Gudun Aure 1 Complete Hausa Novel

Author :  Binta Umar Category :  Romance

Chapter   2 / 18

3K to 6K   out of 51.4K words

mak'arkashiya aka yi wa mijinki a kamfanin, amma zahiri daidai gwargwado yana yi wa ma'aikatasa hidima."

Na ce." To ko annabawan Allah suna kuskure ballanatana mutum, ba wai na ce dole ku yarda ba ne, ni ma kuma babu lallai na aminta da hasashenku akansa ba domin lokacin da aka bawa maigidana takardar sallama mun shiga tashin hankali sosai, shiyasa duk lokacin da na ji sunansa sai gabana ya yanke ya fad'i wallahi."
Direban ya dinga dariya yana ce wa." Lallai hajiya kenan ko da zai fito takara ba za ki zabe shi ba?"
Kai tsaye na ce." Babu lallai gaskiya."

Har goslow din ya tsaigaita muna jayayya suna fad'in ra'ayinsu akan mutumin ni ma ina fad'in ra'ayina akansa. Direban dai in banda dariya babu abinda yake yi mana ganin yadda ni da matar dake kusa da ni fad'a ya kusa ya kaurewa sai ita ta gaji ta yi mini shiru, fad'i yake "Hajiya za ki yi kyau da aikin jarida na lura ba a kada ke a magana, ko dai 'yar siyasar ce ke me.'' Na ce." A a ban ta'ba sha'awar siyasa ba, asalima ni malamar makaranta ce. Ya ce." Haba koda na ji shiyasa duk maganganunki suke fita cikin azanci da hikima. To Ubangiji Allah dai ya yi mana za'bi nagari." Gabad'aya muka amsa da 'Amin."
**
Cikin kasuwar sabon gari nake kutsawa na sayo kayan dinki cikin sau'ki da rahusa. Shiyasa nake rufe fuskata da nikabi gudun had'uwa da idon sani, wasu mutanan basu da gadonka amma suna da gadon magana akanka. Na kammala duk abinda zan saya da ya danganci sana'ata. Na fito bakin kasuwar na sayi kayan miya na k'arasa 'yan kura na sayi kifi d'anye da sauran abubuwan buk'atata.
Na tari shatar adaidaita sahu muka tsadance zai kai ni har kofar gidanmu dake kofar kabuga d'ari takwas. Ya taimaka mini wurin sanya kayan a babur din. Na shiga na zauna babu jayayya domin na san ya yi mini adalci sosai a yadda mai yake tsadar nan wani ma zai iya cewa sai na bashi dubu daya da d'ari biyar.

Gidan namu a bushe da alama Babanmu bai yo aiken kudin cefane ba, tunda sau tari sai ya fita abinda ya samu zai aiko musu su sarrafa. Kowacce tana dakinta. Yara kuma sun fita. Na bude dakina na shiga na zube kayan a gefe. Na cire nikab da hijabi na zauna ina mayar da numfashi.
Yusi ya shigo a guje ya zube a jikina Yana dariya.
"Mama mai ki ke sayo mini?" Tambayar da ya yi mini kenan. Na ce." Ina Kamalu yake? Ya zo ya d'auki wankin nan ya kai wa Halima tun jiya na fad'a mata zan kawo mata wanki."
Ya ce." Muna tashi daga makaranta shi da Saminu suka d'auki buhu."
"Suka d'auki buhu suka je ina?"
Ya ce." Tsince-tsince suke yi a bola su kai kangon Jadda ya basu kudi."
Raina ya 'baci ainun! Na ce." Yusi kada ka yi mini karya ka fad'a mini gaskiya tun yaushe suka fara jari bola."
Ya ce." Ni dai na gansu kusan sau uku, ni ma na ce zan bi su, Saminu ya koro ni gida."
Sai kawai na ji idona ya ciko da ruwan hawaye. Wato duk ko'karin da nake yi akan tarbiyar yarana Saminu sai ya rugaza mini. Ba na son yawon nan da suke yi lungu-lungu. Abin har ya kai su d'auki buhu su hau bola suna suna tsince-tsince bayan duk rintsi ana basu abinci . Na tashi na nufi wurin Ummansu Saminu domin na ji shin ta san abinda yake faruwa.

Tana kwance a tsakiyar rumfa da mafici a hannunta. Ta tashi zaune tana cewa." Na sani wallahi, to ya zan yi Amina, ai sana'a ce, muddin ba za su d'auko abin wani ba to ki kyale su kawai, yanzu fa rayuwar sai an hadu karfi da karfe iyaye da Yara an taimaki juna, sabulun wanki kad'ai ma ya ishe shi bawa, to balle ma duk ba wannan ake yi wa ba, abinda za a ci shi ake fafutuka."
Na ce." Ban 'ki maganarki ba Umma, amma ki yi nazari sosai akan hanyar da yaran nan suka d'auko, ban ce jari bola ba sana'a ba ce, amma ni wallahi a yanzu na fi buk'atar yaran nan su yi karatu, tunda daidai gwargwado ana yi musu hidima, basu rasa komai ba, to me zai sanya su dinga yawo da buhu suna hawa kan bola daga haka fa ba fata nake yi ba idan suka ga abin amfani su sai su d'auka su je su sayar kin ga wa gari ya waya."

Ta ce." To ni babu yadda zan yi Amina. Yaron nan Saminu ya kan taimaka mini idan ya yi buga-bugarsa. Kin fi kowa sanin yadda rayuwar gidan nan take, wataran a baka wataran ace ba a samu ba. Kuma ko an baka ba za a baka wanda zai isheka ba. Ba ni da jarin yin sana'a balle ki ce. Amma duk ranar da Saminu ya fita gwangwan muna ragewa gaskiya kin ga yanzu sha biyu da rabi amma har yanzu babanku bai aiko ba, Yara kuma ba su san babu ba, lokacin cin abinci Yana yi za su fara kuka."
Gabad'aya maganunta suka kashe mini jiki. Na ja k'afafuna da suka sage na bar bakin kofar dakinta.
Na jima Ina tunanin hanyar da zan bi gurin ganin na janye Kamalu daga tarayya da Saminu kaina ya kulle gabad'aya. Babu yadda za a yi su rabu tunda suna kwana a gida daya. Saminu ya girmi Kamalu da shekara uku. Amma a haka suke cud'anya da gwagwarmaya tunda shi Kamalu duk abokanansa yawanci sun girme shi daga na makarantar har na cikin unguwar. Duk wani yun'kuri da zan yi a yanzu dan ganin na datse ala'kar dake tsakaninsu za a yi mini wata fassara ne. Ni kuma akwai dalilin da ya sanya bana son tarayyarsu. Ban dai ta'ba gani da idona ba, kuma bai ta'ba yi mini ba,
amma a unguwar ana rad'e rad'in yaron yana d'auke-d'auke, idan kayi wasarare da abinka sai ya d'auka. Wasu lukutan ma yakan yi wa uwarsa ta kulle shi a d'aki ta yi ta duka.
Ina jin tsoron yau da gobe mu'amularsu ta canza mini yaro. Tunda Kamalu ko nawa zan ajiye a gabansa ba zai d'auka ba. Yana bud'e jakata ya d'auki kudi idan ina bacci ya dawo da canjin ya ajiye mini, idan na duba kudina na gansu cif a yadda suke. Wannan dalilan ya sanya na ke fargabar abotarsu.

Da yake idan na d'auki albashi abinci nake saya da d'an yawa. Dan sai na auno shinkafa kwano biyar na sayo 'karamin buhun taliya na auno garin towo. Da su mangyad'a da manja da hadin maggi. Da har buhun gawayi nake jinginewa, yau da gobe ta sanya na daina saboda idan na sa 'kafa na fita aiki sai na dawo naga an kwashe mini gawayin. Ba damar kuma na tambaya. Sai su ce na 'kala mu sata. Sai na daina sayan buhu nake aikawa gidan Mairo a sayo mini.

Dana gama abinci na zubawa Ashiru tunda shine k'arami a dakinsu. Ita kuma Ummansu Hadiza bata da k'ananun yara duk sun girma tunda itace uwargida. Amma dai dukda haka ina zuba mata itama.
To sai wajan biyu da rabi Babanmu ya Aiko musu da kudin abinci sannan Kowacce ta fara fafutukar abinda zata girka har zuwa lokacin Kamalu da Saminu Basu dawo ba. Raina ya baci ainun! domin lokacin makarantar allo ya kusa, ni kuma a rayuwata na tsani wasa da karatu ganin kamar shine gatan da za ka yi wa yaro, bayan haka kuma ni ma a yanzu karatun ne yake ri'ke da ni bayan d'inkin da nake yi....

Uku saura suka shigo gidan a firgice duk'un-du'kun 'kafafuwa da hannuwansu duk daud'a. Saminu ya yi d'akinsu da kud'i a hannunsa. Shi kuma ganina a bakin rijiya ina jan ruwa ya tsaya. Na kalleshi sama da k'asa kafin na ce." Daga ina kuke?"
Ya yi shiru bai ba ni amsa ba.
Saminu ya fito ya na cewa." Kai Kamalu ungo kudinka." Ya kar'ba da sauri yana fad'in." To ya na ga ka ba ni dari uku da hamsin, bayan gabad'aya abinda aka sayi kayan dubu daya da dari bakwai ne."

"E, Ummanmu ce tace mu bata aron kud'in. Zan cika maka sauran tunda tace gobe za ta bayar."
Cikin takaici na ce." Saminu yawon tsince tsince a bola kuke yi ko?"
"E, ai ni, na kwana biyu ina yi, shine Kamalu shi ma ya ce zai dinga bina. Idan mun samo k'arafuna sai mu kai kangon Adahama ya saya." Hankalinsa a kwance ya ba ni amsa.
Na girgiza kaina ban sake cewa komai ba, na d'auki botocina dana cika da ruwa na wuce na bar su a wurin. Kamalu Yana cewa ba zai kar'bi dari uku da hamsin ba.

Ban iya jurewa ba. Haka nan raina idan ya baci ban iya duka ba. Sautari akan fad'a mini duka ba zai tarbiyantar ba. Cikin wayo da dubara da ja ajiki ake ladabtar da zuriyar yaro. Hakan ya sanya na rage dukansa. Nake yi masa nasiha da kuma kawo masa misalai da hadisai. Amma a yau, raina ya 'baci sosai, na gaza ha'kuri sai da na bari ya sakankace tukkuna na rufe d'akina na kamashi da duka.
A lokaci Baba Sule ya shigo gidan. 'Kanin Babanmu ne. Ya zo ya tsaya bakin kofar d'akin Yana cewa." Amina an fad'a miki ki daina dukansa kin 'ki ji ko? Wato matan gidan saboda ba su suka haifeki ba shiyasa babu wadda za ta fad'a miki kiji. Dama tuntuni ina jin labarin abinda ki ke yi, kina yawo da mu a duniya kina cewa babu wanda yake taimaka miki dake da marayunki. To bari ki ji wad'annan yaran dole ne ki mayar dasu wurin kakarsu tunda tana raye, ba za su lalace a hannunmu ba, azo a yi kuka da mu. Wannan yaron Kamalu takad'iri ne, wa yasan abinda zai zama anan gaba tunda kowa baya furta alheri a kansa."
✍️
*GARUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*07084653262*
[11/12, 10:23 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*

*Marubuciyar*
*Yar bangar siyasa*
*Ba'aboren namiji*
*Madadi*
*Ga irinta nan*
*Goje*
*Babban yaro*
*Sadauki Omar*
*Nida Yaya sadam*
*Da sauransu..!*


'Yan uwa
Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS,
duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su
Sandal flakes
Hawee
Gabgab
Halut
Dorot
Coconut chips
Dufr(farce)
Black khumra
Brown khumra
White khumra
Oil perfumes da
Body sprays
Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku.
Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka
Call/WhatsApp
07037489958
Location:Gonan Ganye,zaria
Kaduna state
Nationwide Delivery

*3*
Na bude d'akin na fito ina kuka sosai na ce." Haba baba Sule wannan wace irin magana ce. Idan ba ku taimaka mini wurin kula da yaran nan ba ai ba za ku dinga furta munana kalamai a kan su ba. Wallahi ko kai ka ji abinda suka aikata sai ka yi musu hukuncu, a gaskiya maganganun nan da kake fad'a akan yaronan Kamalu sun yi tsauri da yawa."

Sai ya harzu'ka yana ce wa." Rashin kunya za ki yi mini don ubanki, ni za ki nunawa ban san abinda nake yi ba, an fad'a din Kamalu takad'iri ne ba ya ji, ko za ki musanta mini ne? yaron da kullum cikin d'auko miki magana yake, kaf zuri'armu babu fitinanne a can dangin ubansa ya samo wannan bakin halin. Akan ya je yana d'auko abin mutane ai gwara ya d'auki buhun ya tafi ya yi jari bola, ai sana'a ce, yara nawa ne suke yi, ko za ki gaya mini naki yaron ya fi na kowa, akan hakan ki ka zage karfi akansa kina dukansa, Murja ta yi mini bayanin komai, to wallahi idan ba ki yi wasa ba da kaina zan d'aukesu na mayar da su can wurin kakarsu su je su 'karata."

Cikin kuka mai cin rai na ce." To baba Sule duk mai ya kawo wannan maganganun? Wahalar nan wai wanene yake yi mini ita ne? yaran nan fa kwanciya kawai suke yi su tashi a gidan nan, duk d'awainiyarsu ni ce, na d'auka ai sai ana wahala da mutum tukkuna za a nuna gazawa akansa. A tsaye nake akansu ba zan iya bari su yi wannan sana'ar ba gaskiya magana kenan, Allah ma sai ya tuhume ni, tunda ya taimaka mini da yadda zany..... Ban yi tsammani ba na ji ya tsinka mini mari a fusace yana ce wa." Za ki nuna mini ba ni na haife ki ba kenan, tunda har zan iya fad'in Magana ki mayar mini da raddi, don ubanki ni ba kanin babanki ba ne, Ina ce ni ne na bada auranki ga uban yaran. Wato Ke har abada bakinki ba zai mutu ba ko?"
Ummansu Saminu ta ce." Ni abin ne ya ba ni mamaki Sule ashe duk zaman da muke yi a gidan nan, Amina ta na yi mana kallon sakarkaru wad'anda ba su iya tarbiya ba. Wato yanzu na gane nufin ki kina so ki janye yaronki a ganinki kamar ana so a lalata shi ko?"
Na ce." Ba haka nake nufi ba. Ni dai na ce ban yadda yarona ya yi jari bola ba, karatu nake so ya yi."
Baba Sule ya ce." To ke ma don ubanki gidan za ki bari aure za ki yi, ai ba a ce don ubansu ya mutu ki sarayar da k'uruciyarki ba. Tun wuri ki fito da miji ki yi aure." Ban ce masa komai ba na bar wurin zuciyata a cunkushe da tunani da fargabar mummunan kalubalen da yake fuskantoni.

Wannan ya wuce da kwana biyu wani abu bai sake faruwa ba. Kamalu ya ji fad'a da dukan da na yi masa. Ya rage wasu abubuwan mussaman da ya ga Baba Sule ya mare ni, sai ya dinga kuka a lokacin yana ba ni ha'kuri da al'kawarin ba zai sake ba.

***
Ranar juma'a da wuri suka yi wanka suka shirya tsaf cikin kaya iri d'aya hula da takalmi ma duk iri d'aya. Yusi ya kalle ni a sanyaye ya ce." Mama me yasa ba za ki je ba, don Allah ki shirya mu tafi tare."
Na ce." Yusi ba na jin dadi, zan bari zuwa wani satin idan muna raye sai mu je tare, idan kun je ku gaishe mini da Gwaggwo da kyau." Na kalli Kamalu dake tsaye a jikin bango sai 'bata rai yake yi, na ce." Kai na gane abinda ya sa duk lokacin da za ku je gidan Gwaggwo kake jin haushin saboda tana yi maka fad'a ko?"
Ya yi shiru bai ce mini komai ba. Na girgiza kaina tare da furta. " Ka d'auko ledar can shinkafa ce rabin kwano da taliya guda uku a ciki, ka kai mata, ungo wannan dubu biyu ce sai ka bata. " Ya kar'ba ya sanya a aljihu. Ya kama hanyar fita yana fad'in." Dallah malami taho mu tafi."
Da sauri na ce." Wallahi tallahi ka ci zalinsa a hanya sai ranka ya 'baci, muddin ka ta'ba mini yaro kasan karon mu da kai." Ya zum'buri baki ya fita."
Na kalli Yusi da yake ta walwala duk ranar da za su je wurin kakar tasu yana kasancewa cikin farinciki da nishadi. Sai na ji kwalla ta ciko mini a Ido. Yanayin sanyi da d'abi'a' sak mahaifinsa, mutum ne mai walwala da sanyi hali, baka ta'ba ganin fushinsa. Yusi kamar Yaya Aminu ya yi kaki ya tofar kamarsu d'aya.
Kamalu kuma wasu suna cewa da ni yake kama.
Na d'auki naira hamsin a cikin jakata nasa masa a aljihu ina fad'in." Idan ka ga wani abu a hanya ka saya. Ka yi kyau sosai
d'an saurayina."
Sai ya fashe da dariya yana cewa." Mama ki saya mini gilashi sannan ba ki fesa mini turare ba."
Da sauri na bude 'yar sif dina na d'auko turare ina fad'in." Kash an yi tuya an manta da albasa yarona d'an gayu ne."
Na fesa masa turare ko'ina a jikinsa. Na ce." Ku gaisa mini da ita da kyau."
Yasa takalminsa Yana cewa.'' To zan fad'a mata Mama zan ce sai wani satin za ki zo." Ya kama hanyar fita da sauri.
Na janye idona, a sanyaye na zame na kwanta kawai sai wasu hawaye masu d'umi suka fara sulmiyowa suna bin kumatuna. Ban yi yun'kurin gogewa ba tunda ni kad'ai ce a d'akin. Kukan kuma shi zan yi na samu sassaucin cunkusar da zuciyata ta yi. Abu biyu ne suka tarar mini. Duk lokacin da zan yi al'ada na kan kasance cikin k'unci da 'bacin rai. Sai kuma matsaltsalun da nake fuskanta. Matsalar Kamalu itace ta fi damuna a halin yanzu ba ni da wanda zai taya ni a gidan. Duk wanda zai bud'e baki sai ya ce masa fitinanne. Na san illar baki domin ana cewa har ya fi maita. So nake yi ni da yara mu yi nesa daga gidan da unguwar gabad'aya domin mu canza wata rayuwar, amma yin hakan ma kalubale ne mai zaman kansa.

Na 'kudindine a cikin mayafi na ci kukana na k'oshi. Cikin zuciyata na dinga nanàta addu'ar nan (Rabbi Inni Lima Anzalta Ilayya Min Kairin Fa'kir) ina ta kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Har Allah ya sassauta mini k'uncin da nake ji a raina. Na tashi na juye ruwan wankan dana d'ora.

A gurguje na yi wanka na shirya jikina tsaf. Lokacin na dan ji sassauci ciwon marar da ya matsanta mini kasancewar abin ya fara zuba. Na shirya na fito duk suna cikin d'aki. Na kulle 'kofata. Sannan na tsaya kowacce daga bakin kofarta na yi mata sallama.
Har na kai bakin kofar fita Ummansu Hadiza ta kira ni.
Na shiga na sameta tana d'aura dakakken yajin da take sayarwa na daddawa dana barkono. Ta ce." Ina ta zuci-zucin yi miki magana gashi kuma kin shirya za ki fita, Ina za ki je ne? Na ga an yi hutun makaranta ko kayan d'inki za ki sayo?"
Na ce." A 'a ba kasuwa zan je ba, gidan Sahura zan je."
Sai ta ce." Ayyo, to dama babanku ne ya ce na fad'a mini za ki yi ba'ko yau, Alhaji Mutari ne ya ce yana sonki da aure."

Cikin fad'uwar gaba da tsananin tashin hankali na ce." Wanene kuma Alhaji Mutari Umma sai kuma akace masa ni aure zan

2 / 18