Taki Zaman Aure Sirrin Zuciyar Mace by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Author :  𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category :  Romance

Chapter   56 / 72

165K to 168K   out of 215.5K words

na yi saving sannan na buga mata warning.

“Ko dai ki fadawa Baba karya kike ki karyata kanki, ko kuma na tura audio nan a gurin surukarki da mahaifin mijinki da kanensa kuma da gaske nake na baki daga yau zuwa gobe”

Ina fitowa na cire airplane mode din na kunna data da domin sakon ya samu isa, sannan na tari Napep na shiga, gidan Mama na nufa domin labarta mata halin da ake ciki na tabbatar bata san wainar da ake soyawa ba, idan har ta sani zata kira ta fada min ko ta tambayi wani abu, wata kila ita ma idan ta saka baki Baba zai aminta ya sauko. Sai dai na yi rashin sa'a ban same ta a gidan ba, sai mai aikinta na samu tana kallo a falo.

Ruwa kawai na sha na kira wayar Mama, ta amsa ni ta fada min bata gidan tana gurin gaisuwa wata kanwar mijinta mahaifin Abdull ce ta rasu.

“Mama idan kin dawo ki kira ni akwai maganar da zamu”

“Ki jira na dawo, lafiya na ji yanayinki haka?”

“Mama bari sai kin dawo”

Kiran Mama na yankewa, sai ga kiran Baba ya shigo wayata ina dauka ya fara zagina yana tambayar ina na tafi.

“Ina gidan Mama”

“Maza maza ki dawo gida yanzu nan”

Na mike tsaye babu shiri na yi ma mai aikin sallama na fice. Tare muka fito gidan da Abdull yana cikin motarsa ni kuma ina tafiya a kafa, ban yi mamakin ganinsa ba domin gidan ubansa ne, kuma Safeena ta fada cewar yana gari. Sai dai abun da ya ba ni mamaki kuma ya tsorata ni a lokaci daya tsayar da ni da yayi yana son magana da ni, ashe karfin halin maza har ya kai haka.

“Magana ce kawai zamu yi Noor dan Allah ki shigo”

Na yi kamar ban san da wanzuwarsa a duniya ba domin babu wanda na tsana irinsa kallonsa ma idan na yi bakinciki nake ji.

“Zamu yi magana ne akan karar da mahaifinki ya shigar, ina nan ya kawo sammaci, magana ce da zata sama mana masalaha gaba dayanmu”

Na tsaya wata idea na zo min, sai na saka wayata a recording kamar yadda na yi dazun idan na samu yadda nake so, zan iya mixing abubuwa su tafi yadda nake so. A gurin da na tsaya ya faka motar ya bude min front seat.

“I know you hate me but please ki shigo mu yi magana magana ce ta sirri”

Na kalli gurin sannan na shiga na zauna.

“Na ga shigowarki, na so na miki magana amman na san ba zaki saurare ni a lokacin ba, shiyasa na jira har kika fito”

“Ka ce zamu yi magana akan abun da ya shafi Shari'a ne ba wani abu ba, idan baka ka abun fada zan fita”

Na fada a tsawace jikina har bari yake ji nake kamar ace akwai wuka kusa da ni na caka masa.

“Akan shari'ar da mahaifin ya shigar ne, baki tunanin hakan zai iya shafar ki ya shafi kanwarki? Ni fa ban aikata komai ba? Wane tabbaci kike da shi cewar ni na yi mata fyade?”

Na dube shi.

“Baka aikata ba karya ake maka?”

Sai yayi saurin dauke idonsa.

“Na ji na aikata, amman ai kaddara ce da bata wuce kowa ba, kuma ke kin san ba zan amsa wannan a kotu ba, kuma baku da wata shaida, na san ubanki ya shirya haka ne saboda kwadayi irin nasa, zan bashi kudi enough, ya janye karar nan karya bata min suna ni da mahaifina, abun da zai biyo baya ba zai muku dadi ba”

Kalaman da suke fitowa bakinsa sun karfafa min guiwar aje wayata a cinyata fa yadda sautin zai samu daukuwa da kyau.

“Sannu namiji wato har kana da baki da karfin halin da zaka min bazarana kuma ka cilasta ni ko mahaifina, bayan duk abun da ka yi? Ka keta haddin kanwata har ka yi mata ciki sannan ka kalli kwayar idona ka yi min barazana Abdull...!”

“Baku da wata hujja akan hakan, kuma fitar wannan zancen zai zubar mata da mutunci ne kawai, dan haka ki natsu ki tattauna da mahaifinki mu taru mu rufawa juna asiri, idan wani abu yake so zan ba shi”

Kiran mahaifina da kwadayayyen da suke ya fi komai kona min rai sai dai babu yadda zan yi domin Baba ne ya budewa kowa kofa. Sam na manta da ban saka wayata a airplane mode ba, sai da kira ya shigo wayar. Wayar ta kawo haske kiran yayi appearing saman screen recording din kuma daga tsayaki daman wayar ba a key take ba, tun da Kareem ya ba ni ita ban saka mata password ba. Na yi hanzarin daukar wayar amman hakan be hana shi gani ba, daga Safeena da take kira har zuwa Recording din da nake.

“Recording kike? Ina kika dosa Noor”

Na bude motar na fita da sauri sai ya bude ya zagayo kamin na yi wani yunkuri ya kamani da kokawa ya murde min hannu ya karbe wayar.

“Ka ba ni wayata Abdull”

Be kula ni ya rufe gefen da nake tsaye ya zagaya zai shiga motarsa na bishi ina fadin ya ba ni wayar.

“Ka goge recording din ka ba ni wayata”

Be kula ni ba ya rufe motar yayi mata key ya bar ni a gurin tsaye cikin bakinciki da nadama. Why I'm such a fool and idiot me yasa ma na yarda na yi magana da shi, no wait me yasa ban saka wayar a airplane mode ba kamar yadda na yi dazun.
Da kafa na taka na isa Family house din su Mama, a gidan na kwana gaba daya na rasa ya zan yi kuma na san idan na koma gida Baba zai rufe ni da fada ne wata kila har da duka. Abun da ban sani ba, ashe bachin da na yi a gidansu Mama na tsira ne, bachin na chanji ne daga wata kaddarar zuwa wata, ashe na bude wani sabon babin ne na kaddara, domin na wayi gari da mummunan labari...
“Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un...”

Haka kowa ke fada sai kallona suke na rasa wanda zai amsa min tambayar da nake, sai rufe rufe suke min.

“Hana ce ta rasu na san jiya na barta bata da lafiya”

“Ke Noor shiga daki ki zauna”

“Ba zan iya ba Kawu, gida ya rikice haka kowa yana uhu amman na kasa fada min komai, ni dai ina son na tafi gidan na ji”

Na mike tsaye na fara takawa domin a bakin gaskiyata gidan zan tafi na ga abun da yake faruwa. Sai wata matar Yayan Mama ta rikoni.

“Dawo Noor zuwanki ba shi da amfani”

“Ku fada mata gaskiya mana dole ai zata ji ba a boye mutuwa”

Na juyo na kalli kanwar mahaifiyata wato Mama Aisha dake maganar.

“Wa na rasa? Mama ko Baba ko Hana ko duka?”

Wani irin numfashi ya fara zuwa min da karfi yana shiga haka ma idan zai fita sai ya fisga da karfi.

“Gobara ta tashi jiya, gidan ya kone gaba daya babu abun da ya fita”

Na rufe ido da sauri ina jin kamar mafarki nake.

“Sai hakuri Noor sai hakuri”

Haka na ji kowa na fada, sai kuma na jini a jikin mutane ashe faduwa na yi ban sani ba.

“Ki yi hakuri Noor haka Allah ya so”

Bana gana mai magana sai kallon gurin da sautin yake fitowa nake amman bana iya ganin komai sai duhu.

“Baba ya rasu kenan? Hana ma? Biyu na rasa ko daya?”

“Biyu kika rasa Noor kin rasa uba kin rasa yar'uwa, sai hakuri”

“Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, Allah ka wakwantar min da hankalina Allah ka ba ni natsuwa Allah ka kara min karfin imani, ka ba ni ikon jure wannan jarabarwar”

Shi ne abun da nake ta fada ina dafe da zuciyata, hawaye kam daman ai ranar yau ta su ce, idanuwan ma sun rufe ruf bana ganin komai sai duhu hayaniyar mutane kawai nake iya ji hankalin ma yana kokarin gushewa.

“Noor noor noor”

Ta rumgume ni, wannan muryar da sanyin da na ji a yayinda ta rumgume ni na ji shi a dabam, dumin jikin na uwa ne data kawo wa yarta dauki a lokacin da ta fi bukatarta. Kuka take ni kuma hawaye nake gidan kuma ihu ake, mutuwa kadai ta kai haka, ba mai iya rarrashin wani. Wasu ruwa mai sanyi na ji an zuba min daga saman kai har jikina aka wanke min fuska da ruwan kankarar sannan aka cire min hijab dina Mama kankam tana kuka.

“Karki tafi bar ni ke kuma dan Allah”

Na daga ido na kalli saitin da kanta yake a yanzu duhun ya yaye amman hawaye sun hana ni ganin fuskarta.

“Da gaske... Da gaske... Baba ya rasu Mama da gaske Hana ta rasu?”

Rufe baki ta yi yana danne kukanta, a lokacin ne na kwala wani uban ihu na fashe da kuka na fara shurin kafafuwana ina buri kamar wata mai aljannuna.

“Ki yi hakuri Noor ki yi hakuri, kowa aka cewa yayi hakuri ya rasa ki yi hakuri Noor Allah yana son bayinsa masu hakuri”

Babu irin kalmar da ba a fada min ba, babu irin rarrashin da ba ayi min ba, amman na kasa rike kaina har ji na yi ina ma ace da ni a cikin gobarar na mutu na huta. Babu irin bala'in da ban kira ba, babu kalar kukan da ban yi ba, da zuciya ta ayyana min sun tafi kenan sai na ji ba zan iya jurewa ba, musamman yar'uwata da take da kurciya da burika masu yawa a gabanta, wayar da muka yi ta karshe da Baba har yayi min fada ta fi tsaya min a rai, sai kuma Hana da na bari a gida cikin rashin na fito.

Ni sha kuka ni da Mama tun ina yi ina jin muryata na fita har ta daina fita. Hankalina be kara tashi ba sai na muka isa family house din su Baba muka tarar da gawar mutum uku ana yi mata sallah, Babana, kanwata da kuma matar ubana...
Mutuwa bata da kyau mutuwa bata da tausayi, bata da sabo, bata da dadi, na fara dandanarta ne tun a mutuwar mijina na farko. Amman bata min ďaci kamar yau ba.

Na yi kamar zan yi hauka, na ji kamar na bisu na ji kamar ace min komai ba gaske ba ne. Daga wajen da aka yi musu sallah aka wuce da su gidansu na gaskiya, ashe tun a jiya na yi bankwana da kanwata ban sani ba, na yi bankwana da ubana ban roki gafara ba, na san ya tafi da bakincikina da fushina a zuciyarsa. Gaisuwar ma idan aka yi min ciwo take min, Allah ya baki hakuri Allah ya jikansu da Rahama ki yi ta musu addu'a haka kowa yake fada, wasu na fadar na gode Allah bana cikin gidan ni ma da yanzu gawace, sai dai Allah yayi ba zan mutu a gobarar ba, babu rabon shan wahala shiyasa ban kwana a gidan ba.

Alhamdullahi nake ta maimaitawa a zuciyata, ba dan ina jindadi ni na rayu su sun mutu ba, sai dan ya wajaba na godewa Allah kuma na bukaci daukinsa a cikin tsanani da walwala a cikin kunci da bakinciki, a cikin farinciki ko kishiyarsa. Bana iya cin komai bana iya amsa gaisuwar kowa idan aka yi min, sai dai na bi kowa da ido. Masu fadar kyawawan hallayar Baba suna ta fada, masu fadar ta Hana ma suna ta fada. Babu zancen da ya dauki hankali kamar wanda Anty Larai take fadar Baba Kabiru yace a daki daya aka same su, kuma hannayensu a daure dukansu.

“Wannan abu yana da daure kai, Allah kadai ya san yadda wannan abun yake”

“Ni ma abun ya ba ni mamaki matuka kam, wata kila gorar ce ta saka suka boya a daki daya, to amman kuma waya daure musu hannayen?”

“Shi ne fa abun mamaki, Allah kadai ya san yadda wannan abun yake”

Haka suke ta juya zancen, Wallahi ban san lokacin da na kwarara ihu ba na fashe da kuka mai karfi, domin na san ni na janyo komai, wata kila sai da aka kashe su sannan aka saka wutar saboda a batar da sawun, wata kila kuma dauresu aka yi aka bar su a gurin har wutar da cinye da su. Ga dukan alamu saka wuyar aka yi ba tashi tayi ba da kanta ba, domin na ji sun fada ko da aka yi abun babu wutar nepa a unguwar balle ace ita ce sanadi.

Na san iya juyawar da za'ayi a juyo ba zai wuce Abdull ba, shi ya aika a yi komai saboda asirin abun da ya aikata ya rufe, wata kila recording din da na yi ne ya daga masa hankali yana gudun tonuwar asirinsa. Daman Baba yana fadar cewar ni ba alheri ba ce a gareshi ashe ma ni zan zama sanadin mutuwarsa da ta kanwata, bayan na zama sanadin lalacewar rayuwarta. Baba yayi gaskiya babu alheri a tare da ni, wannan ya fi komai saka ni a kunci da damuwa.

A lokacin da Safeena ta zo mana gaisuwa tare da yan'uwan mijinta wadanda suka kasance step daughters ga Mama da Hajiyarsu wato abokiyar zaman Mama sai na ji kiyayyar mijinta ya kara fadada a kirjina, gashi na rasa wayar balle na kwatarwa kanwata yancinta ko da kuwa bata numfashi. Duk wani motsi da zan yi yana idon Safeena a yadda take kallona sai na lura kamar akwai magana a bakinta, daman ai ba zata rasa abun fada ba, domin tana cikin tashin hankalin barazanar da na yi mata.

“Sannu Noor Allah ya musu rahama, ya kyautata na mu zuwan”

Ban amsa mata ba sai kanen mama ne suka amsa mata saboda bata da kunya har tambayar take wai ance ba a fita da komai ba

“Komai fa ba a fita da shi ba, ita dai Noor Allah be yi kwananta zai kare ba, shiyasa ta kwana gidanmu, ita bata kwana a can ba”

“Allah sarki Allah ya bada hakuri”

Daga haka bata sake cewa komai ba kuma bata fasa kallona har suka tafi. Da dare yayi Mama na shirin tafiya ta shiga daki sai na bi bayanta na fara fada mata abun da ke raina.

“Mama ganin nake kamar Abdull ne ya saka aka kashe su Baba kuma aka saka wutar saboda ace gobara ce”

Mama ta yi shiru na dakiku kamin ta ce.

“Ni ma jikina ya ba ni haka, ashe mahaifinku ya ji zancen fyaden nan? Har ya saka maganar a kotun”

“Shi na je na fada miki ban same ki ba, kuma Baba ya kira yayi min fada yace na dawo gida”

“Na samu labarin bayan kin tafi, kuma na kira wayarki baki daga ba, daga baya kuma sai na ji wayar a kashe, ashe gida kika tafi”

“Eh, saboda na ji raina ya bace ne sakamakin karbe wayar da Abdull yayi, na ji tsoron fadan da Baba zai yi min shiyasa ban koma gidan ba”

Mama ta zauna gefen gadon dake dakin.

“Ta ya Abdull ya karbe wayar? Ina kika ganshi?”

Ni ma na zauna sannan na labarta mata abun da ya faru tare da kudirina. Dauke ni ta yi da mari ta rufe ni da duka.

“Sakaryar yarinya shashasha, mahaukaciya, dabam da bata san ta tsaya ta yi tunani ba kamin ta aikata abu, ta ina zaki je ki yi recording din matarsa saboda kina mahaukaciya kuma ki yi nasa? Ke lauya ce da zaki yi amfani da wannan a matsayin shaida ko kuma yar daba ce ke da zaki riki hakan a matsayin garkuwa? Me yasa baki tunani kamin ki aikata abu? Mutumen da ya ci zarafin yar'uwarki ya keta haddinta shi zaki shiga motarsa har ki saurare shi? Har abada ba zaki gyaru ba Noor ke dai kam har abada ba zaki taba hankali ba, mahaukaciya sha sha sha...”

Ta karasa fadan da kuka Mama Aisha na rike da hannayenta tana tare dukan da take min, a lokacin da na yi zurfi a cikin nawa kukan, na zube kasa na rarrafa na boya a bayan kofar dakin na takure guri daya, ina jin kaina cikin kuncin marar misaltuwa.
Mama ta yi gaskiya ni shashasha ce, kuma bana da tunani wannan ma gaskiya ne domin gashi na janyo mutuwar mahaifina da kanwata da Umma da bata ji ba ba ta gani ba.

Duk yadda aka so na fito daga bayan kofar sai na ji, domin na fi jin sanyi a gurin, a bayan kofar na kwana har safe kamar wata marar gata, hakan ya ba ni damar tausayawa kaina. Washe gari Sallah asuba ce kadai ta fitar da ni daga gurin, shi ma ina gamawa na dawo na zauna a gurin na takure ina jin tsanar kaina, meyasa na aikata haka? Me yasa ban yi tunani ba? Me yasa ma na roko Hana ta zo gurina from first plate? Wata kila da yanzu tana raye bata mutu ba. Ranar wuni na uku na zama kamar mahaukaciya ina ta tsoron mutane, gashi sai dorawa kaina laifi nake.

Bayan an yi musu addu'a ne mijin Mama ya saka aka kira ni, domin yace ni ce kadai be gani ba gurin gaisuwar, na fito ina rike da hannun Mama Aisha sai kallon mutane nake ina jin tsoro, gani nake kamar wani zai ce saboda ni Baba da Hana suka rasu. A wajen motarsa muka same shi yana zaune daga baya ya bude kofar motar yana jiran fitowata. Na risina a gurin jikina na bari gaba daya a tsorace nake.

“Noor”

Na kalleshi da sauri ba tare da na amsa ba, daman kuma ba zan iya amsawar ba.

“Ya hakuri...”

Na daga mishi kai hawaye shar kamar saukar ruwan sama.

“Ki yi hakuri kin ji, duk mai rai mamaci ne, kuma kowa baya wuce lokacinsa”

Nan ma dai kai kawai na iya daga masa.

“Kuma na ji abun da ya faru, ma samu labarin a daren da Allah ya karbi rayuwar mahaifinki, domin na dawo gida sai na tararda sammaci daga gareshi, wai yana karata saboda ďana ya keta haddin yarsa, ba zan boye miki ba na ji haushi sosai na yi mamaki kuma na yi bakinciki, ashe Allah yayi ba za a tsaya shari'ar ba, ba ni da tabbacin abun da yake zargin Abdullahi da shi...”

Yayi shiru na dan dakiku sannan ya cigaba.

“Zan cika zan iya iya kokarina

56 / 72