka har bacci yadauke shi zuciyar shi cike da farin cikin samun lafiyar Ameesha,

Washe garin tunda ya tashi be komaba yana dakin hajiya yana jiran yaga farkawar ta duk yanda hajiya taso dashi akan yakoma ya kwanta zuwa anjima tana farkawa zata je ta tasheshi amma yaqi fur yace shi bayajin bacci koma hake ya kwanta ba iyawa zeyiba haka ta rabu dashi Ameesha de ba ita ta farka ba sai wajen tara da rabi tafara motsi da hannun ta sanan ta bude idonta duk abun da take akan idon sa da sauri ya tashi ya dawo kusa da ita tare da ruqo hannun ta yana mata sannu da ido kawai ta amsa masa tana qoqarin tashi yayi saurin tashinta ahankali tace zan shiga bandaki da taimakonsa tashiga saboda lokacin hajiya bata dakin tana kitchen ita da me aikinta suna hada breakfast na musamman saboda marar lafiya,
Bayan yakaita bandakin ne kuma sai ta tsaya fitsari zatayi kuma taga ya tsaya yaki fita shiyasa itama ta tsaya shima kuma jiranta yake tayi abun da zatai ya mayar da ita ganin hakan sai yace mata ko zaki wanka tace eh dan daman tana bukatar yin wankan saboda jikin ta duk wani iri take jinsa ruwa me dumi ya hada mata sannan yace to zaki iya cire kayan ko saina cire miki zaro ido tayi jin abun da yace sannan tace zan iyama na yace a'a baza kiya iyaba wlh wankan ma ai ni zan miki nasan ba iyawa zakiyi ba juya muyi sauri kije kici abinci make kafada tayi tace nide wlh ka fita zanyi komai da kaina yace a'a wlh baza ki iyaba hannu yasa ze cire mata riga tayi saurin riqewa tare da sakin yar qara tace Allah banaso dan Allah ka rabu dani tsayawa yayi yana bin dan qaramin bakinta da kallo tare da binta da kallo tundaga qasa har sama yana so yagano abun da take cewa kar yataba ita bata so ita kaza ita kaza yana tunani to ita nan me take boyewa yar qarama da ita koma meze gani nawa take gaba dayanta(uhm uhm fa ale shettima akwai fa yan biyun ta kuma sun fara wayo irin sune ma suka fi tada ehhh irin ehh dinnan😎saboda a tsatstsaye suke🙈 bari inyi ta kaina🏃 naga ya watso min harara dan kawai mafadi gaskiya ko qarya nayi jama'a kutayani ji👂)


*wannan na jiyane da ban qarasaba sai yanzu in Allah yakaimu na yau yana nan tafe zuwa dare*
[4/7, 10:48 AM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode79-80-81

         """"""""""""""""""""""""""""""""

bafa zaki iyaba kibar inyi miki tace uhm uhm nide kabar ni Allah bazan iya tsayawa ka kalle ni ba kawai kaje in kuma bahaka ba to nafasa duk wannan maganr da yakeyi still de ba janye hannun sa ba kwan kwasa kofar bandakin akayi hakan yasashi sakinta hajiya ce tace wai meyake faruwa ne yace hajiya wai bazata tsaya inyimata wanka ba daga waje hajiya ta riqe baki tare da turo qofar tace wanka fa kace taya za ayi ta yarda dallah fita kaban waje sai kace wata yarinya zaka wani ce zaka yimata wanka kallon hajiyar yayi tare da kwantar da kai yace hajiya to meye aciki ni kamar qanwata na dauke ta tace Allah ko ai naga alama to fice min daga nan zanyi mata badan yaso ba yafita dan shi har ga Allah so yake yayi mata din bayan ya fita ta maida hankalin ga Ameesha da tayi wani tsuru tsuru tana kallon su tace yata yi hakuri haka halinsa yake shi be cika jin kunyar abuba bashida ita sam toho inyimiki ahankali tace zan iya da kaina a'a yata bazaki iyaba bakiga jikin ki ba kwariba kibari in dan taimaka miki in gagga sa miki shi kinji badan taso ba saboda matar tunda taganta taga tayi mata kwarjini hakan bazesa tayi jayayya da ita ba tunda de babbar macece ahaka tanaji tana gani ta sutale mata kaya tsaf sanna ta sakata acikin ruwan dumin saida ta gasata sosai sannan ta qara hada wani ruwan ta dirjeta tsafa tabata sabon brush ta wanke bakinta sosai sun dau lokaci aciki kafin ta bata towel ta daura sannan ta dan ruqota suka fita suna fito suka ga baya dakin zaunar da ita tayi sannan ta dauko mata mai ta shafeta dashi kamar de qaramar yarinya haka ta ringa kula da ita bayan tagama yi matane kuma kayan da zata bata tasaka suka fado mata tashi tayi ta nufi wardrobe dinta tanaso tasamo mata doguwar riga wacce zata danyi mata dubawa take tayi amma duk wacce ta dauko sai taga sunyi mata yawa sosai tana cikin haka sukaji sallamar shettima yashigo hannu sa riqe da leda hajiya na ganinsa tagabe meye dan haka kawai sai tasaki murmushi tace yauwa aikwa kayi tunani me kyau kaganni tundazu nake tunani abun da zan bata tasaka na rasa idon sa na kan Ameesha tunda ya shigo ya kafeta da su yana kallon santala santalan cinyiyinta da towel din be gama rufesu lura da hakan yasata dan ringa jan shi duk saitajita atakure saboda kallon da yake mata ba zato ba tsammani yaji antalle masa qeya sannan tace bani kafita beyi musuba yabata ya juya saboda yaji kunyar kamashin da tayi bayan zarowa tayi wata doguwar riga ce ash color sai dan ratsin baki ajikin ta mayafinta ma bakine marar kunya harda bra da fant  duk ya siyo mata kala uku uku bata tayi tace tasaka bari taje ta kawo mata abinci kafin ta shirya bayan ta shiryane ta shiga bin kanta da kallo duk da bata gani ba amma tanaji ajikinta tayi kyau ba qarya ahaka hajiya tashigo da faranti a hannun ta tana shigowa sai gashi shima yaqara shigowa duk tare da ita suka ci abincin suna cikin ci kiran sameer ya shigo wayar sa amma sai yaki dauka hajiya tace wayake kiranka ka dauka mana hade rai yayi sannan yace bazan dauka ba ina dauka wani rashin mutuncin ze qaramin kuma inya qara nima ba barinsa zanyiba shiyasa bazan daga tagane akan wanda yake magana sai kawai tayi shiru bata qara tanka masa ba bayan sungama ta tashi tafita da kwanu kan tana fita Ameesha kamar jira take ta fita ta juya ta kalle sa tace nifa tundazu nake so in tambayeka wai ya akai naganni anan duk de naga alamar gidan kune tunda naga kana kama da mahaifiyar ka  ina asibitin kuma ina 'yan uwana yace zan gaya miki ba yanzu da marairaicewa tayi tace dan Allah kagaya min yanzu wlh tunda na tashi nake so na tambayeka amma saboda maman ka nakasa yace "ok" sannan ya shiga bata labarin abun da yafaru tun lokacin da yafito tasaka kuka harzuwa lokacin da ya dauko ta har fadansu da sameer ma be boye mata ba atake taji wata muguwar tsanar sa ta kamasa wannan wane irin marar imani ne bashida tausayi ashe so yake yarabata da duniyar ma gabaki daya saide kuma Allah yafishi gashi tasamu lafiya fiya da da lokacin da take ahannun nasa katse mata tunani yayi sa cewa tunannin me kike qanwata karkisa komai aranki kinmanta dashi kawai yanzu bagaki da ranki da lafiyar dan murmushi tayi tace ba komai ni bansa komai araina ba nagode sosai da sosai akan dauwaniya da kake yi dani Allah gabika da gidan aljannar firdausi yace Ameen daga nan kuma suka shiga taba hira yana tasakata nishadi da dariya saboda yadebe mata kewa suna cikin haka hajiya ta shigo tace to kayi bako mutumin ka yabiyo ka har gida duk da yagane watake magana amma saida yaqara cewa hajiya wa kenan tace waye zezo neman ka kaima ai kasani yace to ko uban me yazo yimin dan Allah hajiya kece kawai bana nan tace bazan masa qarya ba kuma daman nama sanar dashi kana ciki dan

42 / 49