Author : 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category : Romance
fa, shi ne kawai ya nace sai ya ce wai zai gwada sa'arsa”
“Bana son na ji ya kara zuwa kofar gidanku nemanki, please ki fada masa kina da wanda zaki aura kuma baya son kina kula kowa”
“Okay zan fada masa, amman ka sake fuskarka Kareem ka bata rai”
Na fada a shagwabe kamar zan masa kuka.
“Any thing for my heart beat”
Ya sake fuskar yayi murmushi tare da sumbantar screen din wayar ya shafa shi yana kallona. Mun sha hira sosai irin ta masoya haka muke a kullum baya gajiya da kira bana gajiya da amsawa kamar kar ya bar kasar nan wani irin shakuwa ya shiga tsakaninmu idan ya kir har bana son ya yanke kiran shi ma kamar zai dauke ni ya cinye haka yake min.
Daf da zamu yi sallama ya fada min gobe za a shiga da shi aiki, na ji hankalina ya tashi sosai domin ya damu da ciwo wata kila ya wuce yadda nake gani ko tsammanin ma.
“Na so na ganki Noor kika ki zuwa mu yi bankwana tun ranar ban sake sakaki ido ba and you know how much i love you”
“A matsayina na wa zan tafi? Iyayenka ba su san alakarmu ba, ko da ma sun sani ai da kunya ace ina tafiya ganinka”
“Sun sani mana, baki ga mahaifina ba? Kanena ma sun sani duk wanda ke gidanmu yanzu ya sani”
“Yanzu dai Allah ya baka Lafiya ya dawo da kai lafiya kuma ya sa ayi aikin cikin nasara”
“Ameen ki kula min da kanki please, bana son mazan nan dake kawo miki hari, kin ga ko Ustan din nan ya sake zuwa bayan ganin da na masa ya sauke ki a mota, Noor bana son kina kula kowa, ki rika daukarkanki kamar an daura mana aure”
“I will”
Ya sakar min ido sosai yana kallona.
“Aaryam zai zo ya kawo miki atm ko da zaki bukaci wani abu, bana son ki ji cewar kin rasa wani abu a lokacin da kike tare da ni”
“Bana fa bukatar komai Kareem ba sai ya kawo min ba”
“Ba ki bukata Alhaji Sule yake kawo miki leda kina karba?”
Na zaro ido na juya na kalli gurin d ledar take baya ganinta amman ta ina ga ya ledar har yake fadar haka? Ko dai ya chanka ne kawai, amman fa dazun ya furta cewar Ustas din nan ya zo ta ina ya sani domin ban fada masa ba, amman na san Kareem da wayo wata kila yana son kure ni ne.
“Ni baya kawo min leda”
“Hmmm na dai fada min kar na sake ganinsa a gurinki”
“Gashin shi kake yi daman?”
“Makaho ne ni? Ina nan amman duk wani motsinki idona yana kanki, idan kuma ke kika makantar da ni sai na ji”
Na kyakkyale da dariya sosai har da tintsirawa. A lokacin da na dago sai na ga kallona yake da murmushinsa mai kyau.
“That's my girl, that's the real Noor i know i love you Babe”
Na rufe idona ina jin kunya. Shigowar Mama ne ya saka na yi masa sallama na aje wayar.
“Wannan kuma minene?”
“Wa.. Wannan ne Alhaji nan da yayi muku gaisuwa ya kawo min yau”
Mama ta duka ta dauki kudin ta duba.
“Noor ina ta jan kunnenki, ki dai ba zaki taba hankali ba? Ga mugun kwadayi ki yi ta zubar da kanki mutunci a gurin maza? A tunanin tara maza wannan ya so gobe wani ya so shi ne soyayya?”
“Aa”
Na amsa a sanyaye sai ta nufi gurin ajiyarta ta aje kudin kayan zakin kam ko kallonsu bata yi ba ta sake ficewa.
Bayan sallah la'asar Alhaji Sule ya sake kiran wayata yana karyar da murya da marairaice gwanin shaushi.
“Uhm uhm ni baki kira ni kin ji ko na sauka Lafiya ba, ni na yi fushi zan yi kuka...”
Na yatsina fuska ina jin kamar na buga masa robar ice cream din da ya kawo min dan haushi.
“Me yasa kake magana haka kamar yaro?”
Yayi dariya.
“Soyayya ai bata san yaro ba bata san tsoho ba, soyyayya ce kawai domin na lura har yanzu akwai sauran kurciya a tare da ke Babe na”
Wani amai na zo ya min da ya kirani da Babe.
“Wane irin Baby kuma dan Allah ka daina ni fa na san ba aurena zaka yi ba, kana yara kamar ni da wadanda suka girme ni ma to ta ina zaka aure ni, kuma matanka hudu fa haba”
Shiru yayi na lokaci jin na harbo jirginsa, can kuma ya dan yi murmushi kadan.
“A ina wannan maganar ta fito Khadija?”
“Kasan abun duniya baya boyuwa”
“Haka ne, amman dole akwai wanda ya fada miki haka, ko kuma dai gidanku an yi bincike akaina ne?”
“Aa ai maganar bata kai gurin iyaye ba balle su yi bincike, ina gida aka fada min yanzu ina son ka amsa min maganar haka ne ko ba haka ba?”
“Ba gaskiya ba ne, matana uku ke nake fatan ki zama ta hudu”
“Gaskiya ta gun da na ji ba zan za a maka karya ba, domin wanda ya fada min ya Sanka sosai”
“Ko dai wani ne yake son shiga tsakaninmu? Fada min mana yan mata na waya fada miki wannan maganar? Wa yake min wannan sheri haka da tsakar rana?”
“Aisha...”
Na fada kai tsaye ba tare da tunanin komai ba, kuma na yi hakan ne da nufin ya san ta majiya mai karfi na ji kuma ya san alakata da yarsa.
“Wace Aisha?”
“Aisha yarka matar Magaryi Hafiz”
“Ina kika san Aisha?”
“Saboda mun auri miji daya ni da ita, ni ce amaryar da Hafiz ya aura kamin ya rasu”
“Ahhhhhh.... Ikon Allah da gaske”
“Ka tambaye ta ka ji ta san Noor zata fada maka?”
“Amman ke kin san ni mahaifin Aisha ne daman?”
“Na sani yanzu saboda ta fada min, har abun da ban sani ba”
“Khadija kar dai ace yarinyar ta zo ta miki cin mutunci ne”
“Hmmmm sai anjima, ni dai na fada maka daman ina da wanda zan aura, Allah ya baka wata”
Na kashe wayar ba tare da na saurari abun da zai sake fada ba, kamar zai haukace haka ya fara kiran wayata na ki na daga daga karshe ma sai na saka shi a blacklist.
Bayan saukowa daga salla magariba yaro ya shigo kirana, a lokacin ina daga kwance ina chatting da Kareem domin babu damar yin video Mama tana dakin.
“Je ka ce waye”
“Mama ki ce kawai bana nan ba zai wuce Ustazun nan ba ya zo yayi ta takura min, kuma ai kin ce na daina tsayuwa da maza barkatai, ni da na sani ma ba zan fada masa kofar gidan nan ba”
“Ai kya bari mu ji ko waye ko? Ke kin fi son maza yan duniya ko? Su sauran da suke kiranki a waya suna zuwa fada min kike ne?”
Na yi shiru na cigaba da chatting din da nake ina murmushi, fada min yake irin rayuwar da zamu idan muka yi aure.
“Wai ya ce Zafeer ne...”
Na dauke kaina daga screen din wayar na kalli Mama dake kallona.
“Zafeer kuma? Tohm...”
Mama ta fada ni kuma sai na ce.
“Me zan masa?”
“Ai sai ki je ki ko? Ki san dai Zafeer ya wuce wulakanci a gurinki, duk mutumen da zai so ka farko kuma ya sake dawowa ba karamin masoyinka ba ne”
“Ba fa so nake ba Mama! Abu ne mai wahala Zafeer ya so ni yanzu, bayan duk abun da ya faru”
“Ba sonki yake ba zai yi ta zuwa kofar gidanku ne? Ke ni bana son shashanci tashi ko tafi”
Na aje wayar na dauki hijab dina na saka na fita da tunanin kalaman Mama, ni kam a nawa haukar da tunanin Zafeer ba zai sake kula mai irin sunana ba balle kuma ni fin kaina. Ashe na yi kuskure fahimta domin shi yana nufin maida hannu a miya ba. Ban tabbatar da sai bayan na gama kwance masa ciki na labarta masa halin da na tsinci kaina a duka auren da na yi, yayi min tambayoyi da dama kuma na amsa masa da gaskiya babu boye komai.
“Mutum kamar Abdull be kamata ace yana aiki a kamfanin nan ba ”
“Ba lallai ne su sani ba ai, ni ma da be aikata hakan ba ba zan sani ba”
“Haka ne, amman za su sani yanzu kamfanin na mahaifin Matata ne, ni da na taba aiki da shi a Lagos din na ga halinsa, yana shigewa mata sosai shiyasa na raya cewar ba zaki iya zama da shi ba, ko ba shi ba ma Noor babu wanda zai iya rike ki sai ni”
Na daga ido na kalleshi sai kuma na sauke kai a sanyeyye. Ya gyara tsayuwarsa yana sauke numfashi.
“Noor na zo nan ne, saboda wani abu mai muhimmanci”
“Wani abun ne ya faru?”
“Babu abun da ya faru, a yanzu dai nake fatan faruwarsa tsakanina da ke, hausawa suka ce fa tsohuwar zuma ake magani kuma na yarda, domin na yi yadda zan yi na ga baki fili ki yi iya wasanki, amman na kasa saboda akwai wani abun da Allah yake nufin shiryawa a tsakaninmu, na so ki da farko na yi iya yadda zan iya na ganin na aureki amman ya gagara, amman har yau har gobe bana son kowa yadda nake son ki Noor, na ce zan jira kuma na jira, ina tunanin lokaci yayi da ya kamata ace mun zama ma'aurata ni da ke, burin da muka kasa cin ma a baya wata kila zamu iya cin masa a yanzu, a tsawon lokacin nan ina ta kallon tafiyar rayuwarki ne Noor babu wanda zai fahimce ki ko ya zauna da ke a yadda zan iya, daga Kareem din da yayi kokarin raba ni da ke, har zuwa wanda duk zai ganki ya aureki babu mai iya zama da ke sai ni Noor”
Yana maganar jikina ya fara shocking hawaye suka cika idona, ashe ina da kima da daraja a gurin Zafeer har haka? Ashe soyayyata ta kai ya sake dawowa neman aurena duk bayan abun da ya faru?
“Baby Noor...”
Na daga na kalleshi ta cikin hasken farin wata.
“Shim zaki iya aurena a yanzu? A yanzu na shirya ko gobe za a iya daura mana aure, zaki aure ni?”
Kallonsa nake hawaye na sauko min.
“Ko kuma dai har yanzu wani ya rigani? A yanzu din ma wani zai min kutse kamar yadda aka min a baya? bayan na gina soyayyata? Har yanzu kina jin ba zan iya kula da ke ba Noor? Ina da kudi enough zan baki duk wani jindadi da kuma rayuwar da kike mafarki. Shin zaki aure ni?”
Na girgiza masa kai na yi baya baya.
“Aa aa ba zan iya ba...”
Na juya na shige gida ina hawaye a kofar dakin Mama na tsaya na dafe zuciyata har sai da na samu sa'ida sannan na shiga dakin ba tare da na share hawayen ba. Kan karamar kujerar da nake kwance a dazun na zauna.
“Lafiya?”
Ta dauki fitilarta ta haska fuskata.
“Ba komai kike kuka?”
Ban ce mata uffan ba na sakw fita dakin na yi alwala na dawo na gabatar da sallah Isha'i da aka gama tun 8:10pm, sannan na janyo wayata, ashe ban fita daga chatting din da nake da Kareem ba, hoton tsayuwata da Zafeer na gani fitar da na yi dazun nan da magariba.
“Zan sake rasaki a karo na uku Noor, na sani indai Zafeer zai dawo ba zaki yarda ki aure ni ba”
Shi ne sakon dake biye da hoton.
“Ba zan aure shi ba Kareem ba zan iya aurenshi ba”
Na rubuta masa a matsayin amsa ashe har a fili na fada, ban hakara ba sai da Mama ta taba ni.
“Ke mi ya faru?”
Na aje wayar na fuskanceta.
“Mama Zafeer sake dawowa wai yana son ya aure ni”
Fuskar mamaki Mama ta yi ta zauna kan kujerar dake kusa da ni tana kallona ba tare da tace komai ba.
“Me yasa kika ce ba zaki iya aurensa ba? Saboda Kareem?”
Na kalleta na yi zaton zata fahimci abun da na fahimta ne kamar ni, ashe fahimtarmu ta sha banban.
“Mama idan na yarda na aure shi a yanzu, zaman ba zai mana dadi ba, saboda zai rika kallona a matsayin macen da ta guje shi a lokacin da yake cikin talauci yanzu kuma na aure shi saboda yayi kudi, wannan uzurin Zafeer ya kasa yi min shi ko a can dama, ganin yake saboda ba shi da kudi na guje masa”
“Toh ai ba karya ba ne, na sani da yana da kudi mahaifinki ba zai zabi Hafiz ya bar shi ba, bayan tsawon shekarun da kuka yi a tare”
“Amman shi be fahimta ba, saboda Baba ya hana na yi masa magana ban fahimtar da shi”
“Sai ki fahimtar da shi yanzu mana, Noor karki zama shashasha mana, yaron ya so ki kuma na san kina son shi, saboda rashin aurensa mahaifinki ya sake ni, babu irin yakin da ba mu yi ba ni da ke na ganin auren ya tabbata amman hakan be samu ba, yanzu kuma bayan aure biyu ya dawo yana son ya aure ki ki amsa da cewar ba zaki iya aurensa ba, anya ba ki ji kunya ba?”
“Ji nake kamar...”
“Kamar me? Ki rika yi ma kanki fatan alheri, ni dai na san kina son Zafeer kuma ina da tabbacin zai rike ki amana sosai, domin yaro ne mai kirki kuma mai tsananin sonki, kuma mun san iyayensa tarbiyarsa da komai ba mu da haufi a kai, ba ina son ki aure shi saboda yana da kudi ba, aa sai dan ina hango miki jindadi irin na mai hankali d sanin ya kamata”
Na sauke idona kasa hawaye nake for no reason.
“Ni dai idan har zaki yarda da ni da kuma abun da nake so, to ki auri Zafeer”
“Mama Kareem...”
“Kina son Zafeer yadda kike son k
Kareem?”
Na girgiza kai ko kadan ba za a hada soyayyar da nake yi ma Zafeer da wadda nake yi ma Kareem ba.
“Ko kuma kina da tabbacin Kareem din zai rike ki amana? Bana fatan ki sake aure ki fito Noor, shi ma Kareem din ba natsentse ba ne, kina masa kallon mutumen kirki ne kawai amman ba haka yake a zuciyarsa ba, domin mutumen kirki ba zai yi tarayya da matar aure ba har ta kai ga haihuwa, shiyasa kullum yana shiga cikin lamarin gidanmu yana kyautata mana, na yi zaton sonki yake da farko, amman bayan aurenki na farko da na biyu na gane so yake ya bata miki lokaci ko rayuwa”
Na kalli Mama da sauri ina mamakin a gurin da ta ji wannan maganar.
“Mama a ina kika ji wannan? Kazafi ake masa Kareem mutumen kirki ne”
Na yi hanzarin dora ginin da zai tare zubewar mutuncin Kareem a idon Mama, na san duk abun da ta ji ko aka fada masa a kansa gaskiya, but i know yana da kirki kuma ya fahimci kuskurensa, ba zan taba iya tona masa asiri ba, ba zan iya kara masa bakinciki bayan wanda yake ciki ba, mutumcinsa yana da muhimmanci a gurin Iyayensa kanensa da Yayansa.
“Ke yarinya ce Noor baki san komai akan rayuwar duniya da mutanen cikinta ba, har yanzu baki gama wayewa ba, baki da zurfin tunani da fahimtar rayuwa”
“Waya fada miki wannan Mama?”
“Safeena, kishiyarki kuma abokiyar shedancinsa, har hotunansu ta nuna min wani gurin tana kwance a jikinsa, ita ma yaudararta yayi kamar yadda yake son ya yaudareki, abu ne da kika sani, domin ta fada min kin fadawa mijinta ďan da ta haifa yanzu ba jininsa ba ne kuma mijinta yayi bincike ya gane gaskiyar hakan har ya dauke kafarsa daga gidan yanzu hana tace kayanta a hade suke domin ta san zai iya bata takardar saki a duk lokacin da ya tashi”
Na hade yawu da karfi na sauke kaina kasa a yanzu kam ba ni da wani kuzarin furta wani abu, amman yaushe Safeena ta zo nan? Yaushe ta fadawa Mama haka.? Kamar Mama ta san abun da nake tunani sai na ji ta ce
“Ranar da kika tafi ganinsa Asibiti ita ma ta fito asibitin daga ganinsa ba, ta fada min ta ganki, saboda haka ki kwantar da hankalinki ki daina biyewa Kareem ko da ba aure ba ni bana son alakarku, idan har Zafeer da gaske yake ko kuma mutanen da suke zuwa zance gurinki da gaske suke kawai su fito ayi auren a huta, ki samu gurin da kika zauna kowa ya samu kwanciyar hankali”
“Tohm Mama”
Babu wani abun da zan iya fada, kalamaina ba su isa su kare aikin da Kareem ya aikata ba, da ace be kusanci Zina ba tun farko da abubuwa ba zu masa a haka ba. Na sani idan Mama ta san na amsa masa cewar zan rike yaron da suka haifa ma zai kara sakawa ta tsani Kareem din ko ta rufe ni da duka ma. But deep down i feel something about ina jin tausayinsa fiye da yadda na ji tausayin kaina a lokacin da aka raba ni da Zafeer.
Tun a wannan daren na san ba zan auri Kareem ba domin Mama bata yi maraba da shi ba, kuma tana da gaskiya kowa yana son suruki na gari, kowa yana fatan yarsa ta yi aure a inda za'aji dadi babu fargaba. Na raye daren da sallah da kuma rokon Allah ya bawa Kareem lafiya, ina jin kamar ba zan iya rama masa abun da yayi min ba a ko'ina sai ta nan. Washe gari misalin karfe takwas Aisha ta fado family house din su Mama da zan iya kira da gidanmu a yanzu, ita da kanenta biyu da wata macen da ban san ta ba.
Bangaren mu aka kawota har kofar dakinmu domin ta fada musu ni take nema, ko ya aka yi ta gane gidanmu ma oho, ni dai na sha mamakin ganinta har na rasa taya zan tarbiya, duk kuwa da na san ba lallai ne alheri ya kawo ta ba, bayan abun da na fadawa mahaifinta ta aikata akan karya. Dan haka ban yi gaggawar yi mata maraba ba na daga kai kawai ina kallonta kamar wadda bata wayeta ba. Mama dake hada tea ta mike tsaye ta fito daga dakin tana kallonsu.
“Toh Allah yasa Lafiya”
“Lafiya amman ba kalau ba”
Kanwar ta amsa, Aisha kuma ta juyo ta kalli Saitin da nake zaune tana cin magani ta ce
“Noor ashe wuyanki yayi kauri, ashe kin zama tantiyar yar bariki