Taki Zaman Aure Sirrin Zuciyar Mace by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Author :  𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category :  Romance

Chapter   14 / 72

39K to 42K   out of 215.5K words

wani sai yayi shekaru yake hankali ya natsu wata macen ma zaka ga sai ta haihu, da zaka gwada mata soyayya tsab zaka siye zuciyarta balle ma har ta saki jiki da kai nan da nan ne zaka shawo kanta”

“No ni ba zan iya ruguza soyayyar wani ba, kuma ba zan so kowa ya samu kansa a yadda na samu kaina ba, ba zan so ta auri wadda bata so ba”

“Amman kai kana sonta ai”

“Wannan yar mitsitsiyar yarinyar? Ni fa ba sonta nake yi ba, kawai dai tana burge ni ne”

“Rainonta zaka yi irinsu sun fi dadin aure, yadda duk ka bi da ita haka zata tafi, ni dai burina ka rabo da Safeena kuma ka samu farinciki ne ne manufata”

Hausawa suka ce dan halak kaki ambato, wai da an ambace shi sai ya bayyana haka kuwa ne ya faruwa a daidai lokacin da Hafiz ya ambaci sunan Safeena sai ga kiranta ya shigo wayar Kareem. Abokinsa ba zai iya rejecting ba, ba kuma zai iya kin picking ba saboda Safeena ce, tsohuwar masoyiyarsa dan haka ya tashi a hikimance ya fice daga office din ya nufi wani bangare dabam ya hade rai sannan ya amsa wayar.






__________________


Hmmmmm yanzu ne zamu tsuduma a cikin labarin, ina fatan kun shirya. Kun ji dai Kareem yace shi ba sonta yake ba. To Team Kareem sai ku tattara kayanku a gurin Noor ku ware 😆

Team Zafeer kun ji na ku yana cikin damuwa, sai ku fara tara masa kudin aure ko kuma ku roki Baba ya daga masa 😁

Noor dai tace ta daina anya zata iya? Ga mu dai gani gurguwa da aure nesa 🤔
Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧


𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆


*Talla👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/GY1W0qJiFbJD5A5J6F0fqA
*INA MATAN DA SUKASAN DARAJAR GYARA❓DAKU NAKE MACE MAI GYARAN BATA ZAMA BORA❌*

*KUZO GA INGANTATTUN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI💪BA MUNA KAYABA❌ HAJIYA KIZO KISAI KAYAN MATA WURIN DA BAZAKIYI ASARAR KUDIN KI BA*

*INA MASU CEWA NI KO NASHA KAYAN MATA BASAMIN AIKI HMMM HAJIYA BAKIDAI SIYA KAYA MASU INGANCI BANE, KAYANMU SUNA KARA NI'IMA, TAYARDA SHA'AWA, DADI, TIGHTENING (MATSI), CIKO DA GABAN MACE (DUK BUDEWAR SA), DUMIN GABA GA, KAMSHIN GABA GA KUMA NA KARA DANDANO OVER 💃💃💃💃💃👉 GA KUMA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI DAGARGAZA SANYI KODA YA SHEKARA 10 A JIKINKI* 09038090328

*A DAYA BANGAREN KUMA MUNADA SABAYA MAI GYARAN NONO DUK LALACEWAR SA KO KIN HAIHU GOMA SABAYAR MU ZATA CIKO MAKI DA BREAST SUYI GIRMA SOSAI MADAME*

*GA KUMA TA HIPS (MAZAUNAI)SU CIKO SUYI BULBUL NONO YA CIKO SOSAI HJY KIYI KIBA YAR DAIDAI SKIN DINKI YAYI KYAU KI KOMA TAMKAR TARWADA*

AKWAI KUMA NA GYARAN NONO WANDA BAYA SAKA KIBA💃💃💃

GASKIYA NA YARDA DA INGANCIN KAYANTA👆👆👆




*Chapter - 12*


Kun ji ni shiru kwana biyu sakamakon rashin da muka yi. Amman Alhamdulillahi ala kulli halin.

______________________

Ta dade shiru bata ce komai ba kamar bata jikin wayar har sai da ya dauke wayar daga kunnesa ya duba ya sake mayarwa.

“Safaeena ina tunanin saboda kina da magana da ni ne kika kira ni”

Cikin muryar kuka ta soma magana.

“Ka canja min Kareem, daga lokacin da ka hadu da mahaukaciyar yarinyar nan gaba daya hankalinka ya tashi daga gareni ya koma gareta, yau har ta kai ta daga wayarka ka fada min magana son ranta, Wallahi da ban yi kokarin rike kaina ba da Allah kadao ya san abun da zan aikata a yau din nan kuma Allah ya san halin da zan shiga”

Ya sauko daga matakalal dake gurin yana rike da wayar a kunnensa.

“Ina kokarin shata liyi ne a tsakaninmu, akwai abubuwan da idan suka yi yawa, rashin tunani yana shiga ciki ya zauna, kamar yadda yake kike tunanin son haihuwa da ni yayinda kike da aure da wani, abun da kika yi niyar aikatawa ya tsorata ni, kuma ya bani mamaki, sannan ya farkar da ni daga dogon bachin da nake”

“Baka ji tsoro ba? Lokacin da na ce maka cikina ya zube saboda kishinka? Baka yi tunanin zan iya shiga damuwa idan ka guje min ba, Kareem a can baya ma da muka yi soyayya kawai da na rasa ka sai da na rasa mijin aure saboda na kusa haukacewa, aka rasa namijin da zai aureni sai Abdull, balle kuma yanzu da na riga na san ka farin sani ka tsara jikina ta yadda bana jindadin mu'alama da miji sai da kai, ka san duk yadda zaka yi ka kawar min da kishina ka faranta zuciyata, Kareem saboda ina sonka ne ya saka nake son na haihu da kai, saboda ina da mafarkin da nake son ya tabbata a nan gaba, Wallahi ina sonka Kareem na sabu da kai, idan ka sake guje min a karo na biyu ba zan hakura ba...”

Wani dogon numfashi ya sauke ya juya ya kalli kofar da ya fito sannan ya ce.

“Safeena na san kina so na, ni ma ina sonki amman Allah be kaddara mu zama ma'aurata ba, be kamata mu yi ma yaran mu haka ba, be kamata ke ma ci amanar mijinki ba, ya kamata mu karbi kaddarar mana ko dan karin imaninmu da yafiya daga zunubanmu”

Yana jin lokacin da taja majina tukuna ta amsa.

“Mun karba, shiyasa kake auren wata macen ni kuma nake auren wani namijin da ba kai ba Kareem”

“Idan har zamu cigaba da aikata abun da muke aikatawa kazantar ta yi yawa abun yayi muni, kuma hakan yana nufin ba mu karbi kaddarar ba Safeena”

Ta yi dariya da zai iya ji.

“Ba akan mu farau ba Kareem, kuma shi Allah mai yafiya ne a koda yaushe, ba haka za mu dauwama ba, wasu ma suna matsayin budurwa da saurayi suke yi balle mu da muke da aure, wannan abun duk kauna ce ta kawo, karka bari yarinyar nan ta canja min kai”

“Babu ruwan Noor a alakata da ke, ni ba soyayya nake da ita ba, kawai dai an yi sara ne akan gaba ne, amman ba aurenta zan yi ba”

Fashe masa ta yi da kuka.

“Kana cewa mu rabu kamar abu ne mai sauki Kareem, kana kokarin juya min baya bayan kuma na saba da komai na ka, taya kake son na jidadin rayuwa babu kai a kusa da ni? Wallahi saboda kai bana sha'awar Mijinta yayi sati daya a garin nan, saboda kai bana jindadin duk wata mu'alama da mijina, kullum mafarkina da burina akanka ne Kareem, ka juya min baya a lokacin da na fi bukatarka, yanzu kuma mun sabu da juna kake kokarin guje min a karo na biyu? Ko ka manta wacece Safeena a gurinka Kareem....?”

Tif... Ya kashe wayar ya sauke ajiyar zuciya, jin kamar kalamta na kokarin saukar masa da tausayinta kuma suna kokarin kusanto da rauninsa.

“Me na jefa kaina a ciki? Me yasa na bari zuciyata ta yi nesa? Ba zan sake aikatawa ba, ba zan sake ba, ba zan sake cutar da wani ba, ba zan sake bari zuciyata da yaudari da jindadin da ba zai tabbata ba a gareni”

Ya saka wayar aljihu sannan ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na Biyu ya juya ya koma ciki. A bude ya samu office din babu kowa a ciki ma'ana dai Hafiz ya fita daga office din. Wayarsa ya fara cirewa daga aljihu ya dora a saman teburinsa sannan ya zauna ya dafe kansa. Abu da yake a bayyane gurin kowa kuma sirri dake aje a zuciyarsa yana son Safeena irin son da yake jin ba sai taba samun mai maye masa gurbinta ba, irin son da ya tabbatar sai dai ya mutu da shi domin ba zai iya aurenta ba a yanzu kuma baya jin zai iya cigaba da mu'alama da ita ta kazamtacciyar hanyar da ya sabawar kansa.  Sai bayan sallah Isha'i Kareem ya koma gidansa, yana shiga falonsa ya samu Yusura zaune tana duba waya, laramin danta dake cinyarta ya zo da gudu ya tare shi.

“Daddy Oyoyo”

Kareem ya cillashi sama ya cafke sannan ya sauke shi ya shafa kansa yana murmushi.

“Areef ya kake?”

“Lafeeya lau, amman Momy bata da lafiya”

Kareem ya daga kai ya kalleta sai ya ga har lokacin idonta yana kan wayar dake hannunta kamar ma bata san da shigowarsa ba. Ya maida dubanshi gurin Areef

“Me ya same ta?”

“Jikinta da zafi ta yi amai kuma ta yi kuka...”

“To yayi kyau je dakinka ka kwanta gobe akwai makaranta, ina Tine”

“She's sleeping”

“Okay kai ma je ka kwanta”

Ya sumbance shi yaron ma ya mayar masa sannan ya sake shi ya nufi sama da gudu yana waigensa. Sai da ya haye sannan Kareem ya karasa gurin da Yusura take zaune yana daga tsaye zai yi magana ta riga shi ba tare da ta kalleshi ba.

“Ga abincinka a dinning room”

Ya kalli dinning area din sannan ya sake dubanta.

“Ai da baki girka ba, tun da baki da lafiya kuma abinci ba wani damuna yayi ba...”

Ta tsayar da taba wayar da take ta dago ta kalleshi.

“Idan har ban girka abinci a gidan nan ba, wata kila ina ciwo ne mai tsanani da ba zai bar ni na iya tsayuwa da kafafuwana ba, amman girka abinci, gyara gida, kula da yaranka da kuma tsare mutuncina, wani abu ne da addinin da al'ada suka taru suka samar mana, ina yi ne saboda sauki nauyi na matar aure a gidan Kareem, ba wai ina yi ne saboda Kareem ba, ina jin tsoron tsayawa a gaban mahaliccina ya tambaye ni wani hakki na bawansa na kasa amsa masa, ko Kareem ya ci abinci ko kar ya ci Yusura zata girka, ko ka tsare mutuncinka ko kar ka yi Yusura zata tsare nata, ko ka kula yaranka ko karka kula Yusura zata ba su tarbiya gwargwadon halinta...”

Ya hade wani abu da ya ji yana masa yawo na rashin dadi ya danne zuciyarsa ya sake yin furuci a gareta.

“Ya jikin na ki? Me yake damunki?”

Ta sake daga kai ta dubeshi.

“Kana da bukatar wani abu?”

Ya saka hannunsa aljihu ya ciro wallet dinsa ya cire ATM dinsa ya aje mata a hannun kujerar da take zaune.

“Gashi idan kina bukatar wani abu ki siya, idan kuma kina bukatar ganin Likita ki je ki ganshi, 5885 is the pin”

Yana dauke hannunsa daga aje ATM din ta mike tsaye.

“Bana bukatar komai daga gareka, ina da rufin asirin da zai wadace na yi ma kaina komai, sai da safe”

Ta bar a gurin tsaye ta nufi stairs. Binta yayi da kallo har sai da ta haye sama sannan ya zauna a inda ta tashi ya ja hular kansa baya ya kai hannunsa yana murza gaban goshinsa dake masa ciwo ya rufe ido.


YUSURA POV.

Tana shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta zauna bakin gadonta hawaye suka sauko mata. Ba burinta ba ne fadawa mijinta bakar magana ba burinta ba ne yin zaman auren da babu farinciki a cikinsa, amman tsananin kiyayyar da take yi ma Kareem ya hana ta mallaka masa ruhinta, daman ita zuciyata ta san ba zai taba samunta ba, domin bata taba jin wani abu akansa ba duk tsawon lokacin da suka dauka a tare, tana kone zuciyarta ne kawai tana azabtar da kanta. Kareem yana da kyau da cikar kamala irin wadda yana da kudi ya shahara a cikin sa'aninsa masu irin aikinsa, amman babu dalili daya da kai ya saka ta so Kareem domin ba shi take so ba tun farko, aure da matar da ta rike ta a matsayin uwa ta hada, a lokacin da ba zata iya ce mata a a ba.

“Har zuwa yaushe zan yi ta zama a cikin wannan yanayin? Sai yaushe zaki tafi Momy? Mutuwarki kadai nake jira, ko kuma ta Kareem na yi takaba na wanke wannan bakincikin, bana fatan mutuwa da aurensa, saboda bana son na tashi tare da shi gobe alkiyama, wata kila dai ba zan iya cin wannan jarabawar ba, kiyayyar da kike ganin kamar zata iya zama soyayya ba zama ba Momy, ta ma kara rura wutar kiyayyar da zata iya hada kasashen dake cikin zuciyoyi yaki da ta yi”

Magana take da kanta zuciyarta na mata zafi, abu ne da ta riga ta sani har abada ba zata taba son Kareem ba, ba kuma dan be kai a so shi ba, ba dan yana mata wani abun ba, sai dan bata taba jin tana kaunarsa ba tun farko, shiyasa kullum take jin kamar a kurkuku take ba a gidan aure ba. A hankali ta kwanta gadon tana kallon gefen dakinta tana ta nazarin rayuwa.


NOOR POV.

A wahale na wuni a ranar, daga mama har Ya Nabil babu wadda ya sake bin ta kaina. Hana ce kawai ta taimaka min ta kwashe aman da na yi bayan ta dawo daga makaranta. Ina jin lokacin da Mama take mata fada wai ai da ta bari na kwashe taya zata kwashe min amai ai shagwaba ni da ake ne yasa nake son lalacewa. Wani abun da Mama bata saba min da shi ba shi ta yi min a yau, wato horo da yunwa ta hana ni abinci rana da hana ni na dare ko da wata safiyar ta waye jikina har rawa yake domin na saba ci ba kadan ba gashi kuma na wuni na kwana ban ci ba. Bayan Hana ta wuce makaranta na fito waje ina jin jikina kamar ba nawa ba, na nufi tukunyar dumame na bude na duba babu komai a ciki, sai na lashe tukunyar na dawo dakinmu na zauna ina jin rashin kyauta abun da na aikata tun farko...

Da sannu na sabarwa kaina da zaman daki bana sha'awar fita ko'ina tun a wacan ranar da Zafeer yayi min huduba. Kwana hudu na shafe ko kofar gidanmu ban leka ba, kullum kuma ina sauraren yaron da zai shigo yace Zafeer yana sallama da Noor amman shiru. A ranar da aka cika kwana biyar ne mutumen da yayi ma Baba alkawarin siye masa gida ya zo aka yi maganar gidan da wani abokin Baba amatsayin shi ne mai gidan aka yi ma gidan kudin miliyan uku da yan kai a take ya biya kudin, duk abun da suke ina jin domin ina cikin dakinmu kwance. Ban motsa ba har sai da abokin Baba ya fita tare da shaidun da suka yi shaidar gidan da aka siyarwa Baba. Kareem din da abokinsa suka bukaci ganina. Sannan na saka hijabina na fito daga dakin ban kalli kowa ba har na zauna na natsu sosai kamar ba ni ba, domin ni kaina na san na canja.

“Noor”

Kareem ya kira sunana sai na daga kai na kalleshi. Shi ma yayi rama kamar dai ni, Murmushi ya sakar min yana tambayar ya jikina, a madadin na mayar masa da murmushin sai hawaye suka cika ido na ba tare da dalili ba, na yi ta yunkuri kirkiro murmushin na kasa.

“Waya cire miki bandajen?”

“Ni na cire”

Na amsa ina maida kaina kasa.

“Kina shan maganinki dai ko?”

Na daga masa kai, domin bana son dogon zancen ni yanzu babu wadda nafi bukatar gani kamar Zafeer. Ban san me ya hana shi zuwa ba kusan sati daya yau, gashi Yaya Baya shiri da ni balle na ari wayarsa na kira shi na ji ko lafiya.

“Ko dai wani abu aka mata Baba? Na ga ta canja? Kamar ba ita ba kuma ta yi rama”

Baba ya juyo ya kalleni yayi dariya.

“Ba abun da aka yi mata, mu kan mu muna mamakin yadda ta zama haka”

Abokin Kareem din da ya siyawa Baba gida ya dube ni.

“Duk lokacin da na fada maka wani abu akan yarinyar nan baka yarda ai, she's very simple and easy going cikin kankanen lokaci zata iya canjawa daman”

Kareem din yayi kamar be ji shi ba, ya cigaba da magana da Baba ta zuba godiya kamin ya miko min wayarsa

“Duba ki gani irin wannan maganin ne da na rubuta miki kike sha?”

Na karbi wayar, a madadin hoton magani ko sunansa wani rubutun ne na gani zube a screen din wayar da Kareem ya miko min.

“Me ya faru Noor? Why the sad face? I Miss the old you, indai damuwarki akan Zafeer zamu taimaka masa, idan kuma akwai wata matsalar bayan ita rubuta min yanzu”


Na dago na dube shi sai na ga daga shi har abokinsa idonsa suna kaina, na girgiza masa kai.

“Ba shi ba ne”

“Amman dai babu wata matsala ko?”

Na daga mishi kai.

“Babu...”

Na yi murmushin domin furuncin na cewar zai taimakawa Zafeer ya faranta min rai siye da siyen gidan Baba da suka yi a bisa karya. Ya miko hannu ya karbi wayar ya saka aljihu ni kuma na juya na kalli Mama da ta fito tana musu godiyar siya mana gida da suka yi.

“Ba komai Mama ayi dai cigaba da hakuri da Noor da halinta, wata rana sai labari gashi dai yanzu ta janyo muku alheri”

Cewar Hafiz abokin Kareem, sai Baba ya fashe da kuka kamar gaske.

“Haka ne haka ne, Allah dai ya saka muku da alheri, ita kuma Allah ya kara mata hankali, ya kawo mata miji na gari...”

“Ameen”

Suka amsa ni da Kareem muna kallon juna kasa kasa kamar wadanda suka kula wani munafurci. Wata kila Baba ji yake kamar ba su fahimci zaren addu'ar ba, wata kila kuma sanadi ne da ni ma zan ji halin da ake ciki game da Zafeer domin tsinkayo Baba muka yi yana fadar abun da ban san an yi ba kuma wani be fada min halin da ake ciki ba.

“Shi wannan yace be shirya ba, wai ba shi da hali yanzu, ya turo yan'uwansa sun zo nan kwana uku da suka wuce da dare yana neman a daga har nan da shekara biyu ko daya da rabi, shi ma kuma ya zo da kansa amman ni na fada musu ba zan iya ba, domin so nake na aurar da Noor na huta, ba karatu take ba, kuma ba wani aiki take tare mana ba balle ace za a daga har lokacin Ƴa mace da ta tasa kyauta dakin miji, balle kuma irin Noor kara na aurar da

14 / 72