Taki Zaman Aure Sirrin Zuciyar Mace by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Author :  𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category :  Romance

Chapter   3 / 72

6K to 9K   out of 215.5K words

zaune ya mika min.

“Na gode Yayana”

Murmushi kawai yayi min ya juya ya shige dakinsa na kalli Hana dake sauraren littafi a wayar Mama na ce.

“Kin gani ba irinki ba, ke baki da nasiha ko tufafinki aka taba sai kin fara fada”

Uffan bata ce min ba gaba daya hankalinta ya tattara ya koma gurin wayar dake makale a kunnenta. Sai dai sallamar da Abbah yayi ya saka ta yi saurin cire wayar ta tashi zaune ni kuma na amsa sallamar na masa sannu da zuwa na shige dakinmu, shigata da mintuna kadan Hana ta shigo. Daga ni har ita babu wanda ya sake fita dakin gar garin Allah ya waye.

Kamar yadda muka saba Hana ce take hada mana abun karyawa saboda ita ce mai zuwa makaranta, saboda haka da wuri take tashi ta dumama mana idan an raga abinci idan kuma koko za a siyo ko a dama duk ita ce take yi. Sai dai yau ni dai bana sha'awar cin dumame dan haka ban fito na karbi nawa ba sai da na ji motsin Yaya Nabil yana magana da Mama a tsakar gida. Fitowa na yi na zauna bakin kofar dakinmu a lokacin Hana ta dade da wuce makarantar boko.

“Yaya ina kwana”

“Lafiya Kalau sai yanzu kika tashi”

“Tun dazun ta tashi, wai ita yau bata son dumame shi ne taki fitowa ta karba”

Mama ta fada tana juyowa ta kalleni. Yaya Yayi murmushi ya girgiza kai.

“Ni dai yau ba ni da ko sisi idan zaki ci dumame ki ci, idan ba zaki ci ba cikinki ne”

“Yaya dan Allah ka siya min indomie Wallahi bana son dumeme kullum shi muke ci”

Mama ta saka dariya.

“Wuya bata ci ba yarinya, idan kika ji yunwa da kanki zaki nemi tuwon ma”

Mama ta tashi ta shige dakinta, Yaya kuma yayi fitarsa aka bar ni a gurin zaune, sai da na ga babu sarki sai Allah na dauki kwano na gutsira tuwon kadan na ci na aje sauran, tsintsiya na dauka na share ko'ina na gyara daman wanki da wanke wanke ko girki ba nawa ba ne, a cikin aikin gidan babu abun da na tsana kamar wanke wanke da wanki, girki kuma Mama ta fi sha'awa ta girka da kanta, ba kasafai take bari muna mata girki ba.

Misalin karfe biyu da mintun Hana ta dawo daga makaranta, ita kam bata tsaya neman wani abincin ba ta saka dumamen da na ce ba zan ci ba ta cinye abunta ta bar ni da yunwa a ciki. Ina tsaka da miyar ta cinye min tuwo kawata Zee ta shigo gidan cikin shirinta na ankon kamu, ba karamin burge ni ta yi ba domin ta yi kyau sosai ankon ya karbe ta gashi ni ban yi ba, sai yabon kyauta nake.

“Mama kin gani sai da na ce Yaya yayi min ankon nan ya ki”

“Komai dai Yayanki, ki rika tausaya masa mana Noor abun ai sai ya masa yawa, komai dai shi ne, me yasa baki ce Zafeer yayi miki ba?”

Na kalli Mama dake kare danta.

“Shi ai be da kudi”

“Shi kuma yayanki banki ne ko?”

Na turo baki gabana ina son yi mata kukan shagwaba.

“Yanzu kuma ko sisi ba ni da na tafiya bikin nan fa”

“Daina kallona Wallahi ni ma ba ni da ko naira”

Zee ta saka mana dariya.

“Ashe kuwa ba za aje da ke ba, ni ma ba ni da kudin tafiya, na san dawowa ba zai yi wahala ba saboda samari”

“Bari na tafi gurin Yaya ina binsa kudi 700 ya bani ko 200 na samu na napep”

Na tashi na zuba ruwa a bokita na shiga bandaki na yi wanka na fito na shafa mai na dauki hodar Hana na shafa da jan bakinta na yi kwalliya na yi kyau sosai sannan na saka abayata na dora mayafin, na fito daga dakin na bar Zee tana kara gyara fuskarta sa kayan kwalliyar Hana dake ta yi mana masifa wai sai mun biyata ai kwaliyar kudi take ba kyauta ba.

“Daga nan zaki iya tafiya a kafa har gurin aikinsa? Kuma kika sani ko yana da kudin ko babu, wannan tafiyar kamar ta dole Noor?”

Mama ta fara kokarin hana ni, aiko take na bata fuska.

“Mama komai fa ban tafi ba na Salwa kuma wannan ne event na karshe ni dai ina son zuwa, kuma Yaya ba zai rasa kudin da zai ba ni”

“Allah ya kiyaye ga ki ga hanya, idan be ga dama ba ai ba zai baki ba, ko ma ya hana ki tafiya bikin”

Na saka talkamina na high hill na fice daga gidan, ba a kafa na taka ba titi na isa na tari mai adaidaita sahu na fada masa inda zai kai ni yace na bada 200 naira kasancewar babu wani tazara sosai.

“Kadai san Kareem Restaurant ko?”

“Hajiya tun da ke kin san guri ai babu wata matsala”

Na shiga Napep din ya ina ta rabon ido har muka isa Fancy Restaurant din na fito na shiga ciki domin ba wannan ne zuwana na farko ba, can ciki na wuce na yi magana da wani na fada masa ya kira min Yayana.

“Yana can ciki aiki suke lafiya?”

“Lafiya kalau mai Napep zan sallama kuma zan yi magana da shi”

“Bari na kira shi a waya amman idan suna girki ba a bari su fita”

Ina tsaye a gurin abokinsa yana ta kiransa a waya be amsa ba, hakan ya saka hankali ya dan tashi domin na san halin wasu masu Napep ba su da mutunci. Komawa na yi na leka waje na sake dawowa ganin hankalina ya tashi ya saka Yusuf tambayar nawa ne kudin napep din na fada masa sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro 200 ya ba ni na fita da saurina na kaiwa mai Napep din.
Sannan na dawo na tsaya reception din, ina ta kallon mutane da yadda ake ta sake sabunta gurin, a kullum idan ka zo sai ka ga ya sake zama sabo.

“Noor yayi picking yace ki zauna ki jira shi sai sun gama girkin zai fito”

Abokinsa ya fada, na kalli katon agogon dake gurin na ga uku da yan mintuna, na san ya kusan tashi aikin ma gaba daya, saboda haka na nemi guri a teburin da mutane suke zama na zauna ni kadai ina ta jin rashin sakewa saboda akwai mutane da yawa a gurin, duk kuwa da kasancewar kowa sha'anin gabansa yake. Ta dayan bangaren kuma ina jin dadin yadda sanyin Ac ke ratsa jikina, rabon da na ji sanyi ac har na manta.



https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx


Assalamu Alaikum...
Ina talata muku
KHADEEJA CANDY STORE 🥰🙌
Muna siyar da Atamfa, Laces, Mayafai, Talkami da Jaka, Akwaituna, Kayan Kitchen, Zanen Gado, da kuma kayan kawata gida ko falo.

✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧


𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆


𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫 -3

Ina zaune a gurin wasu iyalai suka shigo, ba zan iya fadar cewar masu kudi ne sosai ko akasin haka ba. Sai dai alama ta nuna suna da rufin asiri. Teburin sake gabana suka kama yan mata hudu ne sai maza uku da kuma magidancin da zan iya shaidar cewar mahaifinsu saboda kama da tsufan da yayi. Wadda ta zauna a gefensa kuma bana bukatar a fada min cewar ita din uwace domin alamu ya nuna haka. Hannu biyu na saka na yi tagumi ina kallon yadda uban yake handling yayansa mazan suka koma a dayan teburin suka zauna matan kuma suka zauna tare shi.

Sai da suka fara daukar littafin dake teburin suka duba kalar abincin da suke so, tukuna daya daga cikin ma'aikatan gurin ya zo yayi taking orders. Ni kam sai kallonsu nake cike da burge, ba kudin ne abun burgewa ba, ba zuwa restaurants ko order abinci, soyayyar ce ta shiga zuciyata yadda uba yake nunawa yayansa soyayya da kauna yana ta hira da matan suna dariya mazan kuma suna jefo na su hirar daga can inda suke zaune. Wani abu ne da ni na rasa tun tashina, ban tana zama da mahaifina ya tambaye damuwata ko dadi ba, wata hirar farincikin bata taba hada ni da shi ba, ban taba aikata wani abu ya nuna jindadinsa.

“Noor....”

Na juyo dama da ni sai na yi arba da Yayana, hannayensa na ji a fuskata yana share min hawayen da ban san sun zubo ba.

“Kuka kike yi? Saboda na dade?”

Ya tambaya saboda ya san ni da kukan shagwaba kamar wata wadda ta tashi cikin gata. Sai na girgiza masa kai na juya na kalli mutanen

“Wani abu da na rasa nake kallon wasu da suke da shi, kalli yadda suke cin abinci tare da Babansu be burge ka ba Yaya?”

Ya daga kai ya kalli gurin kamin ya dube yana sauke ajiyar zuciya.

“Wata rana ina jin kamar hakan zai faru amman na san ba zai taba faruwa ba”

“Kin cika tunani da yawa, a kawo miki wani abu zaki ci?”

Na saka hannuna da kaina na share hawayen da suka sake zubo min na dubi Yaya dake sanye da uniform din gurin sai tausayinsa ya kama ni, na san yayana ba mutum ne mai son zaman banza ba, yana da kokarin nema, saboda dukanmu mun taso a rayuwar talauci mun san babu kuma mun saba da hakan. A aljihunsa ake samun kudin chefane gidanmu a kullum kuma da kudinshi Mama take zuba adashe tana mana tanadin kayan aure.

“Wa zai biya? Ni ba ruwana bana da ko shishi...”

Yayi dariya domin ya san kadan daga halina ne zan iya komai ko bana da ko sisi sai dai duk abun da zai faru ya faru.

“Za a cire salary”

“Toh a kawo, daman Yaya ban ci komai ba tun safe, kuma ban taba cin abinci a Restaurant ba”

“Me kika so?”

“Akawo naman kaza da na kayan ciki da shawarma da pizza da...”

Ban gama zanawa ba ya katsene.

“Ke fa baki da hankali, duk plate daya a nan 5k plate nawa zaki ci?”

Na bude baki na kalli mutanen gabana na kirga si na kirga kudin da za su kashe.

“Tab toh Yaya a kawo kaza”

“Kaza 10k ne ke kuma abun da zaki ci ba zai wuce 2k”

“Toh ai ka ce 5k ne plate”

“Rabi zan kawo miki”

Be jira abun da zan ce ba ya juya ya bar ni a gurin zaune. Babu jimawa ya dawo rike da plate wata yar shimkafa ce kamar na roka sai wani kofin lemu da gorar ruwa mai yawa.

“Yaya wannan ba zai ce min komai ba, iya halshe zai tsaya”

“Masu kudi kadan suke ci ki yi cin masu kudi, ko baki ga yadda Restaurant din yake ba?”

Ya zare min ido sannan ya tafi ya bar ni a gurin. Ba dan kar nutane su kalle ni da ba zan ci wannan abinci ba, wannan ai rowa Yaya yake min a gurin aikinsa. Na daure na kai zuciyata nesa na cinye abincin nan tass ko shimkafa daya ban bari a gurin ba, lemun ma duka na shanye sannan na dauki ruwan na sha. Kamin na mike tsaye sai ga Yaya ya zo yana kokarin dauke kayan har da ruwan aiko na saka hannu na dauke ruwana, gudun siyar da hali yasa be ce min komai ba ya shiga ciki da kayan, babu jimawa ya fito sanye da kayansa na gida ya rika hannuna muka kama hanyar fita.

“Mi zaki yi da gorar ruwa wane irin kauyanci ne wannan Noor dan Allah ki aje”

“Wallahi ba zan jefar ba, ai ba kyau wulakanta ruwa, kuma ai siya muka yi ba sata ba”

Ina jinsa yana jan tsaki amman ban jefar da ruwana ba, ko ba komai kowa ya gani zai san na ci abinci a gurin, masu kudi ma haka nake ganin suna yi ai, suna rike gorar ruwa a hannu idan suna yawa. Sai da muka fita gate din gurin gaba daya sannan yake tambaya me ya kawo ni ma.

“Yaya kudina zaka ba ni, bikin salwa zan je, dari bakwai daka ara zaka ba ni abuna”

Ya daka min tsawa.

“Ba salwa ba kwai, yanxu saboda bikin wata Salwa kika kwaso kafa kika zo har gurin da nake aiki har da aron na Napep, kuma sau nawa zan biyaki bashinki ne Noor shekarab jiya kin karbi dari biyu last week na baki dari uku dari biyu kawai kika biyo ni, kuma yanzu kin hau Napep da ita, gashi nan kin saka ni siyen plate daya 5k sakaryar yarinya kawai”

Ban san lokacin da na tsayar da tafiyar da nake na dube shi.

“Yaya wannan abincin da naman kahirar ne 5k? Kam bala'i Wallahi a ana zalimci duniya, kuma ni kudina 700 ne”

“Da yardar Allah ba zan sake rantar kudinki ba, ke idan an ari kudinki babu zaman lafiya, kuma sai ki rika kari saboda baki tsoron Allah”

Yana masifar yana tare mai adaidaita, yadda fuskarsa ta hade sai ka rantse da Allah ba shi ne yake tarairayata a cikin restaurant din ba.

“Kuma wannan abincin da kika ci bashi ne sai kin biya. Malam Wurno Road”

Ya karasa yana magana da mai adaidaita sahun.

“Yaya ba gida zamu je ba?”

“Ban sani ba, kuma Allah yasa mu je kin zubar min da mutunci mu koma gida ki ga yadda zan miki wulakanci”

“Toh wai ni nace ka kawo min abinci? Ba kai ka ba ni ba dan kanka to miye na masifa kuma”

“Saboda dari bakwai kika zo har gurin aikina, kuma idan ban kawo miki wani abu abokan aikina ai za su min gulma, kuma kin ba ni tausayi da farko”

Ban yarda na sake cewa komai ba, domin abu ne mai sauke ya sauke ni a hanyar ya tafi ya bar ni, na lura ba karamin hawa yayi wannan masifar da yake ta min kamar na ce ya ba ni abinci a dole. Tun da muka shigo unguwar mai adaidaita be tsaya ko'ina ba har sai da Yaya ya bukaci haka. Gaban wani katon gida ya faka Yaya ya fito ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi ya bawa mai adaidainta.

“Zai wuce da ke gida”

Ina jin haka na yi saurin fita cikin Napep din na fara yi masa magiya ina kuka. Har ga Allah ba zan yarda ya shiga wannan katon gidan ba tare da ni ba, ko ba komai ai zan bawa idanuwana abinci.

“Yaya ka yi hakuri dan Allah karka ce ya wuce da ni gida, tare da kai zan tafi dan Allah Yaya ka yi hakuri, na yafe maka 700 din ka yi hakuri Yaya dan Allah”

“Ba biki zaki ba?”

“Na fasa”

Ya tsaya yana kallona kamar wadda ya rasa ya zai yi da ni. Ni ko sai rokonsa nake ina magiya kamar wadda za a saka a cikin wata ni'ima. Ganin haka ya saka ya sallami mai Napep din ya nufi gate din gidan dake rufe. Kwankwasa yayi aka bude masa farin gate din muka shiga ciki yana gaisawa da masu tsaron kofar.
Galala na yi ina tafiya ina kallon yadda gidan ya tsaru da abubuwa gidan sama har hawa biyu, gashi komai na gidan fari ne tun daga motoci har fentin gidan, wata babbar kofar ya nufa ya danna door bell sannan yaja ya tsaya, kallo daya yayi min na natsu sa kyau na sauke kaina kasa, ba sai ya tuna min ba, ni ma ai ina ganin yadda komai yake tsare na san gidan masu alfarma ne.

Wata yar lukutar yarinya ce ta bude mana kofar, fara ce sosai babu alamar kashi a jikinta tsokoki ne suke ta rawa kamar wata tufa.

“Tine babanki na nan?”

“Eh ku shigo”

Yaya ne ya fara wuce sannan na shiga ina maimaita sunan nata da yayi min kama da ba kafirai. Suuuuuu na fara jin sanyin ac na ratsani irin tsarin nan na musamman, wannan sanyin ya ci uban na wanda na ji a Restaurant. Da katon Tv na fara arba indiawa dake ciki suna magana kai kace fasa tv za su yi su fito, ga wani kamshin turare da ke tashi kamar dakin Amarya. Ban raina kaina ba sai da na zauna a kujerar da Yaya ya zauna, wani kalar laushi na ji da ban taba jin na zauna a makamancin abu na ji haka ba. Idanuwa suka ce me muka zo yi ba kallo ba, a nan na fara tantance komai na katon falon da ya kasance fari kamar yadda curtains din da labulaye suke, wata kalar wuta ce a rufin mai blue sai haskowa take.

A hankali na sauke idona gurin stairs da aka kawata kamar ba za a mutu ba, a nan na lura da kasan ba tile ba ne, ba kuma suminti ba, wani abu ne mai tsantsi da daukar ido aka malaya a gaba daya falon har zuwa inda muke zaune, ga wani zare zare da aka saka a ciki kamar maciji.

“Yaya Yaya Yaya”

Na kira sunansa na taba shi ya nuna masa wutar sama dake blinking na nuna masa tv na nuna masa tile din sannan na matse hannuna ina masa rada.

“Ac ac ac, sanyi dadi, kujera laushi, kamshi ko'ina ko Yaya?”

Da sauri ya kawar da fuskarsa yayi kamar be gan ni, can kuma ban san abun da zuciyarsa ta raya masa ba, sai ganin na yi ya mike tsaye ya kama hannuna na Mike tsaye muka nufi kofa ya bude kofar ya tura ni waje ya rufe. Ba dan ina da zuciya mai kyau ba Wallahi da na nuna masa tijara na koma ciki da karfi, daga zuwa gidan masu arziki sai wulakanci ta biyo baya, miye laifina dan na ga wani abu ya burge ni, ina ce ban taba gani ba sai yau. Kuma gidanmu ai ba ac nake ba fankar dakinmu ma ta lalace kullum a zafi muke bachi.

A raina na yi guntun tsaki, ina jin haushin yadda be bari na ga mutanen gidan ba, wata kila ma su kawo masa wani abu mai dadi ya ci shi kadai ko ma me ya zo yi a gidan oho, ta dayan bangaren kuma ina mamakin Ina Yaya ya san masu arziki haka. Entrance na nufa na tsaya a gurin na rumgume hannayena tare da gorar ruwan sa na yi guzuri, ina kallon kofar falon ko za a bude.

“Who's this?”

Wani mutun ne tsaye a gefena rike da laptop a hannuna yana kallona.

“Noor...”

Na amsa masa ina dauke kai irin dauke kan dake nuna fushi

3 / 72