Author : 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category : Romance
zai iya shiga tsakanina da kai, babu wani laifi da zaka aikata a duniyar da zai saka na juya maka baya”
Magana nake masa a zuciyata amman a zahiri na kasa furta komai sai kallonsa nake.
“Noor...”
Ya sake kiran sunana muryarsa a sanyaye, nan din ma ban amsa ba sai ma kauce da nake kokarin yi daga gabansa na cigaba da tafiyata.
“Baby Noor Noor yau ni nake miki magana kina tafiya? Ina kiranki kin ki amsa min? Me yake faruwa? Fushi kika yi? Saboda na ce ba ni halin aurenki a yanzu? Zan aureki Noor ko ta halin Yaya na miki alkawari hakan yayi miki?”
Nan ma ban juyo ba shi kuma be fasa bin bayana yana bayyana min kalaman da suke kara tsuma zuciyata ba.
“Noor please, ina binki a baya kina tafiya kamar wani bakonki miye haka?.... Nooorr!”
Daga karshe ya kira sunana a tsawace har sai da na tsaya cak daga tafiyar da nake.
“Ko dai mutumen nan ne ya fada miki wani abu a kaina? Ko kuma Baba ya fada miki wani abun ne dabam da ba shi na fada ba, me yasa kike min haka? Why?”
Na hade yawu na cigaba da tafiya da sauri na barshi a gurin tsaye, ina shiga gidan na samu Mama sanye da hijab ta nufo kofar fita.
“Alhamdullahi, daman bayanki zan bi saboda na san halinki zaki iya satar kafa ki tafi gurin Zafeer din nan”
Ni dai ban ce komai na nufi dakinmu na kwanta ina ta gurzar kuka kamar babu gobe. A haka Hana ta dawo daga makaranta ta same ni har na yi rama tsabar kuka da tashin hankalin da na samu kaina a ciki.
“Noor dan Allah ki ba kanki lafiya, ki yi ta addu'a idan Zafeer mijinki ne zai aureki babu wadda ya isa ya hana”
A nan na samu damar amsa mata da toh sannan na tashi zaune ina kallon kunun da ya aje min tun safe.
“Baki sha kunun ba?”
“Ba zan iya cin komai ba, Hana”
Na kira sunanta sai ta amsa min ta duko.
“Dan Allah ki roka min Baba yayi hakuri Zafeer yace zai nemo kudi nan da wata uku zai aureni, ki ce yayi hakuri ya bar ni na yi magana da shi, hukuncin yayi min tsauri...”
“A ina kika ga Zafeer din?”
“Dazun da Mama tace na kai kudin adashe...”
“Amman dai ke kam Noor baki jin magan yanzu duk bayan gargadin da Baba yayi miki yace miki be yafe ba idan kika sake magana da Zafeer sai da kika yi? Kin san abun da tsinuwar iyaye take nufi kuwa...”
Na girgiza mata kai da sauri.
“Ban yi magana da shi ba, shi ne yake bibiyata yana fada min haka, ransa ya bace da ban yi magana da shi ba, ni ma na ji kamar na mutu saboda yayi min magana ban amsa masa ba, Hana babu dadi dan Allah ku yi magana da Baba ko zai ji, ni na san haushina yake ji amman ke zai iya saurarenki saboda ya san kina da hankali”
“Aa Mama ma bana jin zata iya tunkararsa da wannan maganar balle kuma ni, indai ba son kike ya tsine min albarka ba ni ma, ki dai ta addu'a ni ma zan taya ki”
“Na gode”
Na fada mata sannan na tashi kamar yakusasshen lawashi na fita daga dakin, alwala na yi na dawo dakin na yi sallah azahar na yi ta addu'a. Misalin karfe hudu na yamma Yaya Nabil ya shigo gidan da ledarsa kamar yadda ya saba, ko da an yi girki balle yau da ba a girka komai a gidan ba. Awaje ya zauna gurin da Mama take zaune domin kusa da kofar dakinmu ne, ina jinsa yana ta fada da alama ransa a bace yake ban fuskanci me yake magana akai ba, amman na ji sunan Zafeer da Oga Kareem kuma na ji zancen yan sanda. Hakan ya saka na mike tsaye ina jin jiri na taka na isa kofar na rike kofar na tsaya ina kallonsa.
“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un abu be yi dadi ba, yaushe wai?”
Na ji mama ta fada sai Yaya yace.
“Yanzu nan ba a dade ba Wallahi, kuma duk Baba ne sila, shi ai yana da gaskiya ko nine zan aikata fiye da haka, me yasa Baba zai yi halin karanta miye amfanin haka? Fisabillilahi haka ake yi, ni gaba daya bana jindadin yadda Baba yake tafiyar da rayuwar gidan nan, ban taba ganin uba irin na mu ba”
Mama ta juyo ta kalleni sai ta miko min hannu.
“Zo nan ki zauna”
Na isa kusa da ita na zauna sai ta saka ni a jikinta ta rumgume ni.
“Wai an kama Zafeer”
Na daga kai da sauri na kalleta.
“Me yayi?”
“Wai ya tafi gurin aikin Ogansu Yayanki yayi masa cin mutunci a cikin mutane shi ne shi kuma ya saka aka kama shi yana can rufe”
Na fashe da kuka ina jin kamar na tashi na tafi amman babu dama. Yaya ya kalleni a tausaye ya ce.
“Ni na rasa gane wane irin kalar uba Allah ya ba mu, gaba daya babu ruwansa da damuwarmu, yanzu mutumen ko auri Noor Wallahi ba zai ga mutuncinta ba saboda ya san yadda aka yi ya aureta...”
“Jarabawa ce ta rayuwa, sai hakuri Nabil duk yadda zaku ji be kai yadda ni nake ji ba, ku ai ubanku ne ni ko mijina ne, duk jarabawar da za'ayi mace ko yaya ko wace iri ce mai sauki ce idan ba a gidan aurenta ba ne, idan mace tana shan wahalar rayuwa akan ce idan kika yi aure kin huta, amman idan ta tararda kaddarar a gidan aure, to wannan ita ce jarabawa mai girma, domin shi aure yana nufin rayuwa ne ko mutuwa, babu yadda zaka yi, duk yadda kuke jin bakincikin ubanku be kai yadda ni nake ji ba, yara biyu na rasa kamin na haife ku, shekara shirin da uku da aure babu ranar da bana kwana da bakincikin ubanku”
Ta karashe zancen cikin kuka Ya Nabil ya sauke kansa kasa rai a bace nikam kuka kawai nake ina jin bana da makiyi a duniyar kamar Kareem, sai kuma mahaifina da nake jin na tsane shi a yanzu. Na dago daga jikin Mama na kalli Ya Nabil
“Yaya dan Allah ko zaka kira min Kareem a wayarka na yi magana da shi please? Dan Allah?”
“Me zaki ce masa?”
“Magana kawai zan yi da shi dan Allah Yaya, kar yaje yayi ma Zafeer wani abu dan Allah Yaya”
Rokonsa nake da muryar kuka hawaye na min zuba, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya kama number sai da ya kira sannan ya mika min. Ni kuma na karba na mike tsaye na shiga dakinmu.
“Assalamu Alaikum”
Ban amsa sallamar ba na yi shiru kamar wadda ta rasa abun cewa. Hakan sai ya fahimtar da shi ni ce a waya ba Yayana ba.
“Noor me ya faru...?”
“Komai ma ya faru Kareem, na yi dana sanin saninka a rayuwata, sanadinka Baba ya raba ni da Zafeer ni shi kadai nake so ba zan taba son kowa ba, saboda me zaka kama shi?”
“Ba a fada miki abun da yayi ba? Planning ma fa nake na yadda zan taimaka masa ya aureki, tun jiya da na fahimci abun da Babanki yake kokarin aikatawa, amman sai gashi yau a restaurant a gaban jama'a yana ci min mutunci yana kira da sunaye kala kala, shiyasa ai na rufe shi sai yayi hankali tukuna”
“Kana takama da kudi ne kawai Kareem, shiyasa ka siye Babana kuma yanzu ka kulle saurayina, to ni ba zan siyu ba, ba zan taba sonka ba, kuma na tsane ka da na san bakincikin da zaka haifar min kenan ba zan yarda ko magana ta shiga tsakanina da kai ba...Ka sake shi Wallahi saboda ka ga shi ba shi da kudi ka yi masa haka...”
Ban gama fadar Abun da nake son fada ba Yaya ya fisge wayar ya kashe.
“Shi ke nan na rasa aikina...”
KAREEM POV.
Sai da kiran ya katse sannan ya kalli Hafiz dake zaune a gabansa.
“Ka ji da kunnenka ko? Shiyasa na saka hands-free ai saboda ka ji”
Hafiz ya dauke idonsa daga wayar ta Kareem dake aje a kan teburin ya kalli Kareem.
“Kurciya ce fa kawai take damun yarinyar nan, ai kai baka fito ka fada mata cewar kana sonta ba ko? In ba shi ba miye na wani kiranka ta fada maka magana haka? Wallahi bata da wayo”
“Ko ma dai minene yanzu ta fadi mind dinta, tun farko na fada maka yaron nan take so, ko na rasa matar aure a duniya ba zan taba auren matar da bata so na ba, kuma ba zan yarda na shiga tsakanin masoya ba, so ka sake tunani Hafiz ka je ka gyara lamarin yarinyar da saurayinta kuma ka nunawa mahaifinta gaskiya, karka cutar da ita ka cutar da saurayinta”
“Amman baka ga abun da ya zo mana ba dazun nan”
“Abun da yayi be kyauta ba, abu ne da kowa ya sani, shiyasa har na saka aka kama shi, kuma yanzu za a sake shi, amman kokarin ganin ka shiga tsakaninsa da Noor daukar alhaki ne, indai saboda ni kake yi ka daina ni dai ba zan auri yarinyar nan”
“Ni fa alheri kawai nake kokarin kullawa, kuma ni ban cewa mahaifinta ya rabata da saurayinta ba, kuma ban cewa saurayinta ko ita su rabu da juna ba, ni dai ina kokarin sama maka mafita ne Allah ya san manufata shiyasa nake ganin zaka iya koya mata sonka cikin kankanen lokaci, amman zan gyara komai kuma na maka alkawari daga yau ba zan sake rokon ka auri Noor ba, kuma zan je na samu mahaifinta zan gyara duk inda kake tunanin na lalata, daga nan har zuwa nadewar duniya Kareem ka cigaba da zama a haka ba zan sake maka magana ba”
“Hakan ya fi ba, na san yadda kiyayya take ba zan yarda na sake aikata kuskure a karo na biyu ba, kuma ba zan yarda na shiga tsakanin soyayyar kowa ba, yadda rayuwar Noor take ba zan yi mata sha'awar ta zauna da wadda bata so ba”
Ya dauki wayarsa ya mike tsaye ya fice a office din a fusace. Hafiz ya bishi da kallo yana murmushin takaici.
“Ba laifinka ba ne laifina ne, kuma zaka gane ka yi da ďan halak...”
Ya fada sannan ya cize bakinsa ya hade rai.
Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*
✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧
𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆
*Chapter 14*
“Kasan halinta ai da shirme da ma dai baka bata wayar ba”
Mama ta fada sai ya juya ya kalleta.
“Na dauka magana zata yi masa ta hankali amman meye na fada masa magana haka gatsai, babban mutum ne fa Mama kawai yana da saukin kai ne shiyasa Noor ta same a ruwan sanyi”
“Yanzu aikin gama ai ya gama, sai a tari gaba, ka je ka bashi hakuri kace baka sani ba ta dauki wayarka ta kira shi”
“Haka zan yi”
Ya juya ya fita Mama ta bi bayansa ni kuma na zauna ina ta aikin kuka. Yadda na kwana banci ba haka na wuni haka wani daren ya sake tararda ni na kasa cin komai sai ruwa kawai nake iya sha...
A daren ma sai na kasa bachi saboda tunanin Zafeer ko ya dawo ko kuma yana can, a wane hali yake a can? Wace kalar azaba suke gana masa? Me zai saka ma su kama shi? Na ji yayi abun da be dace ba amman ai taba shi aka yi domin be taba zuwa haka nan kawai ya ci mutuncin Kareem ko ya masa wani abun ba sai yanzu.
Mama ce ta shigo har cikin damunmu a lokacin da Hana take shirin makarantar Islamiya kasancewar yau assabar ba kamar sauran ranakun da take zuwa makarantar boko ba. Ta zauna kusa da ni ta aje min kunun.
“Noor daure ki sha idan kika ce zaki saka damuwa a ranki zata wahalar da ke, kuma ita kaddara ba a kauce mata komai wayon mutum, idan Allah ya kaddara Zafeer mijinki ne zai aureki babu wadda ya isaya hana, idan kuma Allah yayi shi ne mijin ba ko an taru an hadu za a daura muku aure ba zai dauru ba, kalli yadda kika rame cikin kwana daya da rabi, kin koma kamar ba ke ba, ki yi hakuri kinji ƴata”
Ta kwanto da ni jikinta sai na ji sanyi a raina na lallabar da ta yi min da kuma kokarin kwantar min da hankali. Na bude bakin a hankali ta fara ba ni kunun ina sha har na sha rabin kofin sannan na ji na koshi.
“Na koshi Mama”
Hana ta kalli kunun ta kalleni.
“Lallai na yarda kina son Zafeer kalli yadda kika natsu kika koma kamar ba ke ba, kuma yadda kike fushi ko kuka baki rabuwa da abinci amman yau dubi yadda kika ki cin abinci”
Na kalleta kawai na dauke kai domin ni kadai na san yadda nake ji a raina ni kadai na san halin rayuwar da bake ciki
“Ni ma dai na yi mamakin yadda noor ta natsu kamar ba ita ba”
Mama ta fada kamin ta yunkura ta tashi tsaye ta dauke kunun ta fice daga dakin. Hana kuma ta gama shirinta ta kama hanyar makaranta, aka bar ni a dakin ni kadai ina jin jikina babu karfi tunani ne ko kuma dai yunwar da bana ji ce take karya garkuwar jikina. Ina daga kwance na ji sallamar kawata Zainab, na tabbatar a lokacin Mama bachi take domin ban ji ta amsa mata ba, wata kila kuma tana bandakin ne ko kuma ta fita ba tare da na sani ba. Cikin dakinmu ta shigo ganinta ya saka na tashi zaune domin na san ba zan rasa labarin Zafeer a bakinta ba.
“Noor amman dai baki da lafiya ko?”
Na daga mata kai.
“Me yake damunki?”
“Ni ma ban sani ba”
Ta yi shiru tana kallona kamin ta kawar da kai ta ce.
“Wata magana na ji ana ta yi Noor, ko da yake dai ba zan boye miki komai ba gaskiya Zafeer ma ya fada min kuma ya aiko ni gurinki na kawo miki wannan takardar, amman ina son na san me ya hada ku Noor?”
“Ba abin da ya hada mu, me kika ji?”
“Baki ji an kama Zafeer ba? Jiya misalin sha daya na dare ya dawo gida, kuma kamin a kama shi ina ta jin magana sama sama cewar ke da mahaifinki kun bi kudi wai ana son a aura miki wani ba Zafeer ba, ance har da gida ya siyawa Babanki kuma yana kawo muku kayan dadi a gida”
Mamankin jin cewar ya siyawa Babana gida ba abu ne na mamaki ba, wata kila Baba ne ya fada wata kila kuma abokansa. Amman zancen yana kawo mana kayan dadi wani zance ne da ban san da zamansa ba. Kuma ban san wata rana da Kareem ya kawo mana kayan dadi haka nan siddan ba, har sai idan ni na shigo da su, jin cewar mahaifina da ni kaina mun karkarta ga mai arziki wani abu ne da ya fi ko wane yi min daci, domin idan har abun da Baba yake kudiri ya tabbata mutane za su yi mana kallon maciya amana ne. Musamma ni babu ta inda zan iya wanke kaina. Ta damka min takardar dake hannunta.
“Gashi Zafeer yace na kawo miki, kuma Noor da gaske ne Babanki yace kar Zafeer ya sake zuwa kofar gidanku?”
Hawaye na amsar tambayarta domin su suka fara fita madadin kalma a bakina.
“Ina ganin kamar da akwai matsala a kasa Noor baki son fada ne kawai, ko dai dole ake son yi miki?”
Nan ma bance mata komai ba, zata sake yin wata maganar ta ji muryar Mama da ta fito daga bandaki.
“Zainab ce”
Sai ta tashi da sauri ta fita daga dakin tana gaisawa da Mama. Ban bude takardar ba sai da ta fice gaba daya daga cikin gidan, ina warwarewa gabana yana faduwa kamar ance zan karanta sakon mutuwarsa ne a ciki.
“Noor... Me yake faruwa? Nace ki zo ki same ina son magana da ke kin ki, na hadu dake na miki magana kin ki ki amsa ni, an kama ni jiya na yi tunanin zaki zo ko da gidanmu ne ki tambaya ko ki kira wayata, amman na tambaya baki yi ko daya ba, why? Da farko na dauka ko Baba ne kawai aka yi nasarar sauya masa ra'ayi kaina, amman jikina yayi sanyi a lokacin da na ji baki neme ni ba, ko dai ke ma ya sauya miki ra'ayi akaina ne Noor? Shekara uku da muka yi a tare kike son batawa saboda kudi? Kina son ki manta da ni ki rayuwa da wani saboda kudi? Haba Noor kin san fa ina sonki, jiya da na dawo gida ke na fara tambayar kin zo, Inna ta yi kamar zata kashe ni saboda haushi, amman hakan be hana ni rubuto miki wannan wasikar ba a yau kuma zan sake rokokin ki a karo na karshe... Ina son ki fito mu hadu a bayan islamiyarku, zan jira ki a gurin daga yanzu har zuwa azahar, ina son mu yi magana ne Noor bana nufin cutar dake, kuma hakan zai karyata abun da zuciyata take hararon game dake, na san ke karamar yarinya ce kuma kina son rayuwar jindadi, amman hakan be isa ya saka ki yi watsi da ni ba ki kama wani da baki da tabbacin ko zai iya rike ki... Noor in har baki fito ba to ni ma zan hakura dake har abada kuma hakan yana nufin ya sauya miki ra'ayi akaina kenan!”
Ina karatun hawayena na jika takardar, Zafeer ya zo min da wani abu mai nauyi da ba zan aikatawa a yanzu ba, domin ba zan tsallake maganar mahaifina kuma na yi silar mutuwar auren mahaifiyata a yanzu ba. Ina sonsa amman Baba ya shata liyi a tsakaninmu. A nan wata zuciyar ke ce min na fita naje na dawo ai Baba baya gidan kuma be san an yi ba, wata kuma na ce min na lallaba Mama na ce ta roki Baba naje