Taki Zaman Aure Sirrin Zuciyar Mace by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Author :  𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category :  Romance

Chapter   18 / 72

51K to 54K   out of 215.5K words

ta zauna ta yi tagumi, duk irin yadda take kaunar makaranta da rashin son wasa da karatun da take a yau ban ga tana shirin tafiya makarantar ba. Ina jin motsin fitowar Ya Nabil amman be cewa Baba uffan ba ya koma ciki, ba kamar yadda yake gaishe shi da safe idan ya ganshi ba, ni ma da na saba lekawa na gaishe shi a yau sai na ji bana bukatar ganin fuskarsa ko yi masa magana. Muna zaune dakin kamar wadanda aka yi ma mutuwa har wajen karfe goma sha daya, sannan Yaya ya sake fitowa yana wanke baki wato brush muka ji an buga kofar gidan, gabana ya fadi wata zuciyar na raya min cewar Zafeer ne ko wasani nasa. Sai da Yaya ya gama wanke bakin sannan leka waje, ya dan dauki lokaci sai dai ba sosai ba ya dawo cikin gidan ina hange lokacin da ya shiga dakin da Baba yake wato dakin Mama, sai na ga hango Baba ya fito da sauri ya fita. Wata zuciyar sai ta raya min cewar wani ne daga familyn Mama wata kila ya biyo sawu ya ji abun da ya faru. Sai dai yadda Baba ya dawo ya shigo dakinmu da kuzarinsa ya katse hanzarina.

“Ina... Nooriyya...”

Na tashi zaune jiki babu karfi.

“Taso ga Alhaji nan ya zo”

Na tashi tsaye ina jin kamar ba zan iya tsayi ba, ba kuma dan na san wane alhajin yake magana a kai ba.

“Saka Hijabinki mana”

Na juya na dauko hijabin na saka na bi bayansa, sai da muka fita waje sannan Baba ya tsayar da ni ya ce.

“Ke saurara kar kije ki yi hauka, kin ga dai mutumen nan mai mutumci ne, kuma yayi mana karamci yadda ya dace, zuwan da yayi yanzu yace min ya zo da magana ne, kuma na fahimci maganarsa ta neman aurenki ne, ban riga na bashi ba, amman dai na fada masa ke ma kina maraba da hakan, karki kunyata ni Noor, Allah ya ba mu wannan damar ya ba mu wannan ikon na zabawa yarinyar mijin da zai dace da ita, kuma ni ubanki ne ba zan zaba miki abin da zai cutar da ke ba, dan haka nake son na baki umarni ba shawara ba, duk abun da ya tambaye ki ki amsa da eh karki karyata mahaifinki karki saka kimata ta zube a idonsa, ki tafi a natse ku yi magana ta hankali idan kika dawo zamu yi magana ta fahimtar juna kin ji ko?”

Na daga masa kai ba dan na fahimci duka yaren da yake karanta min ba, ina mamakin yadda ya kwantar da murya yana min magana kamar ba shi ba, abun da tun da na zo duniya be taba min ba, na bude ido ne da tsawarsa da duka ta tsana da fargabar fadan yau dabam gobe dabam. Na fara takawa ina ganin hanyar tana rabe min na isa gurin kofar na fita daga kan da zan yi na kalli dama da ni sai na hango Zafeer a tsaye nesa da kofar gidanmu ya rumgume hannayensa yana kallona. Na dauke kaina na nufi gurin da Abokin Kareem yake a zatona Kareem din yana cikin motar ne. Na karasa gurin na tsaya na rumgume hannuna ina jin hawaye na bin fuskata.

“Noor..”

Na ji ya kira sunana, na kasa amsawa kuma na kasa daga kai na kalleshi.

“Noor magana ce na zo da ita kuma na ga baki cikin yanayin da zamu yi maganar, amman zaki iya komawa ciki zan dawo anjima”

Na girgiza masa kai domin na san komawa ta ciki zai iya zama laifi.

“Noor akwai wata matsala ne?”

Na yi shiru, sai ya gyara tsayuwarsa.

“Please ki shiga ciki zan dawo anjima”

Kamar ina jira sai na juya da sauri na dawo cikin gidan ina jin kamar ana turani. Ban karasa dakinmu ba juri ya dibeni na fadi a tsakar gidan sai ga Baba da gudu ya zo ya kamani.

“Baki ji ciwo ba dai ko?”

Na dubeshi ina mamakin haka ko wane uba yake ko kuma dai nawa ne a haka? Na daga mishi kai sannan na mike tsaye shi ya rika ni ya saka ni a dakinmu sannan ya kalli Hama dake zaune ido a kumbure ya ce.

“Ke yau baki zuwa makaranta ne?”

“Ina zuwa”

Ta amsa sannan ya fice ita kuma ta tashi ta fara shirin tafiya makaranta a lokacin da na san kamin ta isa ta yi latti sosai. A tare suka fice da Yaya aka bar ni kadai a gidan sai damuwata da kunci.
Baba ne ya sake dawowa dakin ya same ni a kwance.

“Noor Allah yasa ba wata maganar kika fadawa Alhajin nan ba, na ga yayi saurin tafiya kuma kin dawo cikin gida”

Na daga kai na kalleshi.

“Ba mu yi magana ba Baba, yace zai dawo anjima ne”

“Tom tom tom shikenan”

Ya juya ya fita daga dakin be fita gidan ba sai bayan sallah azahar, a haukace na dauki Koko da Hana ta siyo na sha saboda wani yunkuri na amai da nake saboda yunwa har ina jin numfashina kamar zai dauke. Daker na iya tattalawa na fita na yi alwala na dawo na yi sallar a zaune saboda ciwon da cikina yake yi. A gurin na zube ban sake motsawa ba sai da aka yi sallah la'asar, ita ma dai haka na yi ta cikin karfin hali, ina jin kadaici da kewa domin ni kadai ce gidan, ba mamaki Hana ta wuce gurin Mama domin ya isa ace ta dawo daga makaranta tun karfe 2pm, Yaya ma be dawo ba balle kuma Baba da be fita ba sai azahar.

Yammancin La'asar na ji an buga kofar gidan har sau biyu, ban fita ba ban kuma tambaye waye ba domin babu kuzari ko muryar aikata hakan a gareni yanzu. Har sai da yaron makota ya shigo ya ce wai ana sallama da Noor inji Kareem da abokinsa, shi ma dai ban amsa masa ba amman na tashi sanye da Hijabin dake jikina ina dukuduku na fita dakin na saka talkamina na isa zaune gidan, sai na tsaya daga cikin zauren har sai da na dan huta sannan na rike gambun karfen na leka waje. Kareem da ya bawa kofar gidanmu baya ya juyo ya kalleni. Abokinsa kuma dake zaune a motar da gambunta yake bude ya fito daga motar, sai na ja baya na koma cikin zaune na duka kana kallona ka san a wahale na ke.

“Noor...”

Cewar Kareem da ya fara shigowa zaure yana kallona, shi ma sai na duka daidai tsayina damuwar da tabbatar ta munafurci ce tana shimfide a fuskarsa.

“Noor...”

Ya sake kirana, muna hada ido sai na ji wani kuka mai karfi ya zo min a take na fasa kuka har ina sarkewa.

“Subhanallahi me ya faru Noor? Kin rame kuma kuka kike yi akwai wata matsala ne?”

Ni dai ban san ya aka yi mutumen da nake fushi da shi ya samu sa'ata ba har na bude baki ina fada masa damuwata.

“Baba ya saki Mama jiya, Hana tun da ta tafi makaranta bata dawo ba, Yaya be dawo ba, ni kadai aka bari a gidan, bana ina cin abinci jikina babu karfi kuma ina ganin jiri, Baba kuma yace ba zai aura min Zafeer ba, kuma Zafeer na san ba zai yafe min ba...”

Haka na jera masa komai tsab ina kuka sai ya matso kamar zai taba ni kuma ba taba din ba, sai ajiyar zuciya da ya sauke ya daga kai ya kalli abokinsa dake tsaye kamin ya sake dubana.

“Saboda ke ne Baba ya samu matsala da Mama? Yanzu ina Mama take?”

Na watsa masa wani mugun kallo ina jin kamar na shake wuyansa.

“Ban san a ina Mama ta tafi ba, kila gidansu gurin Yayarta saboda saki uku Baba yayi mata, amman duk saboda kai ne komai ya faru, kai ka lalata komai Kareem, kai ne kasa Baba ya juya ma Zafeer baya, kuma saboda kai aka saki Mama jiya, kuma ka saka aka kama Zafeer...”

Ya matsa baya da sauri ya mike tsaye ya juya zai fice daga zaure.

“Kareem...”

Na kira sunansa cikin kuka sai juyo ya kalleni.

“Na tsane ka...! Da na san haduwa ta da kai haka zai zame min matsala da ban yarda na hadu da kai ba, kai ba mutumen kirki ba ne, yanzu na gane me yasa matarka bata sonka, kai mai son kai ne i hate you...”

Murmushi na gani a fuskarsa a madadin bacin rai, yana kallona yace.

“Kin jahilci waye ni Noor, na zo miki a baibai ne, kuma ni ban shiga tsakaninki da masoyinki ba, ni bana shiga tsakanin masoya na san yadda abun yake, a gurin ma ni da nake babba balle kuma ke, da wannan nake miki addu'a ina rokon Allah idan aurenki da Zafeer din alheri ne, Allah ya tabbatar kuma ki fada masa ya zo ya same ni zan masa duk wani taimako da ya dace har ya aureki kuma saboda ke zan yi, domin rayuwarki abar tausayi ce...”

Ya juya ya fice ya daga zauren sai ya rage daga ni sai abokinsa, sai da na ji karar rufe mota sannan abokinsa ya kalleni ya ce.

“Noor be kamata ki yi haka ba, kin ga na daya dai Kareem ya girme ki, ba tsararki ba ne, na biyu kuma shi babban mutum ne fiye da yadda kike tsammani, be kamata ki rika fada masa magana anyhow ba, kuma abokina mutumen kirki ne, shiyasa be so zuwa nan ba saboda kina dora masa laifi ni na takura masa da zuwa nan din kuma kin ga ya fita ba cikin dadin rai ba”

“Ba ruwana na da mukaminsa ba ruwana da shekarunsa kawai dai bana sonsa karka sake zuwa da shi”

“Tom”

Ya amsa sannan shi ma ya fice sai kuma na fashe da sabon kuka.




KAREEM POV.

Ya ciro wayarsa ya lalabo Number Nabil ya kirashi.

“Hello ranka ya dade”

“Kana lafiya?”

“Lafiya kalau oga”

“Naje aiki yau?”

Ya dan yi shiru for seconds sannan ya ce.

“Aa ranka ya dade shekaranjiya nan Noor ta dauki wayata ta kiraka ta yi maka rashin mutunci ban sani ba, sai da na dawo Mama take fada min abun da ya faru, na yi tunanin ko akwai wata matsala ne ko ka yi fushi”

Kareem ya shafa fuskarsa.

“Ina tunanin ko ku da kuke yan'uwanta ba ku fini sanin halin Noor ba a yanzu, ita ma ai ba laifi ta yi ba balle har ya shafe ka, ka cigaba da zuwa aiki, yanzu kana ina?”

“Ina gurin abokaina”

“Noor din tana lafiya?”

“Ban sani ba na fito tun safe ban koma ba”

“Toh ka koma ka dubata sai ka dawo gurin aiki”

“Toh ranka ya dade Allah ya saka da alheri”

“Ka rika mata wani abu kamin ka shiga gidan, ba mamaki ma kila bata ci komai ba”

“Toh ranka ya dade Allah ya kara sutura”

Kareem ya sauke wayar ba tare da ya amsa ba, kuma ba tare da ya kalli Hafiz ba ya ce.

“Yaron nan ma yana karatu wai? Ni na manta kamar ya taba fada min yana yi ne ko be yi na manta dai, amman ya kamata ace yana yi saboda rayuwar gidansu abar tausayi ce musamman mahaifiyar da kuma kanensa”

Hafiz ya rage gudun motar ya faka gefe ya kalli Kareem.

“Me yasa ka kira shi?”

Da mamaki Kareem din ma ya kalleshi.

“Baka ga halin da muka baro yar ficikar yarinyar nan ba kuma ita kadai cikin gida? Idan tana bukatar wani abu ai zata fada masa kuma zai dubata ko?”

Hafiz yayi murmushi.

“Ko yargwangwani ce ka damu da yarinyar nan Kareem, da na same ka a office na fada maka Noor tana cikin damuwa kuma tana bukatar ganinka office din ka bari ka shigo motata ka biyo ka dubata a yanzu, kuma Wallahi dazun na tambayi yarinyar akwai wani matsala ne bata min magana ba amman kai tana ganinka sai ta fashe da kuka ta bude maka cikinta”

Kareem yaja tsaki.

“Kai dai baka da zuciya Wallahi, ni ban yi zaton zaka sake min maganar yarinyar nan ba, yanzu gashi kasa na zo na ji bakar magana kawai kuma a gabanka ta nanata wadda take so”

Hafiz ya sauke numfashi.

“Ni ma kaina ban yi zaton zan sake maka maganar ba, amman zuwana dazun da niyar na fadawa mahaifinta gaskiyar cewar ba sonta kake ba sai ya tare ni da wani labari na dabam wai Noor ta fada masa tana so na”

Kareem ya kalleshi ya sake kallonsa ya kasa cewa komai.

“Abun da ban gama gamsuwa a yanzu shi ne, ita Noor din da gaske ta fadi hakan ko kuma dai mahaifinta ne ya fada saboda wani tunani nasa na dabam?”

Kareem ya dantse hakwaransa yana magana da karfi

“Ko dai minene kai ka janyo Hafiz... Mahaifinta be yi tunanin rabata da wadda take so sai da ka shiga rayuwar yarinyar nan, kuma yanzu kana jin yadda iyayenta suka rabo duk saboda kai ne”

“You're just blaming me Kareem, ni fa duk abun da nake yi saboda kai nake yi, bana jindadin yadda kake mu'alama da Safeena, kuma bana jindadin irin zamantakewar auren da kake yi, ina kokarin ganin ka samu farinciki ne ka koma kamar yadda kake a da, ina hango maka farinciki a auren yarinyar nan ita ma kuma ina hango nata farincikin a tare da kai, ubanta be tantance waye mai sonta ba kawai ya fada min tana so na kuma ni na san abu ne mai wahala Noor ta amsa haka, idan mu mutanen banza ne haka zai dauki yarinyar ya ba mu fa, baka kula da yanayinsa ba? Yarinyar nan abar tausayi ce matuka”

“Ni rayuwata ba abar tausayi ba ce? Na auri wadda bata so na yanzu kuma na sake auren wadda bata so na? Mahaukacin ina ne kai?”

“Akwai banbanci, Yusura baka sonta bata sonka, amman ita Noor kana sonta kuma ita zaka iya koya mata sonka cikin sauki, shi wadda take ikirarin tana sonsa hauka kawai take, wannan yaron ba zai iya rike ta ba, baka ga yadda yake mana hauka ba? Sabo ne kawai yake wahalar da ita kai ma tana sabowa da kai zata manta da shi, kuma ni a abun na lura halin da ake ciki a yanzu idan baka aureta ba mahaifinta ba zai bari ta auri yaron ba, kuma ba zai barta ta samu salama ba, saboda kwadayaye ne”

Kareem ya daga masa hannu.

“Hafiz ba zan auri yarinyar nan ba, idan kana tausayinta ko kana tunanin rayuwarta kai ka aureta mana sai ka koya mata sonka ba kace abu ne mai sauki ba, to ka gwada mana, kai ma ai kana bukatar kara aure matarka daya kuma kullum aiki take zuwa bata zama gida, kana bukatar mai kula maka da yara”

Hafiz ya nuna kansa.

“Ni kake fadawa haka Kareem?”

“Akwai illa a fada maka haka ne?”

Hafiz yayi murmushi.

“Tunanin kake kamar cutar da zan yi saboda ina kokarin ganin abubuwanka sun saitu? Zan baka mamaki kuma sai ka yi nadamar wannan maganar da ka fada min, and I'm sure you Wallahi Tsumma Tallahi sai na AURI NOOR, daman ka ce ni na bata komai to zan gyara”

Hafiz ya danna burgi ya ja motar da karfi ya fara tuki, Kareem be sake ce masa komai ba shi ma kuma be sake cewa Kareem din komai ba har ya isa gidansa ya faka a harabar gidan, Kareem ya bude motar ya fita Hafiz kuma yayi reverse ya juya ya fice daga gidan.

Kareem be samu Yusura a gidan ba amman ya samu note a center table rubuce cewar ta tafi dubiya tare da yara. A gurin ya zauna ya rike kansa yana jin kamar kan yana ciwo kuma kamar ba ciwon ba, ya rasa me ke masa dadi. Kamin ya mike tsaye ya nufi upstairs. Yana shiga dakinsa ya ciro wayarsa ya kira mahaifiyarsa da liyinta na waje, ya kuma yi sa'a wayar tana hannunta domin ba ko da yaushe take daukar waya ba.

“Sallamu Alaikum”

“Wa'alaikusalam Momma na kina lafiya?”

“Alhamdullahi ya gidan ya yaran?”

“Kowa lafiya kalau Momy ban da danki”

“Subhanallahi me ya samu ďana nawa?”

“Momy baki kusa kuma kin san babu mai yi ma Kareem gata sai ke, na yi marmarinki Momy”

“Babban mai maka gata shi ne Allah wadda ko bana raye zai kula da kai, kuma yana nan kusa da kai, ni na zo a ta biyu ne idan kuma bana kusa matarka Yusura tana nan dan haka kana da gata ta ko'ina”

Ya sauke ajiyar zuciya.

“Momy yaushe zaki dawo? Ina tunanin daukar hutu na zo na dubaki ko na sati ne”

“Aa cikin satin nan zamu dawo da yardar Allah, jiki yayi sauki sosai matarka ma ta matsa na dawo zamu dawo babu jimawa”

Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba.

“Amman jikin yayi sauki ko?”

“Sosai sai ka yi mamaki idan ka gani”

“Alhamdullahi haka nake so, zan kira ki video call anjima”

“Na turawa matarka video ai tana ta murna ta ga jikina yayi kyau, ta ji dadi bata nuna maka ba”

Samun kasa yayi da kasa amsawa har na dakika biyar.

“Ta fada min, amman ta manta bata nuna min video ba”

“Ta manta kam, Yusura yarinya ce mai kirki Kareem, ka rike ta amana dan Allah yarinyar nan bata da uwa bata da uba sai ni, sai kuma kai da kake matsayin mijinta a yanzu, tana so na tana girmamani kuma tana da hankali da natsuwa, abu ne mai wahala a samu mace kamarta a wannan zamani, ba zaka gane hakan sai ranar da ka kara aure ko ka rabu da ita bana fatan hakan amman duk ranar da ka rasa Yusura ka rasa mata ta gari”

“Haka ne, ai na fi kowa sanin halinta Momy”

“Na san kai ma kana da hakuri amman dai ta fika gashi tun da aka yi aurenku ba a taba jin kanku ba, hakan yana saka ni farinciki kuma yana kwantar min da hankali”

“Hankalinki zai cigaba da kwanciya har abada Momy indai aurena da Yusura ne ba zaki taba jin wata matsala ba har abada”

“Allah ya muku albarka ya raya abun da kuka samu”

“Ameen Momy Allah ya kara miki lafiya kuma ya dawo da ke lafiya”

“Ameen Ameen”

Yayi mata sallama ya sauke wayar, ya dade zaune a dakin sannan ya fito ya sauko kasa dinning ya nufa ya bude abincin dake gurin kamshin ya daki hancinsa

18 / 72