Taki Zaman Aure Sirrin Zuciyar Mace by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Author :  𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category :  Romance

Chapter   71 / 72

210K to 213K   out of 215.5K words

cika rigima na fada miki ki daina shigowa rigata ta front ki rika juyawa so that idan ina son na yi hugging dinki sai na yi, yanzu ya zan yi hugging dinki a haka?”

Na turo masa baki a shagwabe na ce.

“To ni haka nake so”

Yayi kasa da kansa ya goge min hancinsa.

“Rigimammiya duk kin bare min riguna”

“Skin to skin, ruhi to ruhi, love to love”

Na daga mishi gira na kashe mishi ido irin yadda yake min. Sai ya saka dariya sosai yana girgiza kai.

“Funny girl, Allah ya shirya min ke”

Na kwantar da kaina a kirjinsa.

“Ameen”

Na yi lamo ina jin bugun zuciyarsa.

“My king”

“Yes my Queen”

“Satin nan ya Nabill zai tafi kauye gurin yan'uwan Babanmu da suke can, zaka bar ni na je”

“No...”

Ya amsa min kai tsaye, fita na yi a rigarsa na matsa gefe na rufe jikina da blanket na hade rai na ci magani. Sai ya sauka daga kan gado ya shiga yayi wanka ya fito na dauke fuska na juya dayan gefen, sai ya zo ya kama fuskata.

“Hey Angry Girl bring back my Beautiful Girl”

Na kara hade rai, sai yayi dariya ya sake ni ya shirya kansa. Sannan ya dawo inda nake ya rika fuskata ya goge min hancin.

“Hey Beautiful saki fuskarki mana, za ki tafi amman ba yanzu ba, sai kin haihuwa”

“To ai yanzu babu cikin ka bari idan....”

Be bari na karasa ba ya rada min.

“We ganna make one tonight”

Yayi kissing front head dina ya nufi kofa.

“Off to work, i love you”

Na nade hannayena na turo baki na ki nace masa i love you too kamar yadda muka saba, sai ya juyo yana rike da kofar dakin.

“Can i hear i love you back”

“No”

“Come on Beauty”

Ya dawo ya fara min cakulkuli har sai da na fada.

“I love you back”

“Nope ina son na ji i love you too”

“I love you too”

“Good girl”

Ya sake ni sannan ya fice. Hausawa suka ce fadi gareka cikawa ga Allah it take us another year kamin na samu ciki, ba dan kuma ina da matsalar komai ba sai dan lokacin hakan ne be yi ba.

Na fara ne da rashin lafiya, sai kuma na fara jin sauki but jiki ya zama so weak, sai dai gane cewar ciki ba ne till one day na dauki wani karfe da Kareem yake workout da shi sai yayi saurin hanawa ya rike ni.

“Mace mai karamin ciki bata daukar abu mai nauyi careful don't hurt yourself”

“Ai ba ni da ciki”

“Says who?”

“Says me”

“Are you a doctor?”

“Amman ai ni matar likita ce?”

Yayi murmushi ta lankamo wuyana.

“Kina matar likita baki san kina da ciki ba?”

Na yi shiru ina nazari, sai ya dauke ni ya bude kofar baya ta falon ya shigo da ni falo ya aje kan kujera ya zauna kusa da ni.

“Ina mutuwar Sonki Noor balle kuma abun da zaki haifa, dole sai kin yi taka tsantsa kar wani abu ya samu cikin nan dan Allah, kwanta ki huta zan motsa jini waje”

Ya mike tsaye sai kuma ya dawo ya rumgume ni ya sumbance ni.

“Thank you, my happiness, my love”

Na yi murmushi na lafe a jikinsa.

“Baby be son ka yi workout he need a cuddle”

Ya daga kafafuwana ya matsar da ni jikin kujerar sannan ya kwanta a gurin ya rungume ni.

“I will do what ever pleased you and my baby”

Na saka hannuna ina jan gashin dake kirjinshi kamshin turarensa na kwantar min da hankali.

“Da gaske ina da ciki?”

“Uhmm. Why would i lie?”

Na jidadi ya rufe ni.

“Kuma kana son Babyn?”

Ya saka hannunsa ya dago kai.

“Har tufafinki ina so balle babyn da zaki haifa, ba ki san irin dadin da na ji ba lokacin da na gane kina da cikin nan”

Na saka hannu biyu ina jan gashin chest dinsa.

“Shiyasa ka ce na daina zuwa da gudu ina rumgume ka idan ka dawo?”

“Yap”

“Me yasa baka fada min ina da ciki ba?”

“Saboda fitina ta zaki yi, yanzu da kin tashi fita ki ce Baby yana son yawo, and kin san yadda nake kishinki bana son kina fita ko kadan”

Na yi dariya, domin ya canka a daidai yadda yayi zato haka nake aiwatarwa, a duk lokacin da aljannun yawon suka motsa kuka kawai nake kasa masa na ce baby yana son yawo, idan har yana kaunar zaman lafiya a ranar dole ya kai ni yawo ko kuma ya bar ni na tafi gidanmu. Haka muka yi ta fama abinci ma sai an jera min shida bakwai sannan na samu wanda zuciyata take so, abu kadan ya bata min rai, ni kaina taka tsantsan nake da kaina balle kuma Kareem da har tsoron kallona yake domin zan iya cewa kallon be yi min ba haka dai har na shiga wata na takwas.




KAREEM POV.

Sautin kukanta ne ya tashe shi daga bachin da yake, ya mika hannu ya kunna bedside lamp sai ya ganta zaune tana kuka. Ya tashi zaune da sauri ya rikota.

“Hey Beautiful me ya faru?”

Ta ki ta yi magana sai kuka take, sauka yayi daga kan gadon ya dauki jallabiyarsa ya saka ya fita dakin be dade ba ya dawo dauke da ruwa ya rika kanta ya kai mata ruwan a baki ta sha, har tana sauke ajiyar zuciya sannan ya aje kofin ya zauna gefen gadon ya bude kafafufuwanta yana matsawa.

“Me ya faru? Mafarki kika yi marar kyau?”

“Aa”

“Me kike yi ma kuka? Baki da lafiya”

“Lafiyata kalau, na tuna da lokacin da ka zo gidanmu ka ce wai wata yarinya kake so, kuma tana sonka sunanta Hafsa, kuma ka san ni ce miyasa baka fada min gaskiya cewa ni ce wannan yarinyar ba sai da na ji babu dadi”

Kallonta kawai yake ya rasa ma me zai furta mata.

“Yanzu wannan abun shekara biyu da wani abu ba ki tono shi ba sai yanzu? Kuma miye abun kuka a ciki ai ke ce yarinyar”

“Miyasa baka fada ba tun farko? Ka yi breaking heart dina”

“Okay I'm sorry ba zan sake ba, Allah ya baki hakuri, yar kyakkyawata”

“Dauko min riga na saka”

Ta fada a shagwabe kamar mai shirin fashewa da wani sabon kukan. Ya sauka ya nufi wardrobe dinta ya dauko mata rigar da gown irin ta masu ciki mai free size.

“Bana son rigata”

“Tawa kike so?”

Ta daga mishi kai, sai ya juya ya aje nata rigan ya bude side dinsa ta dauko mata T-shirt dinsa ya saka mata daman ko ba ciki tana saka kayansa balle kuma tun da cikin ya fara girma kayansa take sakawa.

“Da short”

Ya bude wardrobe dinta ya dauko mata karamin short ya saka mata.

“Shikenan? Ko kina bukatar wani abu?”

“Ni ka daina tambayata idan ina bukatar wani abu ba ina magana ba”

“Allah ya baki hakuri, na daina”

Ya kwantar da ita a hankali sannan ya kashe wutar ya kwanta bayanta ya rumgumeta. Washe gari ma haka ta tashi da rigima there is one food she hate the most tun da ta samu cikin nan bata son jollop rice, as early morning take fadawa Kareem wai su daina girka abinci a restaurant din

Yana tsaye gaban madubi ya juyo ya kalleta.

“Saboda me?”

“Ba ke ake girkawa ba?”

“To bana dai sonta”

Da ya karanci matarsa rigima take ji sai ya amsa mata da

“Okay zan fada musu su daina girkawa, shi kadai ko da wani?”

“Shi kadai, amman Hubby ina son idan ka dawo da dare mu tafi shopping na siya turare”

Ya juya ya kalli mirror dake cike da turaruka kala kala.

“Okay za mu je In Shaa Allahu”

Ya sumbanci bakinta ya sunbanci cikinta sannan ya sake kissing front head nata ya ja hancinta.

“Take care of yourself sai na dawo”

Ya fice yana dariya shi kadai, domin be tana samun kansa a cikin wannan yanayin ba sai yanzu, yara biyu da suka haifa da Yusura bata taba masa haka ba. Sai gwanarsa Noor.

Yadda yayi mata alkawari haka ya aiwatar misalin tara na dare ya dauketa suka tafi shopping mall gurin siyen turaren da be san ya zata yi da shi ba. Sai da ya fara fita ya zagaya ya bude mata ta fito tana sanye da hijab har kasa.


NOOR POV.

Ina tura cikina muka shiga ciki turare biyu kwai kamshinsu yayi min dadi na zaba sai wasu shoes da abaya, idan na zaba shi nake bawa har na gama muka nufi gurin biyan kudi muna tafe muna hira. Gafen da nake tsaye Abdull yake tsaye amman ni ban kula ba domin hankalina yana gurin kayan wata mata da ake dubawa. Kareem ya bar gefensa ya dawo nawa gefen ya tsaya ya shiga tsakanina da Abdull.

Kamin ya aje kayan hannunsa a gurin ya riko hannuna, sai a lokacin na lura da Abdull din da shi ma jiran yake a duba nasa kayan ya biya kudi. Kallona yyai sai yai saurin dauke ido kamar wanda ya rikice ya bar gurin ta koma cikin mall din. Kareem be sake ni ba sai da muka iso gurin motarsa ya bude min na shiga.

“Abdull ne ko?”

Kamar yana jira sai ya rufe ni da fada.

“Dole sai kin fadi sunansa? Kina da alaka da shi?”

“Aa”

“Na yi nufin na zo na saka ki a mota ki kira ne sai na gama biya mu tafi, amman yanzu na fasa ba za'a siye kayan ba”

Ya rufe min gambun ya zagaya side dinsa ya shiga yayi ma motar key.

“To ni miye laifina dan kawai na ce Abdull ne”

“Kara fada kike yi?”

Na yi shiru kamar zan yi kuka.

“Ka san ai ba kaunarshi ne ke ba, domin ba zan taba manta abun da yayi min ba da Hana, rayuwarsa ba zata kare da kyau ba”

“Kadan ya rage masa ai, ko a yanzu ya halaka tun da ya rasa aikinsa da yake ya koma karantarwa a secondary school, kuma ya kwashi ciwo”

Na zaro ido.

“Da gaske? Taya ka sani?”

“Wani likita naje gani asibitin da naje awo, na ganshi layin yan HIV ko dai ya kamu ko kuma yana tunanin ya kamu ne, in ba haka ba babu abun da zai saka shi tafiya awo”

“Amman tabbas shi ne?”

“Shi ne mana Beb saboda na tabbatar sai da na duba files din ma na ga sunansa, saboda ya saka mask da facing cap ya rufe fuskarsa”

Na yamutsa fuska.

“Daman karshen alewa kasa, Allah ya kara masa ya isar mana, da ma ya rufawa kansa asiri ya maida maitarsa sun zauna, ko da yake ita ma ba zata yarda ba saboda yana da ciwo yanzu ko?”

Be amsa ni ba ya faka gaban wani mai tsire.

“Zaki ci na siya?”

“Eh”

“Okay”

Ya siya mana na 5k sannan yaja motar muka yi gaba.

“Ai Safeena ma bata garin nan ko Hubby?”

“Tana nan”

“Ba kace ta koma garinsu ba? Kuma kace ta yi hadari?”

“Eh amman bayan ta koma gida daga asibiti, last year suka yi gobara a gidan iyayenta suka rasu ita kuma ta yi kuna a jiki, sai mahaifin Abdull ya daukota ya dawo da ita garin nan daman shi ya rika ta ko lokacin da iyayen suke da rai”

“Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, bayan watan nin da ta yi asibiti kuma da ta koma gida sai iyayen suka rasu? Wayyo Allah bata da yan'uwa kuma?”

“Tana da su mana, amman shi baban Abdull din yayan mahaifinta ne ya rigata shiyasa ya sake dawowa da ita yanzu”

“Ta ba ni tausayi”

Na fada har a raina domin rayuwarta abar tausayi ce a yanzu. Kareem ya kai hannu ya rika hannuna ya cigaba da tukin da hannu daya.

“Be kamata ma ki ji tausayinta ba, kin san wutar da ta tashi a gidanku? She's the reasons”

Na rufe baki da hannu daya.

“Taya ka sani?”

“Zuciyata ta raya min haka daman, kuma na karanci hakan cikin kalamanta lokacin da muka yi fada, ta aiko kawarta ta fada min kuma yana neman magana da ke”

“So har yanzu....”

Na tambaya cikin kuka, domin na tuna da mahaifina da yar'uwata.

“Nononononononononononono Wallahi tun da muka rabu ban sake sakata a idona ba, ban san labarinta sai da kawarta ta same ni a office, kuma kawarta nurse ce muna mutunci a tsakaninmu if not ba zan ma tsaya na saurareta ba”

Ya faka motar ya fita ya zagayo ya bude min na fito, ya dauki tsiren ya riko hannuna muka shiga ciki ina kuka, kan tebur ya aje ledar ya zauna kusa da ni ya rungume ni.

“Idan ni na mata laifi me Baba da Hana suka mata?e yasa zata kashe min mahaifi da yar'uwa?”

“Ke ta yi nufin kashewa sai kuma baki kwana a gidan ba, kukan ya isa haka Beb, i already told you no more tears”

Ya rumgume ni tsantsam a kirjinsa yana shafa bayana alamar rarrashi...

Na dago daga jikinsa na kalleshi.

“Ina son na ganta”

Ya kama fuskata da hannu biyu ya rike.

“Baki bukatar ganinta Love”

“Ina son na ganta, ina son na yi magana da ita”

Yatsunsa ya saka yana share min hawayen da saukowa.

“Saboda me amman?”

“Ni dai kawai ina son na ganta”

“Zan yi tunani akai, yanzu manta da ita bari na bude miki namanki ki ci huh”

Ya sumbanci bakina.

“Ka dafa min indomie sai ka saka naman cikin ka saka kwai”

“Okay”

Ya sake ni ya mike tsaye sai na riga hijab dina sai ya rika min na cire na koma daga ni sai skirt da T-shirt dinsa dake jikina. Ya aje min hijab din da dayan bangaren sannan ya nufi kitchen ni kuma na mike kafa ina kallon tv amman hawaye nake kewar mahaifina da yar'uwata.

Tun da ya shiga kitchen din be fito ba sai da ya gama, a lokacin da ya hango hawaye a idona sai ya zo da sauri yana kallon fuskata.

“Na dade gurin dafawa ne?”

Na girgiza kai alamar aa.

“Minene?”

“I miss my Dad i miss my sister”

“Wannan dalilin ne ya saka bana fada miki wani abu Beb, bana son hawayen nan na ki da tashin hankali”

Ya rumgume ni a tsayen da yake yana shafa kaina.

“Addu'a suke da bukata a yanzu, ba kukanki ba, kuma yanzu komai ya wuce I'm right here My Love”

Na lumshe ido ina sauke ajiyar zuciya. Sai ya duko yana taba fuskata.

“Haba yan matana, haba uwargidan Kareem kuma amarya, daga ke babu kari, haba yar tilon Mama, kanwar Nabil, duk ke kadai ehen ga ki kuma yar gatan mijinta, mai son ganin bacin ran Kareem ya taba Noor, haba ta Kareem bada kanki a asare ki je ki cewa Mama ya fadi, haba autar mata....”

Na kalleshi ina murmushi, duk wani abun da Kareem zai yi ya kwatar min da hankali ya san shi kuma yayi kuma yayi nasara domin mun ci abincin da ya girka min cikin farinciki da kaunar juna. Ya wancin aikin gidan shi yake yi ya dauke min nauyi abubuwa da yawa tun da muka yi auren balle kuma a yanzu da nake dauke da babynsa.

Wannan cikin ya zo a dabam ba kamar cikina na farko ba ina fama da yawan rigima abun da be kamata na damu da shi na kan damu, abun da babu ruwana ma sai na shiga, na tabbatar da a gidan haya muke wata kila da yanzu an koramu ni da mijina. Cikina na wata tara mun fito daga family house dinsu Kareem na rika masa magiyar ya bar ni na ga Safeena idan dai tana garin nan.

Ba dan ya so ba ya tafi da ni gidansu Abdull kuma gidansu Safeena a yanzu, kamin a bude masa gate yake fadar ba lallai a bar mu mu ganta ba, ba lallai idan ta san mu ne ta yarda ta fito ba. Ni mna na raya wannan a zuciyata sai dai ta inda muka taki sa'a muna shiga bangaren uwargidan wanda a nan ne ake rikon Safeena sai muka same ta harabar gidan zaune a well-chair tana kallon motarmu.

Gabana ya fadi na ji kamar bana bukatar ganinta kamar yadda Kareem ya fada da farko, sai dai kuma mun riga da mun zo, har Kareem ya bude min mota.

“Zan tsaya a nan, karki dade”

Ya jingina da motar fuskarsa na kallon gate din gidan. Ni kuma na taka ta tulelen cikina na karasa kusa da ita na tsaya ina kallonta tana kallona, can kuma sai ta yi murmushi.

“Na san kin yi nasara Noor baki bukatar nuna min, kin raba ni da wanda nake kauna, kin raba ni da aurena, kin juyar da mutumen da yake tsananin kaunata zuwa makiyi na, yanzu miye dalilin zuwanki? Rayuwata kike nema ko me? Ko kin zo nan ne, saboda ki fada min kin yi nasara a rayuwa? Kin zo ne saboda ki fada min kin auri Kareem har kin samu ciki da shi?”

Na girgiza mata kai ina kallonta ita din abar tausayi ce a yanzu me yasa bata tausayin kanta? Kusan rabin fuskarta zuwa habarta na bangaren hagu ya bar mata tabon wuta alamar kone da aka yi aka warke.

“Ban zo nan saboda na nuna miki na yi nasara ba, zan fada miki na yi nasara ne idan muka shiga aljanna ni da Kareem. Na zo nan ne saboda na tunatar da ke abun da kika manta, mutum baya iya canja abun da Allah ya kaddara zai faru ga bawansa, dabara da wayo basa sauya kaddara, kuma ba zaka saka wani a bakinciki kai kuma ka yi tsammanin zaka dauwama a farinciki ba, ta kika kone nawa iyayen ke ina naki iyayen suke a yanzu? Da kika so raba ni da rayuwa ke ya taki rayuwar take a yanzu? Annabi Muhammad S A W ya fada, imanin dayanku ba zai cika ba har sai ya sowa dan'uwansa abun da ya so ga kansa, ina imaninki ya tafi Safeena? Abun da kika yi nufi da ni, za ki so ya faru da ke?”

Ta dauke kai tana hawaye.

“Ni na yi nufin bawa zuciyata abun da take so ne kawai, kamar yadda kika yi jarabawa ta ce son Kareem, amman kin raba ni da shi, go home and celebrate”

Na juya na kalli Kareem dake tsaye fuskarsa tana wani gafen baya kallon gurin da muke tsaye, sannan na juyo na kalleta.

“Kamin mu yi aure, ba zan iya cewa ina son Kareem ba, ko da ina son shi to ni ban sani ba, amman da kaddara ta yi nufin hadamu sai abubuwa suka faru, daga karshe kuma sai ya zama abokin rayuwata. Amman Safeena namiji be

71 / 72