fita tarr tarr musamman sabeeha da idan ka ganta zaka rantse kamar an sauyata ne ta koma kamar kaza yar shila da aka ciro daga gashi masha allah, fatarta wane ta jariri, har wani yellowish milky haske tayi, kai mace da gyara ba a cewa komai, su kansu matan wajen yabawa sukeyi da kyanta da kuma fatarta,ana gama masu sukayi payment suka fito hamad na jiransu.
Wallahi tunda ya sanya idnaunshi kanta ya kasa daukewa, tun daga nesa ya hango yanda tayi wani extra dashing kyau,sai faman kyalli take, suna shigowa motar kuwa kamshinsu na dukhoon by @amrukt_incence ya bade gaba daya matar ya hade da sanyin ac, ay saida ya lumshe ido ya bude ya kalli sabeeha da itama shi take kallo a lokacin don gaishesa tayi bai amsa ba saboda ya tafi.
“Whats with this lovely scent?”
Laila tayi dariya tace “sirri ne yaya…kaima ya tafi dakai ko?”
Wani irin kallo ya mata tare da harara dayasa ta guntsw dariyarta suka futa daga harabar wajen.
Basu suka dawo gida ba sai gab da magrib, suna dawowa kafin su akiga shiga gida call din bahijja ya shugo wayar sabeeha data riketa a hannu, duniya dadi, bata taba tunanin rike irin waennan wayoyinba sai yanxu, allah sarki rayuwa, irinta wadda taj ya bata tana nan ajiye tunda ta kasheta bata kunna ba.
Kai tsaye suka wuce part din bahijar da sallama, lokacin tana kitchen futowar kenan, tana ganin sabeeha tace masha allah lakuwwata illa billa sannan ta sumbaci goshi ta tace “gaskia wannan saloon dole nayi sponsoring kaina a wajen, haka suka gyara min diyata, wannan kamshi haka kamar amarya”
Dariya laila tayi tace “mummy ay wallahi sun iya gyara sosai, just look at skin din sabewha kamar an bareta a leda saima kinga kalaban da aka mata”
Sabeeha tayi dariya tace “mummy itama bakiga nata ba yayi kyau soaai”
Murmushi bahijja tayi tana mai shafa fuskar sabeeha tace “allah ya maku albarka, kuje kuyi sallah yau anan zakuyi dinner, kinqi dawowa wajen mummynki da daddy ko? Anne da nanna sun kwace mana ke”
Sunkuyar dakai sabeeha tayi, bahijja na ganin haka tace “kuje dakinki kuyi sallah” da toh suka amsa sannan suka wuce dakin nata dake kusa dana maya, har zaau shiga laila tace bari na leka maya naji meysa bata zo mun fita gaba daya ba.
Sabeeha ta girgiza mata kai kawai sannan ta wuce daki ita kuma ta shiga part din maya, tana ahiga da sallama ta taddata zaune bakin gado ta dora kafa daya kan daya tana taunar gummies, laila ta karaso ta zauna gefen gado “baby gurl how far? Bakizo mun fita ba, ke wallahi wa had alot if fun, kinsan blush ta gyara wajenta, wallahi bakiga gyaran datayi ma sabeeha ba ke kyace amarya”
Saurin dakatar da ita maya tayi idanunta yayi jaa jin ta ambato sabeeha.
“Dallah dakata malamaa….munafuka, annamimiya, ai bansan ke munafuka bace sai yanxu, kinata wani abu saboda ke gaki ga cousin dinki ko? Toh nace maki inason naji me kukayi ne????ay wallahi tunda kika zabeta kike binta babu ni babu ke munafuka”
“Karki sake cemin munafuka maya…”
“An fada din munafuka fooliah idiot, mugaye, ni zakici amana, kuna wasu abubuwa kamar ciki daya kuka fito kina binta?”
“Kwarai kuwa na bita, saboda itace asalin cousin dita, saboda yanda nake tsakanina dake shi zaisa karna dunga kulata kenan? Toh ke asuwa zaki hanani mu’amala da yar uwata ta jini?, ba damuwa ni nazo wajenki shiyasa kike fada min maganar banza mteww” tana kaiwa nan ta miqe, laila bata iya fada ba amma fa idan aka kaita bango itama ba kyalle bace.
Batun yanxu maya ke pissing dinta off ba da abubuwan da take yi yanxu, bata kaunar taga kowa a kusa da sabeeh a infact da an fara maganar sabeeha zakaga tsana karara akan fuskarta ko ta fusata.
Ita sabeehar da ya kamata ace itace kejin haushinta saboda sabadiyarta uwarta ta sauyata, don ita tasha wahala rayiwa ita kuma ta taso cikkn jin dadi.
Laila na fita maya ta miqe tana zarya tsakanin dakin, ji take kamar tabi lailar ta shaqeta itama ta huta kawai.
Laila ko tana futa ta shiga part din sabeeha daidai nan sabeeha ta idar da sallah,ta dubi laila data shugo rai a bace ta tambayeta meya sameta tace mata babu komi wani ne ya bata mata rai a waya.
The next day..
Tunda asuba bahijja ta shugo dakin maya ta tasheta tayi sallah, daga yanda ta tashi a fusace kamar zata zagi bahijjar ko ince ta zagenta ma don kncking din da bahijja ta dunga yi a dakin saboda qin budewar sa maya tayi saboda bugewar datayi yasa ta tashi a harzuke.
Tana ganin bahijja ce ta koma ta kwanta ko gaisheta batayi ba bahijja ta tambayeta meke damunta kwana biyu duk ta sauya, abu kadan fada, tace mata babu komi, karahe dai ma kusan futsara ta mata tace “kije ki damu da yarki, nida ba yarki bace daman ba damuqa kikayi da damuwata ba”
Bahijja was so shock ta dubi maya tace “maya wannan wani irin magana ne babu manners?”
Maya tayi shuru batace mata komai ba, bahijja ta dubeta tace “meke damunki”
Tayi banza da ita, bahijja tayi shuru gabanta na faduwa kafin tace “jekiyi sallah, sannan ki shirya da wuri ki sauko breakfast zaku koma school yau”
tana fadin haka ta futa jiki a mace, bata taba taammanin haka daga mayar ba amma tayi mata uzuri.
Maya ta bita da harara, bayan sabeeha babu wadda takeji tsanarta kamar bahijja, kamar yanda nace maku itafa duk wanda taga yana kaunar sabewha to fa babban maqitinta ne duk yabda take da mutun, bakin bahijja take gani,ko ganinta bata kaunaryi tana ganinta take ganin sabeeha akan fuskarta tunda itace ta kawota duniya, ta manta yanda bahijja ta nuna mata so da kauna kuma ta rike a yanxu data kasance ba itace yarta ta asli ba.
Ay yanxu ta gama sama ranta cewa ba sonta suke ba kwata kwata, kuma nan gaba zasu wulaqantata saboda haka ta dauka kudirin duk yanda zatayi saita mallaki taj, don shi kadai ne power da zata samu a gidan, tayi abunda taga dama.
Komawarta tayi kwanciyarta ba tare da tayi sallar ba.
Misalin wajen karfe takwas daidai suka gama breakfast laila ta shugo part dinsu anne ta tadda sabeeha ta gama breakfast, sallama sukayi ma nannan da anne sannan suka futo suka nufi part dinsu maya, suna shiga sabeeha ta taho da sauri ta rungumi bahijja dake zaune a parlor hankalinta yayi nisa sosai game da tunanin maya, saijin sabeeha tayi a jikinta, wani irin farin ciki taji ya lulubeta ta dubi sabeehar tace “morning diyar kirki kin tashi lpy?”
“Lpy lau mummy”
Laila ma ta gaisheta ta amsa sannan ta tambayesu idan akwai wani abu da zasu tafi dashi idan sunaso sukace mata ah ah, laila na duban time a watch din hannunta tace “mummy maya fa? Zamuyi latti”
Sai a lokacin bahijja ta kwalama basira kira tace ta kira maya, basira ta hau sama ko minti biyu bata yi ba ta sauko kasa ta dubesu, bahijja tace “yadai?”
“Hajiya tace wai bata gama shiri ba su tafi kaqai zata taho daga baya”
“Kamar ya bata gama ba?”
“Eh tana shafa mai ne wai”
Mikewa bahijja tayi ta hau saman da sallama tana budewa ta hangota gaban dresser da waya akunnenta tana dariya, ko shafa man ma bata fara ba, ta karaso gabanta maya na ganinta amma tayi knar bata ganta ba ta cigaba da abunda take, “yea babess” maya ta fada wayarta na kunenta har zuwa lokacin,
Bahijja takai wajen minyi daya a tsaye expecting zata kashe wayar amma bata kashe ba, saida ta karba wayar sannan ta dubi screen din taga an saka sweetness, take gabanta ya fadi amma ta dake ta kashe wayar maya ta dubeta tace “waya fa nake mummy”
“Yes na gani, who’s on the line??”
“Ay kin gani” ta bata amsa kai taaye babu respect
“Maya where are you leading to?meke damunki ne eh??? Answer me”
Miqewa tayi tsaye zata juya ta wuce ta gaban bahijja ta dakatar da ita, “don’t dare walk on me maya!!!!” Bahijja ta daka mata tsawa, “dama kin damu dani ne??? How would you know where im leading tunda tsinanniyar yarki kawai kika sani mteww”
Tana kaiwa nan ta juya batayi auni ba sai jin saukar mari tayi akan fuskarta tassssa, cikin sauri maya ta dago ta dage fuskarta, mamaki ya gama cikata sai hawaye, zqta iya cewa mummy bata taba marinta ba amma yau ta mareta saboda wannan tsinanniyar..
Bahijja na huci taabar bacin rai tace “now get ready na baki nanda minti biyar ki sauko kasa” tana fadin haka ta wulla mata wayan nata kan gado ta wuce rai a bace, tanajin wani abu kamar hawaye na neman sauko mata, she felt ao disappointed akan maya, da bata ganin abunda take kwata kwata amma yanxu kamar an vude mata ido haka take ganin komai.
Tana fita maya ta bita da wani matsanancin kallo, abubuwa da dama na yawo a mind dinta.
Bahijja na saukowa ta taddasu zaune lokacin wajen 8:50 saura, sabeeha tayi shuru tana tuna yanayin data ga maman nata, bahijja na zama kan kujera ta dubeau tace “zata sauko yanxu”
Sabeeha ta dago ta kallwta sannan ta kamo hannunta tacw “mummy akwai abunda kw damunki ne?”
Mumushun yaqe bahijja tayi kafin tace “babu komi baby, na tashi da ciwon kaine”
“Subhanallah, ko zakije asibiti,?”
Ta fada tana taba goshin mummyn with so much care, bahijja ta kalleta sai kaqai taji zuciyanta na karaya tayi kakarin danne hawayen dataji yana neman sauko mata.
Maya kam bata suako ba sai tara daidai, ta saka riga da wando ta aza mayafi akanta, ko kallonsu batayi ba ta fuce, bahijj ta bita da kallo ta girgiza kai, suka tashi sabeeha ta mata sallama suka miqe ita da laila suka fita bhijja ta bisu da kallo.
Toh haka dai aka shiga mota cikin bacin rai maya kamar zata balla kofar motar, hamad ko ta kanta baibi ba don ko gaishesa batayi ba, laila ta zagayo ta dayan side din ta zauna, sabewha kuma tace gaba.
Shuru babu wand ayace sa dan uwansa tak sai laila ke dan nagana jefi jefi sabeeha na amsata har suka iso.
Suna isowa itace ta fara bange motar bayan ta futa, sabeeha ta girgiza kanta kawai sukayi sallama da hamad suka wuce class ita da laila don course daya zasuyi.
Hamad bai dade da wucewa ba wata arniyar mota tazo daukan maya, ta fito daga class ko permission bata dauka ba tayi gaba abunta.
Tana shiga motar salim ya dubeta yana smirking yace “duk yanda akayi akwai dalilin dayasa kika kirani, ive been calling you kina denying, kina tunanin threat din danayi maki da nudes dinki karya ne ko?“
“Let’s go please, i need to relive all of my stress and worries”
Yana jin haka ya wage hakora baiyi expecting haka ba kwata kwata, “as you wish” ya bata amsa sannan yaja motar.
Basune sukayi landing ba sai a abuja continental hotel, already yayi booking don kwananshi biyu kenan yana ta’asarsa son ransa.
MATAR TAJ (destined with you)
Written by
Queenmarh
Book2
PAID
Chapter 112
Achan gida ko misalin wajen karfe sha biyu kowa ya hallara cikin katuwar jeep din gidan wadda ake using idan za aje vacation, mota biyu sukayi, anne nanna, fadila, ya sameed, dadyn sabeeha, sai kuma bahijja sai taj.
Tunda aka shiga motar kowa yayi shuru jugum, fadila da bahijja na zaune a motar gaba while dadyn sabeeha ke gaba shima driver kuma na tukasu.
Fadila ta kamo hannun bahijja data zqma so lost in her thoughts tace “are you okay? Ko mu koma gida”
Kamar jira take kawai saiga hawaye, ta soma magana kasa kasa, “no i have to do this”
Tausasata fadila tayi har suka iso, kai zata iya rantsewa batasan ta insa suka biba suka karaso wajen, ta karkashin tunnel sukabi sai ganinsu sukayi a wani gari daban, daidai gate din wajen suka tsaya wasu dima diman samudawa suka taho gadan gadan, ya sameer ya bada identity card dinshi aka barsu suka shiga daga ciki, taaron dake wajen ba a magana ta kowanne sako, kamar jira ake ayi yaqi ko a soma harbi ta ko’ina.
Fitowa sukayi kowa bayan anyi parking daidai nan babban director din dss din ya tarbesu, inda anne take ma suka nufa yaransa suka sara, sannan yace “sannu da zuwa hajiya”
Sanin darajarta da girman ta tundaga villa, wajen presidency shi yasa shigansu baiyi wuya ba.
Kai wajen dai wallahi abun tsoro ne gaba dayanshi, ko’ina yasha fentin baki, su kansu mutanen dake tsaren wajen sunsha wani bakin fenti a fuska.
Ciki suka nufa aka bude kofar shiga kai tsaye aka tunkari bangaren mata, ko’ina bango ne kawai sai wata yar raga da ake turama prisoners abunci a ciki, kai ko kamshi juna basaji, babu wuta babu light, kashunsu futsarinsu duk a waje guda, idan za’ayi masu hukunci kuwa bazakaji karar na gefen ba, azaba 2/47, babu dan adam da zaiyi fatan zuwa wajennan, kuma sai masu tsatsauran laifi.
Daidai gaban wani daki suka tsaya, yasa aka daga karfen dake wajen take bangon wajen ya soma dagawa sama kamar ana daga kofar karfe sama ya bude tarrr,
Juyowa director yayi yace “bismillah hajiya sannan ya wuce, yaransa suka tsaya a wajen da bundigu.
Kowa ya zubama wajen idanu ba’a ganin komai daga ciki, dakin duhu kenan, daya daga cikin yaran ne suka buga bundigar su a gefen wajen dayasa aka soma motsawa daga ciki, kafin wadda ke ciki ya soma tahowa gaban waje.
Innalillahi wa inna ialaihi rajiun, da wani irin bushahsen hannu suka fara cin karo, kamar babu fata a jikin, basu kaiga shiga shock ba saida ta futo sarari karfe na masu matsakiya taakani.
Baya suka somayi jin wani irin wari ya doso su, saiga hadiza ta bayyana bakinta na yoyon miyau, kanta ya chinye gaba daya ta qanjame kamar kwarabgwal wai a haka ma tana cikin prisoners din da basa chan azaba, taji wuta yar qaniya, dakyar take iya bude idanunta, tana ihu baka ma jin sautin muryarta kamar kurma.
“Wannan ta haukace kawai” fadila tayi magana a hankali, “daman abunda ka shuka shi zaka girma komin daren dadewa,”
Anne ta kauda idanunta haka zalika nannan, dan guntun hankalin hadiza dayayi mata saura ne yasa ta gane mutanen dake gabanta, take kuma idanunta ya kaiga bahijja da ido daya, bahijja ta kalleta hawaye ya soma sauka a idanunta,bawai na taisayinta ba sai na aon jin dalilin da yasa hadiza ta mata haka.
Sai kawia hadizar ta fashe da daria kamar mahaukaciya tana kallon bahijja, muryanta baya futa ta soma magana “naci galaba akanki, naci galaba akanki bahijja…kona mutu bazan taba dana sani ba”
“Meysa?’meysa hadiza me na maki a duniyar nan?
“Ay basai kin tambayeta, irin wanan basa taba nadama, tsana ce kawai take maki,wannan bata da mararraba da shiadan”
Fadila tayi magana cikin bacin rai, jami data frka ta taho a guje tana jan kafa ta zama gurguwar dole, tunda akamata wani duka kafarta ta fashe shikenan sai wari.
“Ha..jiyaa ku rufan asiri ku taimakan, yayana uku…mijinaaa, na tuna nidai na tuba wallahi na tuba, azabaaaa wayyo azabaaaaa”
Kai kowa saida yaji tausayinsu wallahi dukda ba abun tausayi bane, bahijja ce ta fara barin wajen majeed ya biyo bayanta sai fadila, ya rage daga anne sai nannan da ya sameer,
“Mu tafi kawai”
Suka juya kenan hadiza ganin bahijja tabar wajen yaza ta soma magana kasa kasa “ yata…yata ..maya..yata, ko sau daya ku hadani da yata”
“Bakida wannan damar hadiza, bake babu ita..” anna ta fada rai a bace tabar wajen sameer na biye da ita ya rage nannnan ce a wajen, sai a lokacin hadiza ta soma kuka “hajiya yata, ku hadani da ita karna mutu ban ganta ba hajiya dan allah hajiya” dole nannan tabar wajen zuciyarta na karaya sosai suka futa daga wajen kowa jikinsa a mace.
Aka basu record din su hadizar, both hadizar da jamila suna da cutar kanjamau, sannan daya ta fara alamun hauka, kamar yanda anne ta bada umarni kullesu kawai akayi bayan hukuntasu da akayi sau daya, amma kalla yanda suka dawo kamar matttun mushe.
4:30pm.
Continental hotel…
Yana kanta anata abu daya,har yana mamaki ko wani abu tasha ne, don normally yasan bata dadewa haka take maganar ta gaji, dake kuma abun harda aikin shedan saiya zamana hes ao excited don ta karo wulaqanci sosai, they had more than 5 rounds of unprotected sex over and over, ada idan zasuyi taka zama very strict akan saidai yayi amfani da c*nd*m yau ko jinta take a sama, babu abunda yake sai lashe baki,
Ba itace ta tashi shiryawa ba sai wajen 5 salim na daga kwance tsurara ya duveta yace “wonderful day…sai kuma yaushe??”
“Gobe!” Ta bashi amsa kai taaye, ya lashe lebensa kafin ya dubeta, gefen side drawwe shi ya bude ya zaro dollars guda biyar ya aje mata, surprinsly ta kallw kudin don bai taba bata in dollar ba karkari few naira bundle.
“Enjoy your self babe”
Ta kwashe avubta ta watsa jaka sannan ta dubeshi tace “tashi ka maidani school?”
“Which school baku tashi ba yabxu ita almost past quarter 5”
“Muje ka kaini gida then” tana fadin haka ya miqe yayi wanka sannan ya futo ya saka kaya suka fito.
Suna shiga mota suka nufi gida ko dar dar bata ji, suna isowa daga bakin gate tace ya sauketa, kafin ta sauka tace “inason bull aphrodisiac 2 pack please gobe”
Wangale baki yayi yace “okay… baby “ yana fadin haka ta futa abunta yaja motarsa.
Kai tsaye ta shige ciki abunta tana duban call din laila, saida ta shugo ta amsa tare da kaiwa kunenta “kina ina ne? Ya hamad yazo munata jiranki we had to lie cewa kina late lectures”
“Na dawo gida..”
Tana fadin haka ta kashe wayar ta shigo parlor, babu kowa kasan wanda hakan yaza ta wuce saka abunta zuwa part nasu.
Su laila na tsaye a faculty dinsu maya idanu zuru zuru sabeeha tace “tana ina?”
“Wai ta wuce gida”
“Toh ya zamuyi da ya hamad? Mun mashi karyar tana late lectures”
“Muje kawai” laila ta fada suka wuce wajen parking wajen karfe shida na yamma.
“Ina mayan??” Hamad ya tambayesu suna isowa, laila ce ta kakalo murmuahi tace “wai ashe ta wuce gida, dazun bata iya zama lectures ba saboda bataji dadi shine ta hau bolt ta wuce gida”
Bawai ya yarda dasu ba haka dai ya kauda kai suka shiga mota sai gida.
The next day haka nan aka sake maimaita abunda ya faru, salik yazo daukanta tunda ta