Taki Zaman Aure Sirrin Zuciyar Mace by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Author :  𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category :  Romance

Chapter   33 / 72

96K to 99K   out of 215.5K words

me yasa Hafiz zai aureni alhalin ya san yana son matarsa kuma ya san ba zai iya adalci a tsakanina da shi ba, ba zai iya tausaya min ba. Misalin karfe daya ina zaune a dakin shiru Gwaggo Saude tare da kanwarta suna shigowa bata duba halin da nake ciki ba ta rufe ni da fada kamar wadda bata da gata, sai kanwarta ce take dan tare min tana cewa ba a bincika ba wata kila ni ce mai gaskiya. Ban san waya fada musu ba ban san ta ina suka ji ba maganar sakin ba domin ban yi maganar da kowa ba bayan Kareem. Haka na yi kwana biyu a asibitin a duk tsawon zaman da na yi Hafiz be leko ba, daman me zai saka ya leko ni bayan ya datse igiyar data hada, mahaifiyata kam ina jin bata da labarin komai sai dai abun da ya daure min kai shi ne rashin zuwa Ya Nabil da Hana duba ni, haka ma Baba be zo ba, Kareem din ma da matarsa ta yi min illa be leko ba ko sau daya be taba shigowa ya duba ni ba. A zaton su raunin da na samu Hafiz ne yayi min duka ni kuma ban damu na fada ba domin ni na kai kaina fadar zai kara janyo min karin wani tsanar ne ko fadan. Idan suka tambaye me ya faru tsakaninmu sai na ce babu komai ban masa komai ba, na samu kaina da nauyin fadar dalilin asalin fada na samun robar c**mdom da maganin planning a jakata, a lura da na yi ne da hakan babban abu ne da zai iya sakawa wasu ma su zarge ni kamar yadda Hafiz ma ya kasa yarda da ni shi da yake mijina. Ranar da aka sallamoni daga asibitin tare da Gwaggo na dawo gida, gaba daya tsoron irin tarbon da Baba zai yi min ya gama firgita ni ya saka na fita hayyacina a take, tsoronsa da nake ji a yanzu ya ninka wanda nake ji a lokacin da ban yi aurenba.

Ban gane dawowa gidan na zauna kuskure ba ne har sai da gari ya waye, na leka daki na gaishe da Baba ya ki ya amsa min, daman tun da muka shigo be sake min fuska ba. Haka Ya Nabil ma be ce min komai ba, hana ma ta kasa sake min kamar ba ita ba. Within a week na lalace kamar ba ni ba, labarin sakin da aka yi ma ya cika unguwa wasu na tambayar yaushe ma aka yi auren har na dawo gidan, daman sun san ba zan yi zaman aure ba, haka Zainab take fada min yadda ake yawo da ni a unguwa. Ga shi cikin zaman babu dadi domin sun hade min kai, Yaya baya min magana, Hana bata hira da ni iyakacinta idan ta girka abinci ta zuba min ta koma gefe ta zauna, Baba kuma idan ya shigo ba yi masa sannu baya amsa min, idan zai fita ko da safe idan na gaishe shi baya amsa kuma be taba tambayata me ya faru ba!! Haka Mama bata kira ta tambaye ni me ya faru ba, na san kuma ba zata rasa sani ba, domin Ya Nabil yana yawan waya da ita, Hana kuma ta tafi gurinta sau biyu a zuwan da ta yi na karshe take fadawa Yaya jumma'ar ne aka daura mata aure.
A tunanina suna min horo ne da wannan saboda a gaba idan na koma kar na sake marmarin dawowa gidan, Sai dai abun da suka kasa fahimta shi ne mace bata sakin kanta, ni kaina na zan iya cewa ga abun da na yi masa ba da har ya saka ya sake ni, saboda suna ganin bana jin magana tun asali ne shiyasa babu wanda zai yarda da ni. Hakan kuma ya saka na ji kamar a gidan yari nake rayuwa saboda kunci da takura, a kowace Sallah sai na roki Allah ya daidaita ni da mijina, sannan na daukarwa kaina alkawari ko da Hafiz sai yanka ni ya ci ko kuma yayi min horo da wuta ba zan taba daga ido na kalleshi ba balle har na yi wani kuskuren da sai saka ya sake sakina. Tsegumin mutane kadai ya ashe ni, wasu har fadar suke wai amanar Zafeer, ba mamaki kuma ta kan iya zaman amanarsa ce ta hana ni zama cikin amincin a gidan Hafiz, domin na cutar da Zafeer na raba kaina da shi da na yi, sanadin Baba wata ila da gaske amanarsa ce Allah kadai ya san halin da ya shiga a sanadin haka.










#KhadeejaCandy

PAID PAGE 1️⃣2️⃣


©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______•••_______


Ina ta tsammanin zuwan Hafiz ko Kareem da sunan gyara amman ban ga ko dayansu, hakan kuma ba karamin Mamaki ya ba ni ba, sai na ke ganin kamar daman can Hafiz ba sona yake ba, ya aure ni ne kawai saboda yana son raba ni da wanda ke tsananin kaunata. Sai dai Kareem ya fi ba ni mamaki domin sanadinsa na san Hafiz ko kuma nace Hafiz ya san ni, kuma na kai masa kukana ba sau daya ba amman har yanzu be yi komai ba.

Idan na zauna ina tunani sai na ji zuciyata kamar zata fashe, gaba daya na rasa tudun dafawa na rasa ina zan saka kaina na ji sanyi, Mijin da ya dauke ni ya saki ni be waiwayo ba, abokinsa da shi ne sanadin auren be yi wani yunkuri ba, a gidanmu kuma Baba baya min magana saboda yana ganin laifina, Kanwata bata hira da ni, yayana baya kulani na rasa, hakan ya saka na dauki laifin na dorawa kaina. Kullum burina taya zan bullowa lamarin na samu komawa dakin mijina. Da yammancin wata labara na saka hijabina na saka talkamina na fito tsakar gidan. A lokacin Hana ce kadai zaune tana karatun biology, sau daya ta kalleni ta maida kanta bata ce min uffan ba duk kuwa da ta san fita nake da niyar ni.

“Hana”

Ta juyo ta kalleni ba tare da ta amsa ba.

“Abun da kuke min ya dace kenan? Kun maida ni bare a gidan nan?”

“Toh ya kike son ayi miki Noor, idan fa ba ki canja hali ba, zaman rayuwar duniya zai miki wuya”

“Amman babu wanda ya tambaye waye mai gaskiya me ya faru?”

“Baba be son jin uzurinki, saboda ya ci buri a aurenki, na san Baba be kyauta miki ba aura miki wanda baki so, amman be kamata ki ce ba zaki zauna ba, da zarra an daura aure kin tashi daga budurwa Noor, Mama farko bata farinciki da auren amman bayan aurenki nan tana ta jindadin yadda mutane suke yaba gidanki, kuma idan ta duba yadda zaman gidan yake babu dadi sai ta ce kara ma da aka miki auren yanzu ta huta sauran ni, to miye kuma na zuwa ki fito Noor auren da ba a dade da yi ba?”

Na share hawayen da suka zubo min.

“Ganin kike laifina ne?”

“Tohm laifin waye? Mutumen dai yana sonki, ke ce baki son shi, kuma Noor kowa ya san halinki na rashin jin magana sanadin haka kika je kika hadu da wannan mutumen sai kuma yanzu ki dawo kina kame kamen ba zaki zauna ba”

“Hannatu ke ma fa mace ce, baki san ya rayuwa zata kasance miki ba, na tabbatar da kin san yadda zafi da bakincikin auren wanda baka so yake da baki fadi haka ba”

“Na sani ni mace ce, amman tun yanzu ai ba irin rayuwarki nake ba, kuma bana fatan na yi kalar rayuwarki Noor, ke ce kin son makaranta ke ce jawo ki ce rashin jin magana ke ce saka Mama kuka bakinciki komai dai ke yanzu kuma ana murna an miki aure sai kuma ki kashe auren ki dawo? Yanzu ai sai ki ji idan zaman gidan dadi ne da shi”

Bana jin akwai sauran abun da zan fada da zai gamsar da yar'uwata a yanzu, ko kuma ya wanke ni daga mummunan kallon da suke min, gaskiya ta fada da ace ni din kamar ita nake mai jin magana wata kila da yanzu ban samu matsala kamar haka ba. Fita na yi daga gidan ina tafiya jikin ba dadi as well as zuciyata bana iya daga kai na kalli ko'ina har na isa titi, Napep din da ta faka kusa da ni na nufa. Ban tana sanin ina tsananin kaunar Zafeer sai a yau da na yi arba da shi ya fito daga Napep din da nufa zan shiga, ya rame kamar dai he is the only person da na kalla daga fitowa ta gida zuwa nan, shi ma kallona yake kamin ya dauke idonsa ya saka hannunsa aljihu ya dubu daya ya mikawa mai napep din.

“Canjin ka kai wannan inda zata je”

Wannan karon muna hada ido hawaye suka zubo min. Ya dauke kai ya matsa baya ni kuma na shiga na zauna ina kallonsa har mai napep din ya fara tafiya...

“Ina zamu je Hajiya?”

A take hankalina ya dawo jikina, kunya da damuwa da bakinciki nadama da kuma dana sani suka rufe ni. Yaushe Zafeer ya dawo garin? Ko dai be tafi ba? Har yanzu yana so na? Ko ya daina? Ya yake kallona? Wata kila ya ji labarin mutuwar aurena amanarshi ta kamani. Ina Son ka Zafeer ina sonka sosai ina son Zafeer Allah ka sani, shi ne abun da nake ta fada a zuciyata, ban hakaro da inda nake ba har sai da Mai napep din ya sake tambayar ina zai kaini. Toh ina zan je kuwa bayan restaurant din Kareem by this time na san Hafiz yana gurinsa, zan fi jindadin tunkararsa a can na bashi hakuri kuma na fada masa ba zan sake aikata kuskure ba, duk kuwa da na san ni din ba ma'asumiya ba ce. Rokonsa a can zai fi min rufin asiri fiye da rokonsa a gidansa kuma a gaban muguwar matarsa wadda ita ce silar faruwar komai.

A gaban restaurant din ya sauke ni, ina jin zuciyata kamar ba tawa ba tsananin kunnar da take min, na fito na doshi gate din sai masu gadin suka tare ni. Suna tambayar ina zan tafi, ban yi mamakin jin sabuwar dokarsu ba ta sanin wanda zai fita ko ya shiga, domin aikinsu ne bada tsaro a matsayinsu na masu kula da gate din. Sai dai abun da ya ba ni mamaki shi ne fadar sunana da suka yi, sannan suka tabbatar min da Kareem baya gurin.

“Ba gurin Kareem na zo ba, gurin Hafiz na zo”

“Shi ma Hafiz din baya nan”

“Zan iya shiga na jira?”

“Aa gaskiya Oga yace kar abarki ki shiga”

Na yi murmushi na juya na kama hanya, yanzu kuma ban san ina zan je ba, ashe abun har ya kai haka? Na zo ace is kar na shiga ciki. Dama na kama na fara tafiya a kafa domin ba ni da kudin abun hawa, idan ma na hau yanzu ban san inda zan je ba. Motar da ke fuskanto ni har ta wuce ni Sai kuma ta dawo ta faka gabana, ban san hawaye nake ba har sai da Kareem ya fito motar ya kalleni ya ce.

“Dole ne sai kin fadawa kowa kina cikin damuwa?”

Na kai hannu na share hawaye ina kallonsa.

“Na zo sun ce kace kar a bar ni na shiga ciki”

Ya dan dauke kansa.

“Wannan zuwan ba saboda kai ba ne, na zo gurin Hafiz ne, saboda bana son na tafi gurin matarsa kai tsaye, na san a irin wannan lokacin yana gurinka ne, na san na takura maka da yawa Kareem, ba zan sake ba na sani ai na ishe kuwa a yanzu”

Ajiyar zuciya na ji ya sauke.

“Me Hafiz zai miki?”

“Hakuri zan ba shi, zan roki ya maida ni gidansa...”

Gambun motar da yake rike da shi ya sake yana kallona kamar mai mamaki.

“Noor ba ayi ma namiji haka, shi ya sake ki ai let him come to his senses idan maida ke zai yi sai ya maida ke, amman be kamata ki roke shi ba”

“To ya kuke son na yi? Kun raba ni da wanda nake kauna yake so na tsakani da Allah, yanzu kuma abokinka ya sake ni na dawo gida, Baba baya min magana be amsa gaisuwa ta, Hana bata hira da ni, Yaya ko kallona baya yi, a unguwa ana ta yi da ni, Mama tana fushi da ni? So kuke na kashe kaina?”

Na karasa maganar ina fasa wani irin ihu kamar wadda ya fita daga hankalinta. Da sauri Kareem ya matso kamar zai rika ni.

“Noor... Lafiya”

“I'm alright...”

Na amsa ina kaucewa daga gabansa na cigaba da tafiya.

“Zuwan da kike gurina yana daga cikin abun da yake haddasa fitina tsakaninki da Hafiz, shiyasa na ce kar abarki ki shigo, domin na san zaki sake zuwa ne, a yadda na lura Hafiz yana kishi da hakan, saboda akwai abun da baki sani ba a tsakanina da shi”

“Ba zan sake takura muku ba Kareem, ba zan sake zuwa ba”

Na fada ba tare da na juyo ba. Sai ya kira ni

“Noor...”

Na juyo ina wani irin kuka har naman fuskata na rawa.

“Hafiz baya garin nan, ya tafi Kaduna gurin wani case tun jiya, amman yau zai dawo. Shim kina son komawa gidansa?”

Na daga mishi kai.

“Shi kenan, Hafiz zai maida ke na miki alkawari”

“Na gode”

Na furta daker sannan na juya na cigaba da tafiyar, daga restaurant din zuwa unguwarmu tafiya ce mai nisa amman haka na tako da kafa har gidanmu saboda ba ni da kudin abun hawa kuma na san babu mai ba ni a wannan karon, tufafi ma tun wanda na zo da su daga asibitin ban ni da na canjawa sai dai idan suka yi datti na wanke da ruwa na shaya idan suka bushe na saka, haka nake kamar wata matar gata...
Ina shiga gidan, Yaya Nabil ya rufe ni da kuka saboda Baba yayi masa izinin haka, wai na ki zaman aure ina son na fara yawa ina na fito? Gurin uban waye na tafi? Na kasa magana sai kuka nake, duka sosai Yaya yayi min har sai da ya sauya min kamanin fuskata. Baba kuma ya kara min da zagi yana fadin ai ya ji labarin Zafeer ya zo garin nan gurin iyayensa ba mamaki gurinsa na tafi mika hadu. Da rarrafe na shiga dakin na kwamta a kasa a lokacin da ake kiran sallah Magariba a kowane Masallaci, a gurin na kwanta ban iya tashi ba har safe...



KAREEM POV.

Tsaye yayi a gurin yana ta kallonta tsawon lokacin da ta dauka tana tafiya a kafa har ta karya kwana. Babu abun da yake bata masa rai a rayuwar Noor da Hafiz kamar kasancewa a tsakani, ya zama tsakanin ma'auratan guda biyu, duk ta inda zai motsa kura zai tayar, and the most sadness thing is sanadinsa ne auren ya kullu, ta wani bangaren yana ganin kamar har da rashin so ke wahalar da su, domin ya san yadda zafi da wahalar abun yake, da ace yana sonta da zai iya hakuri da ita a yadda ya same ta ko da kuwa na dan lokaci ne. Shiyasa Noor din ta fi ba shi tausayi domin abokinsa yana da future, yana da matar da yake so take sonsa ya aureta har suka yi zuri'a yanzu. Ita kuma ya rabata da wanda take so kuma yanzu yana wahalar da ita, at her early age lokacin da ya kamata ace tana jindadi.

Cikin motar ya koma ya dauki wayarsa sai ya tararda miss calls din Hafiz har biyu, ya dade yana kallon wayar kamar mai tunanin abin yi, har ga Allah be so ya sake yi masa magana akan aurensu ba, domin sakin da Hafiz yayi mata ya bata masa rai, saboda me zai saketa a lokacin da ya same shi ya ba shi shawarar yadda zai zauna da matarsa. Be gama yanke shawarar ba kiran abokinsa ya sake shigowa a karo na uku he pick the call ya kara a kunnensa yayi shiru har sai da Hafiz din ya fara magana cikin farinciki da murna kana jinsa zaka san yana cikin jindadi, daman kuma idan dayansu ya samu wani abun jindadi ko farinciki kamin kowa ya sani sai sun fara labartawa junansu.

“I win the case Doctor, we won it...”

Kareem yayi murmushi jindadi ya rufe even though dai baya cikin farinciki a yanzu.

“Congratulations to us, daman na san zaka yi winning ai, bana da shakkun akanka congrats”

“Thank you, ba karamin dadi na ji ba nasarar nan da na samu, domin babban case ne wannan zai kara min martaba sosai zai daga darajar aikina”

“Haka ne, ko da yaushe kana nasara Hafiz, kai mutumen mai tsananin jajirce da hikima da wayo tun muna yara, sai dai abun da yake ba ni mamaki shi ne yadda ka gagara fahimtar matanka ka gagara saita gidanka, kuma ka gagara fahimtar wacece ne? Wane irin zama ya dace ka yi da ita, kuma ya kamata ka tafiyar da rayuwarta”

“Na fahimci gidana Kareem, na san waye Noor, akwai abun da na fahimta a game ita da zai hanata kuma ni ma ya hana ni jindadin zaman aure da junanmu”

“Ka jefa yarinyar a cikin matsala Hafiz, ka rabata da masoyinta mutumen da she can dia for him, ka siye mahaifinta ka aureta yanzu kuma ka sake ta a wace hujja?”

Yayi shiru be ce komai ba sai tukin motar yake.

“Hafiz, zan roke wannan alfarmar a gareka, zan saka ka aikata saboda ina jin na isa da kai, bayan wannan ba zan sake rokon komai ba, ina son ka maida aurenka da Noor yau... Yarinyar tana wahala ka jefa rayuwarta a masifa, wani abun bakinciki kuma duk saboda ni ne, ka san baka sonta you don't have to married her What kind of wickedness is this? Na taina wayonka Hafiz”

“Wait... What....”

“Ka mai da

33 / 72