SARKI SAMEER BOOK 1 Hausa Novels

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   43 / 49

126K to 129K   out of 145.7K words

haka sai kafita zama ma yaqara gyarawa yace ba inda zani wallahi idan yagaji ya tafi hajiya de bata ce masa komai ba ta fice daga dakin dan ta sanar da sameer abun da yace saboda itama bazataso rugujewar alakar su ba komai ya tsananin maganin sa Allah gwara su shirya sudawo yanda suke bata dade da fita ba aka turo qofar aka qara shigowa hankalin su nakan hirar da sukeyi bama suji shigowar sa ba tsaya wa yayi yana qare musu kallo sai yanzu yaji wani irin sanyi da be taba jiba yaji lullubeshi,
qarasa shigowa yayi jin tafiya yasa shettima dagowa dan ganin me tafiya idonsane ya sauka akan sa da sauri ya miqe yana kallon sa yace malam me kashizo kayimin ko kazo ka qarasa cimin mutuncin dabaka qarasa ba ko kuma kabiyota ne ka qarasa ta to wlh karyarka kafice min daga tun muna mu biyu tun muna sheda juna kafita kafin raina yaqarasa baci bazaka ji dadi ba tunda kai kazo inda nake yanzu ba a asibitin ka nake ba ba kuma agidan ku nake bare kace zaka zaka takani duk maganganun da yake hasalima idon sa ba akansa yake ba yana kanta be tanka masa ba ita kuma tunda ya shigo ta kalle sa ta gefen ido bata dago ta kalle sa ba kuma tanajin idon sa akanta jitayi zaman gurin gaba daya ya gundire ta miqewa tayi zata gita daga dakin dan batajin zata iya zama matukar yana cikin dakin, da sauri shettima ya ruqo hannun ta yace ina zaki zo nan ba abun da ya isa yayi maki inde ina gurin idonta ne duk suka cika da kwalla tace ni kabar ni in fita kawai bazan iya zama guri daya da wanda baya kaunata kuma yana neman rabani da duniya yana so yaga bayana me na aikata mishi da ya tsaneni haka har yake so yaga bayana bayana kuka ne ya kwace mata tafashe mishi dashi jawota yayi jikin sa ya rungume ta yana rarrashinta amma duk dahaka taqi yarda tayi shiru gudun kar kukan nata yayi yawa azo asamu matsala irin jiya dan haka sai kawai yarabata da jikin sa ya share mata hawayen yace ya isa haka kiyi shiru kije gurin hajiya tana falo gyada mishi kai kawai tayi sannan tayi gaba zata fita har ta dan gotashi taji anruqo mata hannu tare da fisgota ta dawo da baya ganin wanda ya ruqota yasa ta qara sakin wani kukan,
ran Shettima back qaramin baci yayi ba ahasale yayo kansa yana nuna sa da yatsa yace saketa kasake ta yafada yana qoqrin raba hannu sa da nata amma yakasa saboda baqaramin ruqo yayi nata ya riqe ta gam kamar ze balle mata hannun da karfi shettima yadaka masa tsawa yace nace kasake ta ko kar ranka yazo yana baci bade kace murabu dakai ba kuma munrabu dakai ba to meyasa zaka biyo mu ko sode kake sai ka kasheta hankalin ka ze kwanta har yanzu shide be tanka masa ba duk dashina zuciyar tasa a kusa take cigaba yayi da qorain kwace ta amma yakasa hannu yadaga ze kaimasa duka amma sai ya dakata sakamakon wata qara da Ameesha tasaki ne yadakatar dashi daga abun da yayi niya,
[4/7, 3:05 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode 82-83-84

         """"""""""""""""""""""""""""""""""
da sauri ya yayi kanta ze ruqota amma kafin ya ruqota sameer ya rigasa rungumeta yayi suna cikin haka hajiya ta shigo tace ya isa haka duk naji maganganun ku tafada tana qarasowa kusa dasu hannu tasa ta karbe Ameesha da ga gurin sa sannan tace kusa mu wajen kuzauna kema kuma kukan ya isa haka babu wanda yayi mata musu suka samu guri suka zauna kamar yanda ta umarce su din itama shiru tayi tana shesheqar kuka nan tashiga yimusu nasiha da illar wannan fadan dasuke yi marar amfani kowa ta nuna masa inda laifin sa yake sannan taja kunnen su akan su bawa junansu hakuri kar wanda yaqara cewa wani yarabu da wani suzauna kamar yanda suke da yarinya kuma tunda taji sauke su maidata gurin iyayen ta kawai aci gaba da kula da ita acan suma hakan sai yafi musu kwanciyar hankali yanzu ya dauko yarinya ya kawota wani gidan idan sukaje asibitin kuna basu ganta bafa me zasuce musu wannan ma gangancine kwata kwata be kamata tasss tayiwa kowa fada harda shi uban gayyar da yake tafam cika yana batsewa shettima ne yace hajiya dan Allah kiyi hakuri amma bazan koma aiki a qarqashin saba kawai kowa yakama gaban sa nagaji da zama dashi hajiya ta kalle sa tace daman baka da hankali bansani ba kamanta hallacin da yayi maka ko badan tasanadin sa ba ka isa ka kawo wannan matsayin dake yanzu komai bata sanadin sane ba kai koma me yayi maka inkana da hankali hankali yakamata kagaya masa haka meyasa baza kai hakuri ba tundade ka riga kasan halinsa ai be kamata ma karingajin haushin wani abun nasa ba tunda kasan duk abun da ze aikata da abun da baze aikata ba kasani bekamata karinga damuwa da halayen sa ba dan haka ina gargadinka kar nasake jin wannan furucin abakin ka sunkuyar da kai yayi kawai bece mata komai ba sannan ta koma kan sameer tace kai fa kana da abun cewa kai kawai ya girgiza be ce komai sannan tace to masha Allah yanzu inaso ku sasanta tsakanin ku ku ko kunyama bakwaji aji kanku idan momma dinku taji me kuke tunanin zata ce duk shiru sukayi suna sauraron ta har tagama sannan tace yanzu yaza ayi da ita yarinya zaku kira gidan sune suzo su dauke ta ko kuma zaku mayar da ita da kanku sameer ne ya bude baki yace hajiya amma naji kina cewa iyayenta kuma jiya wanda suka kawota daya daga cikin su yace marai niyace bata da kowa batasan kowa nata ba dalilin da yasa ma nazo kenan inji ta bakin yarinyar da gaske ko kuwa qaryane saboda ina son janye duk abun da nafada akanta kallon kallon akashiga yi tsakanin shettima da Ameesha da kuma hajiya, hajiyace ta kalli Shettima tace da gaske ne maganar da naji tunda naga kunfi kusa kai da ita shettima yace wlh hajiya nima bansani ba yanzu nake ji kallon Ameesha yayi yace da gaske ne Ameesha ke marainiya ce hawayene suka shiga zubo mata cikin sheshsheqar kuka tace ni ba marai niya bace amma de bansan suwaye iyaye naba ahannun kakata nataso naganta kuma idan na tambayeta ni wace ina iyayena amma taqi gaya min kuma naji wasu maqotan mu idan suna zagina suna cemin `yar shegiya kuma dadda tace ni ba yar shegiya bace amma kuma haryanzu bata sanar dani komai game da iyayena ba tun ina tambaya har na dena amma inaji ajikina koma suwaye suna raye saide bansan ina suke ba wannan ne dalilin dayasa kaji nace kar kagaya musu ina cikin hayyacina inso innuna musu ba abun da nasani nasan watakil dadda zata iya bani wata qofar da zan gane wasu abu tunda tasan inma tayi agaba ne bazan fahimta ba,

Sameer ne yakatseta da cewa me ya haddasa miki brain trouma ko accident kukayi girgiza masa kai tayi tace ba accident nayi ba wasune suka zo har gidan mu sukayi min duka tare da buga min abu akai na da sunso ma na mutu tunda da niyar kashe ni sukazo dan jinjina kai yayi kafin yayi magana shettima yarigasa da cewa baki sansu ba kuma tace eh bansan suba kuma fuskar su a rufe take saide bisa ga dukkan alamu dadda ta tasansu tunda lokacin daman muna shirin dawowa gidan bossay saida tabasu labarin haduwar ta da bossay da komawa gidan su da zasuyi sannan ta dora dacewa ranar da za mukoma gidan na shiga wanka tun ina bandaki nake jiyo muryar maza a cikin gidan bayi mamakin jin muryoyin maza aciki dan haka sai nayi sauri nagama wankan na fito dan ganin suwaye ina fitowa naga bakowa a tsakar gida sai na qarasa bakin qofar ina zuwa naji dadda tana cewa dan Allah ku fita namuku alqawarin zan baku duk kudin da kuke bukata meyasa zaku qara biyo ni har nan bayan kuma bahaka mukayi da kuba dan Allah kar ku cutar da ita tunda ba ita tayi muku laifi ba kar kutar da ita na roqeku ku rabu damu tunda de na baku duk abun da kuke bukata dayane daga ciki ya kwashe da wata irin da riya yace ke tsohuwa yau magiyar ki baza tai aikiba domin ance inde bamu kashe ta mu za akashe dan haka koma me zaki bamu yau bama bukata dole mutura yarki lahira kamar yanda muka tura taki yar kema kuma kiji nan gaba nasan oga baballe baze barki da rai ba yana bin komai a hankaline kuma yana daga miki qafa saboda wani dalilin nasa amma duk wanda ya rabita sai yarasa numfashin sa aduniya kema kuma zaki mutu bayan kin gaya mana inda take amma kin tsaya yiwa mutane taurin kai kinqi fadar gaskiya dadda na kuka tace wlh bansan inda take ba bantaba ma ganin taba me yasa shi wanda ya aiko ku baze yarda dani ba wlh bansan taba wai me ta aikata muku ne da kuke so sai kunga bayan ta wani daga ciki yace mu bamu ta aikatawa ba oga ta aikatawa kuma shi ba acin bashinsa azauna lafiya inde kina son ranki kawai kigaya mana inda take sannan abarki da ranki amma jikar ki dole ne mu kasheta wani daga ciki yace kunga muna ta bata lokaci kawai mu aiwatar da abun da aka saka mu inatake ne wani yace tana cikin gidan mana baka ga sai shiri suke ba zasu bar gidan to kisani koma ina kika koma idan mu nakanki ba inda kika isa kishiga bamu nemo ki ba afadin duniyar nan da mamaki ta kalle su tace waya gaya muku zamu tashi yace yana tare da ku wanda yagaya mana kuma duk inda zakije kina tare da shi tunani ta shiga yi to waye yagaya musu kuma yana tare dasu to kode bossay ne yake cin amanar su to inba shiba waye yake kusa dasu wani ne yace kina tunani waye ko to bari kiji shi wanda zezo daukar taku shima dan cikin mune dan haka sai ki kula gaban tane yafadi tace jin ance wanda zezo daukar su tabbas kwa bossay ne shikenan yanzu ina za su dosa daman ta yarda zata koma gidan su bossay saboda ta guje musu daman ashe tayi gudun kura zata tarda zago bata gana tunanin ba taji ihun Ameesha datake waje a guje suka fita daga dakin saboda jin muryarta ita kuma jin ance wanda ze dake sune ze kasheta yasata sakin qara tare da cewa qaryane nasan bossay baze taba kasancewa haka ba sharri kuke mishi da sauri wani yajawo gashin kanta tare da maida ita cikin dakin dadda tabi bayansa tana roqonsa dan Allah yasaketa amma be saurare ta ba Allah yaso ma datayi wankan riga tasaka daman da rigarta ta shiga bandaki saboda saurin da takeyi ta shirya kafin bossay yazo da tuni irin wurgin da yake da ita in zanine da tuni yacire dadda tazo tana qoqarin kwatar ta amma yayi wurgi da ita agurin ta suma da sauri Ameesha ta kwace kanta daga gurin sa ta nufi gun dadda da gudu kafin ta qarasa kuma wani da yake bayan ta yadaga wani qaton qarfe yasauke sa akanta take a lokacin kwa ta baje awajen bata sake shurawa ba ganin hakan yasa suka tattaba ta suka tabbaar da ta mutu sannan suka shiga bincike dakin ko zasu samu wani abun da yakawo su amma basu samu dan haka kawai suka fita daga dakin tare da barin gidan ma gaba daya,

tana fada tasaki wani sabon kukan me tsuma zuciyar me sauraro hajiya ce ta jawota jikin ta ta rungumeta tana dan shafa bayant
gabadayan su babu wanda be tausaya mata ba lokaci nafarko da yafara jin tausanyi mace daman a kwai irin wadannan mugayen be sani ba shettima ba qaramin tausaya mata yayi shi daman ya dade yana jin tausayin ta hakannan ashede tana da abun da za aji taisayin ta din yarinya qarama tana fuskantar irin wadannan abubuwan,

saida kukan nata yadan tsagaita sannan hajiya ta raba jikinta da nata sameer ne yace waye bossay din tace shine wanda yakawo ni asibitin amma wallahi qarya suke masa baze taba aikata haka ba be kulata ba kawai ya miqe tsaye yace muje gidan naku zaki iya ganewa kai ta girgiza masa tace ai bama muje gidan wannan abun yafaru shettima yace muje kawai zan kirashi ai ina da number sa yayi mana kwatance hajiya ce tace a'a kar kuje yanzu kubari abi komai a hankali yanzu ku kirashi nan sai muji ta bakin shi kunga idan iyayen sa basu sani ba zakusaka su cikin wani hali tundade basu suka sakashi ba sameer yace haba hajiya suna da yaro irin wannan amma basu dauki mataki ba dole in koya musu hankali dagashi har su har ita kakar tata ma yau sai tayi bayanin *suwaye su*(my next novel) yaza ayi taringa saka yarinya damuwa bazata fada mata komai ba bani number yaron nidaga nan sai can dan bazan bari maganar nan ta kwana ba Ameesha ce ta sauko ta riqe hannun sa tace dan Allah kayi hakuri wlh ba ruwan yaya bossay aciki kar kayi masa komai da mamaki yake kallon ta yace ni ba abun da zan masa kawaide zan tambaye sane yafadi gaskiya ko kuma jikin sa yakagaya masa karkada masa kai tayi tace ni wallahi ba zarginsa sun fadi hakane kawai dan sunga yana so ya taimaka mana amma ba ahannun sa aciki be kulataba ya kwace hannun sa yace tare da zaro wayar sa ya miqawa shettima yace sakamin number sa karba yayi yasaka masa ya basa sannan yace muje hajiya ce ta qara dakatar da su amma ina basu tsayaba ganin hakan yasa tace sujira ta suje tare sutafi ma gaba daya har Ameeshan hakan ne kawai yasa suka dakata sannan ta shirya ta dan gyara Ameesha suka fito falo motar shettima suka nufa gaba daya shettima ya shiga mazaunin driver shikuma ya shiga gefe yayin da sukuma suka shiga baya sannan shettima yazaro wayarsa ya kira bossay din bugu daya kwa yadaga yana dagawa ya gaida shi ba yabo ba fallasa ya amsa masa daga nan kuma yace kaji nace zan kiraka ko to yanzu de gata nan lafiyar ta qalau tasamu lafiya yanzu haka ma muna hanya kwatancen unguwar ku da gidan zaka yimana cike da jin dadi da gar yana iya jiyo shi ta wayar ya kwatan ta musu daga suka yi sallam sannan yatayar da motar suka fice daga gidan suka dau hanya zuwa gidan su bossay.........✍
[4/8, 10:14 AM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode 85-86-87

         """"""""""""""""""""""""""""""""

sun qarasa lfy kamar yanda ya kwatanta musu haka yabi kwatancen har sukaje unguwar gidan ba a lungu yake ba kuma unguwar ba geto bace shiyasa basu sha wahalar gane gidan ba abakin gate din yayi horn me gadi ya wangale musu suka shiga ciki suna shiga bayan yagama daidaita parking din suka fito gaba dayan su sai shettima yaqara dauko wayar sa yace bossay sun qaraso yazo ya shiga dasu kamar jira yake kwa sai gashi ya fito sai faman wangale baki yake idon sa suka sauka akan Ameesha take yaqara fadada murmushin sa yana zuwa yaqara sakar mata wan wani qayatacen murmushi itama murmushin ta sakar masa duk abun da suke akan idom sameer shima tunda yaron ya fito ya kafe sa da ido

yana zuwa yayi musu sannu da zuwa tare da gaida su amma be qara gangancin qara mikawa sam hannu ba sai ya gaida shi amma yaumade ga mamakin sa be amsa ba sai gudunmawar bazan kallo da yasamu shi daman yama yi mamakin ganin su tare bayan kuma yace zai sauki mataki akan yarinyar to kuma ko meye yakawo shi oho bashida me bashi amsa shiyasa yaja bakin sa ya tsuke ya gaida hajiya da shima yayi mamakin ganin ta duk da kamanni sunnuna masa kamar da suke da shettima,
sameer ne ya dunqule hannun sa yanaso yakai masa naushi duk ba wanda ya lura dashi sai Ameesha da sauri taje gefen sa yanda ba wanda ze fahimta ta zura hannun ta cikin nasa beji riqe hannun sa da tayi na sai jin wani irin shouck da ya kaima sa zira tunda ga qasa har sama wanna ne ya ganar dashi ta riqe shi dan kallon ta yayi ta qasan ido tare da janyewa,

damqe hannun sa tayi sosai tana bude dunqulewar da yayi yagane me take nufi ta qasan ido yake kallon ta amma ita bashi take kallo ba qasa take kallo bayan bossay yagana gaida hajiya sai ya maida kallon sa ga Ameesha da fara'ar sa yajuyo ze yi mata magana amma sai maganar ta ruqe sakamako abun da yagani Ameesha riqe da hannun maqiyin ta to hakan me yake nufi kode ya boye mata be gayamata ba yana gama ayyana tunani ranshi a mugun bace yake kallon idon sa har suncan za kala ga na bakin cikin besan dalilin yin hakan ba ga na kishi dayake jin zuciyar sa nayi masa barazanar fitowa daga qirjinsa shikansa besan lokacin da ya daka mata tsawa ba yace Ameesha kina da hankali kuwa kinsan wanda kika riqe yanzu to kaf duniya baki da maqiyi irin sa ki gaggauta nesantar shi

43 / 49