saida tabari akai sadakar bakwai saboda tadanji dadin zaman gidan tasamu sauyi daga wajen HANNE kishiyar mahaifiyar tata yanzu batai mata abun da take mata da ba duk dade bawani sakar mata fuska tayi ba amma ita hakanma yayi mata dadi bayan sun dawo ne da yan watanni ita ma Nadeeya tafara zuwa makaranta lokacin tana da shekara biyar shikuma yana da shekara 15 tare suke zuwa da sameer su dawo kullum shi yake daukanta yakaita har makaranta ahannun shi dake makarantar basu da ma nisa da gidan kansu kara haduwa yake suna kara shakuwa da junansu ahaka har yakammala secondary dinshi itakuma lokacin tagama primary zatashiga secondary duk dayagama tashi hakan besa yadena kaitaba kafin yasmu yashiga jami'a saboda mlm bashida isassan kudin daze sakashi university dole sai yajira wata shekarar ahaka suka cigaba da rayuwa har Allah yasa yafara zuwa university bayan shekara 2 can nagano ta a tsugunne gaban kurfoti tana tafaman hada garwashin yaki kamawa ta tashi tana gunguni ta mike tsaye doguwa ce me dan jiki irin matan nanne manya ga tsaho ga jiki kuma fara ce dan har tafi mamanta haske tana tafiya ta shiga cikin falon tana cewa ummi dan Allah kizo kiga wutannan taki kamawa tun dazu taqarasa fadar maganar da nuna gajiyawa atattare da ita tana qoqarin zama ummin tata tace wlh nadeeya kifita daga idon in rufe bana son wannan banzan sakarcin naki keda komai na mata baki iyaba duk abun da akasaki sai kice ke kaza ke wannan ke wancan to daga yanzu ma komai nagidan nan ke zanbarwa nadena taba ko tsinke tunda abun naki kullum dada gaba yake tashi daga nan kiban guri kafin intashi kanki tashitayi dasauri tana turo baki tana qoqarin fita sukayi karo da sameer ya shigo dauke da murmushi akan fuskar shi yace to raka mata ni da nake namijima gashinan ai na hada kuma takama saki je ki dora abun daza ki dora tace yauwa yayana nakaina shiyasa nake sonka nagode ummi tace daman mana kyace haka tunda daman ai duk wani abu shiyake daure miki gindi kike yinshi zanyi maganin ku ne gaba daya sai muga inkinyi aure maga wanda ze na miki aikin gidan da ba kya kauna da sauri tace ummi ni ai ba auran da zanyi gwara inzauna awajenku nafi jin dadi tace to tunda agarin gaba gaba muke meze hana muzaun muzuba miki ido tace Allah ummi dagaske nake tace kinga fita kiban waje kije kiyi abun da nasaki tace to tafiya tana qara hade fuska ita ta tsani taji ance mata zatayi aure shikenan kuma sai ta tafi tabarsu ita bazata iyaba tana fita sameer ya juya ze bita ummi tai saurin kiranshi tace dawo kazauna daman ai duk kai kake qara lalatata takewa mutane abun dataga dama yarinya sai rashin son aiki ga shegiyar tsiwa yace kai ummi yanzu meye laifina danna kula da kaunwata itakadaice fa dani dole innu na mata so da kulawa tace ai sai kai tayi kaga nan gaba saika dena zuwa ko ina kazauna karinga yi mata duk abun datakeso da ayyukan ta dan bazan cigaba da wahalaba bayan ina da budurwa acikin gidana yace ai wannan me sauqi ne kar tadamu ze ringayi wlh cike da takaicin shi da yake bata shi kwata kwata komai za ace baze taba goyan bayan waniba sai de yagoyi banyanta tace kaga tashi kabar gurin nan kaida kullin baka canza hali yace Allah huci zuciyarki ummina Allah yabar mana ke yabaki tsawon kwana me amfani daman haka yake kullum idan yaga tana qoqarin jin haushi haka ze zauna yai tai mata dadin baki yana yikuwa zatasaki ranta tana jin dadin hakan har cikin ranta
bayan wasu dan shekaru ya kammala degree dinsa inda yakaranci ai likitanci fannin kwakwalwa bayan kammalawar sane kuma besamu aikin yiba sai malam ya dorashi akan harkar kasuwa inda yanema mishi tsaron wani shagon amininshi da suke kasuwancin su tare yafara zuwa cikin ikon Allah kuma sai suka samu budi adan qanqanin loakaci kuma duk da yawan 'yan matan dasuke kawo mishi qoqon bararsu garashi tunda ga kan yan makarantarsu zuwa masu siyayya wajensa amma beta ba jin ko da wasa wata ta mishiba kwatakwata bawacce ta kwanta mishi arai haryanzu itama kuma nadeeya haryau bata kula Samari anmata fadan amma abanza taqi ji malam da yaga abun masu ba me karewa bane kawai sai yasa mu ummi da maganar akan yakamata fa suyi wani tunanin abun da yadace akan yaran nan bawai subarsu haka suna kallonsuba karkada kai ummi tayi sannan tace ni aganina malam yaran kawai muhadasu aure inaganin hakan se yafi ai yace nima nayi tuna nin hakan amma kuma da na hanga sainaga to shi sameer yaza midashi tundade be san bamu muka haifeshi ba tace hakane malam ai daman ko badade ko bajima dole mu sanar dashi gaskiyar al amari kaga kuma yanzu ai yariga da ya mallaki hankalinshi ze fahimcemu ina ganin kawai yanzu ne lokacin da yakamata musanar dashi sannan muhada aurensu nasan bazeqi hakan ba duba da yanda suka shaku da juna inaganin baze bijirewa maganar mu ba kokwa yakagani yace maganarki gaskiya ce hakan yakamata muyi kawai ai da zafi zafi akan bugi qarfe kawai je ki kirasu dukan su yanzu ayita taqare asan inda aka dosa tace to tare da mikewa taji takirasu sukazo gabadayansu suka zauna aqasa tare da cewa baba barkanka da hutawa yace barkankude saida kowa yanutsu sannan malam yafara salatin annabi sannnan yafara magana a nutse yara kiran sunan shi yace sameer zan fara dakai domin wannan kiranma gaba daya domin kane cike da ladabi da biyayya yace to baba yana qara sake zama da nutsuwa domin jin bayanin da akace domin sane sannan malam yace gaba dacewa dafarko de zanfara maka nasiha akan duk abun da yasameka kadauke shi amatsayin qaddar da kuma jarabtar da Allah yayi maka domin ganin zakai hakuri da tawakkali ko kuma akasin haka ka rungumi qaddararka da hannu bibbiyu kayi addu'ar Allah ya sassauta maka ita kuma muma ka fahimce mu bada son ranmu haka ta faru ba kajini ya amsa dacew eh baba in sha Allahu duk da yadan shiga rudin jin wadannan magan ganun da besan inda suka dosaba mlm ya dan jinjina kai yace to masha Allah haka nake sonji ina qara baka hakuri akan abun da zakaji daga garemu shide haryanzu a qagare yake dajin abun daza ace mishi saida malam yadan numfasa sannan yace gaskiyar magana malam sameer bamune iyayankaba kuma bamune muka haifeka ba hasalima bamusan inda naka iyayen suke ba kawaide a....ba qarasa maganar dayakeba mikewar da yaga sameer din yayi bashi kadai bama har nadeeya saida ta mike dan bakaramin razana sukai ba dajin wannan batun dasauri malam yakamoshi yazaunar yace dan Allah ka kwantar da hankalinka kasaurare mu ko mubakadauke mu amatsayin iyayeba mu mun daukeka amatsayin da agaremu yanzuma muna da daliline shiyasa muka gaya maka da sauri sameer yashiga girgi kai cikin shashshekar kuka da yagama wanke mishi fuska yace baba dan Allah kace min mafarki nake kar kace da gaske ne abun da kakecemin ni wlh koma ina da wasu iyaye bazan taba zuwa wajensu ba ni kune iyayena ku nasani kuma ba inda zani inatare daku rungumeshi mlam yayi yace sameer ya isa haka dan Allah be kamata karinga irin wadannan maganganun ba katsaya ka saurareni da kyau kaji kai yadaga mishi kamar wani karamin yaro yazame jikinshi da ga nashi yazaun aqasa kamar mutum mutumi haka yake agun cikin nutsuwa malam ya labarta mishi abun da yafaru abaya da yanda akai yasameshi sosai sameer yashiga tausayin kansa dashi da mahaifirya tasa ahankali yafurta Allah yasa tana raye suka amsa mishi da Ameen sannan yace baba to a ina mutumin yake yace wlh sameer bansani ba gagan gancin da nayi kenan wlh na rashin karbar number sa danayi sanna yace sade mita addu'a duk ina da take Allah yabayyana mana ita duka suka amsa da ameen malam yamaida dubansa ga Nadeeya yace ke baza ki zauna bane kinyi mana tsaye akai kamar wata yar sanda ahankali takoma ta zauna inda ta tashi sannan yaci gaba da cewa sai abu na biyu kuma danake so na sanar da ku shine zamu hadaku aure tunda har yanzu banji wanda yace ga wanda yake so ya aura ba dan haka muka yanke hukunci da mahaifiyar ku kawai ahada ku tare tunda daman kun saba Kunsan junanku kunga kawai sai ayi tuwona maina ko yakuka gani inda me magana yayi dan ba wanda zamuyiwa dole acikin ku kunji sameer yace baba ai duk yanda kukayi daidene ni bani da zabin da yawuce naku saidema godiya dazan muka akan abubuwan da kuka min da dawainiya dani da bani kulawa ai ba abun da zan iyasaka muku dashi sai addu'a Allah yabiku da gidan aljannar fiddausi yabaku abun da kuke nema duniya da lahira Allah kuma ya..da sauri malam yakatseshi da cewa ya isa haka munyi maka ne domin Allah dan haka kadena ma na gdy kuma kacigaba da kallon mu matsayin iyayenka ko da wasa bamaso muga ka canza daga abun dakakeyi kajini yace In sha Allahu bazaku taba ganin wani canji da gareni ba aure kuma Allah yabamu zaman lfy malam ya amsa da ameen sannan yakalli nadeeya da ta sunkuyar da kai tunda taji anyi maganar hadasu aure yace to kefa muji ta bakinki ko kina da magana da sauri ta giragiza kai alamun bata da magana yace to naji dadi da biyayyarku agaremu kuma Allah yabaku masu yi muku kamar yanda kukayi mana suka amsa da ameen sannan yakara dayi musu nasiha sosai kuma me ratsa jiki itama ummi ta dora da tata suna gama yimusu yace musu zasu iya tafiya ya sallamesu sukai musu godiya da sllama suka fita kowannen su jiki babu kwari.......
*********
Sai munhadu anagab kuma wannan shafin bazan mata da shiba dan har kusan kuka yasani sai da nagama typing dinshi tsafa posting yarage min kawai arashin sani bayi saving dinshi yagoge gaba daya😭naji ciwon abun sosai wlh gashi kuma ni nayiwa kaina da kaina bare inhuce akan wani hmmm abunde ba dadi wlh
daga sabuwar marubuciyarku🖋
❤xeemat....love❤
Plss comment and share this book
[2/19, 7:12 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SAEKI SAMEER....💅
by❤xeemat....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Episode4&5🖋
*****cigan labari****
Furgigit dadda tayi tadawo daga duniyar tunanin da ta tafi sakamakon tabatan da Ameesha tayi ajiyar zuciya tasauke tare dacemata wai harkin gama shiryawar eh tace mata sannan tace nadadema dashirya wa harmafa naci abincin kuma tundazu nake miki magana amma kintafi tuna nin dakika saba waima dan Allah dadda kigagaya min abun da kike tunani kullum baki da aikin yi sai tunani ahankali tace hmmm bazaki gane bane Ameesha amma kiqara hakuri akwai lokacin dazan gaya miki komai sai kin kaqara girma tukunna baki Ameesha ta turo mata baki tace daman ai kullum haka kike cewa dadda ni wai duk wannan girman danayi wane irin girma kikeso inyi kuma tace saikin qara hankali tukun tace kina nufin daman kallon mahaukaciya kike min da sauri tace mata a'a nibaceba daga cewa sai kin kara hankali sai kuma kimin sharri ni yaushe kikaji nace miki mahaukaciya to dadda mekike nufi dahakan duk wanda akace mishi sai yayi hankali ai ana nufin mahaukacine shi tace to yi hakuri ni bahaka nake nufiba kizo kitafi kawai tunda naga bakida niyar baccin naga alamun yay 'yan tsiwarne suka motsa dan qara min bakinta taqara tura mata batace mata komai ba ta juya zata fita cike da jin haushin zantukan daddar tata ta tsani taga tana wannan tunanin da itabata san amfanin shi ba(nace injikiba)tana jiyo maganarta tanacewa au ko sallamama bazaki min ba to sai kin dawo Allah yakiyaye hanya kinji ko kigaishe min da maman Azeeman ko tsayawa bataiba bate tasa ran zata amsa mata ahaka tai ficewarta amma ta amsa mata da ameen acikin zuciyarta tana fita dadda tace ja'rar yarinya kawai me tsiwar tsiya da bata da gurin yinta sai akaina dake ni ta raina ai kin iya zuwa ana da miki na jaki bazaki tabuka uban komai saide ni kidawo gida kina min kuka kuma inrashin mutunciki yatashi ki saukeshi kaina ni ban ma san ubanwa kika dauko wannan halin ba dan nasan duk iskancin gyatumarki batai irin wannan ba ita kadai sai faman zuba take dadda bade mita ba....
Ameesha nafita direct gidan su Azeemar ta nufa tana zuwa ta bubuga gidan wani saurayi yazo ze bude sai kuma yatsaya yana cewa waye tace ya SALEEM nice kantagama fadama ya bude da sauri yana sakin qayataccen murmushi yace A'a ashe babbar bakuwa mukai barkanki da zuwa itama da fuskarta dauke da murmushi tace yauwa ya saleem barkan kade nasameku lfy yace lfy lau wlh shigo daga ciki mana kintsaya awaje sai kace gidan bakonki ne yafada yana matsa mata tashige ciki tana murmushi shikuma yarufe gidan yabiyo bayanta suka shiga cikin falon tare yazauna sannan yace mata kishiga ciki maman bata nan amma azeemar tana ciki kije inkun gaisa kuma kizo muyi zance anan ina jiranki tace to ya Saleem bari inshiga infito shima yace mata to amma dan Allah karkidade idan kuma kika dade harciki zanshigo in dakko ki wlh dariya tayi tace kar kadamu hakanma baza ta faruba yace tama farudin kiga aiki da cikawa yarinya yafada yana dan mata hararar wasa bata cemishi komai tasan inta biye mishi ba barinta zeyi ta wuce ba dariya kawai tayi tashige ciki shikuma ya kwantar da kansa yana wani lumshe idanu yanajinta harcikin ransa yake jin sanyi idan yaganta tana shiga ta tarar da ita tayi dai dai tana sharar bacci hankalita kwance qarasawa tayi gaban gadon nata tanacewa yarinyar nan bata gajiya da bacci wlh kullum mutum sai kace me cutar sleeping skilles hannu tadaga sama da iya qarfinta da Allah yabata ta dala mata duka a bom bom dinta aikwa amatuqar fugice ta tashi tana niyar kwasa aguje tabar dakin dan zafin dataji yasa tama manta a ina take dariyar muguntar da Ameesha take tafamayi ne ganin yanda duk tabi ta furgita daga dan wannan dukan datai mata aikwa a hassale tatsaya tana kallon ta tare dakai mata duka tana fadin wlh sai Allah yasa kamin idan banyafe miki ba wannan ai cin zaline da mugunta kinsan yanda kika tsoratani kuwa ina cikin bacci na me dadi kizo kitasheni kuma ma da irin wannan dukan haka takarasa maganar kamar zatafashe da kuka saboda takaicin abun da qawar tata tai mata cikin kunshe dariyar ta da take cinta tace ayya besty ta takaina besty ta nikadai I'm so sorry kinji nibansan zaki tsorata har haka ba kinji qawalli ta harara ta watsa mata tace anqi hakurin kitaahi ki koma inda kika fito ni ba ruwana dake ko a hanya kika gani kar kinuna kinsani yar rainin hankali kawai da wani bakinki tunna haihuwa da be qara girmaba kina min dadin baki to bazan hakura din ba taqarasa fada tana mikewa zata barmata dakin tiyi saurin tare gabanta tanacewa haba dan Allah nafa baki hakiri plssssss mana natuba bazan qaraba ta riqe kunnata tana matrairai cewa kamar zatai kuka sai lokacin bestyn tata tadan saki fuska tace naji to tace kin hakura kai ta daga mata alamun eh aikwa da sauri ta rungumeta tanacewa yauwa besty nagode daman nasan fushin ba inda zashi nasan dole zaki hakura qoqarin tureta tayi tana fadin au dole ma kikace ko da sauri tace aa wlh da wasa nake tace hmm da bansan halinki bane sai inyarda taraba jikin ta danata sannan suka koma suka zauna Ameesha ta oh ni yar jikar mutum daya nataho da murna ta dannazo na ganki amma nazo sai wani faman wulakanta ni kike tace kikade wulakanta kanki da baki min mugunta ba ai da duk haka bata faruba tace to nide abar maganar komai ya wuce naji zuwa nai kiban shawara akan gidan aikincan danakeyi wlh nagaji da cin mutuncin dasuke min kullum wahalar yau daban ta gobe daban ta gobe daban kullum acikin cin zalina suke dayi min mugunta iri iri kinsan dazu Allah ne ya taimake ni amma da tuni yanzu ina barzahu shegiyar matar nan da jikinta kamar na buhun dankali takusa yimin yankan da akeyiwa rago tsabar rashin imani Azeema ce ta katseta da cewa nashiga uku ni Azeema wane zunubin kika aikata mata haka tace hmm wlh kawai muguntace da baqin hali irin tasu ita da yarta amma ni banga abun laifi anan ba wai kawai dan BOSSAY yazo nikuma nazo fita an aikini sai yakini naje muna gaisawa.......nan de ta kwashe duk abun da yafaru atsakaninsu da kuma abun da sukayi mata ta fada mata tana qara jin zafin abun aranta tana dan goge kwallar da ta zubo mata hannuwanta ta ruqe tace Allah sarki besty kiyi hakuri dan Allah gaskiya na tausaya miki kuma ai Allah ba azzalumin bawa bane yanasane dake kuma zebi miki hakkinki nacin zalin dasuke miki Allah yasakamiki tace Ameen tace ni wlh daman dazaki bi tatawa dakin dena zuwa ma gaba daya tace nima ina tuna nin hakan to amma kinsan kudin da sukeban dashi nake samu inyi duk wani abu daya kama inyi amakaranta dasu nake biyan school peas dina idan nadena zuwa waze nabiya mun wadannan abubuwan kinga dadda bawani kudi ne da itaba itama kudin datake aiki dasu muke dan samu muna cin abinci da kuma dan qananu abubuwa da baza arasaba wlh bansan ya zanyi ba amma harga Allah nagaji da rayuwar nan da muke ciki tafada tana qara goge hawa yanta da yake zubowa cike da damuwa da tausayin qawar tata tace hakane kuma kiyi hakuri kicigaba da kai kukan ki gurin Allah in sha Allah nasan wataran zakiji dadi arayuwar ki Allah ze share miki kukanki yana sane dake nide shawarar da zanbaki kawai kicigaba da hakuri dasu goben kawai kishirya kije gidan sannan kibata hakuri ko me zasuce miki kar kida kai ki kallesu kuma kar kisa