SARKI SAMEER BOOK 1 Hausa Novels

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   40 / 49

117K to 120K   out of 145.7K words

ba ya hakura yabisu suka tafi dakin sai yarage daga ita sai bossay zama yayi akusa da ita yana qare mata kallo dagowa tayi suka hada ido sai kawai yasakar mata murmushi tare da cewa yanzu kinmata dani yakamata kitina koni waye awajen ki kallon shi tayi tace ai nasanka yanzu ba yayana bane kai yaya bossay ko? daga mata yayi yace eh hakane ashe kinriqe sunana to yanzu kiban labari gyara zama tayi sannan tace yaya kamanta ba abun da nasani yanzu na manta da komai taya zan baka labari to saide kai kabani cike da tausayin ta yace to shikenan bari inbaki gyara zama ta kuma yi tana fuskantar shi sosai yanda zatafi jinsa yabude baki kenan zaifara bata sai sukaji anturo qofa dagowa sukayi gaba dayansu suna kallon me shigowar shettima mane yafara shigowa sai sameer abayan sa shettima mane kawai yayi sallama bossay ya amsa masa tare da miqewa ya miqa masa hannu suka gaisa yana qoqarin miqawa sameer yaga yayi gefe be kulasaba mayar da hannun sa yayi yana mamakin wannan kuma waye haka a miqa masa hannu amma yanajin qyashin miqo nashi besan adadin ladan da ake bayarwa ba idan akayi musabaha gaskiya wannan daga gani girman kaine yake dawai niya dashi sai kuma yafara tunanin to kode ba musumi bane da daman yaga kamannin sa kamar ma ba dan nan qasar nan ba,
shettima ne ya katse mishi tunanin sa ganin yayi shiru bisa ga dukkan alamu kuma ya fahimci tunanin abun da sam yayi mishi yake,
dan tabashi yayi yace abokina kar ka damu da wannan karkasa komai aranka kaji haka halinsa yake sai kayi hakuri,
dan murmushi ya qaqalo yaaza asaman fuskar sa kana yace ba komai ai duk da abun be mishi dadi ba amma sai ya basar kawai,
shikam yana jinsu be tanka musuba yaci gaba da aikin da ya kawo sa wani abu naga yana ta hadawa da bansan meye ba saida yagama ya miqawa Ameesha da tun shigowar sa ta hade fuska dan haushin shi take daman na allurar da yayi mata duk irin magiyar da tayi mishi saida yayi mata saboda bashi da imani gashi kuma yanzu abun da yayiwa yayan ta bossay yasa taqara jin haushin shi,

qinkarba tayi harda make kafada cike da shagwaba tace ni bazan karba ba wlh
ajiye wa yayi yana niyar juyawa yafice daga dakin dan ahalin yanzu yan miskilan cin ne akansa bayajin ze iya wata magana dan bakinsa yayi masa nayi bare kuma har ya iya tsayawa ja in ja da ita dan in yace ze tsaya tayi mishi wani abun da be gamsar dashiba ze iya bibbigeta agurin dan baze iya controlling din tampreture din shiba dan haka rabuwa da itadin shi yafiye musu alkhairi gaba dayan su,
har yadaga qafa daya yana shirin daga ta biyun shettima da yasan halin sa kuma yagane abun da yake shirin yi duba kuma da yanayin labarin da yabashi dazu na rashin kunyar da tayi mishi to baya son a qara kwatanta makamancin hakan,
hakanne yasa shi saurin dakatar dashi yana bashi hakuri dan Allah kayi hakuri kar kabiyewa shirmenta kasan ita yarinyace ga rashin lafiyar ta kuma sai kadan yi mata uziri,
tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba shettima yakalli Ameesha yace dan Allah kitsaya ayi komai agama me yasa kike da taurin kaine bakya so kisamu lafiya da wuri asallame ki ku koma gida, tana dan turo baki gaba tace inso mana ni yanzuma naji dauqi a sallame ni tafada tana qara cinno dan qaramin bakin ta gaba, bakin nata yadan kalla sai yadan saki murmushin gefen baki sanna yace da saurade baki ga ko tafiya ba kya iyawa ahaka kike so asallame ki ko so kike ki koma gurguwa da sauri tace a'a yace to inde ba hakaba kibari ya dubaki yayi abun da zeyi yatafi kinga dare nayi ba dadewa zeyi ba just 10 minutes ya gama yatafi abunsa ,

kafada taqara makeya sannan tace nifa bazan yarda koma me zakace har sai yabawa yayana hakurin abun da yayi mishi shettima yace hakurin me kuma tace wulakancin da yayi mishi na gwaleshin da yayi zaro ido yayi yana tunani aransa tab wannan ta dauko da yawa Sam take so yabada hakuri abun kwa da bazeta taba yiyuwa ba kenan ya fuskancin yarinyar nan tana wuce gona da iri bata san waye sameer ba shiyasa take masa haka da ze iya da yabarta da shi ya koya mata hankali saide baze iya jurar hakan ba gwara ya lallabasa kawai a wucen wajen mutu min da arayuwar sa besan bada wani hakuri ba duk iya laifin da ze aikata maka baze taba baka hakuri saide inzaka mutu ka mutu tunda suka taso tare be taba gani ba tun suna yara harkawo girman su yanzu yasan arayuwar sa mutum biyu zuwa uka ya taba bawa hakuri daga iyayen sa sai papa bayansu bayajin ya taba furta kalmar yi hakuri ga wani can daban dan ko amakaran ta malamai sun sha fama dashi akan hakan amma saide suyi sugama su hakura dan baze bayar ba,
bossay ne yatabo shi ganin yatafi duniyar tunani firgigit yayi tare da kallon gurin da sameer yake saide me sai kawai yaga wayam ba kowa agurin ashe shi tunda suka fara tattaunawar su dayaji abun da tace sai yabawa yayan ta hakuri tun lokacin yayi ficewar sa daga dakin shikuma be lura da fitar shi ba sai yanzu juyo wa yayi ya kalli bossay yace karde ya fita kai yadaga masa tare da tabbatar masa tun lokacin da yafita dubansa yamaida ga Ameesha sannan yace to hankalinki ya kwanta nima daga yanzu ba ruwana dake zan zare hannuna akanki duk abun da kika ga damar yi mishi kiyi mishi daidai yake dake dan shi mutum ne me wuyar sa'ani ba kamar kowa bane dakika sani bakowa yake iya zama dashi ba amma ke tun haduwar ku ta farko na fuskanci ba kya shakkar sa ko kadan kuma yaban labarin duk abun da kikayi mishi dazu wlh sa'arki daya baki da lafiya amma da ya nuna miki ko shi waye wannan tsiwar taki dakike mishi ba inda zatakaiki saide ta kaiki ta baro ki inkin saba yiwa wasu tsiwa to shi baze dauka ba kamar yanda nagaya miki dazu kiringayin tunani kafin ki yanke abu kuma irin wadannan abubuwan dakike shi zesama asir.....da sauri ya canza magana dan yama manta yana shirin yimata kato bara sai kawai yamaida maganar dacewa shi zesama kitazama a asibiti dan ze iya dena duba ki gaba dayama yaden shigowa dagana kuma ciwon ki yadawo sabo kinga wa gari yawaya kice aciki shi ba ruwansa be damu da damuwar wani ba damuwar sa kawai yasani yakamata ki gayara kuskuren ki yana kaiwa nan ya nufi hanyar fita dan ba qaramin bata masa rai tayi ba yaudin nan tunda aka kawo fa yake fama da dawainiyar alhalin bashine da hakki akan aikin ta ba bashida hurumi akai saboda ba fannin aikin saba ne kawai yanayine saboda yasanta kuma yana tausayin ta har yakai bakin qofa yajiyo sautin kukanta tana kiranshi tana bashi hakuri amma kin sauraron ta yayi ya qarasa ficewa kawai amma shikadai yasan abun da yake ji aciki zuciyar sa bada son ransa yayi mata haka ba kawai yanaso ta gano kuskuren ta ne kuma ta gyara shiyasa yayi mata haka,

fashewa tayi da wani irin matsanan cin kuka da har saida tabawa bossay mamakin da sauri yaqaraso kusa da ita tare da rungumo ta jikin sa yana bata hakuri ya isa haka kidaina kuka yanzu zanje nabashi hakuri ya dawo amma dan Allah kiyi shiru kar kije kijawowa kanki wata matsalar kuma daban ba arabu da wannan ba wata kuma ta taso yanda kasan yana zugata yana cewa taci gaba da kuka haka takeyi harda shishiqa take numfashin ta na fauke wa hakuri yaci gaba da bata amma ina bata sauraron sa tana cikin yi kuma can yaji tayi diff jikin ta yasaki a tsorace yadagota amma sai ta tafi luuuuu zata fadi yayi saurin tarota tare da kwantar da ita yana kiran sunan ta a tamanin yasauka daga kan gadon yafita daga dakin aguje saida yagita yama rasa inda ze dosa da qyar iya gano office din shettima yana zuwa be jirara wata wata ba ya tura qofar tare da afkawa ciki a rikice ya shiga cewa doctor doctor shettima dayake kana kujera ya kifa kansa akan table yadago da sauri yana duba bossay ai tun kanyace mishi wani abuma ganin yanayin sa yasashi tashi a sukwani be jira cewar sa ba yafice faga office din,

bin bayansa yayi akusan tare suka shiga dakin tana nan kwance inda yabarta ba ta motsi da sauri shettima ya shiga jijjigata tare da daukar ruwan da yagani agefe ya yayyafa mata amma bata motsa ba

da gudu ya fice daga dakin ya nufi office din sameer yana zuwa ya banka masa qofa ya shiga yana shiga yaga yagama shiryawa yana shirin tafiya gida dagowa yayi yace malam lafiya zaka fadowa mutane guri ba sallama

a rude yace ina lafiya tana kwance bansani ba tana da rai ko ta mutu kazo ka dubata dan Allah tana can akwance bata motsi wani irin kallon banza ya watsa masa sannan yace ta mutu maba ina ruwana matsalar tace bata wa ba ina kaima likita ne basai kaje ka dubata ko dole sai ni yafada yana rabawa ta gefen sa ze wuci,
gabashi ya sha sannan yace kasan ba aikina bane da nawa ne ai da bazan tsaya ina bata bakin ba kana wulakan ta mutane saida nace maka karkabiye mata amma kaki jina wai meyasa kake hakane saikace baka san muhimmacin aikin kaba yanzu inta rasa ranta ta sanadin ka fa me zakacewa Allah wallahi kana wasa da aikin ka ko dan nana qasar bazeyi irin sakacin da kake yiba kai bare wanda ya fita waje yayi karatu kuma yake aiki acan amma girman kai da taurin kai da rashin sanin darajar dan adam irin naka ya hanaka tsayawa yin aiki yanda yakamata in kana abu kamar marar ilimi kana da ilimi kuma kasan illar rashin bada kulawa kan iya haifar da wata amma baka damu da hakan ba kai kawai damuwar ka kasani baka san ta wasuba yakamata kacanza rayuwar ka kadawo kan hanyar gaskiya dan rayuwar ka da gyara sannan kuma ka...hannu yadaga masa tare dacewa kaga malam ya isa haka ya ishe ka akan wata banzar yarinya zakazo kana gaya min magan ganun daka ga dama to bazan gyara ba ahaka naga damar yin rayuwata ba wanda ya isa yacan za min rayuwa duk abun da naga dama shi zanyi bawanda zemin dole dan haka karabu dani kariga kasan halina cike da baya inbaso kake musamu matsala dakai ba to kafita a harkata banason shishshigi acikin lamurana,
Allah sarki shettima idon sa har ya canza kala saboda tsabar takaici da haushin magan ganunsa da kyar ya iya budar baki yace ni kake gayawa haka ko saboda nagaya maka gaskiya kai duk abun da kayi ba daidai ba wanda ya isa yayi maka gyara to shikenan ba komai in Allah ya yarda zan fita daga rayuwar ka kamar yanda kace daga nan baza ka sake ganina ba kuma yarinyar ma zan dauketa bade dan ankawota gurin ka bane kake wulakanta mutane to daga yau baza kasake ganintaba bare asaka kayi abun da bakai niya ba nayi alkawari adaren nan zan dauketa zankaita gurin da akasan darajar dan adam dan kana takama da kanka kasan kaine kadai zaka iyayi mata shiyasa da kyar aka samu kayi mata aikin yanzu kuma kayi bazaka lallabata ayi agama ba tasamu lafiya sosai ba ka dau girman ka ka dorawa kanka karasa inda zaka nuna mulkinka da isarka sai akan yarinya qarama wacce bata san me take ba batama gama sanin ko ita wacece ba kaje kayi duniya ce ta isheka riga da wando wataran zata koya maka hankali inbaka bita asannu ba tsawa yadaka masa yace get out of my side be for I loss my temper yafada yayin da idonsa suka canza kala jijiyoyin goshinsa sun tashi rado rado sai faman ciccize baki yake yana futar da iska me huci shima azafafe yanuna sa da yatsa yace kayi lossing din saime zaka dake nine ko baka fada ba daman yanzu zanbar maka office bama shikadai ba zan bar maka duka asibitin ma gaba daya yana fada yajuya afusace ya fice daga office din tare da banko masa qofar bammm............✍


tabbb yau akeyinta aminan juna abokai kuma yan uwa sun rabu tsawon shekaru suna tare yau daya mace zatayi sanadin rabuwar su rabuwa ta baram baram
[4/4, 5:25 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode73-74-75

         """"""""""""""""""""""""""""""""

*sam*
Dunkule hannun sa yayi tare da kaiwa bango naushi idon sa ya canza kala jijiyoyin sa duk sun fito radau radau ji yake zuciyarsa nawani irin tsitstsinke wa kamat zata fito yau shi ake gayawa magana akan wata banzanr yarinya lalle dole ne ya koyawa yarinyar nan hankali ko yar gidan uban wacece agarinnan sai yasata nadama sai yasa ta tsani rayuwar ta daga yau farin ciki ya qauracewa rayuwar ta kujera yasamu yazauna sakamakon jirin da yaji ya na neman dibarsa  yana  qara tuna maganganun shettima musamman lokacin da yake cewa kayi duk abun da zakayi kuma yanzu nan zan barmaka office bama iya office ba zan barmaka asibiti gabada dagayau baza kasake ganin naba bani ba kai zan fita daga rayuwar ka mar yanda kakeso kaje kayi duk abun da kaga dama irin maganganun da suke tayi mishi yawo akai kenan kamar wanda aka tsikara ya mike da sauri yancewa abokina tun na yarinyata da na dauke shi tamkar dan uwa lokaci daya zaki zama sanadin rabuwar mu ke din wacece yar gidan uban wace koma yar wace saina koya miki hankali bama ke kadai hardan ginki sun shiga uku wlh duk saina tarwatsa farin cikin ku (oh ni yar nan saikace wace ta kashe mutum irin wannan masifa haka akan dan karamin abu lalle da kana da aiki oga sam  mude saide muce fatan nasara oga sam👌) a zafafe ya fito daga office din yanufi hanyar waje dan atunanin sa zuwa yanzu sunfito waje da yarinyar yasan ze taddasu agurin  kamar ma yunwacen zaki da ya kwana beciba haka yake tafiya ,

Dr shettima na fitowa yanufi office dinsa duk wani abu da yasan yana bukata ya tattara ya kwashe su abun kashewa ya kashe ya kwashe komai nasa abun da bansa ba ya ajiye masa abun sa  sannan yafita daga office din tare da jawo qofar yabar mukullin ajikin qofar be cire ba bare ya tafi dashi direct ya nufi dakinda take akwance tafiya kawai yake amma hankalinsa duk baya jikin sa  kana ganin sa zakasan ransa ba qaramin baci yayi bare kuma in ka kalli idon sa da suka canza kala sosai kamar garwashin wuta tsabar bakin  cikin da yake ciki yana qarasa shiga ko kallon inda suke bayi ba yace ka daukota kafito da ita inajiranka awaje bejira amsar  sa saba ya juya yafice saboda bayaso bossay yagane halin da yake ciki saide abun da besaniba ko a iya muryar sa zaka gane akwai matsala

yana fitowa sukayi kici bus da sameer a wajen hanyar fita  bai kalli inda yake ba yace gaba da tafiyar sa maganar sam ce ta dakatar dashi daga saurin da yake yi sameer ne ya kira sunan sa be jira ya amsaba ya dora dacewa kai yanzu ka zabi mace akaina ko to ina so kasani abotar mu bazata hanani yin abun danaga dama ba kuma idan bakayi ahankali ba zan iya hadawa dakai nagaya maka kuma kasan halina banason katsalandan acikin lamura na karkayi abun da zesaka danasani kafita daga harkar yarinyar nan naga kanka na rawa akanta da yawa tun ranar da nadawo muka fara samun matsaka dakai kuma duk adalilin ta yakamata kashiga hanklain ka tunkan lokaci be qure maka yaqara fada yana jaddada masa maganar da hannu,
duk atunani sa shettima ze bashi hakuri yace ya janye amma ga mamakin sa sai yaga yasaki murmushin gefen baki tare da shafar gemun fuskar shi,
sannan yace bismillah duk abun da kaga na cancanta da kayi min kayi min shi ka isa ai harkayi yawama  wlh kaban mamaki sosai ai duk abun da yafaru kai kajama abotar mu bata da amfani bakadauke ta da amfani ba dan haka nima dana dauketa da amfanin yanzu na ajiye kowa yayi rayuwasa inga hakan sai yafi da shiga harkar yarinya yanzu ma nafara inde akan aikin lada ne da sanin darajar dan adam yanzu nafara kuma bazan dena ba saide hakan yazama sanadin rabuwar tama rabuwar mu kuma ta har abada inde bazaka canza ba nikuma bazan canza ra ayina ba nima yana kaiwa nan ya qara gaba yana mishi magana amma be sauraresa ba

bossay da yatsaya a dakin yaqi fitowa yana tunanin me yake faruwa dazece ya dauko ta ganin bashi da me bashi kuma bayan da ya iya tunda akace yayi hakan  illa yabi umarnin da yabasa duk da yana buqatar qarin bayani amma a halin yanzude babu wannan lokacin ,

ciccibota yayi yafito da ita yana gama fitowa waje sukayi kicibus da sameer gaban shi yaji yafadi ganin yanda ya watsa masa wani mugun kallo me cike da fassarori be tanka masa ba dan ya lura shimade a kwai matsala watakil sun samu matsala a tsakanin su shiyasa yaga fuskokin kowannen su babu annuri cigaba yayi da tafiya har yaqaraso inda shettima yake a tsaye abakin motar sa ya bude masa baya yace sakata anan beyi musuba yasaka ta a back seat tare da rufewa sanna yamaida hankalin sa ga shettima yana jiran qarin bayani shettima ganin irin kallon da yake

40 / 49