Taki Zaman Aure Sirrin Zuciyar Mace by ๐Š๐ก๐š๐๐ž๐ž๐ฃ๐š ๐‚๐š๐ง๐๐ฒ

Author :  ๐Š๐ก๐š๐๐ž๐ž๐ฃ๐š ๐‚๐š๐ง๐๐ฒ Category :  Romance

Chapter   17 / 72

48K to 51K   out of 215.5K words

an ga Zafeer ko da na iya yau ne kawai. A cikin duka shawarwarin ban dauki ko daya ba, A kowane sakon da minti idan na tuna Zafeer yana can yana jirana sai na ji hankalina ya tashi, a haka na wuni a dakin ina kuka har na ji kiran sallah Azahar.
Shinkafa da miya na daga cikin favorite food dina amman ranar sai na kasa cin wadda Mama ta girka. Da dare ina jin lokacin da take labartawa Mama cewar tun ranar ban sake cin komai ba har yanzu, a madadin Baba ya ji tausayina sai ya rufe ta fada wai ita take goya min baya nake wannan iskanci. Tashi na yi zan fita sai Hana ta fara kokarin hana ni.

โ€œNoor karki fitaโ€

โ€œMagana kawai zan yi da Babaโ€

Na amsa ta sannan na fita na isa har gurin da Baba yake na risina kasa ina kuka.

โ€œBaba dan Allah dan Allah Baba ka yi hakuri karka aura min wani idan ba Zafeer ba, Wallahi Zafeer nake so Baba shi kadai nake so, idan na auri wani ba shi ba mutuwa zan yi Wallahiโ€

Ya haska ni da fitilarsa mai haske...

โ€œEyyyyyyeeee lallai duniya ta miki dadi, tabbas kin samu yadda kike so Noor, yanzu har abun ya kai ki dubi idona ki fada min ga wadda kike so ki aura? Duka nawa kike? Ke har wata soyayya kika sani ma? Dan uwarki can da da ake aure wata soyayya aka sani amman yanzu saboda zamani ya lalace duniya ta bude muku ido kuma uwarki ta saka kin raina ni shiyasa kika zo kika zame ni kina fadar zaki mutu idan ba Zafeer ba?โ€

Ya juya gurin Mama ya rufe da fada tana amsa masa sai ya rufe ta da duka ni kuma na yi hanzari tashi cikin karfi hali da rashin karfin jiki na tare Mama sai ya hada ni da ita yayi mana duka kamar be san inda muka fito ba. Dukan Mama a gaban idonmu wani abu ne da yake saka mana tsanar mahaifinmu kullum kuma wani abu ne da Baba yake jin dadi aikatashi, wata kila yana tunanin hakan zai saka mu kara tsoronsa ne abun da be sani ba hakan yana saka sanar kiyayyarsa a zuciyarmu ne kawai kuma ya kan saka mu yi masa kallon wani azzalumin mutun tsabanin Uba da kowa wane yaya suke yi ma iyayensu.

โ€œDacan ina cewa Haihuwar Noor ce ta kawo min kariyar arziki, ashe ke ma baki so na da arziki duba abun da yaron nan yayi mana daga zuwansa, kuma inda zata huta ne ba gidan wahala ba amman kin bi rana da safiya idan na fita kina hore mata kunne kar ta saurare shi idan ya zo ko? To ni zan kira shi zan bashi ita sadaka na ga uban da zai hana auren idan akwai wadda ya haifa min Noor din, gaba daya baki iya ba su tarbiya ta kwarai saboda baki san zafin haihuwa baโ€

Haka Mama ta mike tsaye tana kuka tana fadin.

โ€œMalam idan har ka aikata hakan ni kuwa zamana a gidanka ya kare, ba ta yadda zan zauna ka wulakanta ni kuma ka aurar da yata a inda za a wulakanta, babu yadda za'ayi wadda ka aura mata ya ga dararja ko taka, babu ta inda zata yi kima a gurinsa, mutumen da be bude baki yace yana sonta ba saboda ya siya maka gida zaka ce ka dauki Noor ka bashi sadaka bayan kuma yarinyar nan ba shi take so? Wannan abun kunyar har ina?โ€

Baba ya dan matsa baya ya ce.

โ€œNi kike fadawa Haka Hajara?โ€

โ€œNa fada maka Malam Naziru, ka yanka ni yau ka ci, na gaji da kai na gaji da halinka...โ€

Baba ya nufi i da fitilarsa take ya duka ya dauka ya haska fuskar Mama da kyau.

โ€œHajara yau ni kike fadawa haka? Idan kika sake fadar wata kalamar a gareni marar dadi to a bakin aurenki...โ€

Wani irin karfi da kuzari da ban san Mama da shi ba, ta yi sufa ta isa gurin da Baba yake tsaye ta saka hannayenta biyu ta tureshi da karfi sai da ya fadi kasa.

โ€œNa aikata wanda ya fi wannan ka kashe ni yau karka bar ni na kwana da rai... Tun da na aureka ban huta, yara har sun girma su ba su huta ba ni ban huta ba, cin mutunci babu kalar wadda baka min ba, to na gaji aure kuma na hakura da shi na fi sha'awar na mutu a hakaโ€

Ni da Hana muka nufi Mama muka rike ta da karfi muka kuka domin ba halinta ba ne, macen dake tsoron daga kai ma ta kalli Baba yau ita ce ta saka hannu ta ture shi a kasa.

โ€œKalu Innalillahi.... Wa'Inna..... Ilaihirraji'un.... Hajara... Ba ke bace, Wallahi ba ke bace..โ€

Yana fada yana girgiza kai, sai kuma aka yi sa'a nepa ta dawo a lokacin, daga ni har Hana muna kallon yadda yake yunkurin tashi ya kasa domin ba karamar faduwa yayi ba. Na saki Mama na nufi inda Baba yake na rika shi ya mike tsaye sai dai be tsaya daidai ba hannunsa daya yana rike da kunkurunsa, na nufi inda fitilarsa take na dauko na kawo masa sai ya karba ya nufi kofar gidan ya fIce ba tare da ya sake cewa komai ba. Ni kuma na gurin ina jin kamar an dora wano nauyi a kai saboda na zama silar fadan iyayena a yau ma, gashi an doki Mama kuma Baba yayi rauni. Na dade a haka ina hawaye sannan na nufi kofar dakin Mama na zauna na fara rusa kuka kamar ba ni ba, Mama da kanwata Hana kuma suna cikin daki suna na su. Shigowar Baba ne ya saka na tashi tsaye da sauri kuma na yi hanzarin yanke kukan da nake ina kallonsa tare da wasu abokansa biyu.

โ€œIna take?โ€

Suka tambaya bayan sun yi sallamar da ban samu amsa musu ba saboda kuka da nake ta kokarin ganin na ci karfinsa.

โ€œTana can ciki ko ta fita Noor?โ€

Baba ya fada yana tsaya daga can baya su kuma suka shigo cikin gidan suka isa gurin kofar Musamman ma Malam Isuhu da ya kasance Malamin Addini.

โ€œTo wai magana suka yi ne ko me? Ke Noor Mamanku tana ina ne?โ€

Na nuna masa kofar daki. Baba kuma ya ce.

โ€œAi na san ba ita bace yadda ta tureni din nan ba karfinta ba ne, kuma duk zamana da ita bata taba nuna min yatsa ba, amman yau tureni ta yi a gaban yara, yanzu haka bana iya tsayawa daidai, ai ba ita ba ce shiyasa ban sake ce mata komai ba, na fita na kira ku ayi abun da ya dace idan karatu za a mata ko addu'a sai ayiโ€

Baba na rufe baki Mama ta taso ta fito daga dakin a fusace.

โ€œBabu wasu aljannu Malam Isuhu kar ya wahalar da ku, azaba ce da zaman auren na ukuba na ganshi a gidan har na gaji, yace idan na sake yi masa masifa a bakin aurena to na yi aure ya kare, ka aurawa Noor wadda duk ranka yake so amma zamana a gidanka ya kare, yara ba kanana ba ne da wayonsu ranar da duk suka so ganina sai su tararda ni inda nakeโ€

Malam Umar da Malam Isuhu suka juya suna kallon Baba cike da takaici da mamaki.

โ€œTo wai miye silar wannan abun ne?โ€

Baba ya nuno ni da fitila ya karaso cikin gidan yana kashe min ido.

โ€œKa ga yar iskar yarinyar da ta assasa komai nan, ita ce silar komai ita ta lalata lamarin nanโ€

Mama ta shiga tsakani ta tare ni.

โ€œBabu ruwan Noor a ciki, ni ka saba yi da ni ka yi da ni, yarinyar da abinci ma ya gagareta ci saboda mugun bakin halinka ita kake dorawa laifi, daman kullum cewa kake saboda na haifo maka ita rayuwarka take cikin matsala, saboda baka yarda da kaddara baโ€

A take masifar ta koma gurin Mama ya koma yana haskata da fitila yana tafiya a karkace ka ganinsa ka san kunkurunsa ya bugu.

โ€œToh... Wai da kike wannan hakilon kina hauka kin isa ki hana ni aikata abun da na yi niya ne? Ai daman na fada miki idan kika sake magana a bakin aurenki to ki je na sake ki saki uku Hajara na gaji da ke na gaji da halinki, kije kya gani Noor kuma sai na aura mata yaron nan mai mutunci mai karamci sai dai ki hadi zuciya ki mutu, ita kuma idan ta haihu ta bijire min na gani...โ€

Ban san lokacin da na dora hannu a kai na kwala ihu ba, domin na san miye saki na kuma san abun da saki uku yake nufi babu sauran zama a tsakanin iyayena kenan. Kuma duk ni ce sila. Malam isuhu ya rufe Baba da fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Malam Umar ma fadan yake yana Allah wadai da abun da Baba ya aikata a gabansu. Hana kuma ta shiga zubewa kasa tana tashi tana ihu.

โ€œMun shiga uku mun lalace, Mama idan kika tafi mun shiga uku Innalillahi...โ€

Na yi zaton Mama zata tausaya mana ko ta tausaya ma kanta amman ban ga alamar hakan a tare da ita ba, domin babu hawaye ko daya a idonta. Sai ma juyawa da ta yi ta shiga dakin ta fara hada kayanta. Malam Umar yana bata hakuri sai abokinsa da suka zo tare wato Malam Isuhu ya ce.

โ€œHakuri me zata yi lamari ya lalace ya sake ta har saki uku? ABu dai kamar wadda aka jefa, baka dubi yaranka ba baka kalli kai kanka ba ka saki mace da girma ya fara kama ku a tare, har ina aka taba haka?โ€

Baba ya fara kokarin kare kansa.

โ€œBaka san halin matar nan ba, Wallahi hakuri kawai nake da ita, yanzu ai sai ta koma can ta zauna cikin dangi ta ji idan akwai mai iya daukar abun da nake dauka, wulakanci take min kala kala duk ita ce silar lalacewar yarinyar nan Noor, ga bakinciki kamar ba mijinta ba, bata kaunar wani abun farinciki ya same ni, na gaji....โ€

Takaici ya saka Malam Isuhu ficewa daga gidan, Mal Umar ne kadai ya tsaya ya fitar da Baba yana masa fada abun da yake be kamata ba. Na taka na isa cikin dakin na tsaya ina kallonta.

โ€œMama tafiya zaki yi?โ€

โ€œTo zama zan yi? Auren ubanku har aure ne? Ku dai da yake ubanku dole ku yi hakuri ku zauna a haka amman ni yanzu kam Allah ya sama min yanci, kuma kin fi kowa zama sakarya wawuya a gidan nan, idan zaki canja hali ki canja idan kuma ba zaki canja ba, to zaki sha wahala rayuwa ba yanzu ba har nan gabaโ€

Na matsa baya na jingina jikin kofa ina kallon Mama har ta gama hada kayanta.

โ€œKar wadda ya bini yana min ihu kuma kar wadda ya sake min kuka, kukan be hana ni tafiya, kuma ni da mahaifinku zama ya kare har a bada....!โ€

Haka ta saka kai ta fice a fusace ko kadan kuka be ziyarci idon Mama ba, ni yau sai ta canja min ma kamar ba ita ba. A dakin muka zauna na tsawon lokaci muna kuka ni da Hana dake ta dora min laifi.

โ€œSai da na ce kar ki fita amman baki ji ba, gashi nan kin yi sanadin da Mama ta tafi, jindadi da sanyi da muke ji ta bangarenta kin yi sanadin da muka rasa shi, kuma duk saboda Zafeer din nan ne, kamar kanki farau soyayya, yanzu kuma sauran ki yi sanadin da Baba zai tsine miki sai kiji sanyi, kullum ke kike janyo mana matsala a gidan nan kullum da ke ake kuka...โ€

โ€œBabu wadda zai sake kuka da ni Hana ba zan sake aikata abun da wani zai yi kuka da ni baโ€

Na tashi ina jin jikin babu karfi, gurin da Yaya yayi min wacan dukan yana taso min da ciwo. Na koma dakinmu na kwanta hankali be kara tashi ba sai da na ji shigowar Yaya Nabil domin na san ba zai min da sauki ba, a take na tashi zaune na zubawa kofar dakin ido ina jiran shigowarsa. Shiru shiru ban ji ya shigo ba, hakan ya saka na tashi tsaye na isa gurin kofar sai na hango shi zaune bakin kofar Mama rike da yar leda ya kifa kai da guiwa a kasa...




*** **** ***

GAM..... ya rufe motar ya saka key din a aljihunsa sannan ya fara waigewaige inda zai samu yaron da zai aika. Daga karshe sai ya nufi kofar gidan ya kwankwasa yaja baya ya tsaya yana kallon agogon hannunsa da ya nuna karfe goma sha daya da rabi. Nabil ya fito yana murza ido da alama a lokacin ne ya farka daga bachi.

โ€œNabil kana ciki...โ€

Sanin cewar abokin ogansa ya saka Nabil ya mika masa hannu da sauri suka gaisa.

โ€œIna Baba fa yana ciki?โ€

โ€œAa magana zaka yi da shi? Allah yasa ba wata matsalar bace?โ€

โ€œAa babu wata matsala na zo ne kawai na yi magana da mahaifinka?โ€

โ€œA game da ni ne? Ko oga ya kore ni ne? Saboda Noor ta ari wayata ta yi masa maganganu marasa dadiโ€

Hafiz ya girgiza kai.

โ€œAa ba haka ba ne, wannan abun ai be kai a koreka ba, ni kaina na san halin Noor a yanzu balle kuma shi Kareem da ya fi kowa fahimtar ta, ba mamaki ace baka sani ba ta ari wayarka ta kira ko?โ€

Ya daga kansa da sauri.

โ€œEh ba da sanina ba neโ€

โ€œBa matsalar ce ta kawo ni ba, wata maganar ce dai mai muhimmanci, kuma bana tunanin Kareem zai koreka gaskiya saboda ya san hanyar cin abinci ka a nan take, Kareem yana da kirki sosai fiye da yadda kake tunani, kuma yana da saukin kai amman be san ma na zo nan ba โ€

Nabil ya ji hankalinsa ya dan kwanta kadan, sai dai tashin hankali rashin mahaifiyarsu yana nan a cikin ransa. Ya juya zai koma cikin gidan.

โ€œBari na sallamo maka shiโ€

Hafiz yaja ya matsa baya ya jingina da motarsa yana kallon yanayin unguwar, ta dayan bangaren kuma yana jin bakinciki yadda Kareem ya watsa masa kasa a ido. Babu bata lokaci Baba ya fito yana gyara hula, ganin Hafiz ya saka shi murmushi ya karasa da kansa ya mikawa Hafiz hannu suka gaisa cikin girmamawa.

โ€œYanzu ake tafe?โ€

โ€œEh Wallahi wani abun ne ya kawo ni, na yi tunanin za a fi samunka da safe ne shiyasa na zo kamar yanzu...โ€

โ€œMaa Shaa Allah aiko na jidadin zuwanka, daman ina nemamka har ina shirin fadawa Nabil ya kira min kaiโ€

Hafiz yayi fuskar mamaki tare da murmushi a fuskarsa.

โ€œIkon Allah toh Allah yasa lafiya dai?โ€

Baba yayi dariya.

โ€œLafiya kalau, sai alheri a game da Noor ne amman dai bari na fara jin abun da ke tafe da kai tukunaโ€

โ€œAa Baba a sawun giwa ya take na rakumi, fada min na ji dalilin neman tukunaโ€

Baba ya gyara tsayuwarsa ya jingina da motar Hafiz tare da sauke ajiyar zuciya.

โ€œWatooo ka san lamarin mace, ko da babba ce balle karama kamar Nooriyya, ni abun ma sai yayi min wani iri Wallahi, ina ce yaron nan yaje yayi muku tashin hankali jiya?โ€

Hafiz ya daga kai sama.

โ€œEh haka ne, shi ne ma dalilin zuwa na bada hakuri kuma na bada shawara....โ€

โ€œToh ai saboda kai ne yaje yayi wannan tashin hankalinโ€

โ€œSaboda ni kuma Baba?โ€

โ€œKwarai kuwa, ai yarinya buga kafa ta yi a kasa tace kai take so, saboda na yi masa maganar idan be shirya ba to fa ya kauce saboda ina son na aurar da ita, shi ne ya zo yana rokonta yana rokona sai na sake zaunar da su na fada musu dalilina na son aurar da ita, sai ya tashi yana zage zage kasan abun ka da marar tarbiya, ita kuma ta fusata tace ba zata ma sake kula shi ba, to in takaice maka da magana uwar ta saka ta a gaba da masifa tace to idan ta juya masa baya sai ta fitar da wadda take so, ita kuma tace kai take so...!โ€

Da mugun mamaki Hafiz ya nuna kansa.

โ€œNi kuma Baba? Ni ko dai abokina Kareem?โ€

Baba yayi dariya kamar gaske.

โ€œKai din dai, sanadin haka uwarta ta yi fushi yanzu haka bata cikin gidan ma, amman waka a bakin mai ita tafi dadi bari na kira maka ita Nooriya sai ka yi magana da ita ka jiโ€

Kamin Hafiz yayi wani yunkuri Baba ya nufi cikin gidan ya shiga. Hafiz ya nuna kansa har lokacin mamaki yake.

โ€œNi...? Baba dai ba fahimta da kyau baโ€

Ya furta yana kallon kofar gidan zuciyarsa na bugawa da karfi...





____________

Toh fa ana zaton wuta a makera....

Anya ana samun uba irin Baba Naziru kuwa?

Auren Mama dai ya kare amman an bar baya da kura.

Nikam na tambaye ku mana, Zafeer be baku tausayi ba?

Hafiz na kokarin kulla alheri reshe na shirin juyewa da mujiya yaya kenan?


Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


โœงโœฆ ๐—ง๐—” ฦ˜๐—œ ๐—ญ๐—”๐— ๐—”๐—ก ๐—”๐—จ๐—ฅ๐—˜ โœฆโœง


๐—•๐˜† ๐—ž๐—ต๐—ฎ๐—ฑ๐—ฒ๐—ฒ๐—ท๐—ฎ ๐—–๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐˜†


TALLA ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡


https://chat.whatsapp.com/DUwtFhhxfsS4zLHhxb28Wo

About us
*Legit contacts
*Verified address including shop address and social media handles
*Wholesale price
*Group support
*Group buying if you can't afford moq
*Connect with supplies from Yaba, trade fair, Lagos island, balugon, e t c just for 2k๐Ÿ‘Œ


*Chapter 15*


Ni da Hana kuka muka sha har muka gode Allah, ni dai sai tunanin ya zame min biyu tafiyar Mama da kuma Zafeer, tsammanin da nake Yaya Nabil yayi min fada ko duka ko ya min wata maganar babu ko daya, haka muka kwana cikin bakinciki da kuka. Baba be shigo ba sai da safe, a lokacin ragowar karfin jikin ma ya tafi ya bar ni, zazzabi kuma ya rufe ni har bana iya daga ido da kyau, ina jin lokacin da Baba ya shigo ya bawa Hana kudi wai ta siyo kunu, ta tashi ya fita bata jima ba ta dawo da kofin kokon ta aje a nan dakin ta nemi guri

17 / 72