Gudun Aure 1 Complete Hausa Novel

Author :  Binta Umar Category :  Romance

Chapter   13 / 18

36K to 39K   out of 51.4K words

girki idan zai fita zai bata dubu biyu kudin kayan miya kawai da markade, tunda Yana Aiko da nama ko kaji daga kasuwa.
Ranar da na kar'bi girki, gabad'aya dubu biyun na karar da ita na yi komai a wadatace kamar yadda suke yi ba. Koda na dibi na maigidan da wanda zan ci sai na bar musu tukunyar domin ban san ya za a yi na raba.Na kira anti Maimuna ganin tana da sau'kin fahimta, na ce ta raba a hankali sai na koya.
Sai suka fara hayaniya. Anti Jamila na fad'in." Akan me, za ki kwashe miyar duk ki juye a kwanukan yaranki, haba anti Maimuna, akwai son zuciya fa."

Na yi shiru ina kallonsu da mamakin irin fitsarar da Jamila ke yi wa Anti Maimuna, ita kuma duk sai ta diririce, hannunta Yana kyarma tana raba abincin take cewa" Kowa za a zuba masa, Jamila ki kwantar da hankalinki."
Ta kalleni tana cewa." Ke ma ai da ki ka yi girkin ke ya cancanta ki raba abincinki, tunda dai kin san gidan iyali ki ka shigo, mijinki ya gaya miki komai, to ba sai ki k'arasa ladanki ba."
Uffan ban ce mata ba, na danne zuciyata da take shirin danna mata zagi.
Anti Maimuna ta ce." Jamila, wai me ki ke nufi ne, na gaji fa da wannan iyashegen da ki ke yi mini, ki dinga yi mini tsawa, tunda Amina ta zo gidan nan, ki ke neman fitina, ina lefi don ta yi abincin ta ce mu raba, ai yaran mu ne gabad'aya. Kuma idan ta ce za ta yi rabon ba ta san ya za ta yi ba, komai sai a hankali. Amma kin zo kina ta yi mini rashin kunya, me ki ke nufi ne?"

"To, ai gani na yi, kin fito da son zuciyarki 'karara, idan ke za ki yi miyar ai ba za ki saki jiki ki yi kamar wannan ba, kuma duk kin d'ibe kina zubawa a kwanukan yaranki, waccan ma da ki ka zuba a robar rufaida yogurt ta wacece?"

Cikin bacin rai na ce." Wai ke don Allah menene haka? Ba fa girma da mutunci ba ne, ya za a yi mata tana iyakacin k'okarinta a gida, kina yi mata abinda ki ke so, ga yaranta suna jinki, idan kuma watarana suka yi miki fitsara fa, don Allah ki daina haka anti Jamila, mu yi hakuri dukanmu."

"Kin ga, don Allah Ya isa, lefin ai na ki ne, me yasa ba za ki raba abincin da hannunki ba, ai mai iyali ki ka aure dole ki yi, ni ma kafin na ajiye nawa sai da na yi wannan bautar, ba zan yadda da sigar munafurci ba, shine za ki kira ta ki ce ta zo ta raba akan me?"

Na ce.'' Babu dole Hajiya, ina lefin ma girkin da na yi, kuma ni dai ki dubi tsabar idona da kyau ki ga ni, ba zan lamunci wannan daga wurinki ba, ban shigo domin tashin hankali ba, amma idan kin ce ayi to a shirye nake, haba ina dalili, mata tunda na zo gidan nan ki ke ta hayaniya, ko kin d'auka hakan zai sanya na ji tsoronki ne."

"To kada Allah Ya sa ki yi din mana, munafuka kawai, wallahi muddin ki ka ce ba za ki zauna lafiya da mu ba, ke ce a wahale, kuma maigidan zai dawo sai na gaya masa abubuwan da kuka fara yi mini. Ni ban iya rayuwar munafurci ba, kome za a yi to a fito fili a yi shi a gaban kowa."

Na ce." Idan Ya dawo ki sanya shi ya sallame ni, tunda ke ki ka sanya shi ya aure ni. Kuma wallahi ki daina kira na munafuka idan ba haka ba, ni duka nake yi ban iya cacar baki, jikinki ne zai gaya miki."
Turzumi babban yaronta ya ce." Aikuwa wallahi sai na kwala miki dutse' na fasa miki kai idan ki ka daketa."
Yaran gabad'aya suka kwashe da dariya. wadda hakan ya kara kona mini rai!
Anti Maimuna ta buga musu tsawa suka yi shiru, ta ce." Kowa ya d'auki abincinsa ya isa haka."
Suna fara hayaniyar d'aukar abincin. Na bar wurin raina a kuntacce wannan wane irin gidane ......
*1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank*
*07084653262*
[11/25, 10:29 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*
*TALLAH!*
*Gidan 'kawa ne da kece raini, abin ma sai wanda ya yi joning da su, nan zai kashe kwarkwartar idonsa ga sau'kin farashi!*
🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨
🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi

https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t

*@Arewa book's*
*Bintuumarabbale*
*Free pege*
*16*
Ta ina zan yi sake na samu ciki har na haihu a irin wannan gida na alhaji Muntari. Lallai dole na yi takatsantsan, domin tashin farko na lura gidan ba irin wurin da za ka saki jiki ka haihu ba ne, dalilin rashin saiti, da gurguwar rayuwar da iyalinsa suka kafu akai. Wannan marayan da Allah ya jarabce ni dashi ya ishe ni. Ina ro'kon
Ubangiji ya ba ni ikon kula dashi tare da d'an'uwansa da kuma tarbiyarsu. Dole kuma koda yarana sun dawo gidan, na sanya ido kwarai a rayuwar da za su gudanar sabili da rashin gamsuwa da tarbiyar yaran gidan. lamarin dai sai da kawai mu ce Allah Ya magance mana.
A daran ranan na fara had'iyar maganin hana d'aukar ciki. Dama na yi guzurin abina, zahirin gaskiya ba zan iya haihuwa dashi a irin wannan yanayin da shi kansa bai san menene rayuwa ba.
Muka cigaba da tafiya a haka. Anti Maimuna macece mai sau'kin hali, kuma mara son hayaniya, yayin da ita Jamila ta kasance bagidajiya mara fahimta. Ko da yake babu mamaki idan an samu hakan daga wurinta domin a can karkara ya aurota wani kauye a karamar hukumar bichi, shiyasa komai nata take gudanar dashi cikin gidadanci, da kuma zargi. Gabad'aya jininmu bai hadu ba, tunda na fahimci halinta, sai nake takatsantsan, ban ta'ba yadda mun yi rigima ba, duk takalar da za ta yi mini, ba na nuna na san ta na yi. Sabgar gabana nake yi. Idan ba ranar girkina ba ma, ba na fitowa, ina ta sana'ata.
Sai dai kuma zamansu a Kamalu a gidan yana nema ya zama d'an zani, domin ko kwana uku ba su yi da dawowa ba, matsaltsalu suka fara kunno kai. Yusi yaro ne mai son jama'a, ba shi da wahalar sabo, kullum Yana cikin yaran gidan su yi ta wasa. Amma ba a k'arewa lafiya sai ya shigo mini yana kuka, Turzumi ya dake shi. Idan na tambaye shi dalili sai ya ce babu komai, kawai dukansa ya yi. Sai dai kawai na rarrashe shi amma abin yana damuna mutuka.
Kamalu ya yi ta kumbure-kumbure, yana jin haushi. Na hana shi motsi, domin dama tunda suka dawo gidan na zaunar dashi a gabana yana taimaka mini da wasu abubuwan na sana'ata
Ba ni da matsala da maigidan, domin kamar yadda ya fad'a tunda yaran suka dawo hannunsa yake iyakacin bakin kokarinsa. Ya kammala musu komai na makarantar boko da Islamiyya wadda yaransa suke zuwa. Satin da za mu shiga za a koma makaranta gabad'aya. Matsalata yadda Turmuzi ke cin zalin Yusi. Wanda na tabbatar da cewa ba zai yi masa lefin da zai kai hannun jikinsa ba, face dai cin zali da ganin gidansu ne. Sai kuma rashin kwa'ba daga wurin uwarsa.

Yau zai dake shi. Amma hakan ba zai hana shi komawa cikinsu gobe ba. Kullum dai sai ya je cikinsu, sai kuma ya dawo mini yana kuka.
Ban ta'ba yun'kurin d'aukar mataki ba. Na d'auke kaina kawai, amma zahiri ba na jin dad'in hakan.
Watarana ya shigo yana gursheken kuka wanda ya fi na koyaushe. Saman goshinsa ya kumbura har ya yi 'kululu! Na kama shi da sauri ina mulmula masa tare da tambayarsa.
Ya ce." Mama Turmuzi ne ya buga mini kai a bango."
Na ce." Me ka yi masa yau kuma?"
" Ban yi masa komai ba mama, ball ya bugo shine don na mayar masa. Ya kama ni da duka Mamansu tana kallonsa."
Kamalu da yake sanya mini zif a jakkunkunan da nake yi na sayarwa. yana huci Ya ce "
Wallahi mama ba zan yarda ba dubi fa ki ga yadda ya lun'kuma masa goshi, na rantse da Allah sai na rama masa."
Ya tashi da mugun sauri ya kama hanya fita. Na dinga 'kwala masa kira bai juyo ba.
Na yun'kura na tashi da saurin gaske na bi bayansa.
Sai kawai na same su a farfajiyar gidan suna dambe. Kamalu har ya kaishi kasa yana saman ruwan cikinsa yana ta dukan bakinsa. Kusan gabad'aya muka isa wurin da uwarsa da sauran yaran gidan.
ihu! ta kurma ganin jini a bakin yaronta gashi a kwance a kasa yana kuka. Ta yi kukan kura ta janyo Kamulu. Na je na fizge shi daga hannunta. Sai ta hau d'ura masa ashariya tana fad'in " Kashe mini shi za ka yi a gidan ubansa, wannan wane irin samun wuri ne, agola da zage k'wanji akan d'an gida. Na rantse da Allah ba zan yarda ba."
Anti Maimuna ta ce." To, wai me ya had'a su ne, Jamila, ba fa a shiga fad'an yarana, a bi komai a hankali."
Na ce." Ka da ki yarda Jamila, don Allah ki yi duk abinda za ki yi, wato ke yaranki ba su lefi ko? Kin taba tuhumar dalilin da ya sanya Turmuzi yake dukan Yusi kullum, na san kin sani. Ki dubi goshinsa ki gani, a wurinki akayi kuma kuna kallo ya buga kansa da bango, ba ki mulmula masa ba. Yanzu kuma ko kunya ba ki ji ba kin zo kina kumfar baki, ki yi abinda za ki yi, ai ba tsoronki nake ji ba."

Aikuwa zan yi wallahi, ba za ki kawo mana alakakai cikin gida ba, shi yaron naki ai ba mu muka janyo shi ba, rashin zuciyarsa ne yake kawo shi wurina, ban ga dalilin da zai sanya ki kawo mana masifa cikin gida ba, dama an ce yaron nan mugu ne, sannan kuma 'barawo ne, duk mun samu labarin haka. Wallahi tallahi sai sun bar gidan."
Gabad'aya wurin ya yi tsit! domin Kalmar 'barawo da ta kira Kamalu ta girgiza kowa, har yaran. Anti Maimuna ta ce." Wace irin magana ce wannan Jamila, shin ke kin san me ki ka haifa, kada fa ki yi wa kaddarar wani dariya, tunda haihuwa ki ke, kuma kowa da k'uruciyarsa."
Na ce." Rabu da ita Anti Maimuna jahilace ai, bagidajiya mutuniyar kauye. Don kin kira yarona 'barawo ba zai dame ni ba, tunda kema kin haifa, kuma sai dai idan ke ce za ki bar gidan, amma Kamalu da Yusi zama daram, tunda ba na ubanki ba ne."

Wannan maganar tawa ta harzukata har sai da kwalla ta ciko a idonta. Muryata na rawa take cewa." An ce masa 'barawon, ai ba karya aka yi ba, ko za ki musanta ne, sau nawa ana kulleshi a Police station? Wallahi za ki ga matsayina a gidan nan na rantse da Allah sai kin yi dana sanin kirana da jahila, 'yar iska mai suffar karuwai."
Na ce." Na ji dai, ni na je makaranta, kuma ba 'yar kauye ba ce ni, ina da ilimi, sannan ba 'kazama ba ce."
Ta goge 'kwallar da ta d'igo a kumatunta. Ta tashi yaronta da yake kwance yana kuka ta ri'ke hannunsa suka kama hanyar barin wurin. Na dube ta tare da furta." Ina jiran matakin da za ki d'auka. Jahila bagidajiya kawai."
Tunda na lura ba ta so a kira ta da hakan, ni Kuma na ri'ke. Sai ta yi wani kukan kura za ta kawo mini cakuma. Anti Maimuna ta shiga tsakani.
Ta dinga d'ura mini ashariya sai ka ce bamagujiya. Na ce." Kin ga aikin jahilicin naki ko, a gaban ya ra ki ke wannan tumasamcin, ni ba zan yi kokawa dake ba saboda na je makaranta.
Anti Maimuna fad'i take don Allah Amina ki yi shiru, wallahi mu ba mu taba fad'a ba, da dadi babu dadi muna zaune lafiya."
Na ce." To ni ba sakarai ba ce, anti Maimuna ba zan zauna wannan bagidajiyar tana juya ni ba, ita din banza, ai ba tsoronta nake ji ba, kuma ba ita ta ajiye ni a gidan ba, wallahi daidai nake da ita, mu zuba shege ka fasa."
Ganin babu sassauci a tare da ni ya sanya ta juya wurinta tana rarrashinta. Ta tura ta wurinta tana bata ha'kuri.
Yaransu suka dinga ihu suna kiran Kamalu da 'barawo hooo! 'barawo ne."
Yusi ya fashe da kuka ya ruga da gudu ya shige wurina. Shi kuwa Kamalu Yana tsaye durmin danya babu alamun firgici, ko nadamar abinda ya aikata. Kuma ihun da yaran suke yi masa bai sanya zuciyarsa ta yi rauni ba.
Na ja hannunsa muka bar wurin zuciyata na 'kuna, duk abinda yake faruwa a gidan, ban tana gaya masa ba, yau kam idan ya dawo zan zayyane masa, ba zan iya ba wallahi.

A ranar dama girkin anti Maimuna ne, na yi ta Allah-Allah gari ya waye ya shigo domin da b'acin ran abin na kwana a raina.
Ko da ya shigo da safe sama-sama muka gaisa gabad'aya na kasa sakar masa fuska. Ga yaran su ma duk sun damu ganin yanayina sun takure kansu wuri d'aya. Hakan ya kara dasa mini kunci tare da dakacen auran gabad'aya, domin da na tabbatar da cewa bai fi karfin gidansa ba wallahi ba zan aure shi ba.
Yanayi na shi ya tabbatar masa da cewa akwai matsala.
Ya fara tambayata. Na dube shi takaicinsa na 'kara nu'kurkusata.
Na kalli yaran tare da cewa." Ku shiga d'aki." Suka tashi da sauri domin cika umarnina.

Na sake kallonsa a karo na biyu Na ce." Ka zauna domin maganar tana da girma, kuma ni ban d'auketa karama ba."
Ya dubi agogon da yake daure a hannunsa.

"Ban 'ki zaman ba ai, ina da uzuri mai girma a waje, ba na son doguwar magana Amina kada dai ki ce mini kema fad'an yaran za ki shiga."
Na ce." Ashe an gaya maka abinda ya faru?"

"Kwarai an gaya mini, Ammaa ban d'auki hakan a matsayin komai ba face zaman tare, dole idan Yara suka had'u sai an yi wannan, muma da haka duk muka tashi, ki yi hakuri kin ji ko".
Idona ya ciko da ruwan hawaye na ce." Ni fa ba wannan ne damuwata ba, yadda Jamila take Kiran Kamalu da b'arawo shine abinda ya bata mini rai, ai itama ta haifa, kuma ba ta san abinda za ta haifa ba nan gaba."
Ya 'bata fuska yana cewa." Kin ga don Allah ki san irin maganar da za ki furta, wane irin lafazi ne wannan? kina fatan na haifi lalatacce kenan?"
Hawaye suka fara gudana a kumatuna, na ce." Amma dai ka san da ciwo ko? kuma a'ina ta samu labarin tsalle-tsallen da Kamalu ya yi sai dai idan kaine ka tara su ka gaya musu."

"Kada ki zarge ni akan abinda ban yi ba, me zai sanya na gaya musu yaronki ba ya ji, wata'kila ta samu labari ne a wani wuri, kuma kema tun farko sai da na gaya miki ki zauna lafiya da su, kuma ki bi duk abinda suke so domin samun daidaito, su ki ka zo ki ka samu, ba zai yiwu ace kin zo da wani tsari ba."

Na dube shi raina a bace." Wallahi tallahi babu wadda zan bi a cikinsu, akan wane dalili? Ai lokacin da za ka aureni ba ka fad'a mini cewa matanka sun fi karfinka ba, ba zan jure ba, akan yarana zan iya komai, idan ba za ka siya mini mutunci ba, ka sawwake mini ba."

Ya ja tsaki Yana fad'in." Ai aure ba wasan yara ba ne, duka sati hud'u kacal, kin fara bayyana mini halinki, ba zan sake ki ba, saboda ina sonki, Yara kuma ni na ce ki zo da su zan ri'ke, idan hakan be yi miki ba, ki tattarasu ki kai su wani wurin, ni babu rabuwa a tsakanina dake."
"Cikin kuka sosai na ce." Wallahi ba zan iya ba, muddin ta kara aibata mini yaro sai na yi sharia da ita, ai tunda ya zo gidan bai ta'ba shiga wurinta ba balle ta ce ta nemi wani abu ta rasa, wallahi 'yansanda ne za su raba mu."
Kuka nake yi sosai. Hakan ya sanyayyar masa da jiki. Ya ce." To na ji zan ja mata kunne, ki yi hakuri, sannan kuma ki bi shawarar da na baki, ki zauna lafiya da su, bayan wannan kuma idan kin yi girki ki dinga rabawa da hannunki, ki daina kiran Maimuna, duk abinda ki ka san zai janyo zargi kada ki yi shi."
Na goge hawayen kumatuna tare da cewa." Ni fa na gaya maka babu wadda zan yi wa biyayya, Kai ka ajiye ni, kaine dole, tsakanina da su girmamawa ce kawai, amma ba zan bi son zuciya ba."

"To shikkenan, ki daina kukan haka, ya isa." Ya fad'a da sigar lallashi. Sai da ya tabbatar na yi shiru tukkuna ya kama hanyar fita yana fad'in."Ashe haka ki ke da rigima dama.

Tun daga ranar Yusi bai kara shiga cikin yaran Jamila ba. Ni ma kuma ban 'kara barinsa ya fita ba. Idan garin Allah ya waye muna tare a wurina. Kamalu na taimaka mini, shi kuma yana ta wasansa shi kadai.
Anti Maimuna ta same ni kan cewa hakan da na yi bai dace ba, na takure yara wuri d'aya na hana su sakewa. Na ce mata yadda na yi shine kwanciyar hankalina. Duk da haka ba ta ha'kura ba sai da ta san yadda ta yi ta janye Yusi ya zama d'an dakinta. Ganin kwana biyu

13 / 18