Author : 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category : Romance
CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*
✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧
𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆
𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫 -7
KAREEM POV.
Kareem yayi kanta da sauri ya rike Safeena yana kokarin kwatar hannun Noor da ihunta ya cika dakinta tana fadin hannunta.
“Safeena karki karya mata hannu”
Daker ya kwaci hannun Noor a hannunta ta murgude hannun har yayi yaushi, gaba daya Noor ta rude kamar wadda ta fita hayyacinta ta fadi kasa ido a zare tana haki.
“Kin fita daga hayyacinki ne? Me ke damunki?”
Kareem ya tambaya cikin tsawa kamin ya juya ya rika ya kai hannu zai taba hannun Noor sai ta juyar da shi dayan gefe.
“Ya karye Azzaluma yar masan wuta ta karyashi”
Noor ta fada cikin kuka. Kareem ya shiga mata magana a hankali cikin rarrashi yana kokarin rika hannun ya duba.
“Be karye ba, kawo na gani”
Wani hawaye mai zafi ya saukowa Safeena, zafin da take ji a zuciyarta ya fi wadda Noor take ji a hannunta. Duk abun da ake Hafiz na zaune yana kallo be ce kuma be yi yunkurin yin wani abu ba, sai a lokacin da ya ga hawaye ya sauko a idon Safeena.
“Tirr da ke, tirr da uwa irinki... Tir da mata irinki... Tir da haihuwar ya irinki, tir da auren mace irinki, indai har sabon Allah ya kai ya rufe miki ido ki kama hannun wata ki murde saboda kishi, A gaban idona to kin yi hasara kuma kin cika tantiriyar yar iska, kuma haka da kika yi ba zai hana Kareem auren yarinyar nan, albashi sai ki hade zuciya ki mutu”
Ta dauke idonta daga barin kallon Noor ta kalli Hafiz, kamin ta kai hannu ta taba hawayen da bata san da saukarsu ba sai a lokacin, ta yi murmushi ta dubi Kareem dake fadin.
“Babu komai tsakanina da Noor, wace magana kake haka? And ka cire bakinka daga magana da ita, babu ruwanka idan zaka yi magana ka yi da ni ba da ita ba, ba ka da wannan hurumin”
Dauke kai Safeena ta yi ta juya ta fice daga office din. Kareem ya kalleshi cikin damuwa ya ce.
“Akan me zaka fadi wannan maganar? Zata dauka da gaske ne, Safeena tana da mugu mugun kishi, baka san abun da zai je ya dawo ba”
Hafiz ya wulga masa wani wulakantaccen kallo. Har zai yi magana sai kuma ya juya ya kalli Noor da ta cire hijabi saboda wani azabar zafi da take jin ya game jikinta gaba daya sai kuka, Kareem ya ci albakarcin Noor tana gurin ba dan haka ba, Hafiz zai fada masa magana ne marar dadi, sai dai baya son Noor ta san komai dan haka yayi shiru. Kareem ya juya ya kalli Noor sannan ya nufi gurin da keys dinsa suke ya dauka, ya nufi inda take.
“Taso mu tafi asibiti zan duba miki a can”
Noor ta girgiza kai tana jin wani irin azaba a hannu.
“Aa a barshi haka, gyaran akwai zafi ni taimakonta kawai na yi, me yasa zata min haka? Miye laifina ni?”
Kareem din take tambaya tana kuka sai gumi take. Kareem yayi shiru yana kallonta cike da tausayawa ya rasa me zai ce.
“Mamana bata san na zo nan ba, jiya sai da ta yi min duka sai da kaina ya fashe saboda kai, bata bar ni na ci komai da na tafi da shi ba, yau kuma wata ta karya min hannu saboda kai, kuma na san Mama sai ta min duka ko Baba, na san haka zata min ba zan biyota na zo ba”
Tausayinta ya kama shi. Ya sake mika hannu ya rika hannun ta kauce tana kokarin mikewa tsaye.
“Be karye ba Noor, duba kawai zan yi sai na baki magani, idan akwai zafi ba zan taba ba na miki alkwari”
Ta kalleshi.
“Rantse”
Ya daga hannunsa.
“Na rantse”
“Ce ka rantse ba zaka taba min ba idan akwai zafi”
“Na rantse ba zan taba miki ba idan akwai zafi”
“Ce Wallahi Wallahi ba zaka taba ba idan akwai zafi”
“Wallahi Wallahi ba zan taba ba idan akwai zafi”
Ya rantse kamar yadda ta bukata sannan ta yarda, ya dauki Hijabinta zai saka, sannan ya nufi kofa ya bude mata, ta fita tana kuka, a yar fahimtar da yayi mata daga jiya zuwa yau ya san ba lallai ne yace ta yi shiru ta yarda ta yi shirun ba, balle yace ta hakura da kuka saboda hankalin mutane dake karkatowa izuwa garesu a duk inda suka wuce. Ya riga isa gurin motar ya bude motar ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga bangarensa ya tashi motar.
Har suka isa asibitin kuka Noor take domin a tunaninta hannunta ya samu kariya ne. Wannan karon be shiga da ita office dinsa ba ya tsaya da ita a gurin da ake duba marasa lafiya kamar kowa. Ya nade hijabin ya kalli hannu yana son ya taba yana tsoron tsare da ido da ta yi.
“Har yanzu akwai zafi?”
“Eh mana, kana ganin hannun ya karkace ba”
“Kashin ne ya bar gurinsa, amman ba kariya ba ce”
“Wallahi Wallahi da ace ni mai gata ce sai na yi shari'a da matar nan, amman na barta da Allah Allah ya isar min, Allah yasa ciwon jikinta kar ya warke har abada”
Kareem dai be ce mata komai ba sai kallonta yake kamin ya mike tsaye ya bar gurin. Be yi minti goma da tafi ba wata likitar ta zo ta duka tana duba hannun Noor.
“Ta so muje”
Noor ta mike tsaye ta bi bayanta suka shiga bani dakin jinya, a nan suka samu Dr Kareem ya sanya safar hannu yana aje wasu kwalabe a saman karamin teburi. Da kai Dr Kareem yayi ma likitar da ta shigo da ita magana da ma wadda ta shigo bayanta. Sai da ta bari Noor ta zauna sannan dayar ta kama hannun ta rike gam, Noor ta kalli Kareem da sauri.
“Kace ba zaka taba ba”
Ya daga hannunsa sama ya cire safar ya juya yayi ficewarsa daga dakin. Be dawo ba sai da aka gama komai, Noor ta yi kuka har ta galabaita.
“Sannu...”
Ta kalleshi kurun tana hawaye, shi kuma ya kalli bandajen dake kanta sai a lokacin ya lura da ba wadda ya saka mata ba ne a jiya.
“Waya canja miki wannan?”
Ta yi shiru tana haye yawu kamin ta fara kokarin sauka kam gadon.
“Ina saki je?”
“Gida”
Ta amsa tare da fara takawa tana rike da hannun da aka daure mata.
“Okay zan kaiki gida, amman me zamu je ce? Ko dai mu kira Yayanki ya zo asibitin nan?”
Ta girgiza kai da sauri.
“To me zan fadawa Iyayenki?”
Ta girgiza kai.
“Kira min Zafeer”
“Waye Zafeer?”
“Shi ne wadda zan aura”
“To zo ki zauna”
“Bana son asibitin nan bana sonta”
Ta fashe da kuka.
“Shi kenan, muje na kira shi a mota sai ya same mu a restaurant haka ya miki?”
Ta daga kai, sai ya nufi kofar ya bude mata ta fita sannan ya fita. Har suka isa gurin motar tana rike da hannunta kamar wadda ke dauke da jariri. Sai da ya fara tukin sannan ya kalleta a hankali cike da tausayawa ya ce.
“Noor ina kika hadu da wannan matar?”
Ta bashi labari cikin kuka. Sai yayi mata wata tambaya da ya saka ta watsa masa harara.
“So na kike yi?”
Ta hada masa da kwafa.
“Toh why do you lie me yasa kika mata karya?”
“Kaddara da rabon sha wahala, ashe ma ta sanka ita din budurwar ka ce?”
Yayi shiru be amsa mata ba ya dauke kai ya cigaba da tukinsa.
“Ina ta sanka?”
“Ba kin ba ni shawara kara aure ba?”
Ya fada yana kokarin kawar da maganarta.
“Wallahi karka aureta, zata hadu da wacan matar ta ka su yi ta maka hauka”
Yayi murmushi sannan ya dauki wayarsa ya mika mata.
“Saka number saurayin”
Ta karba tana kallon yadda wayar ta cika mata ido.
“Me yasa Mama ta dake ki? Gaskiya kika fada mata?”
“Aa bata fada min laifina ba, wata kila ta dauka ko na roke ka ne”
Ya kalleta.
“Duk abun da kika zaba jiya baki ci komai ba?”
Ta daga masa kai tana kokarin kai wayar a kunnenta.
“Ni zan yi magana da shi”
Ya karba ya kara wayar a kunnesa.
“Wa'alaikusalam ina magana da Zafeer ne”
“Eh wake magana?”
“Sunana Kareem, kuma ina tare da Noor yanzu haka, sai dai ba wata matsala ba ce ta ji ciwo ne a hannu shi ma ba sosai ba, tace a kiraka ka zo ka tafi da ita gida”
A take hankalin Zafeer ya tashi.
“Subhanallahi garin yaya? Ina take tana lafita me ya same ta?”
“Ka kwantar da hankalinka da sauki ba sosai ba ne, gata ka yi magana da ita”
Ya mika mata wayar sai ta karba ta fara zuba masa shagwaba.
“Wata ce fa daga na taimake ta sai ya rike min hannu ta murde, sai da aka daure min aka gyara”
“Kina ina?”
“Ina cikin motar Kareem din, shi ne wadda ya kade ni jiya, gamu mun iso Restaurant dinsa ka zo ka tafi da ni gida, bana son ya kai ni kar Mama ta sake yin fada”
“Noor me ya kai ki gurinsa? Me yasa baki jin magana ke? Taya ma kika tafi gurin? Why Noor why?”
Ta yi shiru bata ce masa komai ba. Kareem na ganin yanayin fuskarta ya sauya ya mika hannu ya karbi wayar ba dan ya san me Zafeer din ya tambaye ta ba.
“Ka zo Kareem Restaurant ka dauke ta, idan ka zo kace a kawo ka office dina kai tsaye”
Ya kashe wayar.
“Jiya na so na kira Yayanki na ce ya jikinki, amman wata damuwa ta saka ni a gaba, na manta da komai”
Bayan ya karbe wayar yake fadar haka a daidai lokacin da ya faka a harabar.
“Kasan wannan matar ko?”
Ta aiko masa da tambayar da be san yadda zai sarrafa halshe ya amsa mata ita ba.
“Na ji ka fadi sunanta, ni ban ma san sunanta ba, budurwarka ce?”
Yayi shiru na tsawon lokaci yana kallon waje ta cikin gilashin motar.
“Aa”
“Tace min tana son ta ganka, mesa ta yi karya?”
“Ke me yasa kika yi karya? Already kina da wadda zaki aura akan wace hujja zaki yi karya?”
Ta yi shiru, sai ya bude motar ya fita ya rufe ya bar Noor a ciki, ya busar da iskar bakinsa ya rufe ido ya bude ya girgiza kai. Sai kuma ya bude motar ya dauko wayarsa ya rufe. Number Safeena yayi dialing ya kai a kunnensa. Wayar ta yi ringing har ta gaji bata daga ba. Ya sake cika bakinsa da iska ya koma cikin motar ya zauna.
“Noor karki sake yi ma wani karyar kin san ni, kuma ki daina bin motane any how ko kin san su ko baki san su ba”
Ta daga mishi kai a hankali cike da natsuwa.
“Kuma ki rika jin maganar iyayenki kin ji?”
Nan ma ta daga mishi kai.
“Ka yi hakuri, ba zan sake ba daga yau ba zaka sake ganina ba”
Ta fada tana hawaye sai kuma ya ji babu dadi.
“No ba wai bana son zuwanki ba ne, kawai bana son ki saka kanki a matsala ne, kin ga iyayenki suna miki duka da fada, kuma kin ga yanzu kin samu rauni saboda haka”
“Na fahimta...”
Ta amsa masa murya a sanyaye hakan sai ya kara masa raunin tausayinta dake zuciyarsa.
“Me kike son ki ci?”
Ta girgiza kai, ta bude motar ta fita.
Sai shi ma ya bude ya fita ya wuce gaba ta bi bayansa.
NOOR POV.
Babu kowa a office din, mutunen dazun da ban san waye ba yayi tafiyarsa. Kareem da kansa yaja min kujera na zauna sannan ya zauna a kujerar dake facing din tawa.
“Baki sha'awar cin komai? Ko kuma na miki takeaway”
Na girgiza masa kai, ji nake bana sha'awar komai nasa a yanzu.
“Noor”
Ya kira sunana a hankali a lokacin da na dago kai sai na tarar ni yake kallo.
“Kin sa na ji babu dadi, maganar da na yi ce ta bata miki rai?”
Nan ma na amsa masa da kai. Yanzu kam gaba daya hankalina ya koma gida gurin mahaifiya hukuncin da zan karba idan na koma shi ya tsaya min a rai.
“Ina tunanin gida ne, yau Mama sai ya sake karya min hannun babu wadda zai cece ni”
Na fada hawaye na sauko min, domin a lokacin ne na gane kuskuren da na aikata na biyo matar har nan.
“Ko zamu tafi tare da Saurayin na ki sai mu bata hakuri mu yi mata bayani? Bana son ta dake ki?”
Magana yake min kamar wadda ya damu da ni da gaske. Na girgiza masa kai ina kallon hannuna da aka daure.
“I'm sorry haka kaddara take wani lokaci, ba ma iya kauce mata”
“Ni kaddara ce marar kyau a gidanmu, shiyasa ni ce mai laifi kullum, shiyasa Babana...”
Na samu kaina da fadar haka, sai kuma na yi shiru domin be kamata na fadi ciwona a inda babu magani ba. Wani abun da ban yi zato ba, shi ne tashin hankalin da na gani a fuskar Kareem a lokacin da yake kallona, damuwa da tausayi sun bayyana karara a fuskarsa. Na sauke kaina kasa tare da saukowar ruwan hawaye.
“A duk lokacin da kika ji kina bukatar wani abu ki zo gurina kofata a bude take, ko gobe idan wani ya tambaye ki miye alakarmu ki fada masa abun da yayi daidai da ra'ayinki, karki ji haufi”
Ban ce masa komai ba, kuma ban dago ba hawaye kuma ba su fasa min zuba ba. Ta gilashin dake window na lura da Magariba ta yi saboda duhun da ya fara shigowa. Yunkuri yayi sai mike tsaye sai aka turo kofar office din aka shigo bayan ya kwankwasa.
“Ranka ya dade wai wani ne yake nemanka, sunanshi Zafeer”
“Shigo da shi”
Sai ya koma ya zauna da kyau bayan ya amsa, sannan ya kalleni.
“Share hawayenki kar ya ga kina kuka”
Na share hawayen na maida hankalina da dubana gurin kofar shigowa. Babu jimawa Zafeer ya shigo dakin yana kallon hannuna hankalinsa ya kara tashi.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Baby Noor me ya same ki?”
Na yi shiru wani sabon hawaye ya cika min ido ni da ban saba hawaye sosai ba. Kareem yana masa bayani amman Zafeer ko kallon inda yake be yi ba, da alama daga bakina yake son jin karin bayanin.
“Wata mata ce tace na kawo ta nan...”
Na fada masa gaskiyar yadda komai ya faru. Sai dai a yadda na lura gaskiyar tawa ta masa ɗaci domin kuwa rufe ni yayi da fada abun da be saba ba.
“Me yasa zaki yi haka? Wa kike son ki burge? Me kike nema a gurina da baki samu ba har zaki kwadayin wani ya zama saurayinki? Ita din me kika mata da zata ji Miki ciwo a hannu haka? Saboda me? Daga makaranta sai ki tsallake ki zo nan yanzu matar nan idan cin mutane take sai ta cinye ki”
Wani irin fada yake min da tsawa kamar ba Zafeer dina ba. Lallai na yarda ni sokuwa ce kuma an aikata babban laifi. Ta cikin ruwan hawaye na ke ganin Kareem ya mike tsaye yana fada.
“Haba Malam daga zuwanka sai ka rufe ta da fada, ta ki yarda na kaita gida saboda tana tsoron fada, tace a kiraka saboda tana tunanin zata samu sauki a gurinka sai kuma ka rufe da fada babu sauraren Uzuri, yarinya ce fa bata kai matsayin da kuke tunanin ta banbance daidai da akasin haka ba kuma babu wadda baya kuskure”
Zafeer ya kalleshi.
“Ai kai ka banbance daidai, tun da kana tsaye aka ji mata a hannun, sai yanzu zaka ce bana sauraren uzuri, uzurin me zaka ba ni?”
Kareem ya nuna shi da tsaya.
“Tsaya matsayinka ka kula da kalamanka, wata kila ba dan yarinyar nan ba, da baka da alfarmar shigowa office din nan, so respect yourself”
“Gaskiya ne, kai ya kamata ka fara respecting kanka ai, kamin ka ni, babu ruwanka da yarinyar nan babu ruwanka da ni, baka san abun da ke tsakaninmu ba”
Zafeer ya fada. Kareem ya kalleni ya kalleshi sai kuma ya dauke kai. sannan sannan ya kalleni a fusace.
“Mu tafi”
Na wuce da sauri ya biyo bayana, haka ya saka ni a gaba har muka isa titi. Ya tari Napep ya shiga sannan ni ma na shiga, gaba daya a rikice nake, yadda na ga ran Zafeer ya bace ya saka hankali kara tashi, shi kenan da yake goyon baya baya son bacin raina balle kuma Baba ko Mama ya ransu yake a yanzu.
“Noor”
Na kalleshi.
“Me yasa kika ce mutumen nan Saurayinki ne?”
Na yi shiru domin ba ni da wata hujja da zata gamsar da shi, indai har Hujjar dazun da na bashi labarin komai be gamsar da shi ba ban san me zai kare kaina sa shi ba.
“Saboda yana da kudi?”
Zuciyata ta buga da karfi, Zafeer ya fara lissafin da ban taba yi ba, ya zarge ni da abun da ban yi tunani ba. Sauke murya yayi kasa sosai kamar marar lafiya.
“Zan yi kudin In Shaa Allah Noor zan gina miki irin gidan da kike so, da irin tsarin da kike so, zan wadata ki da komai, zan maida ke sarauniya na maida ke abar kwatance, ki kara hakuri ki kara min lokaci kin ji?”
“Ba saboda haka ba ne, ni dai kawai na yi ne saboda na firgita matar”
Ina jin lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ya kalleni a raunace.
“Dan Allah karki sake, rai na ya bace yau saboda abun da kika yi, ban jidadi ba kin saka na raina kaina, kuma kin saka na miki wani kallo da be kamata ba, Baby Noor ki zama mai sauraren maganar iyayenki kin ji? Ki zama mai bari idan aka hana ki, mai yi idan aka ce ki yi kin ji Baby na”
Na daga mishi kai har lokacin jin nake kamar ba Zafeer dina ba ne, Mai Napep din ya juyo ya kalleni.
“Lafiya?”
Zafeer ya tambaya be ce komai ba ya juya ya cigaba da tukinsa.
“Kin san inda matar nan take?”
“Ban santa ba”
Na amsa ina share hawayena. Zafeer yayi kwafa.
“Zafeer ka yi hakuri ba zan sake ba”
Na fada murya na rawa, sai yayi min ya girgiza min kai. Be