Gudun Aure 1 Complete Hausa Novel

Author :  Binta Umar Category :  Romance

Chapter   17 / 18

48K to 51K   out of 51.4K words

shi a tsanake na ce." Ka je massalacin ko?"
Ya daga kansa alamun "E, sai ya ce." Mama ina Yayana yake? yanzu ina fitowa daga massalaci na ji wasu suna cewa 'yansanda sun kama shi saboda ya zage su."

Na ce." Yana can gidan Gwaggwo k'arya suke yi yanzu nan zan kira Hamusu a waya ya kawo shi gida.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin jikinsa. Na dau'ki wayata da sauri number Hamusu na nema.
Ya daga muka gaisa Yana tambayata ya ake ciki.
Na ce." Hamusu komai ya zo da sau'ki ga Yusi a gabana tun d'azu suka ba dashi saboda gaskiya ta bayyana kanta."
Ajiyar zuciya ya sauke yana godewa Allah kafin ya cigaba da cewa." Yanzu dai an kama wanda ya aikata ko?" Na ce." E, ana kan binkice dai."
Ba na so na fad'a masa yaron gidan nan ne, yin hakan kamar tozarta maigidan ne, kuma na ji dadi sosai da tsayuwar da ya yi akan sha'anin har gaskiya ta bayyana.

Na ce." Don Allah tunda kana da abin hawa ka kawo mini Kamalu akan babur d'inka kada ka bari ya taho da kansa, dama akwai maganar da nake so mu tattauna dangane da bud'e shagunan da zan yi."
Ya ce." A a, Kamalu ai baya nan, tun lokacin da ya zo ya gaya mini abinda yake faruwa ban sake ganinsa ba, bai dawo gidan ba ne?"
Cikin faduwar gaba na ce." Bai dawo ba wallahi, amma don Allah yi maza ka duba gidanmu ko yana can."
Da sauri ya kashe wayar.

Yusi ya dube ni." Mama ya akayi, ina yayan nawa?"
Cike da fargaba na ce." Yana can gidanmu, yanzu Kawunku zai je ya d'auko shi."
Ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na biyu. Ina nan zaune ina sakawa da kwancewa. Hamusu ya kira ni yana tabbatar mini da cewa Kamalu baya can gidanmu.
Na ce." Ka ga Saminu a gidan kuma?"
Ya ce." Kwarai kuwa shine ma ya tabbatar mini da cewa baya nan, don koda sallah bai je musu ziyara ba.
Jikina ya shika, sai fargaba ta yi mini sallama, da ban kawo komai ba a zuciyata, amma yanzu babu irin tunanin da ba na yi. Na ce." Hamusu bari na yi magana da maigidana yanzu zan kira ka zuwa an jima.
Na kashe wayar da sauri na tashi na fita zuwa d'akin maigidan tunda ba girkina ba ne, Yusi ya biyo bayana da sauri yana kuka....✍️
*Gudun aure 1k on talgram via 0542382124....Binta Umar gtbank mutanan nijar dala dari katin Airtel a kankare a tura mini shaida ta wannan lambar*
*07084653262*

*TALLAH*
🌲🌳🌿☘️
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
[11/29, 12:50 PM] Aunty B: *GUDUN AURE!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A.*
*@arewabooks*
*Bintuumarabbale*
*Last free peges*
*20*
Abinci yake ci a lokacin dana shiga d'akin yana tare da anti Maimuna da alama maganar dai suke kara tattaunawa domin cikin alhini na same su. Shigowarmu d'akin ni da Yusi ya sanya suka bi mu da kallo bakidaya
Na ce." Yanzu nan Hamusu ya ke gaya mini Kamalu baya can wurinsu. Tun fa da lamarin nan ya faru ya bar unguwar ni wallahi na d'auka Yana can gidan kakarsu ashe Yana gayawa kanin uban ya fita ba a sake ganinsa ba, duk inda ya kamata a duba mini Hamusu ya duba ba a ganshi ba."
Hawaye ya zubo a kumatuna na sanya hannu na goge gabad'aya jikina Yayi sanyi sai nake ganin kamar akwai abinda yake shirin faruwa da yaron.
Anti Maimuna ta shiga kwantar mini da hankali. Shi Kuma maigidan ya tsame hannunsa daga abincin ya d'auki wayarsa muna zaune ya kira station domin tambayarsu tunda ya ji labarin rashin kunyar da yaron Ya yi. Gabad'aya mun yi tunanin ko sun kama shi.
Suka tabbatar masa da cewa baya hannunsu. Hankalina ya sake tashi. Gidajen redio uku ya kira ya bada cigiyarsa duk ya Basu bayanai akansa. Sannan ya waiwayo gareni ya shiga yi mini nasiha da kawo mini misalai na kaddarori na rayuwa.
A wannan dare na yaba masa kwarai da gaske dashi da anti Maimuna sun yi mini kara, sai kusan sha biyu da rabi tukkuna na yi musu sallama na koma wurina jikina duk Yayi tubus. Yusi kuwa ya ci kuka ya koshi sai ajiyar zuciya yake yi.
Yadda na ga rana haka naga dare.
Ina idar da sallar asubahi na kira Hamusu domin tambayarsa ko ya samu wani labari akan yaron. Ya ce mini babu wani labari shima tun jiyan yake zaga gidajen masu unguwani. Da station da suke area ko an kai shi can.
zuciyata ta dinga raya mini munanan abubuwa Ina ta tunanin ko wane hali yake ciki a yanzu. Fatana dai ace yana hannu nagari.

Kwana uku babu wani labari babu Kamalu babu dalilinsa. A lokacin na gama gigicewa. Komai na rayuwata ya tsaya cak! Na kira anti Yagana na sanar mata da halin da nake ciki. Sannan na bawa Ya Falmata ha'kuri domin halin da nake ciki ba zai barni yin komai ba.
Tsangayu uku na bada sadaka domin a yi mini ro'kon Allah akan lamarin Allah Ya bayyana mini yarona ko da rai ko a mace.
Sahura zuwanta biyu ta ce mini muje gidan wani malami da rigar Kamalu zai yi aiki akai idan ma yana raye zai gaya mana, idan kuma baya raye nan ma zai gaya mana.
Na ce ba zan iya zuwa ba, tunda na sanya a yi mini ro'kon Allah shikkenan. Zuwa lokacin na saduda burina ko gawarsa ce na ga ni.
****
A ranar da Kamalu ya cika sati da 'bata Hamusu ya kira ni a waya da rana gatse gatse.
Ina d'agawa ya ce." Anti an samu labarin Kamalu sai dai lamarin ba dadin ji wallahi."
Na ce." Hamusu gaya mini idan mutuwa ya yi duk inda yake zamuje a ba ni gawarsa ko zan rasa komai."
Ya ce." Yana nan a raye sai dai yana hannun hukuma tare da wasu matasan Yara 'yan nan gaba damu, wata'kila ma zaki san gidan Alhaji mato."
Na ce." Na san gidan Hamusu mai ya had'a Kamalu da yaran gidan nan Kuma?"
Ya ce." Neman mafaka ya yi dasu, ashe bayan ya zo ya gaya mini abinda ya faru, sai ya hadu da daya daga cikinsu yake gaya masa zai kwana a gidansu. Da ya tambaye shi dalili sai ya ce 'yansanda ya zaga shi kuma Yana jin tsoron komawa gida a kamshi.
Shine da yaron mai suna Kamsusi ya bashi mafaka. A kuma washe garin ranar ya gudu dashi legos. Suka shiga wani kamfani sukayi sata aka kuma cafke su har da Kamalu. Inda nake jin dad'i kamfanin da suka shiga yana daya daga cikin mallakar Alhaji Tajo, muna sa ran yaran za su samu sassauci.
Na ce." To Hamusu yanzu ya kake ganin za a yi? kana ganin zasu ba mu yaron nan cikin sau'ki idan an yi duba da irin yaran da suka ja shi, hukuma ba zata aminta da korafinmu ba, dole tunda tare suka aikata barnar a hukunta su.

Ya ce." Ai Kamalu shine k'arami a cikinsu. Bai balaga ba har yanzu shekara sha hud'u, za a samu rangwami. Sauran kuwa duk sun haura ashirin. kwai dai hankalina yana tashi ne idan na tuna ta'adacin da yaran suka jima suna yi. Dama an ce hukuma neman su take ruwa a jallo, tunda basu jima da cinna wuta a wani a shago ba bayan sun kwashi kudi masu yawan gaske.

Jiki a mace na ce." Hamusu duk yadda Allah Ya yi daidai ne. Zan yi magana da maigidana yanzu zuwa an jima abinda muka tattauna zan sanar da kai in sha Allahu rabbi."

Ya ce." To shikkenan anti ni ma ta nan din zan cigaba da bincike akan lamarin in sha Allahu za mu sau'ki."

Muna gama waya da Hamsu na kira maigidan na gaya masa. Sai ya ce ai ya samu labari don har gidajen jaridu sun buga da kafafen da zumunta. Shi ma a fece book ya gani. Ya kwantar mini da hankali kafin ya dawo har ya na fad'in lamarin zai zo da sauki tunda mamallakin kamfanin mutumin kirki ne.
Tun kafin Azimi rabona da sa data a wayata saboda ba ni ma da sukunin shiga media kallace kallace dalilin ayyukan da suke gabana.
Ashe lamarin har ya yi girman da gidajen jaridu ke watsa labarin. Ko da yake mutumin babba ne a kasar hakan ba zai zama abin mamaki ba tunda motsi kad'an zai yi media zata d'auka balle wani abu da ya shafe shi. Yanzu kenan hotonan Kamalu suna can suna yawo a duniya kowa yana fad'in albarkacin bakinsa.

Da yamma Sahura ta kira ni a waya tana jajanta mini. Itama dai a fecebook din ta gani, maganar dai guda daya ce na kwantar da hankalina yaran za su samu sassauci saboda adalcin mutumin da suka yi wa ta'adacin. Ban iya ce mata komai ba saboda na san ta riga ta yi ammana da ubangidanta, ba ma ita kadai ba kowa alherinsa yake fad'a to ina addu'ar Allah Ya sa wannan karon ya gwada mini, ni ma sai na gazgata.

Duk wanda ya jibance ni a wannan ga'bar sai da ya jajanta anti Yagana tana daga can duk ta damu, ni ce ma nake kwantar mata da hankali ina kara gaya mata ai mutumin da suka yi wa b'arnar Yana da kirki za su samu sassauci. Jin yadda jama'a suke fad'a ni ma sai na ara na yafa dukda a can baya bai kwatanta mana adalcin ba, amma ai ba ni da bakin bakin magana a wannan yanayin.

Kwana daya zuwa biyu maigidan bai ce mini komai ba tun bayan tattauna yadda za a bullowa lamarin da muka yi dashi ranar da Hamsu ya kira ni a waya.
Da ya dawo yake ce mini za su shirya zuwa Legos din da shi da wasu abokanansa wad'anda suka kasance 'yan unguwar da aka haifi Alhaji Tajo din wato 'Danbatta sun san shi sosai kuma sa'i da lokaci idan ya shiga unguwar tunda har yanzu anan mahaifiyarsa take zaune suna gaisawa har ya yi musu alheri, to Yana ganin za su shige masa gaba, domin komai ya zo da sauki. To tun ranar da muka yi wannan maganar bai sake ce mini komai ba, dan har Sahura ta kira ni a waya tana fad'in ta samu lambar wayar PA d'insa idan na amince sai ta kira shi domin ya sanar da ogan nasu muna san ganinsa, na ce ta bari tukkuna na ji daga maigidana.

Da yake ba girkina ba ne a ranar bayan ya dawo sai da na tabbatar ya ci abinci tukkuna na same shi domin na ji Ina aka kwana.
Sai ya ce na kara ha'kuri ashe duk abin nan da yake faruwa shi uban gayyar ma baya garin amma dai yana da labarin komai, ya ce a jiraye shi ya dawo tukkuna.

Ni kad'ai na san irin fargabar da nake kwana na tashi da ita. Babu irin tunanin da baya zuwa k'wa'kwalwata akan yaron da yanayin gari, da wurin da aka ajiye su tare da garadan samari lalatattu wad'anda suka girme masa.
Na gane kuka ba shine mafita a gare ni ba, domin ta wani gefan ma zubaar hawayen nawa zai iya janyowa yaron wata masifa. Wannan dalilin ya sanya na tsananta kai kukana ga Ubangiji akan ya gaggauta kawo sau'ki a cikin al'amarin.
Kowa ya na ta sabgar da take gabansa ni kuwa komai na rayuwata ya tsaya cak! Abincin kirki ba na iya ci, ga yawan koke koke da Yusi yake yi mini akan rashin ganin d'an'uwansa. Ni dashi muka zabge lokaci guda tunda shi ma ba abincin yake iya ci ba.

Sati daya sati biyu babu wani labari Hamusu ya kira ni a waya ya fi sau biyar ina dakatar dashi bisa bin umarnin maigidan wanda shi kuma tun ranar da muka yi magana dashi bai sake tayar da maganar ba. Da dai na gaji na sake tuntubarsa sai ya ce mini ya dawo amma baya hayyacinsa dalilin rashin lafiyar mahaifiyarsa. Sai na tuna wani zuwa da Sahura ta yi mini take gaya mini sun je dubata. A ganina hakan ai ba zai hana shi bin ba'asin abubuwan da suka faru bayan baya gari ba, idan ma ba zai saurari cas din ba sai ya wakilita wasu.
Na kira Sahura a waya domin ta tabbatar mini da dawowar tasa ta kuma ba ni tabbacin cewa ai kwanansa uku ma da dawowa.

Raina ya kai ma'kura wurin 'baci. Na fahimci ba kowa ne zai gane halin k'unci da fargabar da nake ciki ba, shiyasa duk a ka yi shakulatun 'bangaro da lamarin.

Babu abinda ya fad'o mini a wannan ga'bar da zuciyata ta bushe sai yin amfani da social media domin tura sa'kona ga wanda al'amarin ya shafa. Idan hukunci zai sa ayi musu gwara ya fito ya yi magana, idan kuma zai yi musu afuwa sai ya fito ya sanar da mutane.
Ban yi shawara da kowa ba na sayi data wurin TEEMA DATA SERVICES
08112392177///08037026306 domin dàtar ta akwai kyau da inganci tun a gida nake saye haka zalika ma mafi akasari na ga Hamusu da datar ta yake amfani a cewarsa nan da nan yake gudanar da komai babu wani jinkiri ko daukewar network.
Fecebook na shiga. Duk da ba ni da wasu abokai da yawa amma na yi imanin rubutun da zan yi akan mutumin zai ja hankali mutuka har sa'kona ya iske shi.

"Assalamualaikum warahamatullahi ta'ala wabrakatuhu. Jama'a sunana Amina Malam Salisu mai hula. Ni haifaffiyar jahar kano ce kuma ni uwar marayu ce. Jama'a ina so don Allah ku yad'a wannan sa'kon nawa zuwa wurin mutumin da duniya da mutanan cikinta suke yi masa kallon mutumin kirki. Kai tsaye sa'kona zuwa ga Alhaji Tajo Ibrahimu 'Dambatta ne na san kaf kasar nan babu mahalukin da zai ce bai san sunansa ba ko baku ta'ba ganinsa a zahiri ba ina da tabbacin kun ta'ba katari da hotonsa. Ina yawan ji jama'a na fad'in kyawawan halaye da nagartarsa sai dai ni Amina Salisu mai hula har yanzu na kasa aminta da hasheshenku. Ban fito duniya domin na zage shi ko na 'bata shi a idon duniya ba sai dai na fito ne domin na fadi ra'ayina. Mutumin nan bai san muhimmancin alkawari ba, wannan shine abu na biyu wanda ya yi mana wanda na kara tsanarsa a duniya. Ni ina daya daga cikin iyayen yaran da suka samu nasarar shiga d'aya daga cikin kamfaninsa dake Legos suka yi 'barna. Yarona Kamalu shine k'arami a cikinsu. An yi magana dashi kan cewa idan ya dawo daga inda ya tafi zai magantu akan sha'anin yaran amma yau tsayin sati uku kenan bai ce komai ba. Duniya ta yi masa sheda mutumin kirki ne har ana yi wa yaran murna cewa za su samu sassauci. Amma cikar kamala da mutuntaka shine cika alkawari. Ina so ya fito ya gayawa duniya abinda yake zuciyarsa a game da yaranmu. Ya yafe musu ne ko kuma zai bawa hukuma damar hukuntasu. A madadina da sauran iyayen yaran muna jira daga gare shi domin mu samu nutsuwa da kwanciyar hankali.
Jama'a da wannan nake yi muku sallama, kuma ina ro'kon alfarmar ku yi shearing din wannan sa'kon nawa har ya isa gare shi. Na gode sosai."
Amina Salisu (Mai wankin hula.)
✍️
*Alhamdulillahi, anan na kawo k'arshen book 1 kamar yadda na fad'a muku kyauta ne ga kowa da kowa amma book 2-3-4 na kudi ne akan 1k a manhajar talgram ga wad'anda kuma suke karatu a arewa books akwai more peges a can domin na yi nisa. Ina fatan samun hadin kai da goyon baya daga wurinki. Littafin gudun aure yana 'kunshe da dambarwa daban-daban. Kada ku yi jinkirin wurin sayan littafin domin akwai darrusa masu yawa uwa uba akwai kuma irin soyayyar da kuke so mai sanyaya zukata😃 kun san dai yadda karshen book 1 ya kasance akwai rikice a kwance. Hanyar da za a biya kudin shine 0542382124...Binta Umar gtbank ko 7084653262... Binta Umar Opey bank. Mutanan nijar dala dari katin airtel sai ku kankare hoton a tura mini da sheda.*
*07084653262*
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*MAI MAGANIN GARGAJIYA*

*TALLAH!*
🌲🌳🌿☘️
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da

17 / 18