Taki Zaman Aure Sirrin Zuciyar Mace by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Author :  𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category :  Romance

Chapter   6 / 72

15K to 18K   out of 215.5K words

matsala, amman masu cikin shige ni bana zubarwa”

“Duk yadda zaka yi ba zaka gujewa mutane ba, wata ma cikin banza zata dauko ta zo tace maka mai matsala ne ka burke mata ta zubar”

“Aa sai na yi bincike nake yi ai, ni ba shashasha ba ne irin Noor”

Hafiz da sai a lokacin ya rufe motarsa ya kalli Kareem.

“Muje ka bani labarin yarinyar nan there is something special about her...”

Kareem ya jera da abokinsa suna tafiya ya zuba hannayensa duka biyu aljihu. Har suka isa office labarin abun da Noor ta yi masa yake ma Hafiz, and Hafiz was so excited domin ya dade yana jiran irin wannan labarin daga gurin abokinsa.

“Amman be dace mahaifi ya furtawa yarsa haka ba, ko da daga ita sai shi ne balle kuma har a gaban wani”

Hafiz ya fada bayan ya zauna. Kareem ya daga kafadunsa.

“Ni ma shi na gani, irin haka ke sa yaro ya lalace, ni ma ban jidadi ba balle kuma ita, amman tace min ita ai ta saba, duk sai ta ba ni tausayi Wallahi, gata karamar yarinya she's just 14 no 15 this month”

“Kasan fa wasu iyayen idan talauci ya halbo su ido rufewa yake”

“Baka da kirki Barrister amman fa akwai alamar haka, domin daga ganin gidan nan da unguwar ma ka san suna fama da talauci ko'ina kwata”

Ya fada yana ciro wayarsa dake ringing ya duba, ganin sunan Safeena ya saka shi dan shakkun dagawa a gaban Hafiz domin ya san ba karamin abu ba ne su yi fada saboda kiran, but babu yadda zai yi dole ya daga domin ba zai tana iya rejecting kiran Safeena ba kuma ba zai ga kiranta ya kasa dagawa ba.

“Hello...”

“Kareem guess what?”

Safeena ta fada daga dayan bangaren.

“Ina guest's House dinka”

“Safeena i thought mun yi magana idan mijinki yana nan ba zamu ga juna ba? Dazun nan ma ba mun yi maganar nan ba?”

“Na kasa rike kaina ne, kuma i have surprised for you shiyasa na zo, kawai magana za mu yi”

“Shi ke nan gani nan zuwa”

Ya amsa da kamar yanayin damuwa, sannan ya sauke wayar.

“Yanzu baka ko jin kunya barina zaka yi a nan ka tafi ka gurinta”

Cewar Hafiz cike da takaici. Kareem yayi murmushi.

“Kamar baka san tsakanina da Safeena ba? Tana son ganina and i can't say No”

“Ka ji tsoron Allah Kareem, kana mu'alama da matar aure macen har da yayanta hakkin ai sai ya maka yawa”

“Shiyasa na ce idan mijinta yana gari ba zamu rika ganin juna ba”

“Yanzu idan wani ya kwanta da matarka ya zaka ji? Amman kai kana yi ma matar wani?”

“If wani ya aikata matata haka, kashe shi zan yi, ba zan iya jurar komai ba, ko da kuwa Yusura ce da bana so balle ace wadda nake so”

“Amman kake aikatawa matar wani? Idan kuka mutum a wannan halin kace me? Waya sani ma ko ita ma tana tare da Ex dinta”

“Ex dinta yana can kasar waje, ba dan an cilasta mata aurena ba, da yanzu tana can tare da shi suna rayuwa ni ma da yanzu da Safeena nake rayuwa, amman ya zamu yi kaddarar mu ta zo a haka”

“Ka yi sabon Allah kace kaddararka ce a haka? Kareem ka raina wayon mutane Wallahi”

Kareem ya busar da iskar bakinsa.

“Wai da duk wannan abun why not ta kashe auren ka aureta?”

Kareem ya girgiza kai da sauri saying no to Hafiz question.

“Har abada, ba zan iya aurenta ba, idan ta fito gidan mijinta wa zai rike mata yayanta? Ni dai yadda nake da kishin nan kasan ba zan iya rike yayan wani ba, kuma...”

Yayi shiru.

“Kuma me? Ba zaka aureta ba saboda kana jin ba da kai kadai take tare ba?”

“Da ni kadai take tare a yanzu na sani, amman daga lokacin da zan aureta ba ni da wannan tabbacin, what after na aureta ta koma tana mu'amala da tsohon mijinta kuma? Ko wani? Daga lokacin da na fara kaiwa jikin Safeena sai aka tsinke igiyar aminci a tsakanina da ita, for now na san ni kadai ne, amman idan na aureta ba zan samu aminci ba”

“Kenan haka zamu yi ta zama har bada?”

“Not har a bada, ina fatar canjin”

“A hakan?”

Hafiz ya tambaya yana masa wani kallo. Kareem yayi dariya grabbing his phone ya mike tsaye ya fice daga office din.

“Allah ka tsare mana imaninmu ka tsare mu da auren mata irin Safeena”

Ya fada yana juyawa ya bi kofar office din da kallo. Kareem na shiga motarsa ya dauki hanyar gidansa da ya gina da kansa saboda Safeena da kuma irin tsarin da take so, sai dai kaddarar rayuwa bata ba su damar zama ma'aurata ba, sai suka zama ma'aikatan aikata zunubi. Yana yin horn mai gadi ya bude masa gate sai ya shiga ya faka motarsa, yana ganin motarta ya tabbatar tana gidan kamar yadda ta fada masa. Ya bude motar ya fito ya nufi kofar falon ya saka key ya murda ta bude ya shiga. Yanayin arba da ita sai murmushi ya baibaiye fuskarsa ta taso da sauri tana kamshi turare mai karfi ta rumgume shi.

“I miss you so much”

Ta fada tana shafa fuskarsa, bakinta ya sumbanta ya rike bayanta.

“I miss you too, kwana biyun nan da baki kusa kamar na yi hauka”

Ta yi dariyar jindadi.

“Ba ga matarka ba?”

“Matata ai kin san once in a month ne, amman ke kullum ne, kin san yadda nake sonki ai”

Ta sake yin murmushi ya kai bakinsa cikin nata, sun dauki lokaci a haka kamin ya cire bakinsa.

“Yau kam ba zamu wuce nan ba, Safeena ina son ki rika jin maganata, na fada miki idan mijinki yana nan ba zamu rika haduwa ba”

“Na sani, yanzu kawai na zo maka da abun mamaki ne kuma abun Farinciki”

“Surprised din me ne?”

Ya tambaya yana kokarin raba jikinsa da nata, sai ta yi baya ta nufi jakarta ta bude ta dauko abu sannan ta boye a bayanta.

“Rufe idonka”

Ya rufe idon yana murmushi har sai da ya ji matsowarta kusa da shi ta ce ya bude sannan ya bude. Yana yin arba da surprised din sai murmushin dake fuskarsa ya gushe, mamaki ya koma masa tashin hankali.

“Innalilillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Ya furta har sau biyu sannan ya karbi PT scrip din yana dubawa.

“Me hakan yake nufi?”

“Ciki mana Kareem, kai fa likita ne”

Ta fada cikin tsananin farinciki, da tsammanin shi ma farincikin zai yi. A take ya ji gaba daya tsigar jikinsa tana tashi.

“Cikin waye Safeena?”

“Cikin Kareem, mijina shekaranjiya ya dawo ai ba za ace na yi cikin tsakanin jiya zuwa yau ba, kuma tun da liyin ya nuna sosai that's mean cikin ya dade, kasan for the whole 3 months muna tare, I'm happy Kareem zan haifi ďanka...”

Ta kai hannunsa ta taba fuskarsa tana murmushin jindadi sai ya buge mata hannaye ya fadi zaune ya shafa kansa ya mike tsaye ya sake komawa ya zauna.

“Me ya faru? Wannan abun Farinciki ne a tsakaninmu Kareem”

Ta nufeshi ta rika shi sai ya kauce daga rikon.

“Baki da hankali Safeena baki da hankali, miye abun farinciki a nan? Kina da aure ki yi ciki da wani a waje kuma ki ce abun farinciki?”

“Saboda naka ne Kareem, duka yara uku da na haifa na Abdull be, ina son na haihu da kai, ka san yadda nake sonka...”

Ya aje PT din trying to calm himself down.

“Na sani, amman ban da ciki, wannan kuma mun wuce gona da iri ba zamu iya rumgumar abun da ya biyo baya ba”

Ta kalli cikin idonsa hawaye na cika idonta.

“Me kake nufi?”

“Zamu zubar Safeena ba zamu taba haihuwa a tsakaninmu ba har abada, babu wannan”

Ya matsa zai taba ta sai ta matsa baya tana kallonsa.

“Me kake nufi kenan?”

“Zubar zamu yi, ba zam iya wannan ba Safeena ba mu wuce gona da iri ba”

“Na yi mamakin jin wannan kalamar daga bakinka, ban yi zaton haka ba, ni ina son cikin idan kai baka so ni ban daina kaunarka”

“Ni ma ban daina kaunarki ba, amman ba zamu yi cikin banza ba, kuma da igiyar aure akanki”

“Ba zan iya zubarwa ba Kareem, ba zan iya ba”

“Safeena na san muna son juna amman...”

“Ba zan zubar ba Kareem ka daina magiya...”

Ya tsaya yana kallonta da mamaki.

“Shi ke nan ki aje cikin, ni kuma zan tsinke duk wata alaka tsakanina da ke”

Yana furta haka ya nufi kofar fita falon ransa a bace.

“Kana wasa da mace Kareem”

Ta fada masa cikin fushi sai ya juyo ya kalleta.

“Ke kuma kina wasa da rayuwarki...”

Ya juya Fuuu ya fice daga falon ya barta tsaye cike da mamaki.




NOOR POV.

Sai da Yaya ya fara aje ledodi sannan ya ciro dubu goma cif ya mikawa Baba.

“Gashi yace a siya mata magana”

Baba ya karbi kudin da sauri ya kirga sannan ya saka aljihu ya mike tsaye be kula abun da ke cikin ledodin ba yayi ficewarsa ba tare da ya ba ni ko sisi ba, balle kuma Mama. Da kadan yake jira tace yayi rufeta da masifa, ni kam ban yi hanzarin tana komai ba har sai da na dan jira na ji ko Yaya zai yi fada amman ga dukan alamu damuwa ta hana shi cewa komai. Hana ta janyo ledodin da fara budewa daman tuni kamshi ya kara cika mana hanci.

“Nidai bari na bude idan ba za ku bude ba”

Na kai hannu na taba leda daya sai Mama ta buge min hannu, ina kokarin juyowa na kalleta ta dauke ni da mari har sai da yatsanta ya fada min ido, zan yi ihu ta rufe ni da duka iyakar karfinta.

“Shiyasa ubanki kullum yake kuka dake, halinki ya fara isata, na gaji da ke Noor na gaji da halinki sakaryar yarinya dakikiya marar hankali da bata san ciwon kanta ba, yar iska gantalalliya, kullum haka kike ke babu ranar da za ki gayu”

Daker Yaya ya kawace a hannun Mama ina kuka sosai. Ba zan iya fadar dalilinta na duka ba, iyakar abun da zan iya shaida shi ne ranta a bace yake tun shigowata har zamana, wata kila Baba ne yayi mata ba daidai ba, dalilina ko kuma wani abun ne ya faru kamin dawowata.

“Babu abun da zaki ci a cikin nan, wannan Mugun kwadayin da rawar kai sai ya zama ajalinki matukar baki daina ba, yar iskar yarinya da bata gudun abun magana”

Na mike tsaye ina kuka har bada iya gani saboda hawayen da suka min zuba. Ji nayi an kwashe min kafafuwa na fadi kasa ribbbb gurin da na ji rauni a dazun ya sake buguwa har na yanzu ya fi na dazun radadi da zurfi.

“Mama dan Allah ki yi hakuri, ki yi hakuri Mama dan Allah ki yafe mata”

Shi ne abun da na ji Hana na fada Yaya kuma yana rikon Mama.


Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧


𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆


𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫 -6


Duka sosai Mama tayi min tun tana dukana tana zagina har ta kai tana dukana tana kuka kamar yadda nake kuka. Hana ma kuka take saboda ta ga ina kuka daman haka take duk fitinarmu da ita idan wani abu ya bata min rai ko ya saka ni kuka ita tana shiga damuwa sosai, wani lokacin har ta kan fi ni ma saboda Mama tana cewa ni ban san ciwon kaina ba, sai dai wani ya sanin min. Na rarrafa na tashi zaune ina jin tsiyayar ruwan da na tabbatar na jini ne a kaina.

“Mama yanzu me ye amfanin haka? Gashi yanzu kin ji mata rauni a raunin da ta ji, yanzu kuma a koma jinya ana neman na magani Baba kuma ba badawa zai yi ba kin san tun da kudin nan suka kai hannunsa ba zai bada su ba, kuma halin nan ba dainawa zata yi miye amfanin dukan?”

Bana ganin fuskar kowa saboda kuka, sai dai zan iya shaidar muryar Yaya Nabil ne mai maganar cikin yanayin damuwa.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”

Shi ne abun da nake ta jin Mama na maimaita cikin kuka, na dai na samu na isa bakin kofar dakinmu da rarrafe, na shige ciki na kwanta. Daga lokacin da na kwanta sai kukan ya tsaya min daman can Allah be yi da son kuka ba, ba komai ke saka ni kuka na dade ba, sai dai na bar abu a cikin zuciyata idan na tuna ya kuna min rai, shi ma kuma da zarar na samu wani abu da zai dauke min hankali a take zan manta sai idan an bude sabon shafi kuma.

“Jinin ya tsaya?”

Na ji muryar Yaya Nabil sai na tashi zaune na kai hannu na taba gurin har lokacin zafi yake min sosai, kuma jinin yana zuba sai dai ba kamar dazun ba.

“Rashin jin magana ke ja miki shiga matsala Noor, ke babu ranar da zaki yi hankali? Kuma kin san idan kika aikata wani abu laifin a gurin Mama yake komawa, fitar nan da kika yi babu kalar fadan da Baba be yi ma Mama ba saboda ta barki kin fita, na dawo gida na tarar baki gidan sai wani sabon fada ya tashi”

“Ka ce Mama ta yi hakuri ba zan sake ba”

Shi ne akwai abun da na ji zan iya fada, domin ni na janyowa kaina matsala da kaina, kuma Mama ta yi gaskiya kwadayina ne sila. Yaya Nabil ya fita daga dakin be jimawa ya dawo rike da maganin ciwon kai ya mika min.

“Ki Sha biyu idan jinin be tsaya ba anjima sai mu tafi gurin Saminu ya sake gyara miki gurin, ni ma gashi kina son ki zama silar korata daga aiki, Allah kadai ya san me kika masa da yace na zauna gida na kwana biyu”

Na san fadar gaskiyar zai sake jefani a matsala ne, dan haka na zabi shiru daman hausawa sun ce shiru ya fi yawan magana alheri. Ina cikin dakin ban fito ba sai da aka yi sallah magariba, a lokacin jinin ya daina min zuba, dan haka na nemi tsumma na gyara gaban kaina na goge jinin na saka wani kyalle na daure gurin sannan na fito na nufi gurin da buta take na dauka na zuba ruwa na yi alwala. Ina ganin ledodin Kareem Restaurant a tsakar gidan na san Mama sun cinye komai, hakan kuma ba karamin koma min rai yayi ba, ashe wahalar banza na sha ba zan ci komai a ciki ba. Da hawaye na gama alwala na mike tsaye kenan Hana ta fito daga bandaki rike da buta, Mama kuma tana dakinta tana sallah.

“Mama ta rantse ba zaki ci ba, shiyasa ban shiga da shi dakinmu na ci a dakin Mama”

Na kalleta cikin yanayi na rashin jindadi dake bayyana har a muryata na ce.

“Kun cinye duka kuma?”

Ta daga min kai.

“Mama ta miki haka ne saboda karki sake aikatawa gobe, dan Allah ki daina abun da kike Noor, dan Allah ki daina”

“Ba roka na yi ba, shi ya ba ni ku tambayi Yaya idan ba ku yarda ba, Hana har da yar tsutsar kun cinye?”

“Aa zubarwa aka yi, waye zai ci tsutsa idan ba ke da abinki ba Noor, abun kyama”

Ban sake ce mata komai ba na nufi dakinmu na shimfida dankwalina na saka hijab na fara sallah idan na yi sujuda sai na kai gefen goshina a kasa saboda rabin ciwon yake min. Ina gama sallah yaro ya shigo yana sallama, ina jin Mama ta amsa masa.

“Wai Zafeer yana sallama da Noor”

“Ka ce gata nan zuwa”

Yaron ya juya ya fita, shiru ban ji Mama tace na tashi na tafi ba, na san kuma Zafeer ba tafiya zai yi ba sai ya gan ni, ko kuma idan an fada masa ba zan samu fitowa ba. Dan haka na mike tsaye na fice daga dakin na isa bakin kofar dakin Mama na tsaya daga bakin kofa na fara da bata hakuri.

“Mama ki yi hakuri, ba zan sake ba”

Ta yi kamar bata ji ba.

“Na tafi gurin kiran da Zafeer yake min?”

Na tambaya a kokarin na zama yarinyar kirki.

“Idan kika tashin fitsararki umarnina kike nema? Yar iskar yarinya marar mutunci”

Daga jin wannan kalama na san Mama bata gama sauka daga fushin nan ba. Sululu na fice daga gidan kamar macijiya, ina fita waje na samu Zafeer tsaye yana danna wayarsa, kamin na karasa gurin da yake tsaye na fashe masa da kuka a take ya dago kai da sauri ya kalleni hankalinsa a tashe.

“Me ya faru Baby Noor waya taba ki?”

Ya kunna fitilar wayarsa ya haska fuskata.

“Subhanallahi me ya same ki waya fasa miki kai? Me kika yi Noor who did this to you? Who touch my Babeee”

Tambayata yake hankalinsa a tashe zuciyarsa na cika, ban yi mamaki ba domin ya saba fusata a duk lokacin da aka taba ni.

“Waya miki wannan duka Noor fada min mana...”

Cikin kuka na fada masa abun da ya faru tun daga irin karyar da Kareem yayi ma su Mama cewar mota ce ta buge ni, har zuwa dukan da Mama ta yi min.

“Kuma sun cinye duka naman ba su ba ni komai ba, ko yar tsutsar nan da na so na ci ba su ba ni sun zubar”

Juya baya yayi yanayin fuskarsa ya sauya kamar zai fashe da kuka, ya jingina da ginin gidanmu ya kife kansa. Kamin ya dago ya kalleni.

“Iyeyenki kadai suka kai su yi miki haka Noor, su kadai ne suka da ikon dukanki su fitar miki da jini haka kuma na kyale su, Allah ya daran talauci Noor, ba dan shi ba da yanzu na aureki da yanzu karkashina kike rayuwa, wani abu duk ba zai faru ba”

“Sun cinye komai har tsutsar nan irin wadda masu kudi suke ci, na so na ci na ji me ake ji”

“Ana zancen rauninki kina zancen tsutsa, idan kin ci me zaki ji?”

“Na ji abun da suke ci mana, har kai na dauko maka naka fa, ai kasan komai na samu sai na kawo maka”

Na fada cikin kuka.

“Ni dai dan Allah ki daina daukar komai kike gani

6 / 72