Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  M Shakur Category :  Romance

Chapter   77 / 107

228K to 231K   out of 320.4K words

done talking to you”
Banging kofar tayi ta kalleshi rai a bace, “zanzo gidanku anjima, wallahi inna kira baki dauka ba…”. yayi kwafa kafin ya danyi dariya yace “anyways zan iya kiran uncle dinki sai ya turo min ke ko?”
Saurin juyowa tayi ta kalleshi hankali tashe tace “you don’t have to, send me your location zanzo anjima”
“Smart girl!!” Ya fada yana dubanta harta fita daga motar nashi.

Tana futowa daga motar saiga daddy da taj da hamad zasuje sallah don an kira sallan dhur, hankali tashe take kallon daddy da taj, fatanta allah yasa basuga futowanta daga motar hamad ba.
Takowa tayi har inda suke tace “daddy!!”
“Me kikeyi anan?” Ya tambayeta babu wasa, “daman nayi ordern pizza ne za’ayi delivery to shine na futo na karba”
Kallon hannunta yayi da yanda take magana , kana ganinta kaga mara gaskia daman yafi saninta, he knows when shes lying ko idan bata da gaskia.

Ganin irin kallon da yake mata ne yasa taji gabanta faduwa.
“Zamuje masjid”
“Tohm daddy saikun dawo”

Suna dawowa daga masallaci lokacin anne ta farka, tayi farin cikin bahijja sosai aranta ba kadan, dataji harda majeed sukazo sai yanayin ta ya dan sauya.
Lokacin da suka shugo kuwa dady ya karasa inda take ya gaisheta haka ta amsa babu yabo ba fallasa, bahijja na gefen fadila ta sunkuyar da kanta gaba daya sautaji babu dadi ganin yanda anne kema mijin nata, ta dauka yanxu da shekaru suka jaa komai ya rigada ya zama tarihi, tunda an rigada an zama daya kuma gashi harda rabo a tsakani babban rabo ma.
Dafata fadila tayi tace “dan allah karkice kkmai bahijja”
“hmm fadila amma yaushe wannan abun zai kare ne? Shekaru nawa kenan, maya fa is 23,“

“Kinsan tsohuwar tamu akwai kafiya, amma wallahi ni nayi imanin komai ya wuce, ta karbesa kawai dai bata san nunawa ne”
Shuru kawai bahijja tayi tana tuna abubuwa da dama….
Misalin wajen karfe biyar duk suka soma shirin komawa gida.
Yanda sukazo haka suka koma gaba dayansu.

Kamar yanda nace estate ne babba garesu, bangarensu kuwa babban mansion ne mai dauke da apartment daban daban a ciki, wannan ka’ida tun alhaji santuraki shi kanshi lokacin da yake da rai, yayima yayansa gaba daya da jikokinsa provision din da har su mutu jikokin nasa suka yayansu zasu amfana da komai, wannan hali nasa anne dashi ta taso, shiyasa yayanta kowanne yana da muhalli a kusa da ita, kowanne duk mai ra’ayi zai zauna shiyasa aka samu hadin kai gaba daya.

Bayan main house Akwai apartment din fadila, na sameer da iyalanshi gida biyu kowacce da nata sai kuma na bahijja daga gefe sai extra apartment da basu kai sauran girma ba inda taj ke zaune a ciki.
Already tun kafin su koma gida fadila tasa wasu cleaning agency sukazo don au gyara bangaren bahijja don anan suke sauka duk sanda sukazo, anan komai da aka mata na aurenta ke ciki, kuma yanda anne ke sawa ayi upgrading kayayyaki na zamani na gidajen haka itama nata ake gyarawa dukda ba anan suke zaune ba.
Koda suka dawo gida it was very simple for them to move in, maya ma ta dawo bangaren iyayenta, tsabar missing dinsu datayi suma hakan.
Kwana sukayi suna murnar ganin juna musamman bahijja, a tare sukaci abunci ma.
Da daddare daddy ya tambayi maya ya batun karatunta, with full confidence ta shaida mashi komai yana tafiya smoothly, a haka ma sun kusa kare karatun don saura mata semester daya.
Ayanda ta fadi ma dady kenan, don carry over ne jibge akanta da batayi retaking ba tsabar unseriousness ko ta yaya zatayi passing out oho.
Dady yaji dadi ganin nutsuwar data karo, atunaninshi dawo da ita da yayi was the very best decision don da tana chan tare dasu da tuni ko tankwarata shi kanshi bazai iya ba, tun daga lokacin dayaga wasu substance din kwayoyi a jakarta ta school.

Bangaren su sabeeha da mutumin nata kuwa, tunda suka futo daga asibiti gaba daya ya dauke wuta, ba kamar yanda suka fito ba, ya hade rai sosai ko kallon inda take baiba, koda suka shugo mota kuwa yana kallo tana struggling da belt yayi kamar bai ganta ba, ita kanta ta lura how cold he is amma kuma hakan takeso daman ya futa harkanta shiyasa bataji wani abu har suka iso gida.
Suna isowa gida ya bude ma nanna kofa ta futo sannan ta wuce main house ya rage daga shi sai ita, booth ya bude yana kallo ta babu wasa akan fuskanshi yace “pack it up, when you’re done meet me at my apartment”
Yanda yayi maganar kamar bashiba, da safe he was so calm and sweet yanxu kuka ya sauya mata gaba daya daga yanda yake magana ma, tana kallo ya barta tsaye ya wuce apartment dinshi.
Ba dan komai ya bata wannan cold attitude din ba don shima baisan dalilin yin haka ba.
Haka ta dunga daukan warmers dinnan tana shigar dasu cikin gida tana gama wa ta rufe booth din sannan ya wucewarta bangarensu, gaba daya tama mance da wani zancen ta sameshi a apartment dinsa.

After 2 days…
Cikin kwana biyun nan kiri kiri sabeeha taqi yarda taje part din taj da sunan gyara, shima kuma bai waiwayeta ba, tunda yace ta sameshi a part dinshi taqi zuwa ya fuskanshi raini na neman shiga tsakanin su, which he despises alot, at the same time kuma bai fasa cika alkawarin daya dauka ba na neman asalin iyayenta a duk inda suke, yasa merk ya nema mashi professional investigator.
Kullum idan zaiyi breakfast wajen nanna yake zuwa yayi haka zalika dinner da bai wani cika yi ba don Cikin kwana biyu dai baya zama shi kanshi.

kwanan su bahijja biyu a nigeria, maya sai dadi akeji sosai, cikin kwanakin nan kullum sai sunje asibiti domin dubo anne, dady daya shiga aka gaisa ya tambayi me jiki yake futowa, anty bahijja ce ke wuni a asibitin.
Alhamdulillah anne nata samun sauqi sosai,
Dadyn su laila ma ya dawo, babba ne don gaskia zaifi majeed girma sosai, mutumin kirki shima da sanin ya kamata, kana ganinshi kaga hamad.
Ranar sunday da sukazo asibitin gaba daya har suka hadu, yanda bahijja taga anne na treating din mijin fadila saitaji babu dadi, don batayi ma baban maya haka kwata kwata, kodan shi mijin fadilan zabin datayi mata ne, daman shi majeed tun farko anne bata sonshi, bataso aurensu ba kwata kwata saidai abu na allah babu wanda ya isa ya ketare.
Yau ya kasance sunday, hamad zai daukesu ya kaisu shopping for preparation na komawa school, don washe gari zasu koma.
Gaba daya futowa sukayi maya da laila, a daidai lokacin kuma dadyn maya zai futa shima, har sun shiga mota suka futo saboda motar taqi tashi tana buqatar service, zasu sauya wata motar kenan daddyn maya yace suzo ya kaisu, ba karamin dadi maya taji ba harda murnar ta, zasu shiga motar kenan hamad yace “ina fatima, naga bata futo ba ko baku kira ta ba?”

Maya najin an ambaci sunansa sai taji wani abu ya tsaya mata a moqoqon zuciyanta, wata dabara ce tazo mata dayasa ta dubu hamad din tace “ya hamad bari na kira ta”
Tana fadin haka ta futa daga motar, laila da hamad suka dubi juna tsabar mamaki.

Cikin gidan maya ta shiga rabonta da part din kwana biyu kenan ko dan lekowa, kayanta ma sawa tayi a kawo mata.
Tana shiga directly part din yan aiki ta nufa, tun kafin ta kaiga dakin su sabeeha ta hadu da hadiza tana kokarin futowa daga daki kamar munafuka, gaba daya ta zama wata iriya kamar wadda ta burkice.

Tana ganin maya tayi saurin karasowa inda take tana komarin kamo hannayenta tace
“Hajiya karama meysa baki fada min ba zaki koma wani bangaren daban? Kuma kwana biyu baki leko ni ba? Gaba daya hankalina ya tashi a wani hali kike ciki ko kina buqatar wani abu”
Wani irin disgusting kallo maya ta mata tace “saboda zan koma bangaren iyaye na shine saina nemi izininki? Ke a wa?”
“Ah ah ba haka nake nufi wai ai da saiki fada min, duk hankalina ya tashi” hadiza tayi magana
Saurin warce hannayenta tayi tace “toh wai ke awa kenan? Saikace wata uwata? Mteww karki wuce gona da iri mana saboda kinga ina sake maki”
“Allah ya baki hkuri, na bata maki rai ko? Yi hkuri hajiya ta”
Kwafa maya tayi ta dubeta tace “zamu fita shopping,ki kira yarki tazo muje”
Da mamaki hadiza ke kallon mayar, haka nan maya bazatace sabeeha tazo su tafi shopping ba dole akwai wani abu da take cooking gashi ita kuma bata son sabeehar na futa kwata kwata, cikin kwana biyun nan ma itace maqasudin hana futar sabeehar kwata kwata.
“Ay da kin barta, bai kamata tana shiga cikin ku ba”
“Ance maki bansan abunda nake bane? Ki kirata Kina wasting mana time, daddy zai saukemu,”
Ayfa jin haka yasa gaban hadiza sake faduwa dole ta juya zuwa dakin su ta kira sabeehar.

Suna zaune cikin motar sabeeha ta karaso, hamad na tsaye ya bude mata seat din baya ta, gaba daya kunya ta gama lulubeta ta shiga.
Bata lurada wanda ke tuka motar ba don ta duaka tare da hamad zasu fita sautaga akasin haka.
“Saikun dawo” hamad ya fada yana rufe motar.
Dagowa daddyn maya yayi ya ganta suna hada ido tayi saurin sauke nata kasa tace “ina kwana”

Murmushi yayi na manya yace “lpy kalau”
Maya ta wani hade rai sosai don tana zaune gidan gaba, laila kuka na baya kusa da sabeehar.
Suna futa hadiza ta futo daga labewar datayi don akan idanunta suka shiga motar, gabanta na mugun faduwa sosai.
Daki ta koma as always ta dauki waya ta kira jamila cikin tashin hankali.

Wajen Saloon daddy ya fara saukesu da zarar sun gama sai hamad yazo ya daukesu, ya basu kudi da yawa yace idan sunje shopping su saya duk abunda sukesu, maya ta karbe tare dayi mashi godiya laila ma tayi godiya, sabeeha da tunda suka fito ko uppan bata ceba ta sauke kanta kasa sai a sannan ta dago ta mashi godiya.

Bayan sun gama da saloon suka kira hamad ya dauko wata motar yazo ya daukesu sai shopping, as usual sabeeha saita zama kamar yar rakiya, taqi daukan komai saboda abunda hadiza ta fada mata, suna gamawa suka fito hamad ya maidosu gida.

Akan idanun taj dake tsaye ya futo zaije masjib suka shigo gidan, lokacin an kira sallar magrib, sabeeha na daga zaune gidan gaba duk suka firfito, kowacce ta kwashi ledojinta ta kara gaba, saida suka shiga hamad ya dubi sabeeha yace “meysa baki sayama kanki komai ba?”
“Ya hamad bana buqata ne,”
Baija maganar ba ya tambayeta ta gama shirin komawa? “Tace mashi eh sannan sukayi sallama ta wuce ciki shi kuma ya nufi hanyar masjid.
Kwata kwata tunda suka tsaya shida ita basu lura da taj dake tsaye gaban apartment dinshi ba yasa hannayenshi jikin aljihunsa, ya dade tsayen nan abubuwa da dama na running a mind dinshi, hartazo ta wuce ta gabanshi bata lura yana tsaye ba don tsakanin compound din da apartment dinshi akwai dan nisa.
Saida ta wuce kafin ya wuce masjid.

Ana idar da sallah ya shaidama nanna zaiyi dinner a bangarensa.
Bayan shigarta bangarensu hadiza kanar jiran dawowar su take ta biyota har daki da tambayoyi iri iri, “ina kukaje? Waya saukeku?” Gaba daya yanda take magana saida ya tsorata sabeeha, ta fada mata komai in details daga yanda suka shiga mota har suka dawo gida, sauke ajiyar zuciya hadiza tayi tace “ki kama kanki, wallahi duk sanda naga kina rabar koma waye a cikin yan gidan nan saina maki lahani, baki ba kowa,”
Maganganu fa take marasa gaba bare baya, wanda ita ka ta sabeehar ta kasa ganema maganganunta.

***
“Yau dai naga what shock me the most?“ laila tayi magana tana kallon maya data futo daga bathroom.
“Menene?” Maya ta tanbayeta
“Wai da gaske kiran fatima kikayi?ke da kanki? Keda kika tsani yanda ake hadamu da ita, musamman idan zamuje school ko shopping”
Murmushin mugunta maya tayi tare da cewa”hmm..”
Laila najin haka tace “ maya what are you cooking this time around?? Eh?”

“When the time comes zaki sani koma menene”
Suna cikin hira bahijja ta shugo dakinsu ta kawo masu snack data danyi, laila tace “thank you mummy”
“Ashe daddy ya kaiku dazu?” Bahijja ta tambayesu
“Eh motan ne yaqi tashi, ya hamad yace ba ayi mata monthly service ba shiyasa” laila tayi magana.
“Wallahi mummy banason yanda ake hadamu da yarinyar nan,” maya tayi magana a shagwabe.
“Wace yarinya kenan?”
“Househelp dinnan mana, duk wani abu da ake mana sai anne tace harda ita, i just don’t get it”
Shuru bahijja tayi tana tuna yanda aka dunga hadasu da hadiza lokacin da suke zuwa makaranta, kamar tarihi na maimaita kansa haka take ganin abun,ta rasa dalili tunda yarinyar tayi mata sata taji bata sonta kwata kwata balle kuma data kasance jinin hadiza? Hmm
“Ba komai next time saikuje kuyi naku daban, daman bai kamata ace ana hadaku da yan aiki ba, kowaya tsaya a matsawar shi kafin abun ya kaiga hassada, don idan tana ganin ku yan gida ne dole wata rana zataji kamar kun fita gata dukda an jawota an hadata daku, irin su basuda godiyar Allah”
Da mamaki laila ke kallon maya da maman nata, saitaji maganganun nasu kamar basu daceba, idan da mami ne ta tabbatar bazata fadi haka, saidai ma tace da na kowa ne, ba laifi ne ba idan anyi ma sabeehar.
Haka tayi shuru tana jinsu suna maganar batace uppan ba.

The next day ta kasance monday, sai wajen karfe goma duk suka shirya, kamar koda yaushe itace ta fara futowa kafin sauran yayan gwal din suka futo.
Daman first day of resumption registration ne sai selection of courses wannan yasa suna gama abunda suke kawai hamad ya wuce dasu asibiti.
Daga asibiti sai wajen dare suka dawo gida gaba daya harda mummy.
Tun ranar nan da suka hadu da salim a asibiti yake kiranta bata dauka, messages dinshi ma bata budewa balle tasan abunda yake nufi da ita.

Washe gari tun wajen asuba ta farka, tana wanka ta shirya ta futo kitchen, yan abubuwan da take taimakawa rabi ta soma yi kafin rabin ta futo, tana futowa suka gaisa rabi tace “kedai fatima badai kokari ba, sannu da aikii”
Dariya sabeeha tayi tana kokari jera plates cikin dish washer zatayi drying, sama sama suke hira ita da rabi har suka kammala breakfast rabi tabzuba mata taci.
“Ko ya zamuyi da gyaran bangaren yallabai balarabe, gashi kina zuwa makaranta, ke kodai wani abu kikayi ne dayasa ya dakatar da gyaran bangarenshi?,”
Take gaban sabeeha ya dan fadi batace komai ba tadai dago ta kalli rabin, “ah ah nima bansan dalilin dayasa yace a dakata ba” sabeeha tayi magana tana kokarin wanke plate data gama cin abunci, allah allah take ta futa daga kitchen din kawai.
Baifa dakatar da itaba haka kawai ta shirgama rabi karyar cewa yace adaina zuwa bangarensa kuma abun saiyazo da bai nemi azo a gyara masan ba.
Tara daidai suka fito gaba dayansu, a maimakon suka hamad kawai sai sukaga taj ya futo, cikin Sauri maya tace “good morning uncle taj”
“Morning” ya amsa ta laila ma ta gaishesa, sabeeha ta rakube kamar munafuka ta gaishesa kasa kasa yayi kanar bai jita ba kai wannan abu yayi ma maya dadi.
“Lets go..”
Ya fada, duk suka kalleshi da mamaki, maya dadi kamar ya kasheta ta shiga gidan gaba, laila ta shiga baya, sabeeha ta tsaya kamar ruwa ya cita, gabanta na faduwa ta bude bayan ta shiga ta zauna.
Ta jikin mirror ya dago karaf idanunshi ya suaka cikin nata tayi saurin sauke nata kasa yayi reversing motar.
Maya ko sai smiling take tana murma yau zata bada mamaki idan sukaje school, aka ganta da taj ay an dago mata mutunci sosai.
Notification din message ne ya shugo mata a waya dayasa ta duba, laila ce ta turo mata “ashe ya hamad ne yayi tafiya yau da safe, yanxu naga message dinshi”
“Haba ina ya tafi?”
“Ban sani ba wallahi, it lools like office related work ne don tare da uncle sameer suka tafi”
“Wow thats nice allah yasa su kwana biyu kafin su dawo”
Sanin me hakan ke nufi yasa laila cewa “kardai hopes dinki su hau sama da yawa”
Banza maya tayi da ita ta soma janshi da hira, yana amsa ta sama sama.
Bini bini yake dagowa yana kallon sabeeha data sauke kanta har suka iso school, suna isowa duk suka fito maya ta zagayo inda yake harda knocking windown shi don a rufe yake dukdan a ganta tare da shi tace “thank you uncle taj”
Girgiza mata kai kawai yayi suka wuce ciki already sabeeha ta rigasu tafiya.

Tana shiga first lecture dinsu tun kafin ta kaiga zama ta jiyo muryar haya “babessss!!!!!”
Da sauri ta juyo, take wata fara’a ta bayyana akan fuskar sabeeha suka rungume junansu, haya tace “kwana biyu, ya hutu? Inna kira wayanki koda yaushe a kashe”
“Wallahi haya i cant recall when last na dauka waya, abubuwan dake gabana sun isheni ma banida time din waya”
“So how far muje mu zauna lets talk”
Zaka sukayi haya ta dubeta tace “i have a surprise for you”
Sabeeha excitedly tace “uhmm haya keda surprises dinki,”
Bata rufe baki ba ta dago hannunta tana nunama sabeeha zoben hannunta tace “i got engaged”
Da mamaki sabeeha ke kallonta, rayuwar yan gata kenan, kamar cristoci, “aure zakiyi? Kai masha allah na maki murna sosai allah ya sanya albarka”
“Ameen sabeeha nagode, next year insha allah after graduation dinmu,”
“Masha allah” sabeeha ta fada tana rungumeta don har cikin zuciyarta take tayata farin ciki
“And youre going to be my best girl”
Dariya sabeeha tayi tace “allah ya nuna mana”
Suna cikin magana lecturer dinsu ya shugo ya fara masu lectures.
Ana tsakiyar yin lectures din security ya shugo class din, magana yayi da lecturer din kafin ya futa shi kuma lecturer din yace “who’s sabeeha?”
Hankali tashe sabeeha ta daga hannunta sannan ta tashi, “someone is looking for you”
Kallinta haya tayi tace “kodai ya hamad ne bai gaji da ganinki ba”
Saurin girgiza kai tayi tace “bashine ya kawo mu ba”
“Toh kije ki duba ko waye”
Jiki a mace ta miqe ta futa, security dunnan na tsaye tabi bayanshi suka fito, tun kafin su karasa ga motar gabanta ya wani mugun fadi, “hes the one looking for you”
Zuge glass din motar yayi ya miqa ma security din kudi sabbi, salim ya koya mashi wannan bad character din😂ya gama gano yan nigeria sai kana dan basu abun hannu kake samun abu cikin sauqi.
Kallonshi tayi shima yana kallonta babu wasa kan

77 / 107