Author : Binta Umar Category : Romance
yi, ko ni kad'ai ce bazawara?"
Ta zuba mini ido na minti biyu kafin ta ce." Matsalarki kenan Amina rashin tauna magana, ni sa'arki ce da za ki ba ni amsa cikin gatsali."
Na sassauta fuskata na ce." Umma zancen ne na ji shi kamar saukar aradu wallahi, ki yi hakuri don Allah."
Ta ce." Alhaji Mutari Ubangidan Babanki Sule shine ya nuna masa hotonki, shi kuma ya yi Allaragaf dake."
Na ce." To ba za ta yiwu ba, Umma ba aure zan yi ba, tarbiyar yarana ce a gabana a yanzu, kuma ko zan yi aure ni zan duba mijin da zan aura wanda ya cancanta babu ruwana da dukiya nagarta nake nema kamar dai Yaya Aminu, in sha Allahu zan samu."
Ta ce." To, ni dai na isar da sa'kona Amina, amma ki yi nazari sosai akan maganar kafin ki yanke hukunci."
Na yun'kura na tashi ina cewa." To zan yi, in sha Allahu Umma sai na dawo."
Ta ce." Ki gaishe da Sahura da yaranta." Na kama hanya na fita ba tare da na sake cewa komai ba tsabar tashin hankalin da nake ciki.
Cikin zullumi da tunani mai zurfi na isa gidan Sahura. Na same ta tana shirin fita. Ganina a hargitse ya d'aga mata hankali.
Na nemi wuri na zauna kawai sai na rushe da kuka!
Ta kid'ime ainun! Ta rirri'ke ni tana fad'in." Sis menene don girman Allah ki yi shiru kada ki jazawa kanki lalura, ba fa ke kad'ai ba ce, kuna nan da yawa iyayen marayu, kuma ki godewa Allah da ya ba ki sana'ar da za ki yi d'awainiya da yaranki, wallahi akwai wad'anda aka mutu aka bar musu marayun ba su da yadda za su yi, wasu ma sai sun yi bara da ro'ko suke samun abinda za su ci, ni kaina da nake da mijin kullum cikin fafutuka nake, kin san komai ba sai na fad'a miki ba, Abbansu Yasir bashi da tartibiyar sana'a, kasuwa yake shiga Yana tare mutane idan an yi katari sai ya kai su shagon da suke nema, da haka fa yake samun abinda zai kawo gida, ki yi hakuri ki godewa Allah, ki kuma cigaba da yi wa Mijinki addu'a, Allah Ya gafarta masa."
Hannu nasa na goge hawayen da yake zuba. Na ce." Na san Allah Ya yi mini Sahura, ba zan butulce masa ba, yana taimakona ta fannoni da yawa. Amma sis ina da damuwa sosai, ba zan iya aure yanzu ba sai yarana sun yi 'kwari, sis Baba Sule kwana biyu ya sani a gaba, ga Kamalu Yana nema ya fi 'karfina."
"Wace irin magana ce wannan Amina, ki haifi 'dan a cikinki sannan ki ce yana nema ya fi karfinki, me yake yi? kuma me Baba Sule yake yi miki, na ga dai ke kike hidima da kanki da yaranki, na d'auka ai ba ki da wani kalubale da mutanan gidanku."
Naja majina cikin jin ciwon abubuwan da suke faruwa na fara bata labarin abinda ya wanzu kwanaki biyu da suka wuce.
Ta ce." Ki yi hakuri, kada damuwar hakan ta janyo miki ciwo, aure dai a yanzu sai kin yi ra'ayi za ki yi tunda dai ke ba yarinya ba ce, bazawara ce muddin za ki ri'ke mutumcinki ki cigaba da sana'arki domin ki kula da yaranki, Ubangiji zai shige miki gaba, ki yi ta addu'a dai, sannan maganar Kamalu kada ki dinga yi masa kuka domin hakan zai sake jefa shi a garari, ki yi ta yi masa addu'a. In sha Allahu lamarin zai tsaya iyakacin 'kuruciya, kuma wallahi irinsu idan sun girma ba su iya hankali ba. Suna da biyayyar iyaye. Kowane yaro da irin 'kuruciyarsa.
Zuciyata ta sassauto sakamakon irin rarrashi da tausasan kalamanta. Sahura k'awata ce tun ta k'uruciya tare muka dinga fa'di tashi muna 'yan mata. Daga gidansu na samu taimako sosai a harkar karatuna. Sai dai ta riga ni aure har sai da ta yi haihuwa ta biyu tukkuna Abbansu Yusi ya yi fito da zummar aurena.
Ta ce." Tunda kin zo na samu abokiyar tafiya dama ba na son zuwa ni kad'ai wallahi, duk da hakan ba wani abu ba ne, amma dai bibiyu tafi dadi.
Na kalleta cikin nazari sai a lokacin ma na hangi ramar da ta yi, yanayinta ya nuna tana cikin damuwa.
Na ce." Da Ina za ki je ne?" Ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce." Hotoro zan je sabon kamfanin Alhaji Tajo na leda suna buk'atar ma'aikata. Maman Anisa makociyar nan tawa ta kar'bar mini form a wurin mijinta kin san shi ma yana aiki a 'karkashinsa amma dai Yana da matsayi ba 'karamin ma'aikaci ba ne, to shine suke neman ma'aikata da na gayawa Abbansu Yasir ya amince, yanzu na cike form din zan je na kai wata'kila ma a yi mini interview."
Idona a kanta har ta ajiye maganar. Na ce." Sahura ba wai zan dakile ki ba, don Allah kada ki yi aiki a kamfanin nan, ki cigaba da neman aiki na gomnati, ni ma zan cigaba da nema miki har Allah Ya sa a dace, amma hankalina bai kwanta ba wallahi tunda Abbansu Yusi ya yi aiki a kamfanin mutumin nan aka zalince shi nake jin tsoro. Kin san suna amfani da lafiya da kuzarin mutum ne, duk wahalar da za ka yi musu da lafiyarka daga ranar da Allah Ya jarrabeka da ciwo ka kwanta sai suce ba su san wannan ba, 'karshe a rubuto maka takardar sallama kuma babu ko sisi."
"Amina ni kaina akan dole zan yi wallahi, na fad'a miki tun farko Abbansu Yasir ne ya cuce ni, farkon auranmu na samu aikin rabon magani 'kauye-k'auye ya ce ba zan yi ba saboda mugunta. Gashi kuma yanzu muna nema Ido rufe dalilin hidimar gida da ta Yara tunda shi ba k'arfi ne dashi ba, wallahi idan lokacin biyan kudin makaranta ya yi hankalina yana tashi Amina, wasu lukutan Ina ji ina gani za'a koro mini Yara daga makaranta. Kin ga kuwa idan Ina aikin zan samu hanyar da zan dinga biya musu da yin wasu hidindimun babu fargaba."
Na ce." To yanzu kina da tabbacin idan mun je za a d'auke ki, wulakanci nake gudu Sahura, shiyasa ki ka ji ina wannan maganar wallahi."
"A a ai ina da hanya kai tsaye muna zuwa zan kira wayar mijin Maman Anisa d'in tunda shi ya kawo mini form din, in sha Allahu ba za a samu matsala ba."
Na gyad'a kai tare da cewa." Daga nan ja'in zuwa hotoro nawa za ki kashe Sahura, kuma nawa ne kud'in albashinki komai fa d'an lissafi ne?"
Ta ce." Gaskiya ba zai haura dubu saba'in ba, bayan haka kuma an ce sa'i da lokaci yana yi wa ma'aikatasa alheri, har da su kayan abinci Yana bayarwa."
Na ce." To ni dai tsayin shekara biyu da Abbansu Yusi ya yi aiki a k'arkashinsa bai ta'ba gaya mini ya samu wani abu ba bayan albashinsa. Kin ga fa koda aka sallame shi ma fa ba'a bashi ko kwabo ba."
A sanyaye ta ce." Zan dai jarraba na gani Amina, idan na ga babu ci sai na ajiye, don Allah ki taya ni da addu'a, ki kuma cigaba da nema mini wani aikin ko koyarwa ne irin naki."
Cikin kulawa na ce." In sha Allahu rabbi, zan taya ki da addu'a kawata, zan kuma cigaba da yi miki fafutuka, Ubangiji Allah Ya sa mu dace gabad'aya."
✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*07084653262*
[11/13, 9:30 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*
*Marubuciyar*
*Yar bangar siyasa*
*Ba'aboren namiji*
*Madadi*
*Ga irinta nan*
*Goje*
*Babban yaro*
*Sadauki Omar*
*Nida Yaya sadam*
*Da sauransu..!*
*Tallah!*
Albishirinku mata 'yan gayu yan gwalisa ku yi maza kugar zayo shagon
(Aysha/Addah beauty saloon and spa).
Shin kin taba zuwa ingancaccen saloon din Aysha/Addah, idan baki taba zuwa ba ki yi maza kar a barki a baya domin sun qware a wajen aikinsu wanda suke services dinsu cikin sauki tare da annasuwa
Suna wanke kai(wash and set)
suna wanke qafa(pedicure)
And sunayin steaming iri iri suna saida (supplements)suna kitso dama duk wani abu daku so Wanda akewa mace ta amsa sunanta mace yar qwalisa
Address dinsu nanan a Federal low-cost opposite open University *GOMBE STATE*
Ko kuma ku tuntune mu a wannan number kamar haka,
08037925676
Or
08167764242
Whatsapp ko kuma Call we’r available 24/7..
Tabbas ni ma na shaida ingancin ayyuka da kayayyakin shagon anti adda mutuniyar kirki. Babu tsada komai ana samunsa cikin sau'kin farashi mutanan gombe kada ku bari wannan sau'kin ya wuce ku.🥰
*@Arewa books*
*Bintaumarabbale.*
*Free pege4*
Ba mu fita ba sai da yaran suka dawo daga cefane tukkuna. To abin dai gashinan a hannu a hannu. Na ce." Yanzu Sahura shinkafa gwangwani biyu ce zata ishe su har su uku?" Tana gyara zaman hijabin wuyanta ta furta." To ya zan yi Amina, babansu da wuri ya fice don ma kada na tambaye shi kudi, ko sallama bai yi mini ba. Jiya dai da daddare na gaya masa zan fita. Wallahi dubu dayan kenan ta rage mini na ba su suka yo cefanan nan. Kudin mota kuwa dama cewa na yi zan kar'ba a a wurin Maman Anisa, idan na samu daga baya sai na bata.
Na dubi Yusra dake juye shinkafar a faranti domin tsincewa. Na ce." Tashi ki je ki auno kwana daya sai ki dafa muku yadda za ta ishe ku. Ki karo man'kuli da maggi da wake." Na zuge jakata na d'auko dubu biyar na mi'ka mata." Duk abinda babu ki saya a ciki." Sahura ta yi sakato tana kallona. Na tashi ina fad'in." Wannan rayuwar Allah Ya magance mana. Ta ce." Sis, anya kuwa ina lefin ki bata kudin rabin kwano."
Na ce." Don Allah kada ki bata mini rai Sahura." Yadda na fadi maganar cikin fushi shi ya sanya tayi shiru da bakinta ta juya kan yaran tana cewa.'' Yusra ki rufe gidan idan mun fita, duk wanda zai k'wankwasa kofa kada ki bude, ki ce bana nan."
Ta ce." To Ummi sai kun dawo."
Ba mu wani jima a bakin titi ba muka samu abin hawa. Ya ce sai dai mu bashi dubu daya da d'ari shida duk mutum daya d'ari takwas kenan. Na ce." Sahura shiga mu tafi a hakan ya yi mana adalci, tunda gaskiya tsakanin hotoro da ja'in akwai tazara mai tsayi.
Wajan d'aya saura muka isa. Ya ajiye mu daidai bakin kamfanin duk da sabo ne hakan bai hana masu sana'ar adadaita sahu saninsa ba idan an yi duba da shuhurar mamallakinsa.
Masu tsaron wurin ba su bari mun shiga kai tsaye ba sai da ta yi musu bayani ta fito da takardu ta nuna musu tukkuna suka bari muka shiga. Wurin ya yi sosai an ka'wata shi ga ko'ina a tsaftace ma'aikata na ta shawagi tare da tashin sautin injina.
Sai dibi dibi take yi tana zare Ido. Na ce." To Sahura ina zamu nufa ne yanzu?"
A rikice ta ce." Bari na kira Abban Anisa a waya."
Na yi shiru ina kallonta ta d'auko wayarta ta kira shi bai daga ba har sau biyu.
Jiki a sanyaye ta ce." Kin ga bai daga ba."
Na ce.'' Na ji, wata'kila ko yana wani uzurin ne, kin ga yanzu lokacin shiga massalaci ne. Mu bari an jima kad'an sai ki sake kiransa."
Muka je muka samu wani wuri muka zauna muna tattaunawa. Wani ma'aikaci da uniform ajikinsa irin na tsaro ya zo ya tsaya akanmu fuska a daure Ya ce.'' Me kuke yi anan?"
Da sauri ta ce." Form din da aka ba ni na cike shine na kawo, ina neman Sulaiman sha'abu ja'in." Ya yi jim na minti biyu kafin ya ce." Ba anan yake dindin din ba. Amma yana iya zuwa da kowane lokaci. Ku tashi ku shiga cikin nan akwai wad'andasu a ciki irinku." Yadda ya fadi maganar cikin izgili shine ya bata mini rai.
Na ce." Ranka ya dad'e. Ubangiji shi ya karrama dan'adam, ya kuma fifita shi akan kowace hallita. Kaga kuwa wani mahalu'ki bai isa ya 'kas'kantar dashi ba. Ba mu zo wurin nan a matsayin wulakantattu ba face neman dogo da kai."
Ya yi jim Yana kallona kafin ya furta." Kada ki yi mini rashin kunya ko kin ji na fa'di mummunar magana akanku ne?" Na ce." Ba ka fad'a ba Yallabai."
Sahura ta ri'ke hannuna muka tashi. Ya ja tsaki tare da nuna mana inda za mu shiga da hannuna.
Muka kama hanya muna tafiya raina duk a 'bace. Ba na son raini ko kad'an. Kuma dai d'abi'ata ce rashin yin shiru idan an ta'bo ni. Shiyasa wasu suke yi mini kallon mara kunya tunda gaskiya ba na iya bari, duk girmanka ka nemi ka takani na kan nuna ban yarda ba. Dalilin da ya sanya kenan matan gidanmu suka tsaneni tunda kuruciya. Ba wai Ina yi musu fitsara ba ne, kawai dai ba na yarda da son zuciya.
Mun zo shiga manager wurin zai fito a gurguje muka gaisa da alama massalaci zai je. Ya ce mu shiga mu jira shi.
Mata hud'u muka samu a zaune a kan kujera. Uku duk da 'kwarinsu. Dayar kuma dattijuwa ce sosai shekarun girma sun cimmata.
Muka gaisa kafin mu nemi wuri mu zauna. Wurin tsaf da sanyin Ac ga tibi falasma nan k'atuwa a bango tana aiki.
Wajejan biyu da rabi wani ma'aikaci ya shigo ya dube mu kafin ya ce." Ga Yallabai nan zai shigo."
Bai jira wata magana ba ya fice da gaggawa.
Dattijuwar nan fadi take 'Alhamdullahi' bakinta ya gaza rufuwa. Sahura ta kalleni itama da farinciki a tare da ita ta ce." Lallai mun shigo da kafar dama 'kawata."
Shiru na yi ban ce komai ba kawai dai na zubawa hanya ido. Ina mamakin yadda gabad'ayansu suka rud'e.
Mutum uku ne suka fara shigowa kafin shi din ya shigo da masu tsaronsa a baya. Hakan ya nuna akwai masu kula dashi a gaba da bayansa.
'Kamshin turaransa ya gauraye wurin. Farin bafulatani ne mai madaidaincin jiki da manyan idanu kamar dai yadda hotonsa yake a kalanda Yana da kyau da fuskar salihai. Yanayin jikinsa shi ya b'oye shekarunsa. Amma dai da shekarun tunda ga tsalli tsallin furfura nan a gashin da yake kewaye da matsakaicin bakinsa, yana sanye da farar shadda babbar riga da 'yar ciki, da jar dara tare da farin gilashi a idonsa. Cikin 'yan sakwanni na karance shi.
Gabad'aya muka mike tsaye. Cikin nutsuwa ya tsaya yana amsa gaisuwar da muke yi masa.
Ya ce." Sabbin ma'aikata ne ?"
Da sauri manager da shigowarsa kenan shi ma ya ce." E, Yallabai." Ya jinjina kai yana dubanmu ta cikin farin gilashin da yake idonsa.
A nutse ya furta." Kun gama dasu ne? Ina nufin kowacce ta san matsayinta."
Manager Ya ce." Ranka Ya dad'e. Wad'annan daga baya suka zo. Sulaiman sha'abu ja'in ne ya turo su. Yanzu Muna buk'atar masu shara ne da goge-goge."
Ya juya Yana kallon dattijuwar nan. Ya ce." Mama za ki iya aikin nan kuwa?"
Da saurin gaske ta ce." Zan iya Yallabai."
Ya yi murmushi a tsanake Ya sake cewa." Aikin fa ba irin na gida ba ne Mama, kin ga wurin nan da girma ba ki dai da wata lalurar ko? don ba kasafai nake d'aukar dattijai ba, ai irin wannan yana buk'atar masu lafiya da k'ananun shekaru"
Ta ce." Zan iya Alhji in sha Allahu."
Ya juyo yana kallonmu ni da Sahura sai ya ce." Ina fatan za ku kula sosai, idan na d'auki mutum aiki ba na son wasa, shine dalilin da ya sanya ma na fi buk'atar zawarawa ko 'yan mata, irin wad'anda ba su da uzuri na miji da yara. A dinga zuwa akan lokaci in sha Allahu ni kuma za ku same ni da kyautata muku."
Ba tare da rashin kunya ba na ce." Ranka ya dad'e ni babu ni a cikin masu neman aiki, ina da abin yi, ni ma'aikaciyar gomnati ce, sannan ina sana'ar hannu, wannan 'kawata ce Sahura ita na rako."
Ya ce." Okey ita tana da aure ne ko bazawara ce?" Raina ya d'an sosu da maganarsa. Na ce." Tana da aure da Yaranta uku." Na dubeta tare da cewa." Sahura ki yi bayani mana."
Ta ce." Ina da aure Yallabai, yarana uku ina zaune a unguwar ja'in." Ya ce." Wannan ba zai hana a d'auke ki aiki ba muddin za ki ri'ke shi da muhimmanci, sakarci ne dai ba na so a duk sha'anina. Na san duk dokokina kun karanta a cikin form din da kuka cike ko?"
Gabad'aya suka amsa. Ya ce." To, Allah Ya yi mana jagora gabad'aya."
muka amsa da "Amin."
Ya juya domin fita mabiya bayansa suka take masa baya.
Minti biyar sai ga d'aya daga cikin escort d'insa da kudi a hannu. Ya zo dukkaninmu ya bi mu da dubu biyar biyar Yana fad'in oga ne ya ce a baku kudin mota."
Ya gama raba mana sauran ya zura a cikin aljihunsa ya fice da saurin gaske.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
*07084653262*
[11/14, 10:42 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*
*TALLAH!*
🌲🌳🌿☘️
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar