Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  M Shakur Category :  Romance

Chapter   51 / 107

150K to 153K   out of 320.4K words

akan duk wani source na income dinshi, da ownership din kamfanin sa gaba daya komai baya karkashin sunansa,”
“So???? Kana nufi yana yima wani aiki kenan?”
“Yes ma’am”
“Who could that be?”
“Shi nake buncike akai,” ya bata amsa
“Nayi trippling payment dinka, Na baka nanda gobe, ka bincika min ko’ina, you need to find who ever is behind him”
Shida yasan irin kudin datake bashi dayaji zata biyashi sau ukun kudin tuni yaji wani energy yazo mashi, yau duk yanda za ayi ba zuwa gobe ba saiya nemo mata abunda take nema.
Jiki na bari yace
“Yea ma’am”
Yana kaiwa nan ya futa.

Ta juya akalar motarta.
Waya ta gani daga school dinsu barad tunda safe ake kira amma bata cikin natsuwar da zata iya dauka, sai yanxu, nan aka shaida mata yayi accident dukda is minor, hankalinta ya tashi sosai ta kasa natsuwa ba kadanba, bata taba jin tayi negleting din danta ba sai yanxu, amma duk da haka yanxu is not a perfect timing to think about that, and tasan for sure he’s on a safe hands.

Gaba daya lisaafinta ya gama juyawa a ranar gaba daya ko rintsawa bata iyayi ba, ta shiga nan ta fita nan, dukdan ta samu yanda zatayi ta maida komai how it is supposed to be, shareholders dake kamfanin gaba daya kowa data kirasu saisu juya mata baya, su nuna mata babu yanda zasu iya, she couldn’t get the support from them, sai a lokacin ma ta gane waenda suka sayarma basit nasu shares din kamfanin and to think of mutanen nan tare sukayi building taheel da mahaifinta abun yayi masifar daure mata kai.
Lallai yanxu she’s tasting the feeling of being betrayed, tukunna ma dai…..

Kwanan ranar a zaune tayishi, ta kasa rintsawa kwata kwata, bata yafiya, kuma batajin duk wanda yayi betraying dunta zata taba yafe mashi, bazat iya runtsawa ba saitaga taheels a hannunta, a gobe goben nan.

Dan rintsawar datayi a study room dinta na rabin awa ko cikawa batayi ba karar wayarta yasa ta bude shanyayyun idanunta.
Call din wanda ta gani ne yasa tayi saurin dagawa takai kunne,
“What?????
“Yes madam, na tura maki documents din,,”
Kasa tsaywa ta saurareshi tayi ta kashe wayar tare da bude e-mails dinta, taci karo da wanda ya tura mata, ga sunan daya bayyana a jiki, (fattu) saida ta nanata fattu dinnan aranta,suna ne mai girma a wajenta don sunan mahaifiyarta ne.
Wayar ta sake kiranshi tace “who’s she? Wacece ita? Menene alaqarshi da ita?”
“Identity dinta is hidden ma’am but…”
“Menene amfaninka if you cannot find her identity?are you not professional enough? Inyi hiring wani ne?? Give me full details, whoever she is, koma wacece,”
Ganin kamar tana neman hasala yasashi cewa
“There’s something else ma’am”
“I hope this will Be helpful if not…”
“Allegedly..na samu wasu bayanai kan cewa yanada diya mace,”
“What?? Yanada ya mace? From binciken dakayi banga alamun ya taba aureba balle ya aje heir,”
“Babu wanda yasan ko wacece ma’am, “
“If that’s the case ya boyeta kenan from the world, but why? She could be his threat kenan”
“Yes ma’am yanda kikayi assuming”
“Inason ka nemomin hotonta,“
Tana kashe wayar kawai tayi murmushi, this is the best news data samu da safiyar nan kuma zata iya runtsawa yanxu, idan har zai boye diyarshi that means bata hanyar daya dace aka haifeta ba kenan, dole ta gano koma wacece don ta hanyar nan ne kawai zata yi amfani dashi ta hanyar koya mashi hankali.

Misalin karfe bakwai daidai ta fito daga gida, as usual looking so dashing, fuskarta a hade babu annuri ta shiga motarta, driver yaja motar suka kama hanya.
Da zamanta da tafiyar tasu bazai wuce thirty minutes ba gaba daya don zataje school dinsu barad ne, karar notification din wayarta yasa ta dago wayar.
Ba tare da wani bata lokaci ba tayi clicking message din tare da rubutun dake tafe da message.
Hoton basit ne da fadwa different types don yakai kusan guda goma on a different occation, sauke idanunta kasa tayi inda ya rubuta “FATTU”
Jikinta hannuta komai ma bari ya somayi har wayar ta sulale ta fadi kasa, kamar mahaukaciya tabi wayar ta dauka tana duduba idanunta kamar zai zagwanyo, innalillahi wa inna ilaiahi rajiu’un,
Hannunta na rawa tayi dialing number shi, “me…me..nene..wannan? Who…is she?”
“Thats his daughter fattu”
Wani irin gajeran suma tayi ta farfardo da gaggawa tace “kasan wacece wannan kuwa? Ya akayi fadwa ta zama fattu? Ya akayi ta zama diyarshi? Ina ka samu wannan? Its possible sun hada bakine shida ita, ay bansan cewa haka take cin amanata ba sai yanxu,”
“Madam…wannan itace fattu, sunanta fattu ba fadwa ba”
“Kai bakada hankali ne? This is my sister…fadwa abdullah taheel”
Shi kanshi investigator din ya rasa ta yanda zai mata bayani, yanda she’s shocked haka shima hes shocked sosai, ya kasa comprehending komai.
Ya akayi yar basit ta shigo gidan su? Bai sani Babu wanda ya sani, gashi nan dai identity dinta a duniya shine fadwa amma a badini ya ce ga basit wato fattu, bincikensa kenan.

Kashe wayar kawai hidaya tayi, a daidai lokacin maganganun abdallah na zuwa akanta, “kina tunanin mahaifinki shine yaci amanar mahaifiyarku ko? Toh ita mahaifiyarku itace taci amanar shi,“
Wannan tsoron da tashin hankalin da fadwa ke son gani akan fuskar hidaya shine ya bayyana, don ni har kamar hawaye hawaye nake gani kan fuskarta, ta umarci driver ya juya akalar motarshi zuwa island dinta.
Gudu suke sosai har suka iso tama manta da wani barad tana isowa ta shiga yatch dinta.
Suna isowa tayi hanzarin shiga motar da zata karasa da ita, har zuwa lokacin wayarta na hannunta tana kallon hotunan fadwa da basit sannan da documents din nan daya tura mata da asuba.
Wayar na hannunta messages suka dinga shugowa rutu rutu kamar yaqi, notifications daban daban daga social media, saiga calls na biyo baya, wannan na kastewa wannan na shugowa, messages din ta fara dubawa bata fuskanci komai ba yoh ta ina ma zata fuskanci abunda ke faruwa, hankalinta a tashe da abunda taji kuma ta gani, wanda take fatan ba haka bane.
Driver na tsayawa ta tunkari cikin uncompleted building din, su black basu san da zuwanta ba don bata zuwa a wannan lokacin kwata kwata.
Ciki kawai ta shiga suna kwakwance sun shawu sosai basu farfado ba ta fada dakin da abdallah ke rufe.

Tana shiga ta kunna haske ya bade dakin gaba daya sannan ta tako har inda yake kwance,”abdallah!!!!”
Shine abunda ta furta kawai, yanajin itace ya tashi zaune gaba daya yayi busu busu da gashi yau shekara kusan nawa ta kamashi, yana mai fuskantarta, yanayinta ya gane cewa ranar dayake jira ta bayyana kenan.
Yau shekara kusan uku ne, ta kulleshi akan mahaifiyarta, akan ya fadi sirrin mahaifiyarta da babu wanda ya sani sai shi kadai.
“Kin dawo ne na sake maimaita maki ko kuma har yanxu baki yarda ba?”
“Karya kake yi karya ne, mahaifiyara bazata tana cin amanar abbu ba, zan iya sawa a kasheka yanxu idan baka karyata kalamanka ba”
“Karki yaudari kanki, idan kinsa an kasheni bazai chanza gaskiyar almari ba, mahaifiyarki itace butulu, itace taci amanar mahaifinki, da kaskantacce, kuma wulaqantacce, wanda mahaifinki ya taimaka wa alokacin da yafi kowa buqata, saboda san ransu suka ci amanarshi,”
“Karya kake!!!! Karya ne bazai taba yuwu ba…mahaifiyata ta kasance mai amana, abbu yaci amanarta, shine yaci amanarta”
“Alamu sun nuna gaskia dake boye Shekara da shekaru sun bayyana a gareki, kuma kin kasa amincewa da hakan?, toh ki bude kunenki dakyau, ko ki yarda ko karki yarda wannan ita ce gaskia daya…”
“Mahaifinki ya kasance mutun mai mutunci mai taimakon na kasa dashi, mai adalci, ya daukeni nida basit ya rufa mana asiri amma hakan baisa mahaifiyarki da basit sun ci amanarshi ba, babu wanda yasan da abunda ke tsakaninsu shekara da shekaru sai ni kadai, don ko su kansu basu sani ba, nayi dakon wannan cin amanar akan idanuna na shekaru, banida damar bayyanawa, haihuwar yar uwarku shine symbol na cin amanar taheel da mahaifiyarku tayi…..yar uwarki Fadwa yace ga abdul-basit.”

Sharrrr saiga hawaye kan fuskar hidaya kamar fanfo, sosai fa ba kadan ba tayi taga taga zata fadi kasa ta zube a wajen.
Babu abunda take sai jujuya kanta, maganar shi ta karshe na yawo akanta..”yar uwarki fadwa yace ga abdul-basit”
Takai wajen minti goma a haka ta kasa motsawa, abubuwa da dama na yawo akanta, lokacin da mahaifinsu ya kawo taj gidan, da irin yanayin da mahaifiyarsu ta shiga, da yanda suka dunga treating mahaifinsu saboda ita, wallahi baqin cikin su ne na yanda suka daina kusantarshi gaba daya yasa zuciyarshi ta buga, sun nuna mashi tsana mafi tsanani musamman ita.
Abdalla dai na zaune yana kallonta bai sake cewa komai ba, tana daga nan zaune aka banko kofar, warrant na arrest dinta aka bada amma zuwa wajen nan da akayi suka tadda yaran black dakeda illegal makami bindigu yasa dole a kama duk wanda ke ciki.
Ba kowa ne kuma ya bada tip din inda take ba sai black.
Yaranshi gaba daya aka kamasu.
“You’re under arrest mrs hidaya abdallah, for……..”
Haka suka dunga jero mata crimes da charges iri iri kanta ma yayi wani irin dumm batajin abunda suke fada kwata kwata.
Aka fidda abdallah aka sashi a mota zuwa asibiti don bashi taimakon gaggawa.

Few minutes ego..
Lokacin da take zaune a mota bayan investigator ya tura mata hoton fadwa da basit, wannan mesages din da suka dunga shigo mata bana komai bane saina abubuwan da aka tashi dashi a safiyar, an fidda evidence dumu dumu na illegal business datake a karkashin kamfanin, bayan ta iso island lokacin data wuce su black, batasan baya tare da yaransa dake sheme sun shawu ba, kuma yaga isowarta, yayi mamaki sosai wannan yasashi sauraron conversation dinsu ta hanyar recorder daya saka a dakin, bayan ya gama jin duk maganar tasu yaci karo da news din dake yaduwa wannan yasa yayi gaggawar tura sako da jiran a bashi umarni, ana bashi kuwa ya fita daga island yabar yaranshi sannan ya samu waya ya kira ya shiada ma police inda take sannan akwai wanda tasa akayi kidnapping idan anje za a ganta a wajen.
Daman already anyi tracking line dinta don anje gidan da warranty din questioning dinta ba a ganta ba, ana tracking location dinta kuwa yayi daidai da inda aka turo report, wannan ya basu damar zuwa don ayi arresting dinta….
Wayyo rayuwa kenan….😭




✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 91
Abuja nigeriaa…
Tun daga nesa ya hango su biyu,kowacce na rike da jaka a hannu sai faman yanga akeyi, maya kam tafi kowa yauqi kamar bazata taka kasa ba.
Duban agogon hannunshi yayi ganin 4 daidai, da yasan yauqi zasu fara da yayi sallar sa kafin ma ya karaso school din, ganin babu sabeeha a tare dasu yayi mamaki sosai, don yawanci ma da zarar sun futo take yin gaba tabarsu, itadai badai sauqin kaiba, ya lura kwata kwata batason a bata mashi lokaci.
Gashi dagashi har ita ba ma’abotan son magana ba amma yanxu sun dan saba sama sama, he’s picking interest on her, yanda take da kamewa da sanin darajar dan adam wannan yafi burgeshi game da ita sosai ga biyayya.
“Hello ya hamad..”laila tayi magana suna karasowa inda yake.
Bai kalleta don suna isowa ya kauda idanunshi akansu, da mamaki yaji muryar maya tace “Hi”
Bai amsa masu ba don sallama yayi expecting daga garesu kamar yanda sabeeha ke mashi da zarar ta ganshi sannan ta gaishesa.
“Wa’alaikum salam, tunda baku iya sallama ba, “sorry ya hamad assalamu alaikum”
Banza yayi da ita maya ko ta wani irin tabe baki suka bude kofar baya.
Ya tsaya bai motsa ba yana jiran isowar sabeeha, maya tayi winding glass din tace “mu tafi mana tana da extra class yau sai anjima zata dawo”
Ko kallon inda take baiba saida laila tace “ya hamad da gaske, dazu munyi class din statistics da ita lecturer yace duk wanda is left behind baiyi catching up da lectures din yau ba ya tsaya za ayi extra classes, probably ta tsaya ne for the class”
“Ke maisa bazaki tsaya ba?”
“Ya hamad bazan iyaba marana yana min ciwo, sabeeha will help me out”
Girgiza kai kawai yayi ya zagaya mazaunin driver ya kunna matar tare da barin wajen.


Yana saukesu gida yasa laila ta fada ma anne asa daya daga cikin driver suje su dauko ta zuwa anjima don zai koma office bazai samu dawowa ba sai dare.

Ko minti biyar basuyi ba da barin wajen ba ta fito cikin sauri ganin 4:15 saboda tasan hamad by 4 yake isowa gashi batason bata mashi lokaci kwata kwata, gaba daya tayi wani iri, fitowanta kenan daga office din lecturer da akace yana kiranta koda taje office din nashi ya shaida mata bai nemeta maybe wani lecturer din ake nufi ba shi.
Hakanan ta fito jiki a mace, gashi class rep din ya tafi shine daman yace ana kiranta.
Haka nan ta tsaya wajen minti talatin babu ya hamad wajen inda yake parking, tayi mamaki sosai ba kadan ba wata dabara tazo mata ta wuce inda tasan su laila na zama ko zata gansu, koda tace nanma babu su, haka nan ta juya zuwa masallaci tayi sallah sannan ta fito ta zauna wajen inda yake parking gudun kar yazo suna nemanta don bata neman abun magana.

Tana nan zaune abubuwan da suka faru dazu suka dunga mata flashing a kwakwalwa, hankalinta ya tashi sosqi ba kadan ba, abu daya za ayi mata dake tayar mata da hankali shine qazafi, tana jin zafin abun sosai, dukda anyi clearing komai hakan baisa taji wani iri ba don har toilet ta shiga tasha kukanta ta godema allah yanda maya ta tsaya kyam tana kallon cikin idanunta tana attacking dinta da sata, batajiba bata ganiba, daa allah yaso class din basuda yawa sosai don da irin general class ne idan akaji wannan wani ba lallai ya yarda ba itace tayi satar ba.
A zuciyarta ta soma magana “banajin inada rabon jin dadi a duniya ne shiyasa”
Hawaye mai dumi ya sauko akan fuskarata tayi saurin gogewa tare da dago kanta jin alamun mutun a wajen.
Irin patrol securities dinnan ne dake assisting wajen parking.
“Baki tafi ba?”
“Ina wuni” tayi saurin gaishesa ganin babba ne.
“Lpy lau, inace kece ake zuwa daukan ku a wata katuwar bakar mota keda yan uwanki? Ay sun tafi tun dazu? Ya akayi baki bisu ba?”
“Wallahi ban sani ba, qila sun jirani ne ban fito ba da wuri” ta bashi amsa.
“Toh ki kirasu a waya,”
“Tohm nagode”ta amsashi ya kara gaba.
Wayar ta zaro tana kallonta, tama rasa me zatayi, what if da gaske sun jirata bata fitoba suka tafi? Ita a wacece zasu zauna jiranta ita da ba kowan kowa ba?” Da wannan tunanin ta aje wayar kawai ta kasa kira, nan ta fara tunanin ya zatayi, yoh ta ina ma zatayi kiran babu kati a wayar.
Jikinta yayi sanyi sosai kalau ta zama stranded gaba daya.

Acahn gida suna isowa kowacce tayi hanyar part dinsu, fadila ta wuce nasu while maya ta wuce na anne, zansu dabarar da takeyi duk welends take kwana wajen anty laila donta samu damar fita son ranta.
Kuma anne bata hana ba don ya sameer yayima anne magana akan ta dunga barinta tunda tana taya laila hira don batada yar budurwa kamar laila.
Anne batayi jayyayya dashi ba don babu wani abun kawai dai daman so take ana sa ido akanta tunda nanna ta ganta a hotel.
Shi ko ya sameer anty laila ce ta sashi gaba da mita da qananun maganganun yanda ta saba ay ba’a sonta a gidan da anty mubina ce baza ace maya ta bar part dinta ba dayake ita aka tsana itace yar agola wadda keda bakin jini shiyasa ake kyamatarta, wannan qananun maganganun nata yasashi zuwa wajen anne ya roki abarta tana zuwa tayata hira tunda duk an zama daya.
Lokacin data shugo part din anne babu kowa a kasan sai hadiza da sukayi kicibus hannunta rike da iced squeeze orange, kamar ta daidaici lokacin dawowarta kuwa.
“Sannu da dawowa hajiya”
Ko kallonta maya batayi ba ta wuce sama, hadiza tabi bayanta.
Tana gab da shiga bedroom dinta hadiza ta cimmata “in shugo?”
Dan dakatawa maya tayi sai kuma tace “shugo”
Rufo kofar hafiza tayi tana duban mayar data watsar da takalmanta da handbag dinta a kasa ta yaye yalolom gyalen data rikeshi a hannu sannan ta fada gadonta tana sauke ajiyar zuciya.
“Sannu kin gaji ko? Ga juice nan mai sanyi yanxun nan akayi juicing dinshi”
Hannu maya ta miqa mata ta karba sannan ta zauna tasha juice din kadan ta miqa ma hadiza, a tunanin fita zata yi saiyaga akasin haka, “in hada maki ruwan wanka?”
“Hada” ta amsata da gadara.
Jiki na tsuma hadiza ta shiga bathroom ta hada mata ruwa mai zafi sosai a jacuzzi ta watsa mata liquid bath soap dake wajen masu kamshi sannan ta fito.
Miqewa maya tayi ta wuce hanyar bathroom tana rage kayan jikinta ta watsar anan kasan.
Haka hadiza tabi kayan tana tattaresu ta saka a laudry basket sannan ta futo ta gyara mata gadon fess fess kamar ba a haushi ba sannan ta tsaya don jiran fitowarta.
Takai wajen 30mins cikin bathroom bata futo ba hadiza dai na tsaye ta fito.
Da mamaki maya ke kallonta, cikin rashin iya magana tace “ke kuma zaman me kikemin a daki? Ko dan hannu za amin ne ban sani ba?like mother like daughter?”
“Yo hakuri hajiya maya, daman na tsaya ne naji ko kina buqatar wani abun? Ko zakici abunci? Ko kinason a dafa maki wani abun da kikeso”
Wajen dresser maya ta nufa tana daukan man ta zata shafa tace “kije ki kawo min pepper soup din kaza, amma thighs din kawai nakeso, karki cika yaci sosai”
Murmushi hadiza tayi tsabar jin dadi tace “toh sai me kuma kikeso, fada kin duk abunda kikeso zan maki”
“Shiknen, idan kin gama kizo ki wanken undies dina sai bathroom dina ba a wankeshi da kyau ba”
“An gama hajiya maya, ay babu abunda baza a yi maki ba gimbiyar gidan nan”
Maya ji tayi kanta kamar zai fashe sosai ba kadan ba, hadiza na fita tayi smirking “lallai wannan anyi bagidajiya,”

Fitar hadiza daga saman taci karo da rabi data futo daga part din anne da sauran yan matan dake hauro mata da abunci sama.
Rabin ce ke assigning dinsu inda zasu dinga aiki kuma tayi mamakin ganin hadiza a sama don aikace aikacen ta bai shafi sama ba wannan yasa tabi hadiza da kallo suna saukowa kasa tayi kicibus da ita a kitchen tana kokarin daura

51 / 107