Gudun Aure 1 Complete Hausa Novel

Author :  Binta Umar Category :  Romance

Chapter   16 / 18

45K to 48K   out of 51.4K words

d'auko musu naman gabad'aya na ce su juye akan abincin.
Ruwa muke dashi babu lemo nasa aka sayo musu katon biyu. Suka yi facakarsu yadda ransu yake so ban hana su ba. Da za su tafi kowacce na bita da dubu d'aya sannan na bawa Hadiza atamfa turmi biyu iri d'aya dukda tace daga nan gidanta zata wuce na ce don Allah ta koma gidanmu ta kaiwa Ummansu da anti Sakina Ummansu Saminu, na so na dinka musu aiki ya yi mini yawa, na dora musu dubu bibbiyu akai kudin dinki.
Alhamdulillahi shekarar ta zo mini da bud'i da nasara mai yawa. Domin ayyukan da na yi sun tara mini kudi masu nauyin gaske Ya Falmata tana da zuciya mai kyau bata ha'intata ko kad'an, duk wani matakin nasarar da zan taka a rayuwa zata kasance mace ta farko sai ko Sahura data ba ni gudumuwa daban daban. A maza Kam Yaya Aminu shine madubi na.
Sati daya da sallah na shirya fita zuwa gidanmu da gidan Gwaggwo domin tunda na auri Alhaji Muntari bai fi sau uku kacal na shiga cikin garin ba.
Gwaggo ta ji dadin ganina da yaran cikin koshin lafiya. Bakinta ya gaza rufuwa ta dinga murna. Ni ma kuma ban je hannu rabbana ba. Atamfa mai kyau da tsada na saya na dinka mata irin na manya, na hada mata da takalmi da mayafi, sannan na dora mata dubu biyar a kai. Ta dinga godiya har da hawayenta. Hakan ya k'ara karyar mini da guiwa ni ma hawayen suka ciko idona.
Gidanmu kuwa da na je nan naga tsantsar kulawa ban yi mamaki ba saboda na riga na san a yanzu babu abinda ya fi saurin kankaro da mutunci irin kud'i. To Allah Ya hore mini shi a yanzu shiyasa kowa ke ganin girma na. Babanmu ma sam baya ganin aibuna duk sanda za mu had'u ya dinga fad'in auran naki ai Yayi albarka Amina. Ai na gaya miki mutumin kirki ne gashi bai yi miki keta ba ya rike miki yara sannan ya barki kina sana'a. Lallai Ubangiji Allah Ya yi mini sakayya.
***
Na cigaba da rayuwa a gidan Alhaji Muntari da dadi babu dadi ana ta turzawa. Na dai ki yadda na samu ciki domin dabara nake yi a duk lokacin da ya yi auratayya da ni. Muna gamawa zan yi sauri na kada gishiri da ruwan dumi nasha. Kafin gari ya waye duk abinda ya zuba mini ya tsinke ya fito.
Shi dai adduarsa Allah Ya tsananta rabo a tsakaninmu. Ni kuma ina jin na gama haihuwa da kowane namaji wanda Allah Ya ba ni sun isa.

Yara suka koma makaranta. Ayyuka suka yi mini yawa. Sai na fara shawarwari mai zai hana na nemi shago a bakin titi na sanya Hamusu ya binciko mini kwararrun teloli maza na zuba kekuna kawai mu fara gudanar da aikin tare don gaskiya abin ya yi yawa sosai gashi koyaushe suna nake karayi a fad'in najeriya da kewayenta.
Ban yi zaton maigidan zai amince mini da sauri ba, Ina gaya masa ya ce." Ai babu komai ke ma tunaninki ya dawo kan auranki, na yarje miki amma ki kula sosai da yaran da za ki zuba, a samu masu Amana wad'anda suka gwanance da aikin." Na ce." In sha Allahu za a samu." Godiya na yi masa sosai domin da ba na samun goyon bayansa da ban kai matakin da nake a yanzu ba. Amma har yanzu zuciyata ta kasa aminta da haihuwa dashi.

Ina ta shirye-shiryen fadada harkokina, don har mun gama magana da Hamusu ya ce wannan duk ba zai zama matsala ba, zai tsaya mini akan komai. Wani mummunan lamari ya rikito mini wanda lokaci guda hargitsin ya gigita mini rayuwa. Na shiga halin d'imuwa da tashin hankali mai tsananin gaske......✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
[11/28, 9:51 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A.*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*TALLAH!*
🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨
🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi

https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t
*@Arewabooks*
*Bintuumarabbale.*
*Free pege*
*19*
Tunda aka shiga hidimar sallar nan wata yarinya 'yar nan, ma'kotanmu ke shigowa gidan namu, a can wurin anti Maimuna take zama tunda nan din ne yara suka fi yawaita, tun kafin na ga yarinyar na ji sunanta a bakin Yusi Ihisan. 'Yar madamanciya ce dan bata fi shekara takwas ba, yawan ambaton sunanta da Yusi yake yi yasa nace idan ta shigo ya kawo mini ita na ganta, dan da alama jininsu ya hadu, yadda bashi da wahalar sabo ba haka itama take. Yarinya mai fara'a da ita. Na bata chocolate irin wad'anda nake ajiyewa suka fita tare da Yusi din. Can wurin anti Maimuna suka nufa cikin nishadi.
Da yamma likis ina kwance gajiya ta kayar da ni, ina ta lissafin abubuwan da zan saya dangane da bud'e shagunan dinkin da zanyi. Anti Maimuna ta shigo a kid'ime tana kiran sunana.
Na tashi zaune cikin tashin hankali don na d'auka mutuwa aka yi, ko maigidan na mu ne ya samu matsala.
Ta ce." Yarinyar nan Ihsan akayi wa fyad'e."
Gabana ya buga da karfin gaske na ce." Kada dai ki ce mini yar nan makota da take shigowa wasa wurin yara."
Ta ce." Itafa, yanzu nan yara suka shigo suna fad'a."
Na dinga nanata Innalillahi ina fad'in" Yarinya 'yar shekara bakwai, me za a samu a tare da ita, amma ya kamata ayi binkice akan wanda ya aikata wannan mummunan lamari."
Anti Maimuna za ta yi magana kenan. Uwar yarinyar ta shigo tana kuka da yarinyar a hannunta tana cewa." Ai tace Yusi ne kullum yake cire mata wando."
Cike da d'imuwa na ce." Yusi kuma? baiwar Allah wace irin magana ce wannan? Yusi me ya sani da har zai aikata haka."
Anti Jamila da shigowarta kenan ta bude baki tana cewa." Ai ba a shedar d'an yau, yo shekararsa sha d'aya fa, ai daf yake da balaga, yaron da aka haifa yau ma gabansa yana tashi balle saurayin da yayi wannan shekaru."
Na mi'ke tsaye da sauri ina fad'in." Karya kike yi munafuka yarona ba zai ta'ba aikata haka ba, a dai binkita a cikin yaranku."
Uwar yarinyar tana kuka take fad'in." Wallahi ba zan yarda ba fa."
Na dubeta tare da cewa." Kada Allah Ya sa ki yarda din, ki yi duk abinda za ki yi."
Ta juya ta fita a fusace.
Jamila ta bi bayanta tana kara zugata.
Na zube a kasan wurin cikin tashin hankali. Anti Maimuna ta dafa kafad'ata tana cewa." Amina a bi komai a hankali, tabbas na sheda Yusi ba zai yi wannan sakarcin ba. Dole dai a tsananta da bincike. A cikin gidan nan fa akayi can koridon da yake bayan dakina.
Na dubeta hawaye na ko'karin kwace mini na ce." Anti Maimuna lamarin nan ba na zama ba ne, ba yadda za a yi na yi lako-lako a d'orawa yaron nan abinda bai aikata ba."
Ta ce." Ni ma ban ce ki yadda ba, amma dai abi a hankali."
Ban ce mata komai ba har ta fita.
Kamalu ya shigo yana nishi kafafun wandonsa duk a tattare. Sai gumi yake yi.
Na dube shi zan yi magana ya katse ni Yana fad'in." Kokawa muka yi da su Turmuzi da Shahid Yayan Ihisan din, sun kama Yusi suna ta duka, sun d'auko almakashi wai zasu yanke masa wurin fitsari."
Cikin kad'uwa da d'imuwa na ce." Ina Yusi din, don sai a lokacin ma na tuna da cewa ban ga gilmawarsa ba tunda lamarin ya fasu. Kafin yayi magana Salima ta shigo tana kuka.
"Anti 'Yan-sanda ne a waje suka ri'ke Yusi gashi can a hannunsu. Suna neman Babanmu. yanzu Mamanmu ta kira shi a waya ya ce gashinan zuwa.
Hijabina nasa da sauri na kama hanyar fita yaran suka rufo mini baya.
Kofar gidan ta cika da mutane yara da manya. ga Yusi a hannun daya daga cikin jami'in yana kuka.
Yayin da wasu ke ta tambayar abinda yake faruwa.
Na iske wurin da yarona yake kai tsaye na ce." Sake shi domin ba shine ya aikata abinda ake zargi ba."
Jami'in ya ce." Ai magana ta kare tunda yarinya ta ce shine yake cire mata wando idan suna wasa, kuma kowa ya tabbatar da cewa shi din abokin wasanta ne, ke kin san haka, sannan iyayen yarinyar ma sun sani."
Wani zazzafan hawaye ya kwaranyo mini na ce." Wallahi ba shi ba ne, yaron ma guda nawa yake da zai aikata hakan, ku dai kara binkice, maraya ne, Allah ne gatansa, ni ce gatansa."
Ya ce." Ai marayun sun fi iyashege, saboda haka ba zamu sake shi ba sai mun gama gudanar da bincike."
Yusi ya rike gefan hijabina yana kuka, yana cewa." Mama wai me na yi?" Shi bai ma san akan me aka ri'ke shi ba."
Jami'in ya fizgeshi hannunsa daga jikina ya kwada masa mari mai tsanani!
"Tambaya kake yi me ka yi ko? za ka ci ubanka idan muka je station." Murya Kamalu na ji da k'arfi yana ce wa." Kai ma ubanka, shegu mugwaye sai Allah Ya saka masa." Sai kuka ya k'wace masa.
Wurin ya cika da hayaniya! wasu na fad'in." Dama ai yaron bashi da kunya, dan iska b'arawo ne shima, wasu kuma sai jajantawa suke yi. Yayin da wani jami'i daga cikinsu ya yi kukan kura zai cafko shi. Ganin haka ya sanya ya fafara da gudu ya yi gabas!
kaina na ya dinga bugawa kamar ana kwala mini guduma! Na dinga jin Hajijiya da kyar anti Maimuna ta zo ta janye ni daga wurin, rashin makama yasa na bi bayanta zuwa cikin gida tana rarrashinta tare da cewa na kwantar da hankalina inshallah gaskiya zata bayyana.
Na zube kasa cikin sanyi jiki na ce." Anti Maimuna ya zan yi ne?"
Ta ce." Addu'a za ki yi itace magani."
Da karfin gaske na furta." Inna lillahi wa'ina ilaihi raji'un!"
Tunda na dingi nanata Innalillahi na ji sauki yana saukar mini. Can kira ya shigo wayata dake uwardaki. Kafin na yi wani yun'kuri Salima ta shiga d'akin ta dauko mini da sauri ta ba ni. Hamusu ne ya kira. Na daga don ban yi mamaki ba tunda zan ce irin wannan sai ka tsince shi a wurin da baka ta'ba tsammani ba.
Cikin damuwa yake tambayata labarin da ya samu gaskiya ne. Na ce." Kai wanene yake gaya maka?" Kai tsaye ya ce." Kamalu ne." Na girgiza kai, ashe yaron can ya nufa lokacin da ya yi wa 'yansanda rashin kunya. Na ce." Haka dai iyayen yarinyar suke zargi Hamusu Amma a duniyar nan me Yusi ya sani da zai yi haka."
Ya ce." Wane police station suka tafi dashi?"

"Ka bari kawai ba sai ka je ba, Babansu Salima Yana can, in sha Allahu abun ba zai yi tsanani ba gaskiya zata bayyana. Kada ka gayawa Gwaggwo."

"Ba zan gaya mata ba in sha Allahu Amma anti Amina ki bari na je don Allah, kada duniya ta zage mu, wannan sharri ne?"
Na goge hawayen dake zuba a kumatuna na ce." Hamusu muddin aka binkita lamarin ba Babu gaskiya bisa zargin da suke yi wa yarona wallahi sai na d'aukaka kara ba zan yadda ba."

"Da damuwa mai yawa a tare dashi ya ce." Mu ma ba zamu yadda ba anti Amina, kawai ki gaya mini station din, zan je a yi komai a gabana."

Na ce." Ka bari zan kira ka zuwa an jima, don a halin yanzu ni ma ban san station ba, amma na gaya maka maigidan Yana can zamu yi waya idan an jima."

Na kashe wayar tare da ajiyeta a gefana. Na kalli anti Maimuna tare da furta." Ba zan yadda ba wallahi sai na d'auki mataki akan wannan sharrin da aka yi mini."

Shiru ta yi ba tace komai ba, gabad'aya duk jikinta ya yi sanyi, yanayinta sai ya nuna kamar akwai abinda ke damunta ko take 'boyewa, shine dalilin da yasa take ta cewa da ni na yi hakuri na bar maganar. Ni Kuma ba ta san yadda nake ji a cikin raina ba.

Muna zaune ni da ita da yara cikin alhini maigidan ya shigo da Yusi a hannunsa. Gabad'aya muka zuba masa ido. Ni dai ganin yarona kalau, ya sanya na dinga godewa Allah, Amma yanayin mijin na mu shi ya fi d'aukar hankalina. Ya zauna kan kujera kamar mara laka. Ya dubi yaran tare da basu umarnin fita, Salima da yan'uwanta suka fice gabad'aya, Yusi din ma ya bi bayansu.

Anti Maimuna ta ce." Da alama an samu maslaha sai dai yadda na ganka a sa'bule kamar akwai matsala."
Ya ce." Matsala babba ma kuwa." Sai ruwan hawaye ya ciko kwarmin idonsa.
Na ce." An gano wanda ya aikata kenan?"
Kai tsaye Ya ce." Turmuzi ne!"
Gabad'aya muka shiga gigita! hawayen da ya ciko kwarmin idonsa ya zuba a kumatunsa. Ya nisa kafin ya yakice kuttun takaicin da yake sasakarsa ya ce." Yaron nan Yusi bashi alhaki kuma dukan da jami'an nan suka yi masa sai Allah Ya saka masa, abinda ya faru shine; Wato rud'u da firgice da kuma tsoratarwa ya sanya yarinyar nan fad'in Yusi ne yake cire mata wando. Amma a zahiri Turmuzi ne, tun farkon fara shigowarta wasa gidan nan yake janta bayan korodo yana cire mata wando ya bata alawa. Mahaifin yarinyar shi ya yi mata wayo da daburu ya lallabata kan ta gaya masa wanene tana kuka tace Turmuzi ne ya ce duk wanda ta gayawa sai ya kasheta. Ya kunna mata wani film yana nuna mata irin kisan da zai yi mata da wuka.
A ranar da ya cire mata wandon ya danneta." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! sai kawai ya fashe da kuka yana girgiza kansa, tabbacin abin yana susar zuciyarsa.
"Yaushe Turmuzi ya lalace haka, yaushe ya balaga da zai iya haikewa yarinyar mutane. Shekara sha hudu me ya sani, a cikin gidana, ni ban kasance mazinaci ba, Allah kada ka jarrabe ni."
Babban mutum Yana kuka tukuru!"
Gabad'aya jikinmu ya yi sanyi. Kudirin da yi na d'aukar fansa akan haka na janye ganin irin gigitar da ya shiga.
Anti Maimuna ta ce." Yanzu a wace matsayar aka tsaya?"
Yasa hankice ya share fuskarsa." Maganar ta mutu, mahaifin yarinyar ya janye karar da ya yi. Yanzu sun kaita asibiti an duba wurin raunin kad'an ne, yarinyar ta yi bayani bayan gabansa da yake sa mata har hannu yana sa mata a wurin."
Na sunkuyar da kaina k'asa kawai sai wasu hawaye masu rad'adi suka goce mini suka dinga fafara gudu a kumatuna. Yaushe rabon da na yi kuka irin wannan har na manta. Ba komai ne yake daga mini hankali ba yadda tarbiyar yaran k'ananu take nema ta gurbace. Wai kamar Turmuzi shekara sha hudu shine da aikata wannan lamari.
Sai na ji anti Maimuna tana fad'in." Ban yi mamaki ba, dalili wayar da take hannun yaron babu abinda ba zata janyo ba. Tuntuni na gayawa Jamila cewa ta kwace wayar bata da amfani tunda ba aikin karatu yake yi da ita kallace kallace yake yi da, ya yaudareta ne kawai ya ce ta siya masa zata dinga taimaka masa bangaran karatunsa. A gabana akayi hakan, kuma ta saya masa. Na tabbata idan ka bincike wayar ba za a rasa fina finan banza ba, domin wasu lokotun idan ya shigo wurina Yana kallo baya barin kowa ya zo wurin da yake. Ya kan rage murya ko ya sanya airpix a kunnansa."

Fad'a sosai ya shiga yi, domin shi duk abinda ake yi bai san yaron yana da waya ba, uwar bata gaya masa ba a lokacin da zata saya masa sai lefin ma yake ko'karin shafar anti Maimuna. Ana haka Jamila ta shigo. Ganinmu a hargitse ya sanya ta dan yi sanyi tana fad'in." Yanzu nan na ga yaron nan Yusi nace ashe an samu maslaha sun ba dashi kenan."
Lokacin da take maganar hankalinta yana kan maigidan. Aikuwa tana rufe baki ya fara bata amsa, ya warwarewa mata zare da a bawa, har da barazanar saki muddin ta cigaba da yin abu ba tare da saninsa ba, domin ya tabbata wayar ta taka muhimiyar rawa wurin lalacewar yaron.
Bata yarda ba don kuka ta fashe dashi tana fad'in an yi wa yaronta 'kage, wallahi ba zata yarda ba sai ta d'auki mataki. Ya kuwace sai dai ta d'auka a gidan ubanta domin idan tace zata yi wani yun'kuri na fitar da maganar sai ya sake ta.
Jin haka yasa ta fita tana kuka. Ya tashi ya bi bayanta. Can muka dinga jin hayaniya a wurinta da kururuwar Turmuzi
Gabad'aya muka nufi wurin. Ya samu narkeken itace yana dukansa dashi. Duk ya fasa masa hanci. Wahala ta sanya yaron fad'in shine ya aikata amma ba zai kara ba. Da kyar na kwace itacen hannunsa ita kuma anti Maimuna ta rirri'ke shi. Lokacin ne Jamilar ta dadi a wurin tana wani irin abu wanda ya tabbatar mana da cewa aljanune suka buge ta. Maigidan bai tsaya ba ya kama hanya ya fice da wayar da ya kar'ba a hannun yaron. Ni da anti Maimuna muka tsaya a kanta da tofi da addu'a har suka saketa bacci ya d'auketa.
Lokacin da muka fito na kalli Anti Maimuna cikin sanyin jiki na ce." Dama anti Jamila tana da aljan u?
Ta ce." Tana dasu amma ba koyaushe suke tashi ba, sun fi zuwa yayin murna ko bakinciki idan ta haihu ma haka suke tashi akai akai har sai an yi suna."
Na girgiza kai ina mamaki, tabbas hakan zata iya faruwa idan aka yi duba da yanayin halayyarta. A hargitse take koyaushe kuma bata da yarda gata da mugun izza da girman kan tsiya.


Sai bayan sallar isha'i tukkuna hankalina ya daidaita.
Yusi ya shigo ya zauna kusa dani jikinsa duk a sa'bule. Na dube

16 / 18