Gudun Aure 1 Complete Hausa Novel

Author :  Binta Umar Category :  Romance

Chapter   4 / 18

9K to 12K   out of 51.4K words

rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*@Arewa book*
*Bintuumarabbale*
*free pege*
*5*
Bayan an gama komai sai muka fito bakin titi muna jiran abin hawa. Na dubeta a nutse kafin na ce." Sahura kin fahimci azancin wannan mutumin ko?"
Ta d'an yi shiru daga bisani ta ce." Na fahimta sis, amma kuma ban ga lefinsa ba, idan ba hakan ya yi ba sai a samu matsala. Kin san halin mutanan mu da son zuciya. Muddin dai zai kyautata kuma zai cika alkawari kamar yadda ya fada, ni kuma zan yi kokarin ganin na rike aikin da muhimmanci, ba za a samu matsala daga wurina ba."
Na ce." Hakane, amma dai dole sai kin kiyaye Sahura, domin aure shi yake gaba da komai, yadda na fahimce shi kamar bashi da damuwa akan auran mutum hakkin mijinki da yara. Shi dai kawai ku fito aiki akan lokaci, ba ki ji abinda ya ce ba, ya fi buk'atar zawarawa da 'yan mata wad'anda ba su da nauyi kowa a kansu, sai ya yi amfani da kuruciyarsu da lafiyarsu, kin ga kenan hakan yana nuna duk ranar da kuka kuskure ba za ku wanye lafiya dashi ba, gaskiya ni ina ganin kamar akwai fa son zuciya a sha'aninsa."

Ta yi murmushi tana ce wa." Ke dai Amina tunda aka kori marigayi daga kamfaninsa ki ka tsane shi, dukda cewa jama'ar gari na shelar mutumin arziki ne, amma ke ban ta'ba jin kin fad'i alherisa ba. Kwanaki fa har zagi ki ka d'ura masa, kin ala'kanta rasuwar mijinki dashi. Allah ina tsoron kada watarana ki yi su'btar baki a gaban jama'arsa su yi miki dukan tsiya."
Na ja tsaki tare da furta." Sahura kin san Allah da sanya hannun mutumin nan wurin mutuwar Ya Aminu. Abban Yusi jajurtacce ne sosai ya yi masa bauta kwarai da gaske, kema kin san da haka ranga-ranga magashiyan aka kawo mini shi gida ciwonsa ya tashi sakamakon aikin da suka yini suna yi a kamfanin. Haka ya kwanta jinya, mutumin nan bai ta'ba zuwa duba shi ba, daga 'karshe ma sai kawai takardar sallama muka gani, wai an d'ora wani a madadinsa. Kuma babu ko sisi. Duk ranar dana tuna wannan wula'kancin sai na yi kuka. Sahura tun daga lokacin fa jikinsa ya sake rikicewa har sai da ya mutu. Ya ba zan tsane shi ba."
Nasa hannu ina goge hawayen da suka zubo a kumatuna. Ta dafa kafad'ata cikin taushin harshe ta ce.'' Ki yi hakuri don Allah kin ga akan hanya muke, na yarda mutuwa d'aya ce, amma kuma tana da sanadi. Ki cigaba da yi masa addu'a. Sannan ki godewa Allah ni'imar da ya yi miki, ki tsananta da yi wa yaranki addu'a."

Na ja hanci tare da furta." Sis, ba na sha'awar aure wallahi, ina jin tsoron mazan yanzu, ina ganin kamar ba zan samu mai nagartar Yaya Aminu ba. Sannan kin ga ina da yara ba kowane namiji ba ne zai yarda ya aure ni dasu ba. Ni kuma ba zan iya tafiya yawon aure na bar su a wani wuri ba."

Ta tsayar mana da adaidaita sahu muka shiga. Ta ce." Kina da hujja Sis, amma fa kin san iyayenmu ba za su barki ki yi ta zama a haka ba, wand'anda suka fi ki shekaru ma suna yin aure ballantana ke da ki ke da talatin da wani abu. Kin ga a yanzu ne ki ke kan ganiyarki, amma zan yi miki uzuri idan kin ce ba za ki yi a yanzu ba sai yaranki sun girma tukkuna. Wannan kowanene zai iya duba hujjarki akan haka ."

Kira ne ya shigo wayata dake cikin jaka. Na fito da ita da sauri ina dubawa sai na ga anti Yagana ce. Da sauri na daga tare da furta."Anti barka da Juma'a. Ta amsa tana fad'in." Mai yasa ne yanzu ba a samun wayarki ta dadin rai, sai a yi ta kira tana katsewa. Na ce." Sai dai idan matsalar network ne anti fatan duk kuna lafiya ya yarana?"
"Kowa lafiya Lou alhmdullhi dama bikin babandi ne ya tashi satin da zamu shiga za a fara, na ce bari na gaya miki tunda an yi hutun makaranta ki zo ki shiga dangi, da yawansu suna tambayarki sai ki zo ku gaisa."
Na ce." Zan zo kuwa in sha Allahu anti Babandi ai mutumina na ne, in sha Allah zan gayawa Babanmu idan na koma gida."
"Kina Ina yanzu na ji kamar k'arar abin hawa."

"Muna cikin adaidaita sahu ni da Sahura na rakata neman aiki a wani kamfani." Ta ce." To an dace dai ko?" Na ce." E, an dace anti."
"Ki ba ni ita mu gaisa." Da sauri na mi'ka mata wayar.
Bayan sun gama gaisawa ta mi'ko mini wayar muka yi sallama tana sake jadadda mini lallai na gayawa Babanmu maganar bikin da wuri idan da hali shi ma ya zo d'aurin aure.

Ni ce na fara sauka a bakin titin gidanmu. Ita kuma aka wuce da ita. Ina sane ban kar'bi kudin da aka ba mu ba. Daf da zan shiga gida ta kira ni tana fad'in"Sis kudinki kin manta."
Na ce." Ina sane Sahura ki ri'ke sai ki yi amfani da su."
Ta ce.'" Amma ba ki kyauta mini ba wallahi. Kenan duk wahalar ke za ki yi mini."
Na ce." Ina wahalar take ni ban ganta ba." Sai ta kashe wayar na san ranta ya baci da abinda na yi. Ina da kudi tunda ba a jima da yin salary ba, bayan haka kuma na yi jakkunkuna da yawa an kai mini kofar wambai. Don na barwa Sahura dubi biyar ba wani abu ba ne idan na yi duba da irin d'awainiyar da ta yi da ni a baya.

Shaf na manta da maganar Ummasu Hadiza ina shiga gidan ko zaman minti goma ban yi ba ta leko tana cewa."Amina kin dawo?" Na ce." E, na dawo Umma."
Ta ce." Babanku da ya shigo cin abinci ya sake jadadda mini maganar d'azu akan Alhaji Muktari."
Na tashi zaune a nutse na ce." Umma ku yi ha'kuri don Allah ni fa ba aure zan yi yanzu ba, sai yarana sun girma tukkuna."
Ta jim tana kallona kafin ta ce." Ni kuma sai na ke yi miki sha'awar auran Alhaji Muntari domin yana da rufin asiri gashi da kula da gida."
Shiru na yi ban ce mata komai ba yadda zuciyata take tiriri zan iya furta wata maganar ta yi mata zafi.
Sai ta juya ta fita tana fad'in." Wani lokacin arziki yana kiran mutum sai ya yi ta gudu, ina lefin Alhaji Muntari in banda abin Amina.

Na koma na kwanta da nazarin yadda zan kawowa rayuwata da ta yarana cigaba.
Da 'kyar na tashi na d'ora mana taliya Ina da miya dama na kan yi ta kwana biyu ko uku."
Daf da magariba Yusi ya shigo shi kadai da ledar goruba a hannunsa. Na ce."Gwaggwo ce ta baka ne?" Ya daga kansa yana zaro kudi a acikin aljihunsa ya ce." Baba Hamusu ne ya ba ni dari da hamsin."
Na ce." An gode masa, ina Kamalu yake?"
"Mama tunda muka je gwaggo ta zuba mana abinci muka ci, sai aka neme shi aka rasa. Yanzu ma Baba Hamisu ne ya tsallako da ni titi, na 'karaso gida.

Cikin fad'uwar gaba da fargaba na ce." Aka neme shi aka rasa kamar Yaya?" Ya yi shiru bai ce komai ba.
Na d'auki wayata da sauri na nemi lambar Hamisu kanin Babansu ne. Muka gaisa na ce." Yusi ya dawo gida shi kadai, yana ce mini tun d'azu ba a ga Kamalu ba."
Ya ce." E, wallahi ni ma dawowata gida kenan gwaggo take gaya mini, tunda suka ci abinci ya fita, amma ki kwantar da hankalinki zai dawo in sha Allahu, kin san halinsa ba ya zama wuri daya."
Na ce." Hamisu Ya zan yi ne? Kamalu ne damuwata a halin yanzu, ka dubi shekarunsa ba su kai sun kawo ba, amma yana so ya fi karfina."
Ya ce." Ki daina fad'in haka Anti Amina, duk yaran namu haka suke k'uruciya ce kawai, da ya kara shekaru zai daina. Sannan ki dinga tsinkaye kafin ki fad'i magana a kansa."
A sanyaye na ce." Shikkenan Hamusu don Allah daga ya dawo ka kawo mini shi har kofar gida."
Ya ce." In sha Allahu rabbi."
Na kashe wayar na ajiye jikina duk babu kuzari na tace taliyar na juye a fulas.
Idar da sallata kenan na ji kaya-kaya hayaniya na tashi a kofar gida. Yusi ya shigo da gudu yana fad'in." Mama wasu ne suka daddaki Yayana har sun fasa gefan ido suna ta ce masa 'barawo, 'yansanda sun riko shi."
Gabana ya yi mummunar bugawa. Na tashi da azama na fita. Lokacin matan gidan da yaran duk sun yi waje. Kofar gidan namu ta cika da jama'a, ga Kamalu ri'ke a hannun 'yansanda da wasu yara su biyu a tsakiya.
"Wacece mahaifiyarsa ne?"
Muryar d'ansandan ta daki kunnane.
Saminu ya nuna ni da hannu yana ce wa." Gata nan."
Ya kalle ni." Yaron nan an kama shi ne yana yun'kurin 'kwacewa yaran nan kud'i an aike su sayan shinkafa a wurin mai awo na kan kwanar layin nan."

Shiru na yi ban ce komai ba illa kaina da yake mugun sarawa. Ya cigaba da cewa." Ku dinga kula da yaranku, duk dai yaran yanzu sai addua amma dai duk da haka sai iyaye sun tsananta kula da addu'a. A dinga basu abinci duk rintsi kada a bar su da yunwa domin itama tana taka muhimmiyar rawa wurin gurbata tarbiyar yaro. Kasancewar shekarunsa basu kai matakin hukunci ba, za mu 'kyale shi. Amma da sharad'i idan ya sake shigowa hannunmu sai mun hukuntashi."
Usaini 'kanina ce ya ce." Mun gode Yalla'bai in sha Allahu kuma za a kula, wallahi mahaifiyar yaron nan a tsaye take akansa maraya ne kuma mahaifinsa ya rasu, kawai rashin ji ne irin na mutumin yanzu."
Ya zaro dari biyar a aljihunsa ya basu. Suka kama hanya suka tafi. Baba Sule ya 'karaso wurin Yana cewa." Tunda naga cincirindon jama'a a kofar gidan nan na san d'an iskan yaron nan ne ya janyo magana."
Jin abinda yake fitowa daga bakinsa ya sanya na shige gida ba tare na tsaya gaishe shi ba.
Gabad'aya suka shigo gidan har shi Kamalu da Yake rike a hannun Usaini Baba Sule yana kai masa duka yana ta zagi da aibata shi.

Na kwanta hawaye masu d'umi suna bin gefen fuskata. Sai kawai na tsinkayi maganar Ummansu Saminu tana cewa." To dama ai ba dabararka ba ce ba kuma wayonka ba ne. Kullum dai ana ganin namu yaran sune lalatattu, to yau sai gashi kuma su Kamalu har da 'yansanda."
Baba Sule ya ce." Shine dama d'an iskan cikinsu ai, za su zo su gurb'a ta mana zuri'a.

Ita dai Ummansu Hadiza ba ta ce komai ba. Har ya gama zage-zagensa ya dago labulan dakina yana fad'in." Ke kina Amina." Shiru na yi ban amsa ba. Ya shigo d'akin sosai yana fad'in." Tashi zan yi magana dake." Na tashi ina goge hawayen da suka kasa tsayuwa.
Ya ce." Ki mayar da yaran nan danginsu shi ya fi miki kwanciyar hankali, ki yi auranki tunda ba ki wuce ba, akan me za ki zauna ki lalata k'uruciyarki a banza, ba fa ke kike da hakkin kula dasu ba, dangin babansu ne suke da hakki a kansu. Ki kwantar da hankalinki, ki samu nutsuwa in sha Allahu idan ki ka auri Alhaji Muntari ba ke kadai ba, mu kanmu za mu ji dadi, domin mutum ne mai wadata da bushasha ko ni zan huta ta dalilinki."

Na dube shi Ina 'kara ganin ba'kinsa a cikin raina. Na ce." Baba Sule ba zan yi aure ba, tunda ba farilla ba ne, musulunci da maslaha ya zo mana. Gaskiya yanzu Babu wannan ajandar a tare da ni, saboda inda da hujja. Bayan haka kuma ni ba yawon ta zubar nake yi ba balle ace ina neman janyo abin kunya, sannan ni nake wahala da kaina da yarana. Don Allah ku 'kyale ni da maganar auran nan haka."
Cikin fushi ya ce." An ki a kyale ki din wallahi tallahi ba ki isa ba, sai kin yi aure Amina. Mu ba al'adar gidanmu ba ce haka iyaye da kakkani, ba za ki zauna mana god'od'o a gida ba."
Na dube shi cikin rashin shakku na ce." To shikkenan zan nemi Babanmu da maslaha sai na je na kama haya, tunda ka ce ba zan zauna muku a g.......Ya bi kuncina da mari mai tsanani!
Jikinsa na kyarma yake fad'in." Kin samu kudi ko Amina, kina ji babu wanda ya isa saboda ba kya nema a wurin kowa shiyasa ki ke gaya mini maganar da duk ta zo bakinki, wallahi ba ki wuce duka ba, zan zage gabad'aya karfina akanki na nakastaki muddin ba za ki bi umarninmu ba."

Ina kuka haikan na ce." Zan fi son ka nakastani Baba Sule ni wallahi ka kashe ni ma, na gaji da wannan duniyar ba zan iya ba, me yasa lokacin da nake budurwa ba ku damu da aurena ba, sai a yanzu da Ubangijin da ya hallice ni ya ba ni za'bi. Ina da hujja Baba, ba wai ina gudun auran ba ne, akwai dalilina."
Kuka nake tu'kuru Ina fad'in." Baba Sule ka dake ni, idan hakan zai sanya ka huce! ina so na mutu na riski Yaya Aminu a aljannar Firdausi."
Kamalu ya zo ya ru'kunkume ni yana kuka. Shi ma dan'uwan nasa ya zo ya zube a jikina ya fashe da wani irin kuka mai soya zuciya....✍️
*1k on talgram via 0542382124..Binta Umar gtbank ko 7084653262...Binta Umar Opey bank mutanan nijar katin Airtel na dala dari*
*08089965176*
*07084653262*
*What'sapp kawai!*
[11/15, 9:38 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*

*TALLAH!*
'Yan uwa
Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS,
duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su
Sandal flakes
Hawee
Gabgab
Halut
Dorot
Coconut chips
Dufr(farce)
Black khumra
Brown khumra
White khumra
Oil perfumes da
Body sprays
Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku.
Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka
Call/WhatsApp
07037489958
Location:Gonan Ganye,zaria
Kaduna state
Nationwide Delivery


@Arewa books
Bintuumarabbale.
*Free pege*
*6*
Ya kama hanya ya fice daga dakin yana cigaba da fadin." Yadda ki ke ganin kin yi 'kwari a yanzu babu wanda ya isa ya gaya miki ki ji, to nan gaba idan ki ka fi haka za ki ce ba mu muka haifeki ba, ni Sule idan ni ne waliyinki to tabbas ba ki da miji sai Alhaji Muntari, domin ba za mu ta'ba bari wannan damar ta wuce mu ba."
Duk cikin maganganusa babu wadda ta razana ni. Dole dai sai da yarda ta tukkuna za a d'aura mini aure, ba zan yi ba din saboda hujjata ta fi ta su karfi.
Muryar Hamusu na tsinkaya a tsakargidan suna gaisawa da Ummansu Hadiza. Na ji dad'i da bai riski Baba Sule ba, lokacin ya tafi. ya shigo d'akin yana ce wa." Ina Kamalun yake?''
Jin haka ya sanya yaron da sauri ya zo 'buya a bayana ya fara kuka. Ya kuwa janyo shi ya fara gwaura masa mari wanda ya gigitashi ya k'wallara ihu! ya rike tsintsiyar hannunsa da kyau! yana fad'in." Mai kake so ka zama Kamalu? nawa shekarun naka suke a duniya da za ka dinga daga mana hankali, kai ba ka tausayin uwarka da take ta fadi tashi a kanku, ba zaka ri'ke maraicinka ba ko? idan ka yi wa Yaya Aminu haka ba ka yi masa adalci ba, sannan ba ka yi wa kanka adalci ba, kaf zuri'armu babu wanda ya ta'ba shiga hannun hukuma sai kai daga tasowarka zaka jaza mana abin bala'i da maganar mutane."
Bai dubi ihun da yake kurmawa ba ya 'kara kai masa wani marin a d'aya kumatun. Ya kid'ime sosai yana fad'in." Don Allah Baba Hamusu ka yi hakuri ba zan sake ba. Wayyo Allah Ummansu Saminu ki zo ki cece ni." Ya rike shi da kyau! ganin yana ta kiciniyar fizgewa daga hannunsa. Ya ce.'' Wallahi ni ne maganinka Kamalu makaranta zan kai ka, a d'aure ka da sa-sari(mari!) ka je can ka zama almajira mahadaccin al'kur'ani, ba za ka d'orawa mahaifiyarka ciwo ba."
Jin haka sai ya sake gigicewa yana fad'in." Na rantse da Allah ba zan sake ba, Baba Hamusu don Allah ku yi hakuri." Ya juyo yana kallona " Mama ki yi hakuri ba zan sake ba." Yusi yana kuka sosai kamar shi ya aikata lefin ya daddafa 'kafafuna har sai da na ji yadda jikinsa ya rawa. Ya ce." Mama ki yi hakuri, ki ce kin yafe masa, don Allah kada ki bayar dashi aka shi almajiranci kin ji mama."
Wasu hawaye ne masu tsananin zafi suka kece mini. Tausayin yaran ya kara tsananta a cikin zuciyata. Haka suke yi a junansu mussaman shi Kamalun ya yarda ya ci zalin d'an'uwansa, amma bai yarda wani ya ta'ba shi ba. Ko a makaranta ne idan aka ci zalinsa a ajinsu ana tashi sai ya tare hanya har sai ya ramawa d'an'uwansa hankalinsa yake kwanciya. Duk lokacin da Kamalu ya yi lefi ina yi masa fada. Yusi shi yake shiga damuwa fiye dashi wanda ya yi lefin, ya dinga ba ni ha'kuri kenan.
Ya je da rarrafe ya rike kafafun kawun nasa Yana cewa." Baba Hamusu don Allah ka yi hakuri ba zai sake ba, kada ka kai shi bara."

Ummansu Hadiza ta le'ko tana fad'in." Hamusu ya isa haka, ai ya bada ha'kuri, dukan ba zai shiryar ba sai dai addu'a, kuma dai kowa da irin k'uruciyarsa. Tasa ce kawai ta fito fili,

4 / 18