Author : Binta Umar Category : Romance
idan na tashi fitar da kayan da zan bayar tana buk'ata. Na ce mata in sha Allahu zan zabar mata masu kyau.
Ana jibi d'aurin aure, anti Yagana da Ya Falmata suka dira. Kaya sosai suka had'o mini na gyara
dana sanyawa. Na yi farincikin zuwansu ba kad'an ba, domin dama kad'aici ya isheni. Sune suka je suka ga d'akin da zan zauna a unguwar Kawo Jirga. Su ka dawo suna 'kwarzanta gidan, da kuma sakin fuskar da suka samu daga matan gidan..
Hakan ya kara kwantar mini da hankali, na ajiye a raina in sha Allah zan yi iya iyawata wurin ganin na zauna dasu lafiya, zan kuma toshe kunnena daga barin jin gutsiri tsoma na jama'a..
Aka daura aure ranar juma'a, shedu suka shaida, kuma a ranar na tare a gidan. Inda na samu rakiyarsu Anti Yagana da Ya Falmata Sahura da kuma Anti Sakina.
Ummansu Hadiza ita da yaranta babu wanda ya raka ni. Ita a ranar ma kwanciya ta yi a d'aki ta ce zazzabi take yi.
Hadiza kuwa dama sai Yamma ta zo, Fati kuma tsohon cikine da ita ba ta fita, Hassana da Usaina kuma sam ba su zo ba, na fi zargin ba ta gaya musu ba, amma da ko Hassana ba ta zo ba, na tabbata Usaina zata zo, tunda muna shiri da ita.
A ranar da na tare na d'auka zai tattaramu wuri d'aya ya yi mana nasiha, sai na ga akasin haka. Bai yi wannan ba, gabad'aya ya d'okantu sai barin jiki yake yi. Ya manta da sunnar da annabi ya koyarwa sabbin ma'aurata. Na gaza yin shiru na tunasar dashi akwai sallar nafila fa, mu yi da kyakykyawar niyyar domin wanzuwar farinciki a cikin auranmu.
Kamar dai wanda na tilasta haka ya bi ra'ayina da yadda nake so, muka yi nafilar. Ina ta nazartarsa a tsanake na fara hangar wasu halayensa. Wato kowa dai ka ganshi kawai. Dama ana fad'in yawanci maza suna auran sha'awa ne, masu yi don Allah kad'an ne, na fara gazgata haka a dare daya da Alhaji Muntari, amma ba zan yanke hukunci kai tsaye a kansa ba tukkuna sai tafiya ta mi'ka. Yadda dai ya nuna zulamarsa a kaina shine abinda ya fi daure mini Kai, tamkar wanda bai da iyali haka ya kasance da ni a daran, ya gudanar da sha'aninsa, cikin nishadi da sambatu kala-kala.
Muka wayi gari cikin aminci. Amma har yanzu ban daina mamaki a kansa ba. Da Ya tambaye ni Yara na ce "
Suna can gidan kakarsu sai na yi sati tukkuna za a kawo su."
Sai Ya ce ." To Hakan ba lefi, kema kin yi kyawun kai, na gama morewa ko?"
Na yi murmushi ban ce masa komai ba. Ya ce." Za ki shiga ku gaisa da matan gidan hakan ya yi ko?"
Na dube shi a tsanaki na ce." Ai na d'auka kai za ka yi mini iso a wurinsu mu gaisa sosai, idan da wani karin bayani a kaina da kansu sai ka yi mana."
Ya girgiza kansa yana furta." A'a, ki je dai ku gaisa, ai kina fita kowacce ga kofarta nan. Ku dai zauna lafiya don Allah, ki ba su girmansu, tunda su ki ka samu a gidan, ki bi tsarinsu, muddin babu cutarwa. Suma na yi musu bayani akanki, ba ki da matsala, abinda dai na sani kansu a had'e yake, haka zalika ma yaransu, idan kin bi su a yadda suke so, za ku zauna lafiya da juna."
Na jima Ina kallonsa da kuma nazartar maganarsa. Ai idan da wanda zan bi sau da k'afa shine, tunda shi ya ajiye ni, banga dalilin da zai sanya ace mini na bi wata ba, zaman aure ai ba wasa ba ne.
Amma ban nuna masa damuwata akan maganarsa ba na ce." Babu matsala zan shiga mu gaisa da su zuwa an jima, amma wani hanzari ba gudu ba, wallahi abubuwa sun sha mini kai, tun farkon had'uwarmu nake so mu yi maganar da kai, Allah Bai nufa, amma wata'kila Baba Sule ya gaya maka Ina aiki ko? Ina koyarwa gwale firamare skull, sannan ina dinki sosai, ina so na cigaba daga inda na tsaya, ba don komai ba sai don kula da yarana, ba zai yiwu duk wahalarsu na sakar maka ba, ni ma zan taimaka da wani abun."
Fuskarsa ta canza da wani yanayi da ban ta'ba ganinsa a ciki ba. Ya gyara zama Yana fuskatantata sosai Ya ce, "A gaskiya bai gaya mini ba, kuma kema kin yi ragwan azancin da ba ki sanar da ni ba tun farko ai da na fada miki ra'ayina, ba zan iya bari iyalina na fita aiki ba, bayan Allah ya yi mini komai, ba ni da wannan tsarin."
Gabana na wani irin fad'uwa na zuba masa ido, Ina tunanin yadda zan yi don wallahi ban ta'ba tsammanin zan samu matsala a wurinsa ba.
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Ki ajiye maganar zuwa aiki Amina, babu ita a tsarina, sai dai ba zan katseki ba, adalci daya zan yi miki, ki cigaba da dinkinki, a cikin gida, ai aure ba wasa ba ne, da zan fita matata itama ta fita tana cud'anya da maza a waje, ba mu ta so da wannan akid'ar a gidanmu ba. Matayenmu suna gida a lullube mu ne muke fita mu nemo musu abinda za su ci, maganar yaranki kuma, ni na ce zan ri'ke su ai, kada ki damu zan miki kokari a kansu, a marayu ne, wata'kila sai na samu aljanna ta dalilinsu, in sha Allahu zan kula miki da su.......✍️
*1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank*
*07084653262*
[11/24, 9:34 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*
*TALLAH!*
🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨
🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi
https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t
*@Arewa books*
*Bintuumarabbale*
*Free peges*
*15*
Gabad'aya jikina ya mutu da kalaminsa na karshe. Dole haka na ha'kura tunda ya riga ya gama kashe mini jiki da tabbatar mini cewa zai kula mini da yarana, wanda dama duk abinda nake yi saboda su nake yi. Na kuma yi nazari sosai, akwai tazara mai mugun tsayi tsakanin nan kawo jirga da gwale makarantar da nake koyarwa, za a dinga samun tsaiko da tangard'a na makara da sauran matsaltsalu. Dole dai babu yadda zan yi na ha'kura, na ajiye aikin, na rungumi sana'ar hannun, tunda bai nuna mini keta a kanta ba.
A d'akina ya shirya sosai, ya yi gayu, nan na sake fahimtar mutum ne shi mai son ado da nuna 'kawa, hatta waya da biyu yake amfani, kuma masu girma da kudi. Kafin ya fita yake gaya mini idan ya gama kwanaki ukun da musulunci ya ba ni, sai na fara binsa dakinsa kamar yadda sauran suke masa.
Na ce." To shikkenan hakan ya yi." Sai bayan da ya fita da kamar minti ashirin tukkuna na zura hijabi na fito babban tsakargidan. Gashinan dai babu gyara, bakin kicin duk kwanuka. Da takalman yaran gidan a watse.
Na dinga jin kayaniyar yara a d'akin da yake fuskanto ni. Kai tsaye can na nufa cikin nutsuwa na shiga da sallama.
Tana kwance kan duguwar kujera, da kayan bacci a jikinta. fara ce gajera, kamar dai yadda ya nuna mini ita a hoto, ba ta da muni. yaran suna ta wasa, wasu daga ciki da littafain makaranta, wasu kuma game suke yi a wayar da nake tsammanin ta ta ce. Ta mike zaune da sakakkiyar fuska tana cewa." Shigo mana." Na saki fuskata sosai na shiga na zauna kan kujera, ina fad'in." Yaran duk suna nan kenan, ko da yake ai da sauran hutun tukkuna."
Tana gyara zamanta ta ce." Ai hutu kuma ya kare tunda litinin za a koma, kada ki so ki ya yadda zaman nan nasu ya isheni, dan bacci nan na safe basa barina na yi."
Dariya na yi, ina kallonsu yayin da suke yi mini wani irin kallo, na rashin sani, cikinsu kuma babu wanda ya yi tunanin ya gaisheni.
Na ce." Ina kwana, ya yaran, fatan na sameku lafiya."
Ta amsa a sake tana cewa." Lafiya Lou ki ka same mu, yanzu nan dama Babansu da ya shigo yake gaya mini za ki zo mu gaisa."
Wani d'an matashin yaro da tun zamana a wurin na ji ana kiransa da Turmuzi Ya ce." Mama itace amaryar Babanmu ne?"
Ta ce." E, ita ce" Shiru ya yi bai ce komai ba, sai kuma can ya tashi ya fita da sauri. Sauran yaran kuma suka cigaba da sha'aninsu babu wanda ya gaisheni a cikinsu.
Na cika da mamaki sosai, kuma ita Anti Maimuna haka sunanta yake ba ta tsawatar musu ba.
Minti kusan goma ina zaune muna dan ta'ba hira. Na lura tana da sakin fuska, kuma dai a haka kamar babu wani kulli a zuciyarta. Tana gaya mini yadda tsare-tsaren gidan yake. Sai dai yadda na fahimta tana da son jiki da kazanta a jikinta da falonta na lura da hakan, tafin 'kafafunta duk sun yi daud'a. Kuma kayan bacci ne a jikinta masu ruwan haske,
Amma sun dafe, gashi dai safiya ce, amma kusancina da ita hancina yana ta sha'ko mini warin hammatarta, dukda hallita ne, amma dai akwai kazanta a sha'aninta, tunda mutum ya san yana da ki'bar da za ta ajiye masa gumi sai ya bi matakan gyarawa.
Shigowa ta yi babu sallama tana cewa." Tun d'azu Turmuzi ya je yana gaya mini ga amarya nan a sashenki, anti Maimuna ai sai ki ce na zo ni ma a zauna da ni, a kalla fa kun fi minti ashirin a tare, ni ba fa na son haka."
Cikin kausasa harshe take yin maganar. Ita kuma sai ta fara dariya tana cewa." Yanzu nan nake cewa Salima ta zo ta rakata wurinki ku gaisa, ai na yi tsammanin bacci ki ke yi ne."
Ta zauna tana d'an kallona kafin ta ce." Ba bacci nake yi ba, kuma da ki ke cewa Salima ta rakota wurina makauniya ce ita, ai babu wanda ya yi mata jagora ta shigo wurinki, haka Turmuzi ya gaya mini.
Anti Sakina ta ce." Ke fa matsalata dake Jamila gajan ha'kuri wallahi, wannan ba a bin damuwa ba ne fa."
"Gajan ha'kuri kamar yaya Anti Maimuna, gaskiya na fada fa, kin san ni komai a bud'e nake yinsa."
Na ce."Haba baiwar Allah, kya bari mu gaisa ko? Ai zan shigo har wurin naki dama bisa bin umarin maigidan, ina fata dai na sameku lafiya."
"Lafiyarmu lau wallahi, ya hidima fatan an tashi taro lafiya."
"Alhamdulillahi, na shigo cikinku da kyakykyawar zuciya, ina fatan zaku karbe ni hannu biyu." Ta ce." In sha Allahu rabbi."
Falon ya yi shiru. Yaran duk sun zubo mana Ido. Sai na dube su a tsanake na ce.' Babu wanda ya gaishe ni a cikinku, kuma duk ku gaya mini sunayenku." Da yar dariya na yi maganar.
Sai suka fara rige-rigen gaisheni, kowa yana ko'karin gaya mini sunansa. Na dubu Anti Maimuna da fad'in." Salima ce babbarsu ko?" Ta ce." E, itace gata nan sai tsawon kafar tsiya." Na ce." Ai girman 'ya mace ba shi da wahala, daga zarar ka fara da mace sai girma ya kamaka."
Ta yi dariya tana cewa." Wallahi hakane. "
Anti Jamila tasha kunu bata tofa mana ba. Ni Kuma ina sane ban sanya maganata da ita ba, saboda karon farko na fahimci bata da hankali, sannan yadda take nuna gadara akan Uwargidan, tana gaya mata magana kausasa bayan ko banza ta girme mata, to ni ba zan d'auka ba, duk cikinmu babu yaro, ba na tsammanin itama ta ba ni wasu shekaru da yawa. Shiyasa tun bayan gaisuwar da muka yi da ita, ban 'kara tanka mata ba, daga karshe ma sai na tashi na yi musu sallama na koma wurina da tunanin yanayin zamantakewar da suke gudanarwa mara kangado.
Ciki da falo ne wadatattu, kuma kayan katakon da ya zuba mini masu kyau ne da tsada da manyan labuleye. Harda tibi irin ta bango. Na yaba masa sosai domin d'akin nawa ya yi kyau k'warai ko na wata budurwar albarka. Matsalar dai kawai babu bandaki a d'akin duk suna can waje. Dakinsa ne kawai dashi. Kicin din ma na had'aka ne. Amma gidan akwai yalwa irin gini ne na wadata babu takura. Har da wurin saukar baki a cikin gidan
Na d'an gyara abinda bai yi mini, na ware kwanukan da zan zuba a kwando, da fulasai, da duk abinda zan nema domin ba na tunanin zan kwashi kayana na kai kicin din gabad'aya, domin fitar da na yi d'azu, na hasashi akwai gyara sosai a tare dasu, gidan gabad'aya babu tsafta har kicin din, kudaje sai bi suke yi, ban sani ba ko suna da mai aiki oho. Na zauna ina hutuwa amma gabad'aya hankalina na kan yaran, mussaman Yusi jiya ya sharbi kuka lokacin da za mu taho sai wayo aka yi masa aka fita dashi daga gidan.
Gwaggo wayarta ta lalace sai na nemi ta Hamusu dukda ba ni da tabbacin Yana gidan, amma dai ai garin yanzu ya waye.
Muka gaisa Yana 'yar dariya yake cewa."Amina Anya yau kin yi bacci arziki kuwa, na san hanalinki Yana kan yaran nan."
Ni ma cikin barkwanci na ce." Ban yi ba gaskiya, ai shiyasa ma na gaza ha'kuri na ce bari na kira ka, na ji ya suka kwana."
Ya ce." Suna nan lafiya lau, ga Yusi nan ya warware Yana ta wasansa. Shi kuma Kamalu gashi nan, Yana zubawa Gwaggo ruwa."
Na ce." To fara ba ni Gwaggon mu gaisa tukkuna."
Ya mika mata watar. Na ce." Gwaggo ina kwana, Kun tashi lafiya?".
Cike da kulawa ta amsa tana cewa." Ya kwanan bakunta Kuma." Na ce." Alhamdulillahi Gwaggo. Sai ta dora da cewa ." Ai ana ta fad'in nagartar abokanan zamanki, an ce kansu a had'e yake ba su ta'ba fad'a ba, kema ki bi su a yadda ki ka gansu domin samun daidaito. Ubangiji Allah Ya sanya alheri."
Na ce." Amin Ya Allah, ai kam babu lefi, akwai fahimta a tsakaninsu, in sha Allahu zan zauna dasu lafiya."
Ta ce.'"To Allah Ya kad'e fitina."
Hamusu Ya kar'bi wayar yana fad'in." Fita zan yi anti Amina, ga Yusi ku gaisa, idan na dawo da yamma zan kira ki sai ku gaisa da Kamalu, don ya fita yanzu, na ce miki dama Yana zubawa Gwaggo ruwa, yau me ruwanta ne bai kawo mata ba."
Na ce." To shikkenan bawa Yusi wayar." Ya mika masa da zumud'i a tare dashi Yana dariya yake cewa." Mama shine jiya ku ka yi mini wayo kuka gudu ko?"
Na sauke ajiyar zuciya a nutse na ce." Babu gaisuwa sai korafi ko Yusi."
"Yi hakuri Mama, ina kwana ya kuke?"
"Na ce." Ina lafiya lau, zaka zauna a hannun Gwaggo ko?"
"Um-um!" Ya furta da sauri."
Na yi dariya tare da cewa." Shikkenan zan zo na d'aukeku sati mai zuwa in sha Allahu." Farincikinsa Ya tsananta ya ce." To daga yau zan fara lissafi Mama." Na yi dariya tare da cewa." Ba wa Baba Hamusu wayar zan yi magana dashi."
Yana kar'ba na ce." Don Allah da yamma idan babu takurawa kai da Usaini ku kawo mini kekunan d'inkina mana, akwai sauran kayan jama'a a hannuna. Maigidan Ya ce na ajiye aiki Hamusu, shiyasa gabad'aya yanzu hankalina ya karkarta wurin ganin na kafu anan din. Dukda na san da yawa wad'anda za su biyo nan din, amma ina so nan din ma a san ni akan sana'ata."
Ya ce."Anti Amina dadina dake akwai himma, kina da zuciya da neman na kanki, Allah Ya dafa miki, in sha Allahu kuma daga na dawo daga kasuwa zan je can gidan naku na samu Usainin."
Na ce." Shi ma na gaya masa Ya na jiranka."
Ya ce." To shikkenan za mu zo in sha Allahu."
Muka yi sallama na kashe wayar na ajiye. Ina sake nazarin yadda al'amurana za su kasance a sabuwar rayuwar da na tsinci kaina a cikinta.
To cikin kwana uku kacal na fahimci yadda al'amuran suke gudana a gidan Alhaji Muntari. A kwai kusakurai masu girma da suka riga suka yi karfi a yanzu wanda idan an ce za a gyara su za a samu matsala babba, tunda tun fil'azal a haka suka gina gidan da kuma mijin nasu.
Alhaji Muntari rayuwarsa yake gudanarwa irin ta bahaushe zalla, karin abin kuma iyakacinsa sakandire bai yi zurfin karatun boko ba, na addinin ma akwai matsala domin Yana tafka kusakurai a sha'aninsa, kuma yadda na lura dashi ba mutum ne mai so a yi masa gyara ba. Irin mutana nan ne da duk abinda suka yi daidai ne. Tun ranar da ya fara auratayya da ni, na fuskance dhi. Idan mun kammala yana kallona zan shiga bandakin da yake cikin dakinsa na tsarkake jikina, amma sai dai na fito na same shi Yana bacci tare da najasar a jikinsa. Abin takaici kuma da ban haushi baya tashi sallar asubahi. Har sai gari ya yi haske tukkuna zai yi sallah.
Sun samu bambamci da Yaya Aminu ta wannan gefan, domin shi Abbansu Yusi akwai ibada. Ta inda dabi'arsu ta zo daya wurin mayatar yin jima'i, duk dare lokacin Yaya Aminu sai ya kwanta da ni, shiyasa da Allah Ya had'a ni da wannan din ban damu ba, tunda jikina ya riga ya saba da Hakan.
Alhaji Muntari d'an sharholiya, aji dad'in duniya kawai. Addini bai dame shi ka'in da na'in ba. Ya yi ado da kwalliya ya ci abinci, sannan ya kwanta da mace, wannan shine abinda ya fi bawa muhimmanci. Gidansa babu yunwa da abinci, Yana kuma ko'karin tsarewa kowa mutumcinta. Sai dai 'keta da matan gidan suka sanya a zukatunsu. Abinci d'anye dai gashinan a store. To duk wadda take da