Author : 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category : Romance
yaranta uku, sauran duk iyayensu sun fita, ni ma sai bayan auren nake ji, wata kila shiyasa ta kama kanta”
Ina jin haka na san an gudu ba a tsira ba ne, kenan ita ma idan ta yi masa ba daidai ba zai iya sakinta. Daga bangaren Mama muka fito muka shiga bangaren matar da take gidan a yanzu. A cike muka samu falon da mata da maza, Mama ta yi sallama suka amsa suna gaisheta da mutunci.
“Noor Ya hakuri?”
Wata budurwar da ban waye ta ba ta fada sai na amsa da Alhamdullahi na gaishe da Hajiyar.
“Lafiya Kalau Noor, an fita wanka ko? Tohm Allah ya bada hakuri ya kawo na gari”
Mama ta amsa da Ameen.
“Alhaji ne be santa ba sai mita yake ina boye masa yara, tare da yayanta take jibi zai wuce Sudan gurin karatu, ya zo bankwana amman be tsaya ba, ita kuma ba ce ya tsaya ta gaisa da yan gida”
“Ta kyauta gaskiya, da ma dai kin maido nan kila zata fi jin sanyi kin san gidan na mu cike yake da mutane”
“Mahaifinta ne ai be yarda ba, ko takaba a nan ya so ta yi amman uban yace ba zata yi ba”
“Kin san wasu mazan akwai kishi”
Haka dai suke ta hirarsu ni dai kaina na kasa ban dago har sai da na ji an bude kofar falo alamar mutum ya shigo. Dagowar da na yi sai muka yi ido hudu da Safeena tana dauke da cikinta da be gama girma ba. Bata kallon kowa sai ni ni ma kuma bana kallon kowa sai ita muka rika kallon kallo wata kila ita ma tana mamakin ganina ne kamar yadda nake mamakin ganinta. Gidansu ne? Ko kuma zuwa ta yi? Ko kuma dai tana da wata alaka ce da mutanen gidan?
“Kin dawo Safeena?”
Hajiyar ta fada sai Safeena ta amsa mata ba tare da ta kalleni ba, har lokacin ni take kallo.
“Na dawo Hajiya, na karbo files din gobe zan tafi asibitin na kai”
“Toh Allah ya taimaka ya raba lafiya”
“Ameen”
Ta amsa sannan ta dauke idonta ta zauna a kujerar dake facing dina, sai kuma ta sake dasawa daga inda ta tsaya.
“Anty Safeena kin santa ne?”
Na kalli mai tambayar wata kila su ma sun lura da kallon da take min yayi yawa. Ga mamakina sai ta amsa da cewar
“Aa ban san ta ba, wacece hala? Ta yi min kama da wata kawata ce ta yarinya”
“Noor ce yar wajen Anty Amarya, wanda mijinta ya rasu”
“Allah sarki Allah ya masa rahama”
Ya juya tana kallon Mama dake amsawa da Ameen sannan ta sake kallona. Har muka baro bangaren babu abun da take sai kallona kamar wata bakuwarta. Ban kuma san dalilinta na boye cewar ta san ni ba. A bangaren Mama na koma na zauna har dare ina jiran dawowar mijinta saboda mu gaisa, be shigo ba sai bayan Magariba a lokacin da ake hada hadar Sallah Isha'i.
Na yi mamakin yadda yayi murna da farinciki ganina babu wata kyama, har na na yi sha'awar ina ma ace shi ne mahaifina ba Baba ba, zaunawa yayi a falon yana ta min nasiha akan hakuri da rayuwa na halin da na samu kaina da kananan shekaru, na yi masa godiya ya saka hannunsa aljihu ya ciro 10k ya ba ni.
“Aa na gode”
A bakin gaskiya ta ba zan karba ba, domin ko na karba ban san miye zan yi da su ba a yanzu. Sai dai na lura hakan be masa dadi ba domin rufe ni yayi da fada a dole na karba na yi masa godiya.
“Tafi bangaren Hajiya ki ce na ce cikin yaran nan duk wanda yake nan ya sauke ki gida”
“Tohm”
Na mike tsaye na yi ma Mama sallama sannan na fice daga falon yana ta kallona. Bangaren Hajiyar na dawo na sanar mata abun da Alhaji ya fada sai mutumen dake tsaye a gabanta yayinda take zaune ya juyo ya kalleni. A nan ma wani mamakin ya kara kama ni, mutumen nan da ya taba yunkurin biya min kudin siyayyar da na yi a wani dare da muka fita tare da Hafiz.
“Kamar na sanki?”
Na bude baki kamar zan yi magana sai kuma na yi shiru, ban san me zan ce ba, ni dai ina da saurin gane mutane shiyasa na gane shi.
“Noor ce Yar wajen Anty Amarya ce, ita ce wadda mijinta ya rasu”
“Ai ban sani ba, Allah ya jikanshi da Rahama”
“Ameen, ku tafi tare sai ka sauke ta ka wuce, Noor bari ga Abdull zai fita yanzu sai sai ya wuce da ke, ki jira shi a waje”
“Okay”
Na juya na fito daga ciki, ban san wacece motarsa a cikin motocin gidan ba dan haka zauna a balcony har ya fito.
“Kika zauna a kasa?”
Bance komai na na mike tsaye na bi bayansa muka isa gurin wata sabuwar mota, sai da ya fara shiga sannan na bude na shiga front seat. Ba tare da yace min komai ba yayi reverse ya fice daga gidan.
“Ina ne unguwarku?”
A lokacin da na dago sai na ga idonsa akaina suke. Na fada masa na sake maida kaina kasa kamar ba ni ba. Na ji lokacin da wayarsa ta yi kara ya amsa.
“Hello Safeena...”
Sai kuma yayi shiru, yana sauraren abun da ake fada masa.
“Yanzu na fito gida, amman zan biya ta can, sai na zo miki da shi, shi kadai kike so ko da wani abun?”
Na yi shiru ina saurarensa kamar wata Munafuka kamin na ji ya ce.
“Okay sai na dawo”
Ya aje wayar ya dago zan kalleshi idona suka fada cikin nasa da sauri na dauke kaina ina jin sautin murmushinsa. Ban sake kallon gefen da yake ba har muka isa unguwar.
“Ka sauke ni a nan unguwar bata da kyau can ciki”
Na fada.
“Karki damu, amanarki aka ba ni sai na kai ki har gida”
Yadda ya fada haka ya aiwatar har kofar gidanmu ya isa da motarsa ya faka, ni kuma na bude na fito zan rufe kofar ya ce.
“Ba godiya”
Ban ce masa komai ba na rufe motar, na gode masa sai ka ce rokonsa na yi ya kawo ni. Sai da na shiga gida sannan na ji motarsa ta bar kofar gidan.
KAREEM POV.
Yana gama sallah asuba ya shiga kitchen hadawa yaransa breakfast. Domin Yusura bata musu komai tun da ta dawo gidan, Kullum shi zai hada musu breakfast ko kuma ya saka aika musu daga restaurant dinsa kamin su tashi break.
And now cooking is one of his favorite things, yana samun nishadi a girkin, musamman idan yaran suka farka suka same shi a kitchen suna hayani yana aikinsa har ya gama, ya karya tare da su wani sa'in kuma ya zuba musu na su, ya tafi da nasa a office ko kuma su su tafi da na su school shi kuma ya ci a gida. Idan ya fita sannan Yusura take saukowa ta gyara ko'ina ta dora na rana. Tun da ta dawo gidan be taba leka dakinta ba, be taba ce mata uffan ba, ita ma kuma bata bari sun hadu ba, da zarar ta ji motarsa ko ta san lokacin dawowarsa sai ta shige dakinta.
Yau ma sai da ya raka su har gurin bus sannan ya dawo ya zauna ya ci nasa breakfast. Bayan ya gama ya mike tsaye ya shiga dakinsa yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya ya fito yana rike da lab coat dinsa da wayarsa sai kamshi yake zuba. Yayi kyau sosai ramar da yayi ta kara masa kwarjini da haifa. Sai da ya fice daga falon sannan Yusura ta sauko a zatonta ya fice gaba daya, dinning ta nufa ta tsaya tana kallon kayan karyawar da ya shirya, biredin da ya gasa ta dauka taba tabe baki ta shinshina ta aje.
Sannan ta ja kujera ta zauna ta bude flask din ruwa zafi, a daidai lokacin Kareem ya turo kofar falon ya shigo domin daukar wallet dinsa da ya manta a dakinsa. Kallo daya yayi ma gurin da take zaune ya dauke kai ya haura sama ya dauko wallet dinsa ya sake fice. Yusura bata taba jin kunya irin ranar ba, bayan amincewa da aurensa da ta yi wannan ne abu da na biyu da take bakinciki a rayuwarta, ji ta yi kamar ta fasa komai na gidan dan bakinciki.
Tuki yake a hankali har ya isa asibitin, ya faka motarsa a gurin da aka rubuta Dr Kareem sannan ya fito ya dauki kayansa ya rufe motar ya shiga cikin Babbar asibiti ana miko masa gaisuwa yana amsawa. Office dinsa ya shiga ya fara duba takardun dake gurin sannan ya fita ya fara duba marar lafiyar da aka aje da ya kamata ya duba su.
After ya gama ya dawo ya zauna a office dinsa patient din dake shigowa suka fara shigowa yana dubata. Third person da ta shigo ita ce Safeena, tana sanye da dogon Hijabinta har kasa sai dai hakan be boye cikin dake jikinta, har ta zauna ita yake kallo. Sai da ta aje jakar dake hannunta sannan ya jingina baya ya kwanta jikin kujerar yana kallonta.
“Wai ke wace irin yarinya ce Safeena?”
“Ni din wata yarinya ce, mai wuyar warke ciwo, wata yarinya ce da ka koyawa soyayyarka kuma kake kokarin guduwa bayan ka yaudareta da farko”
“Gargadin da na yi miki, da kuma tazarar da na baki daga lokacin da muka yi haduwar karshe zuwa yau bata fahimtar dake, na rumgumi kaddarata, ke ma ki rumgumi taki?”
“Ka rumgume kaddara saboda Yusura tana sonka tana kyautata maka a yanzu? Ko kuma daman can karya ka yi min kace bata kula saboda kullum ka rika samun biyan bukatarka da ni? Ka yi breaking heart dina da farko yanzu kuma bayan na saba mu'alama da kai na saba da kwanciya a kirjinka na saba da soyayyar kake tunanin sake guduwa ka bar ni?”
Ya mike tsaye daga zaunen da yake ya nufi windows dinsa ya bata baya.
“Kana da kyau, Kareem kana da kudi amman duk wannan be tabbatar min da ina sonka ba sai da mu'amala ta hada mu, all this while na kyale ka ne saboda ina dauke da cikin nan”
“Me kika zo yi yanzu? Tashi ki fice daga office din nan”
“Baka da wannan damar ba saboda da kai na zo ba, saboda cikin nan ne, na dawo da awon cikin nan a nan ne, a nan zan yi ta zuwa har zuwa lokacin da zan haihu”
Ya dafa Window ya rike kansa.
“Namiji zan haifa suka ce, kuma ina alfahari da haka”
Kareem ya dauki lokaci a haka kamin wani tunanin ya zo masa sai ya juyo da sauri ya kalli cikin na ta sannan ya kalli fuskarta, sai ta yi masa murmushi.
“Fita ki bar office din nan”
Ya nuna mata kofar, zata sake magana da daka mata tsawa har sai da ta zabura.
“Fita ki bar office din nan na ce”
Ta mike tsaye da sauri ta dauki jakarta tana kallon yadda ya hade fuska kamar be taba ganinta ba, ta fice daga Office din. Dawowar yayi ya zauna kan kujerar ya dafe kansa ya runtse ido yana numfashi da karfi, ya girgiza kai kamin ya daga hannunsa ya buga a tebur din yana jin wani irin bakinciki marar misaltuwa...
It could be a joke maybe tana gwada shi ne, if not ai tana da hankali matukar ba wata manufa take da ita akansa ba ba zata taba sha'awar haihuwa da shi alhalin tana da aure ba, ta dauki dawainiyar cikin da ba na mijinta ba ta kai masa yayi komai, ba zata fara ba. Abun da zuciyarsa ta raya masa kenan har ya ji ya samu saussaucin cigaba da aikin da yake. Sai da lokacin tashi aikinsa yayi ya tuna da ba shi da abokin hira ko shawara a yanzu domin Hafiz is no more balle ya fada masa hasashensa ko damuwarsa.
Tafiyar Ya Nabil karatu ta zame ta bude min wani gurbi a gidan. Domin ruwan da yake debo mana da safe yanzu nauyin ya koma kaina, ni nake cika gidan da ruwa ga jikin nawa ba mai son wahala ba ne amman haka nake daurewa ina yi saboda gujewa hayaniyar Baba bana son ya jefe ni da wata kalmar marar dadi a yanzu. Haka ma ba fita nake son yi ba, saboda idanuwan mutane yana kaina, idan na hadu da kanen Zafeer har jefa min magana suke kamar ni na so mutuwar auren ko kuma zaman gidan.
A haka dai na daure na danne zuciyata ina cigaba da rayuwa a gidan ubana. Ranar wata labara Anty Larai ta kawo mana ziyara har da tsarabarta domin ta dade rabonta da gidan. Rabon da na saka a ido kuma tun a gurin gaisuwar Hafiz. Na yi murna sosai da ganin tana cikin Gwagganina masu hankali da kamanta adalci daidai gwargwado. Ina zaune kusa da ita nabban danta Ridwan Wanda ya kasance cousin ne a gareni sai tsokana ta yake, ni kam baki ya mutu bana cewa komai, Hana ce take ramawa sai Umma dake dan jefo magana sama sama.
Gwaggo ta shafa kaina zuwa bayana tana murmushi ta ce.
“Ka bi ka saka min yarinya a gaba, saboda yanzu ka samu ta yi lafiya ko? Da ada ne ai ba zaka iya da ita ba”
“In ji waye ko a da ne zan iya, kawai ina daga mata kafa ne”
Anty Larai ta bude jakarta ta dauko goro ta gutsira tana fadin.
“Nabil an tafi ko? Ya zo min bankwana ai, Allah yasa ayi karatu cikin nasara”
“Ameen”
Na amsa ina daga kai na kalli Ridwan dake shirin tafiya.
“Zaki dare nan?”
“Aa idan dai ka yawato ka samu abun da zaka samu sai ka dawo ka dauke ni mu tafi gida”
“Yaya Ridwan har yanzu Napep din kake ja?”
“Toh ya za'ayi abincin a nan yake”
Ya amsawa Hana dake tambayarsa domin tun tashinmun, Yaya Ridwan ba shi da wata sana'a da ta wuce jan Napep, da ita ya rike gidansa ya yaransa da matansa biyu har ma da mahaifiyarsa.
“Allah ya taimaka”
Cewar Umma, dukanmu muka amsa da Ameen sannan ya fice. Shimkafa da miya Umma ta girka saboda zuwan Anty Larai, bayan mun ci mun yi sallah Hana ta dauki awara ta fice gurin sana'ar da ta zame mata dole, ni kuma na zauna da Anty Larai muna ta hira, a cikin hirar nake gutsura mata irin zaman da muka yi da Aisha da yadda yan'uwansa suka jajirce ba za su ba nu gado ba.
“Daman can Allah ya gani, zuciyarta bata natsu fa yarinyar nan dari bisa dari ba, mata makircinsu yana da yawa, ke kuma ba wayo ne da ke ba kuma babu mai tsawata a tare da ku, dama ace irin gidanmu ne da muke hade kin ga wani abun ko dan ganin idon uwar miji dole a bar shi”
“Ni kadai nake zaune kuma kowa da bangarensa, amman hakan be hana ta cutar da ni, gashi ya yarda da ita, komai aka fada masa akanta baya yarda”
“Ki barta da Allah, yanzu ai mai rabawa ta raba, Allah ya ba ki na gari ita kuma sai ta je can ta karata”
Na yi shiru ina zane a hannuna da karen tsintsiya, kamin na kira sunan Gwaggo.
“Anty Larai”
“Na'am Khadijatu”
“Anty Larai, alfarma nake nema a gurinki, na san Baba yana jin maganarki, dan Allah ki roka min shi yayi hakuri yace ya yafe min na yi magana da Zafeer”
Na kora bukatar tawa ne ba tare da na kalleta ba, domin ina jin nauyin kallon idonta a yanzu.
“Zafeer din ya dawo ne? Aiko ya kai masoyi kuma lallai yana sonki da gaskiya bawan Allah nan”
“Be dawo ba, yana da zuciya sosai wata kila ba zai sake sona ba har abada, amman ni ina son a duk lokacin da na ganshi ko kuma na samu dama na masa bayanin da zai gamsar da shi cewar ba wai na ki aurensa saboda ba shi da kudi ba ne, na lura yan'uwansa har yanzu ganin suke kudi na bi na bar Zafeer”
“Idan har yana sonki da gaske zai dawo, ai mai sonka be ganin ramar ka, be ganin tsufanka, kuma shi ma mahaifinku ai be dace ya shata muku layi mai kauri irin wannan ba, saboda zuciya bata da kashi”
“Dan Allah ki masa magana, yace ya yafe min”
“Zan mishi magana idan ya shigo, noor har yanzu kina son yaron nan ko?”
Na daga mata kai ba tare da boye ko jin kunya ba, zan iya fadar ina son Zafeer a gaban, duk kuwa da na san a yanzu yayi min nisa. Sai na ji ta yi dariya tana buga bayana.
“Aiko da har ina cewa Ridwanu ya shigo ko Allah zai ba shi sa'arki, sai ayi tuwona maina tankaden bakin gado?”
Murmushi ne kadai abun da zan iya yi na kwanci kaina a wannan lokacin kuma shi na yi, sai dai ko kadan manufar da take son isarwa a gareni ba mai yiyuwa ba, sai idan cilasta Baba zata yi yayi min auren dole. Baba be shigo gidan ba, sai da yamma liss ya dawo a gajiya. Na debi ruwan wanka na kai masa yayi wanka ya fito ya zauna kusa da yar'uwansa yana cin abinci suna gaisawa.
Ina alwalar magariba na ji tana yi nasa maganar Zafeer.
“Ai wannan duk da ne, yanzu kam komai ya wuce, ko lokacin da na yi mata wannan furucin ta fusata ni ne shiyasa kuma na lura a wacan lokacin tana son ta biyewa zugarsa ne ta bijirewa umarnina, amman yanzu komai ya wuce”
“Duk da haka dai ka ce ka yafe ka san bakin iyaye lalle ne”
“Haka ne, toh na yafe Yaya Larai kina shagwaba Noor”
Ta yi murmushi ni ma murmushin na yi ina jindadin janye takukun da Baba yayi tsakanina da Zafeer. Daki na shiga na yi sallah bayan na gama na fito na yi ma Anty Larai godiya a lokacin Baba yana masallaci. Shigowar Ridwan da mintuna kadan Baba ya dawo daga masallaci suka gaisa Ridwan yayi masa alheri sannan ya fita waje jiranta. Ni kuma na yi mata bankwana Baba ya rakata har waje suna tafe suna hira har suka fice daga gidan.
Hana na shigowa na labarta mata cewar Baba ya daga min kafa a yanzu, yace