Gudun Aure 1 Complete Hausa Novel

Author :  Binta Umar Category :  Romance

Chapter   10 / 18

27K to 30K   out of 51.4K words

shima ba lefi yana da rufin asiri a ka kaita gidanta dake karkasara. Sai na cigaba da rayuwa ni dasu Hassana da Usaina wanda suma a lokacin sun kere mini tsawo da girman jiki. Ni ba ni da wani girma A
amma ba na cikin jerin masu tsamurmuri jiki. Daidai misali ina da tsayi da cikar kirji da baya don wuyana a cike yake kowane d'inki na sanya a jikina yana zama mussaman fittedgown da riga da siket. Irin jikin Mamanmu ne da ni, mai kyau da boye tsufa. Sannan ba ni cikin farare haka zalika kuma ba ni cikin ba'ka'ke wuluk ina tsakiya fatata tana da kyau sosai shiyasa bana Gigigin shafa mata mai in banda cocorbutter quin Elizabeth shine man shafawata har hazar yau. Su kuma suna da girman jiki kuma a sake yake sharkaf irin na Ummansu. A wasu lukutan ma mutane suna d'auka yaran duk sun girmeni ni sai dai kawai na yi ta dariya ina mamakin yaran da aka haife su a gabana ya za a yi a ce sun girmeni kawai dai idan kana da jiki mai kyau ne sai ka ci zamaninka ka ci na wasu haka abin yake.

***
Hadiza ce koyaushe take cikin matsalar aure. Ita Fati tana zaune kalau. Sai narka ki'ba take yi. kuma shekara da yin auran ta haihu lafiyar Allah aka sha shagali. Ita kuma Hadiza ga dai gidan 'kato da kuma ci da sha amma babu nutsuwa. Bata sati daya sai ta zo gidanmu sun fita da Ummansu.

A cikin wannan hargitsin Iya kakarmu ta rasu sakamakon ciwon wuya da ta kwana biyu ta na yi. Abin ya zo da 'karar kwana Allah Ya kar'bi abarsa. Muka ci kukanmu muka koshi domin ba 'ya'yanta kawai ne ba suka yi rashin har da mu. Saboda tsohuwar akwaita da dattako da k'aunar jikokinta. Kuma ba ta ta'ba nuna bambamci a tsakaninmu.

Bayan an share makoki
sosai na mayar da hankali wurin koyan d'inkin da na sanya a zuciyata. Allah kuwa ya taimaka mini na gwanance kamar wasa Maman bokola za ta yanka d'inki ta ba ni ta ce na hau keke na had'a. Duk wahalarsa kuwa haka zan hade shi tsaf. Ta dinga mamaki. Tana fadin kina da fikira da ko'kari Amina, za ki ci abinci da d'inki in sha Allahu rabbi.
Idan na had'a mata riguna sai ta d'auki kudi ta ba ni, ni kuwa naki kar'ba na ce ai bata d'auke ni aiki ba tukkuna yanzu akan koyo ne don haka ba zan kar'ba ba. Haka za mu yi ta bugawa da ita har dai ta gaji ta ce to ta d'aukeni aiki na dinga zuwa shagonta. Na ce mata tunda daf muke da zana jarrabawa hankalina zai kasu gida biyu idan mun kammala sai na kama aikin gadan-gadan, yanzu sai dinga zuwa ina taimaka mata. Ta ce Hakan ya yi, ta yi mini addu'a da fatan alheri.

Bayan mun yi jarrabawar fita daga sakandire da kwana biyu aka kawo kudin auran Sahura. Sai a lokacin ne jikina ya dan yi sanyi da abinda yake faruwa da rayuwata. Wato tunda na taso nake ganin yadda samari suke karakaina akan 'yan'uwana, amma ni babu wanda ya ta'ba sansanta da sunan so. Ban san wane irin bakin jini ne da ni ba, gashi yau an kawo kudin auran Sahura wadda muke fad'uwa tare mu tashi tare, sannan Hassana da Usaina su kansu akan hanya suke domin an gama magana da iyayen samarin da za su aure su, kudi kawai za su kawo a tsayar da magana.
Sai na ji hankalina ya tashi, na fara tunanin ko dai Ina da matsala ne ban sani ba.
Ashe irin tunanin da nake yi shi Gwaggo take yi. Watarana ta kawo mini magunguña da turare ta fad'a mini yadda zan yi amfani dasu.
Ban yi kasa a guiwa kullum da magariba zan yi turaran. Har Ummansu Hadiza ta ankara ta tambayeni na gaya mata. Sai ta kama dariya tana cewa ai dole sai da turaran a lamarinki Amina. Ko a ina ki ka gado bakin jini oho. Ta wuce ta barni tana ta dariya. Na ji Anti Sakina tana cewa ko dai ki ka jefeta ai bata da makusa yarinyar duk tafi yaranki kyau, amma kin sanya gilli da bakin kishi a ranki, kowa ya ga wannan abin ya san jifa ne.
Wannan furucin ya haddasa musu rikici a gidan suka dinga cacar baki ni dai na yi shiru ban ce musu komai ba har suka gaji suka yi shiru kowacce ta shige d'akinta.

Haihuwar Fati ta biyu ta yi daidai da bikinsu Hassana. A lokacin kuma ni da Sahura mun samu damar shiga makarantar gaba da sakandire wanda ba yadda Ummansu Hadiza ba ta yi ba akan Babanmu ya hana ni, shi kuma ya ce ba zai yiwu ba tunda babu kwabonsa a ciki, ba zai dakatar da ni ba. Na je na yi karatun tunda mijin bai samu ba. Ta dinga jifana da mugun baki tana fad'in babu abinda ake koyowa a jami'a, sai Iskanci, ita ba zata bari yaranta su yi zurfin karatu ba aure shine gaba domin umarnin Allah ne. A wannan lokacin ne Babanmu ya yi mata jan Ido akaina ya ce duk lokacin da ta sake jifana da wata mummunar kalma sai ya yi shari'a da ita. Hakan ya sanya ta ce to ta zare hannunta daga kaina. Tunda ta gama wahala da ni, na girma za a nuna mata ba itace ta haife ni ba. Hakan ya yi wa anti Sakina dadi, sai ta fara jana a jikinta. Ban yadda na janyu ba saboda na riga na san hakan duk salon makirci ne, kadaran kadahan nake zaune da su. Ina basu girmamsu daidai gwargwado amma ba na yarda su taka ni, tunda na girma na san abinda yake yi mini ciwo.
Aka yi bikinsu Hassana kowace aka kaita dakinta. Sai na zama ni kadai a d'akin, idan zan fita na kan kulle tunda anti Yagana ta saya mini keken d'inki. Akwai kayan mutane a ciki na aikatau huluna da jakunkuna. Da nake yi suna biyana. Sannan wasu lukutan na kan d'auko aikin da nake dashi a shagon Maman bokola na yi a gidan. Shiyasa na sayi katon kwad'o nake kullewa a duk lokacin da zan tafi makaranta.

Muka dinga fa'di tashi da zurga-zurga makaranta tare da Sahura, kuma kamar yadda Yayansu ya yi alkawari bai bambamta ni da ita ba, duk abin buk'ata da ya danganci karatunmu tare zai saya mana Wanda ita a d'akinta ta kammala. Ni kuma har lokacin ba ni da wani tsayayye. Ina dai ta addu'a da neman yadda asirina zai rufu domin a lokacin na mayar da hankali sosai wurin neman aiki, da kuma fitar da style na din'kunan mata. Sosai nake neman kud'i a gidan. Hakan ya janyo mini kwarjini da mutunci a wurin matan Babanmu Mussaman Ummansu Hadiza da ta watsar da makamanta a kaina ta fara jana a jiki tana nuna mini k'auna. Hadiza da a can take ganin tafi karfin ma ta kula ni idan ta zo gidan sai ya zamana tana shakkata don ganin irin sutturar da nake sanyawa tana nema tafi karfinta ita da take da miji. Babanmu kuwa yadda nake taimaka masa shiyasa koyaushe cikin sanya mini albarka yake. Anti Sakina itace muke sama-sama Hakan ya samo asali ne dalilin 'kin auran 'kaninta da na yi saboda binciken da na yi akansa aka tabbatar mini da cewa ba shi da wata cikakkiyar sana'a sai maning, sannan uwa uba yana shaye-shaye, kullum yana shagonsa a kwance da waya a hannu wasu ma suna zargin yana harkar yahoo (damfara) ita kuma ta kawo mini shine a ganinta ta rufa mini asiri ganin yadda duk na tsofe a gida, an aurar da 'yan uwana, 'yan matan unguwarmu a yanzu duk babu sa'ata. Shine ta yi mini wannan gwanintar. Tabbarar mini da munanan halayensa ya sanya na ce ban amince ba. Babanmu ya goya mini baya, shine dalilin da ya sanya take jin haushina har tana fad'in dama can na yi masa girma tunda na girmeshi kawai dai ta tausaya mini ne shiyasa tace masa ya aureni . Maganarta ta ba ni dariya sosai a lokacin sai na shareta ban tanka mata ba, muka cigaba da zama a haka ina ko'karin kaucewa duk abinda zai janyo mini samun matsala da su a gidan, amma ba na yarda su zo mini da son zuciyarsu....✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[11/22, 10:12 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*

*@Arewa books*
*Bintuumarabbale.*
*Na yi nisa a arewa idan ba kya son jira ki yi maza ki garzaya can Kisha karatu!*
*Domin biyan kudin karatu a talgram kuwa 1k ne ga hanyar biya 0542382124...Binta Umar gtbank mutanan nijar dala dari ne katin airtel sai ku kankare hoton a turo mini sheda ta wannan lambobin*
*Whasap kawai*
*08089965176*
*07084653262*
Astagfirullah jiya na yi mistake typing error inda zan rubuta Alhaji Halilu wato mijin da Hadiza ta aura sai na rubutu akasin hakan. Wad'anda suke bibiyar littafin nasan za su gani bisa kuskure ne, ina neman afuwa.
*Free peges*
*13*
Watarana katsam Yaya Aminu ya zo yana gaya mini ya sama mini offer ta aikin koyarwa. Saboda murna kamar na rungumeshi na rasa ina zan tsoma kaina. Na dinga yi masa godiya wanda har na gaza ha'kuri na tambaye shi yadda aka yi ya sama mini aikin da har na fitar da raina da samuwarsa. Nan yake gaya mini wani abokinsa ne da suka yi harkar siyasa. To shine mutumin da suka wahaltawa da ya samu kujera ya raba musu offer biyar domin su taimaki makusantansu. Cikin ikon Allah ya kaiwa kanwarsa daya ya rabar da sauran. Tunda lokacin shi yana aiki a karkashin kamfanin Alhaji Tajo. 'Kanwar tashi sai ta rasu, shine ya nema mini alfarmar maye gurbinta da ni. To komai dai rabo ne, kuma na tabbata addu'ar da nake yi ita Allah Ya kar'ba ya kawo mini aiki cikin sau'ki da rangwame. A daidai lokacin ne itama Sahura ta samu aikin rabon magani 'kauyika amma mijinta Idiris ana ta turzawwa dashi ya 'ki amincewa bayan kuma ba haka akayi dashi ba kafin auran.
Cikin hukuncin Allah na fara zuwa aiki da zuciya daya. Sai dai yadda 'yan gidanmu suke ko'karin juya mini manufa shi ya fi damuna. Mutanan unguwarmu ma suna ganin kamar yanzu na yi karfin da babu wanda ya isa ya gaya mini na ji, tunda babu uwata a gidan matan Babana ban d'auke su a bakin komai ba. Wasu ma suna fad'in duk an yi wa 'yan'uwana aure ni kuma na tsaya za'be sai mai kudi. Kowa dai da irin kallon da yake yi mini akwai masu cewa ma zaman kaina nake yi, na fi karfin Babanmu tunda ina bashi kudi na toshe masa baki. Wannan maganar kuma daga bakin Ummansu Hadiza ta fita, domin itace mai yawan fad'in haka har jama'ar unguwa suka d'auka.

To da yake komai ya yi farko yana da k'arshe. Idan kaddara ta gifta babu yadda bawa zai yi dole ya kar'beta hannu biyu, ya kuma roki Allah Ya sa alheri ne faruwar Hakan.
Budurwar da Yaya Aminu yake nema da aure har an kai kudi da sa ranar d'aurin aure rana tsaka ta bijire tace ta fasa. Kuma kada ku d'auka lafiyayayyace kamar kowa. Bai yi gigin haka ba saboda shima ya san ga yadda Allah ya yi shi, sai ya nemi daidai dashi don har ya fi ta lafiya ma tunda shi yana yawo da 'kafafunsa, sa'banin ita da kafafun suke a nanna'de a keke take yawo. Sai dai kyakykyawar gaske ce fara tas da ita. A haka suka kulla soyayya har suka kai matakin aure rana tsaka wani gurgu d'an wani attajiri ya ganta a wani taro da suka yi irin nasu. Ya ce Yana sonta. Ganin daga gidan da ya fito ya sanya iyayenta da ita kanta suka dawowa da Yaya Aminu kudinsa wai ya nemi wata.
A lokacin ya shiga rud'u sosài, domin ya d'okanta da auran da ya shafe shekaru sama da arba'in a kasa bai yi ba, har furfura ta fara feso masa, kuma a hakan ma bashi gwaggo ta fara Haifa ba, ta yi haife-haife kafin zuwansa yaran suna rasuwa. Sai da shekarun girma suka cimmata ta haife shi, Allah Ya raya shi tare da d'an'uwansa Hamusu da tazarar da take tsakaninsu take da yawa. Wannan dalilin ya sanya hankalinsa ya tashi. Ita kanta Gwaggo ta shiga damuwa. A lokacin ne ya zo har kofar gidanmu ya aiko nazo.
Na fita na same shi muka gaisa ba yadda yake duk ya yi rama. Ya fara tambayata ko Ina da tsayayyen wanda zan aura. Na ce masa babu. Sai ya bijiro mini da bukatarsa akan na share masa hawaye, idan kuma da takura ko ba na sonsa kada na cutar da kaina na gaya masa sai ya ha'kura.
Na ce wallahi ko ka fi haka nakasa da talauci zan aureka Yaya Aminu, kuma da zuciya daya, na amince Ubangiji Allah Ya tabbatar mana da alheri.

Ba'a ja dogon lokaci ba iyaye suka shiga lamarin. Ummansu Hadiza ta dinga fad'in dama tuntuni na fahimci soyayya kuke yi, tun kina yarinya. To tunda shi ki ka gani, ai ba mu da abinda za mu ce akan haka. Anti Sakina kuwa dariya take yi tana fad'in. Ai ta gwammace ta auri nakasashe an kawo mata mai lafiya da aikin yi ta ce ba ta so. To za mu ga zuwan da dawowar ai. Duk maganganunsu akan lamarin bai dame ni ba. Kawai dai ni na tsananta da addu'a Allah Ya sanya mana alheri da albarka a cikin auranmu.
Danganin Mamanmu ba su k'yamaci lamarin ba sanin wacece Gwaggo ya sanya suka nuna faricikinsu da hakan. Kuma suka yi mini shatara ta arziki a lokacin auran duk abinda ake Yayi da buk'ata sai da suka saya mini aka shirya mini dakunana biyu wanda Yaya Aminu ya kama hayar gidan a can sharad'a wajejen kamfanin da yake aiki ya yi hakan ne domin ya samu sau'kin zuwa neman abincinsa.
Zaman lafiya muka gudanar a zaman auranmu, tunda aka yi babu wanda ya ta'ba jin kanmu, Muna ta rufawa juna asiri, duk wanda zai zo gidana sai ya yi sha'awa domin ba na yin girki lami sai da nama ko kifi, kuma idan mutan zai tafi na bashi kudin mota. Na ri'ke aikina da sana'ata hannu bibbiyu, muka dinga cud'a rayuwar har na yi haihuwar fari, wata matsala ba ta faru. Irin sa'banin nan na zama ba mu taba samu ba, tunda kowa yana ko'karin kiyayewa da kyautata mu'amula da abokin zamansa.

WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA RAYUWATA TA BAYA.

Saukar hannu na ji a kumatuna. Da sauri na bud'e idona, sai na ga Yusi a gurfane a gabana Yana kuka harda shashsheka. Gefe kuma Kamalu ne ra'kube a jikin kusurwa sai ajiyar zuciya yake saukewa.
Ganin haka ya sanya na yi namijin ko'karin daidaita kaina. Na tashi na dan gyara abinda ya samu a d'akin. Na gyara musu shimfida kafin na kira Usaini na bashi kudi ya sayo mana abinci, don ba zan iya yin komai ba saboda gajiya da fargaba.
Suna cin abincin na ce dasu su kwanta sai da safe kuma.
Suka shiga net din a tare Ina kallon yadda Yusi yake ta rirri'ke dan'uwan nasa da har yanzu yake a tsorace Yana ganin zan shammace shi ne kamar yadda na saba na zane shi.
Kiran anti Yagana ya shigo wayata dake cikin jaka. Na d'aga da sauke ajiyar zuciya. Tambayar da nake hasashe ita ta jefo mini.
Na ce." Ai an gama komai sun ba mu yaran. Amma sai da aka yi dauki ba dad'i sosai da jama'ar unguwar.
Ta ce." Ubangiji Allah Ya kiyaye faruwar hakan anan gaba, ki yi ta addu'a watarana sai labari."
Na ce." In sha Allahu rabbi anti, sai da safe."
Muka yi sallama na ajiye wayar na fita na d'auro alwala domin ban yi magariba da isha'i ba. Da kyar na iya tsakurar abinci, hakan ma don dai kada na kwanta ban ci ba, na cutu, shiyasa na ci kad'an, na zame na kwanta a kan daddumar ina lumshe ido. Bacci ya fara fizgata kira ya shigo wayata a karo na biyu, ban kawo kowa ba sai Alhaji Muntari, shine ya kan kira ni a irin wannan lokacin, sai na kan rasa azancin hakan, mutumin da yake da iyali ai a irin wannan yanayin ya kamata ace yana tare da wadda ta yi girki.
Ban saki jikina ba sosai, dalilin damuwar da nake ciki, da kuma fargabar kada hakan ya haddasa masa rikici a cikin gida domin na san ba kowace mace ba ce za ta iya daurewa da hakan, na dinga yin hamma ina amsa masa magana a kasalance. Hakan ya sanya shi yi mini sallama yana fad'in da safe zai sake kirana mu k'arasa tattuna maganar tunda na dawo a satin yake so a yi komai a gama.
Na ajiye wayar. Idona a lumshe na cigaba da nazarin yadda abubuwan za su kasance anan gaba, ko na'ki ko na so, dole na auri Alhaji Muntari domin katange kaina da mummunar kaddarar da take shirin rufto mini. A zahiri na furta 'Allah Ka takaita mini wahala'

Ban yi wani baccin kirki ba dalilin tunanin da ya'ki barina, akan kunne da idona asubahi ta yi. Na yi sallah, yaran ma na tashe su kamar koyaushe suka daura alwala suka fita. Ban koma bacci ba domin na san akwai wad'anda za su dako mini sakammako abinda ban k'arasa ba, na kammala. Duk wadda ta zo kar'bar dinkinta ba na yarda na bata sai ta cake mini kudina tukkuna. Domin zurga-zurgar nan, da wannan matsaltsalun kudin hannuna duk sun kare, don dai ma Alhaji Muntari ya taimaka mini da wasu.
Yusi ne ya shigo shi kadai jikinsa sanyi kalau saikace wanda ya tashi daga ciwo fatar samar idonsa duk ta tasa, tamkar shi ya aikata lefin duk ya shiga damuwa. Na kalleshi a nutse na ce ." Ina Kamalun yake?"
"Yana can massalaci a kwance Yana bacci, wai kafarsa ce take ciwo. Mama kin ga har ta kumbura."
Na ce." Je ka taso shi, ka ce ya zo in ji ni."
Ya kalle ni. "Mama tsoro yake ji kada ki dake shi, shiyasa ya kwanta a

10 / 18