Author : Binta Umar Category : Romance
da bayansu. hausarta ma bata fita sosai." Na ce." Ai na ga alama, Babandi Allah Ya sanya alheri. Shekara mai zuwa mu dawo suna."
Ya amsa da "Amin Yana gyara tsayuwarsa ya ce." Ke wai yaushe za ki yi aure ne, na san dai ba kya rasa mane ma."
Hankalina yana kan abinda nake yi na ce ." Duk ranar da Allah Ya nufa zan yi, Babandi aure da haihuwa da mutuwa duk na Allah ne, amma ina mamaki naga ana titsiye mace wai ana tambayarta yaushe za ta yi aure, abin yana daure mini kai wallahi."
Ya ce." Hakane gaskiya, amma fa sai kin sanya abin a ranki tukkuna. Allah Ya ce ka taimaki kanka ni ma zan taimake ka, Amina tunda mijinki ya mutu na ga take takenki ba kya son ayi miki maganar aure ."
Dariya na yi na ce." To ai auran ne ya zama abinda ya zama Babandi, da wahala yanzu na samu mai sona tsakani da Allah kamar Yaya Aminu. Wallahi gabad'aya mazan basa burge ni balle na ji sha'awar auran, ko ka ga na yi to Allah ne ya kaddara."
Ya dube ni a tsanake ya ce." Mu cire maganar wasa anan Amina, wanda ya mutu fa ya riga ya mutu, kada ki tauyi rayuwarki da k'uruciyarki, ki ce za ki zauna haka, ko bayan haka ma kina da sha'awa irin wadda Allah Ya 'kaddarawa bayinsa, aure shi zai katange ki daga fad'awa wani halin."
Na numfasa tare da ce wa." Babandi ban san me yasa rashin aurena yake damun mutane ba wallahi. Sai na ga 'yan mata suna zaune a gaban iyayensu ba a matsa musu ba sai zawarawa. Duk wanda zai dube ka sai ya yi maka wata fahimta. Babandi ka ganni nan wallahi babu wanda yake yi mini wahala ni nake yi kayata. Kuma ina kula da kaina sosai bana taba barin wata kofa da zata janyo mini 'bacin suna. Sana'ata kawai na sanya a gaba, a yanzu burina yarana su yi wayo Allah Ya taimake ni su tsaya da kafafunsu, su samu ilimi da tarbiya. Sai na ji dadin auran."
Ya harareni Yana furta." A lokacin kin tsufa kenan, kina maganar shekara ashirin fa anan gaba Amina. Lokacin kin yi hamsin, wane namiji ne zai yi kwad'ayin auran tsohuwa."
Na fashe da dariya ina cewa." Shikkenan ka ga sai na k'arasa rayuwata a haka, dama ba na so na yi aure ranar lahira na tashi a matar wani, nafi so na tashi a matar uban yarana."
Ya ce." Wannan ba hujja ba ce Malama sai kin yi aure fa, idan ba ki da tsayayya a cikin abokaina akwai wanda yake son kari, idan ma ba za ki auri mai mata ba akwai samari. Tunda Allah Ya sa kina da jiki mai kyau na san da gudu za a aureki."
Na ce." A a ba sai ka kawo mini kowa ba. Na kusa in sha Allahu. Akwai wani mutumin Ubangidan Baba Sule a kasuwa, akan maganarsa muke ina fata zaka tayani da addu'a Allah Ya sa alheri ne. Wata'kila ma ina komawa gida da 'yan kwanaki ku ji labarin d'aurin aure."
Cike da farinciki ya ce." To Alhamdullahi, ina
taya ki murna da fatan alheri, Allah Ya sa idan kin shiga kin shiga kenan, Allah Ya kad'e fitina."
A takaice na amsa da Amin." Maganarsa da muka yi yanzu ita ta tuna mini da wayata dake kashe. Jiya da daddare bayan mun gama waya dashi na kasheta ba don komai ba sai don gudun kada ya kira ni ina cikin jama'a, na lura kuma shi yana son yawan waya kamar matashin saurayin da yake da sabuwar budurwa. Ni Kuma sabgogina sun isheni zaman yin wayar nan ba ni dashi, don sai na ga kamar batawa kai lokaci ne.
Sai da na koma gidan anti Yagana tukkuna na kunna wayar bayan na gabatar da sallar isha'i. Jikina ya yi tubus gajiya ta dirar mini, ta zaman mota da zaman keke. Bacci ya fara surata, Yusi Yana can cikin yaran anti. Da yake Yana da saurin sabo ya sake dasu duk inda zasuje sai su ja shi. Anti Yagana ta shigo tana fad'in." Ga abinci nan na tawo mana dashi, idan za ki ci sai ki fito ki d'iba."
Na ce." To shikkenan anti Gajiya ce ta addabeni wallahi." Tana ko'karin fita daga d'akin take cewa." Ai dole, zaman mota da zaman d'inkin nan da ki ka yini kina yi. Ki sha Panadol mana."
Ido a lumshe na ce." Anti ba na so na sabawa kaina da shaye shayen maganin nan, gari Ya na wayewa zan warware."
Ta fita daga d'akin ba ta ce komai ba.
Ina jin kiran waya na san wanda nake tsammani ne. A nutse na daure na daga wayar da sallama a bakina.
Ya sauke ajiyar zuciya Yana cewa." Wato saboda kin lura na kamu da sonki shine za ki yi mini jan aji ko Amina, da alheri fa na zo gare ki, ba zan cutar dake ba."
A sanyaye na ce." Ba haka ba ne wallahi, yau na yi ina wani uzuri ne, shaf na manta ban kunna wayar ba sai yanzu, amma ka yi hakuri, kuma ai ka bari mu gaisa ko."
Ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na biyu Ya furta." Dukda haka dai ba ki damu dani ba Amina, ai jiya kafin mu yi sallama kin yi mini alkawari za ki kunna wayarki, sannan Zaki sanar da ni shawarar da ki ka yanke akan sha'aninmu. Amma gari Yana wayewa na ji waya a kashe, yini na yi cikin zullumi wallahi."
Yadda yake tausasa murya da lallashi. Sai Yaya Aminu ya fado mini a raina. Kwalla ta taru a idona. Shi ma haka yake yi mini wasu lokutan ma ni na ce da laifi amma sai ya mayar dashi kansa yayi ta rarrashina. Nasa yatsa na goge kwallar da ta fara zuba. A sanyaye na ce." Ai na
bada ha'kuri Alhajina, a yi mini afuwa ba zan sake ba."
Ya ce." Na yi miki afuwa, amma ki dinga kira na kina jin lafiyata Hakan shi zai tabbatar mini da cewa kin damu da ni."
Murmushi na yi na ce. " In sha Allahu rabbi zan yi Hakan, sannan albishirin da zan yi maka shine na amince da auranka. Daga zarar na dawo sai mu tsayar da magana."
Cikin wani irin yanayi na farinciki da karsashi yake furta." Alhamdullahi. Allahamdullahi, na gode Allah Amina, ni ma albishirin da zan yi miki shine idan an daura auranmu zamuje saudia mu yi godiya ga Allah."
Cikin jin dadi na ce " Aikuwa na gode sosai da wannan karamcin, Allah Ya kara suttura, Ya kuma raya zuri'a." Ya amsa da "Amin cikin walwala da farinciki, yadda yake nunawa shi yake sake tabbatar mini da cewa 'Sona yake yi bilhaki da gaskiya' Ba auran dandano zan yi da ni ba. Zuciyata ta kara aminta da auransa na san a hankali idan da kyautatawa soyayyarsa zata shiga cikin zuciyata. Muka yi sallama cikin mutumci da kulawa.
Bacci ne ya d'auke ni mai nauyin gaske anan na bingire ba tare dana hau katifar dake shimfide a gefe ba. Wajan sha biyu da rabi anti Yagana ta tashe ni. Wai na hau katifa kada jikina ya yi ciwo. Sama sama nake jinta na ja jikina na hau katifar na kwanta ta kashe fitilar d'akin ta fita. Gefin asuba na tashi na zauna gabad'aya dan'kon baccin ya saki idona. Gabana ya dinga bugawa. Wani mafarki na yi mara kyau wai ga mutane a kofar gidanmu a tsaye anata hayaniya. Wani Yana cewa a tafi a nemo Kamalun duk inda ya shiga.
na sauka daga kan katifar na nufi bandakin da yake cikin d'akin cikin sanyi jiki da kiran Innalillahi wa'ina ilaihi! Ban kwanta da abin a Raina ba ballantana na ce. Gabad'aya sai hankalina ya yi gida don mafarkin ya tsorata ni sosai.
Muna karyawa da Anti Yagana na ce." Jira nake Babanmu ya tashi daga bacci anti yau za mu tafi tunda an daura aure, na bar din'kunan mutane wallahi, ga Kamalu, kin san abin sai a hankali."
Ta ce." Malama kya bari dai sai gobe wace irin tafiya ce wannan da gaggawa haka, Shi ma Babanmu haka yace sai gobe sai ku tafi a nutse, jiya ai mun jima dashi da daddare muna hira.
Kiran waya ya katse maganar da zan yi. Ina dubawa na ga Usaini. Gabana ya buga. Hannuna na rawa nasa a kunnena.
Ya ce." Anti Amina an tashi lafiya? Yau za ku dawo ko?"
Na ce." Lafiya Lou, wata'kila yau ko gobe, ina fatan dai lafiya, ina Kamalu ka bashi wayar mu gaisa."
Ya yi shiru bai ce komai ba."
Cikin mi'kawa Allah lamarin na ce." Usaini tunda na ga Kiranka na tabbatar da matsala, ka fad'a mini kawai, abinda ba sabon abu ba ne, me ya faru?"
A sanyaye ya ce." Anti abin ne babu dadi wallahi, da har na ce kada a gaya miki. Ummansu Hadiza ta ce a fad'a miki kawai, ki san abinda yake faruwa."
Na daga kai ina kallon Baba lokacin yana ko'karin shigowa. Na ce." Usaini gaya mini don Allah, ba na son kwane kwane Kamalun mutuwa ya yi ne?"
Ya ce." A a, da asuba ne da aka tashe su shi da Saminu domin su yi sallah, bayan sun fito daga massalaci sai suka je tu'ka-tu'kar kofar gidan Alhaji Lawan. Suka kwashe jarkokin mutane har da sababbi sun kai goma suka had'a da zungureriyar kurar ruwar wani dan garuwa. Suka nufi cikin kasuwa, su uku Saminu Kamalu da kuma Shamsu 'kanin Bashir abokina. To Allah dai Ya rufa asiri ba su sayar ba, Malam Maharazu na bayan gidanmu ya shiga kasuwar da wuri shine ya gansu a gurin masu sayarwa ana ta ciniki, to da yake akwai police station ana gane sato wa suka yi, gabad'aya su ukun aka kama su suna can a cell a kulle."
Ajiyar zuciya na sauke na ce." To Usaini Allah Ya kyauta, idan hali ya yi za mu iya dawowa yau, idan kuma hakan bai samu ba sai gobe idan Allah ya nufa ."
Ya ce." Shikkenan anti Amina, amma don Allah ki kwantar da hankalinki, na sanki da sanya damuwa a cikin rai, kin ga ba ke kad'ai ba ce, wallahi ba ki ga yadda Ummanmu take kuka ba yanzu ta yadda da cewar Saminu shine shugabaa cikinsu."
Na ce." To, zan danne Usaini, ba zan sanya damuwa ba, na gode kawai zan kira ka idan an jima, yanzu ya mu tattauna da Babanmu."
Na kashe wayar na dube su. Gabad'aya hankalinsu Yana kaina, ba sai na yi musu karin bayani ba sun ji komai tunda handsfree na sanya wayar rad'au duk sun ji komai.
Anti Yagana ta fashe da kuka tana fad'in." Wannan wace irin masifa ce, yaran nan suke nema su janyo mana, jarkokin ruwa uban me za su yi da kudin idan sun sayar, Yara k'ananu dasu."
Na bita da kallo ban ce komai ba, domin a lokacin ma ni kaina kullewa ya yi na rasa tunanin me zan yi, na san dai tun lokacin da Usaini ya fara yi mini bayanin abinda yake faruwa wani abu mai nauyi ya tokare mini a wuya.
Babanmu ya dubeta Yana fad'in." Ai ba sabon abu ba ne Yagana ke yanzu ki ka ji shine dalili. Ki daina yi musu kuka, yi musu addu'a kawai, Allah Ya tsayar musu iya nan, kuruciya ce kowa da irin tasa."
Tana goge hawaye wasu na sake zubowa. Gabad'aya ta rikice sai Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un take yi. Ya dube ni yana cewa." Tashi ki shirya mu tafi a samu a fito da su, zaman cell din ma wata masifar ce, bari na fita na yi sallama da jama'a."
Ya tashi ya fita da saurin gaske.
Na dubi anti Yagana da kanta yake a sunkuye hawaye na zuba tana sharewa na ce." Ashe ba ni kad'ai ba ce mai saurin kuka."
Ta kalle ni, na yi murmushin da babu nishadi a cikinsa. Na tashi kafafuna na rawa na shiga d'aki na fara had'a kayana. Cikin zuciyata ina ta kiran sunan makagina da ya kawo mini d'auki
***
Tafiya ce muka yi ta a gigice cikin rashin kintsi shiyasa ba kowa muka yi wa sallama ba. Allah Ya nufa muka samu mota mai kyau da rashin tsaye tsaye. La'asar sakaliya muka sauka a tasha nan kasuwar kwari.
Na kira Usaini domin jin karin bayani. Ya ce mini ai har yànzu yaran suna can cell a rufe domin jama'ar unguwa sun ce sai an shiga kotu an hukuntasu tunda an jima ana sace musu kayan ruwa."
Na ce." Kai kana ina yanzu, ko kana shago ne?"
Ya ce." E, ina shago anti kin san Babanmu da zaku tafi ni ya barwa dan mukkuli, idan an samu aiki na yi, nake basu kudin abinci, yanzu haka ma akwai aikin mutane a hannuna."
Na ce." To yi zamanka tunda kana da aiki, amma ka samu wani ka turo shi muna nan tashar kwari, ya zo ya d'auki kayan nan zan bashi kudin mota."
Ya ce." To yanzu kuwa anti." Na kashe wayar. Na dubi Babanmu da yake tsaye a jikin wata tumba ta wutar lantarki, tausayi ya ba ni kwarai, haka dai na daure na yi masa bayani duk yadda muka yi.
Ya ce." Ai dama da wuya jama'ar unguwar nan su ha'kura, kin san babu had'in kai, idan matsala ta faru a maimakon a had'u a kashe wutar sai a samu wasu a gefe suna rurata. Yaran nan kowa yana dasu sai addua."
Na ce." Baba tafi gida ka huta, ni zan wuce station din, in sha Allahu abin ba zai yi girma ba."
Ya ce." A'a, ba zan bari ki je ke kadai ba, mu je tare Amina, idan da namiji abin zai fi yin kyau."
A sanyaye na ce." To shikkenan Allah Ya taikaita, su kuma Ubangiji Allah Ya shirya mana su."
ya amsa da "Amin Ya Allahu......✍️
*1k on talgram*
*0542382124...Binta Umar gtbank*
*07084653262*
[11/19, 9:07 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*
*Marubuciyar*
*Yar bangar siyasa*
*Ba'aboren namiji*
*Madadi*
*Ga irinta nan*
*Goje*
*Babban yaro*
*Sadauki Omar*
*Nida Yaya sadam*
*Da sauransu..!*
*TALLAH!*
'Yan uwa
Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS,
duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su
Sandal flakes
Hawee
Gabgab
Halut
Dorot
Coconut chips
Dufr(farce)
Black khumra
Brown khumra
White khumra
Oil perfumes da
Body sprays
Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku.
Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka
Call/WhatsApp
07037489958
Location:Gonan Ganye,zaria
Kaduna state
Nationwide Delivery
*Free pege*
*10*
*@Arewa books*
*Bintuumarabbale*
Lokacin da muka isa station din yaran suna cikin cell a rufe. Wani d'an-sanda ya ce maza a sayo musu abinci domin tunda aka rufe su da asubahin babu wani abu a cikinsu.
Na fito da dubu d'aya na ba wa wani 'karamin ma'aikaci daga cikinsu ya je ya sayo musu abinci da ruwa ya shiga ya kai musu.
wanda case din yake hannunsa ya yi mana bayanin duk yadda suka yi da mutanan unguwarmu. Shi ma ya so maganar ta mutu ganin yaran kananu ne amma wasu daga ciki suka ce ba su yarda ba, kamar dai yadda Usaini ya fad'a suna cewa an jima ana yi musu sace-sace a cikin unguwar.
Babanmu ya ce bari ya je ya samu mai unguwa zai dawo yanzu. Ya tashi ya fita da saurin gaske. Ina zaune ina kallo ana ta shigowa da masu lefi har da mata daga cikinsu akwai wadda na kusa zubarwa da hawaye budurwa ce duka bata wuce shekara sha shida ba take sace-sace. Matar da suke zaune a gidanta haya tana sana'a idan ta fita unguwa yarinyar sai ta shiga d'akinta ta k'asan 'kofa da yake akwai rara ta sace mata kud'i sai yau da dubunta ta cika ta kamata. Da aka tambayeta tana kuka tace Mamanta ce take turata ta d'auko kudin sai su sayi abinci. Koda aka tambayi uwar ba ta yi jayayya ba tace hakane.
Ita kuma matar da suke zaune a gidan nata tana ta rantsuwa wallahi sai ta yi 'kararsu a kotu tunda duk abinda take yi musu basa gani sai sun cutar da ita.
Dubu hamsin da biyu ta d'auke mata Allah Ya sa ba su ci da yawa ba. Aka lissafa dubu hud'u suka ci, na zaro a jakata na bata. Na ce. " Don girman Allah ki dubi maraicin yarinyar nan ki rufa mata asiri, kada ki fitar da maganar nan, wanda ya suturta wani Allah zai suturta shi. Dan kuskure ta yi, haka nan mahaifiyarta amma ki yi hakuri, idan ya so sai ki tashe su daga gidanki, Amma dai maganar nan ta mutu anan."
Ta yi shiru sai huci take yi. Uwar da d'iyarta Kuma sai kuka suke yi. Na ce." Ke kuwa baiwar Allah ba kya jin tsoron ranar da Ubangiji zai tuhumeki akan abinda ya baki kiwo. Kada fa ki manta yarinyar nan amana ce a wurinki ki bar ganin ke ki ka haife ta, tana da hakki a kanki, haka zalika ma Allah Yana da hakki a kanki, me yasa za ki dinga tura ta tana yi sata, ki lalata mata rayuwa. Ba zaku nemi taimako ba? Ke me yasa ba kya yi sai ita, ki ji tsoron Allah, kuma ki yi nadama akan abinda ki ka aikata."
Ta share hawayen da yake gudana a fuskarta tana fad'in." In sha Allahu zan kiyaye wallahi rashin yadda zamuyi ne ya sanya shaidan ya ribaci zuciyata, amma na yi alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba.
Na ce." To Ubangiji Allah Ya yafe mana gabad'aya, Allah Kuma ya shirya mana.
Jami'in ya gama rubuce rubucensa ya tura su wurin d.p.o domin ya sake yi musu sulhu. Ina nan zaune suka shiga suka fito. Muka yi sallama suka fita.
Jin shiru Babanmu bai dawo ba ya sanya hankalina ya tashi. Don ba na k'aunar yaran nan su kwana a wurin nan, ina so a samu maslaha. Na kira Usaini a waya domin jin Ina aka kwana nan yake tabbatar mini da cewa suna nan tafe gabad'aya har da mai unguwa."
Na kashe wayar zuciyata gabad'aya babu dadi.
Koda suka so station din zama aka yi sosai a office din D.P.O aka fito da yaran gabad'aya sun firgice yini daya da suka yi a rufe. Har da yar rama a tattare dasu. Gefan idon Kamalu ya dan tasa kamar duka kamar kuma alamun kuka.
Kallo daya na yi musu na