group dinsu suke.
Sune overall best a cikin group dinsu kuma sabeeha ta kasance leader dinsu don itace jagaban, beauty and brains.
Tunda suka fito daga auditorium din class mates dinsu da waenda suka zauna akayi presentation din dasu babu abunda suke ce mata sai “nice presentation,”
Lokaci guda saita zama kamar wata celeb, babu abunda yafi burge kowa sai yanda ta dunga debating lecturers din da aka ajiye for questioning.
Tunda suka fito hamad yake kallonta, gaba daya ya shagala da murmushin da takeyi, duk wanda ya ganta yasan she’s so excited.
Gefenta ya kalla yaga samarin da suke tafe tare dasu sai kawai ya hade rai ya kauda kai.
Dan tureta haya tayi ta dago ta kalleta chan kasa kasa tace “ga admirer dinki chan”
Cikin saurin ta dago kanta idanunta ya sauka kan nashi, tayi saurin dauke idanunta ta dubi haya tace “ki bari dan Allah”
Dariya haya tayi ta tsaida samarin da suka fito tare dasu ita kuma sabeeha tayi saurin karasawa inda yake ya wani hade hannayenshi a kirjinshi.
“Ya hamad! Ina wuni, kazo da wuri yau”
Bai amsa ta ba yace “how was the presentation?”
“Alhamdulillah”
“Good” ya bata amsa kai tsaye sukayi shuru gaba dayan su aka rasa wazai magana, “su waye waenchan? “ ya sake tambayanta yana kallon wajensu haya.
“That’s haya, my friend,”
“I know!”
Ya bata amsa kai tsaye and still looking into her eyes yana jiran amsar da yake nema.
Wani iri taji ganin irin kallon da yake mata saita samun kanta da cewa “group members dinmu ne sauran”
Dan tabe baki kawai yayi kamar bazaiyi magana ba yace “are they also your friends?”
“No ya hamad, kawai munyi presentation ne tare”
“Okay!!” Ya fada kai tsaye, daidai nan su maya suka tunkaro inda suke tsaye, ko kallon inda take batayi ba ta shiga mota, laila tayi mata murmushi ta shiga itama.
Ganin haka yasa sabeeha kallonshi don yana tsaye har zuwa lokacin, ganin yanayinsa har zuwa lokacin yana nan yanda ta taddashi yasa ta bude baki zatayi magana kenan ya juya ya shiga motar.
Bude motar tayi itama ta zauna yaja motar suka bar harabar school din bayan ta tura ma haya message din cewa ta tafi.
Around wajen 3:30pm suka iso gida, maya ce ta fara fita kafin laila, ya rage dagashi sai ita, tana kokarin futa daga motar ya tsaidata.
“Male friends are prohibited islamically, don’t make one”
Tana jin haka tasan me yake nufi wannan yasa babu gaddama tace mashi “Insha Allah”
Laptop dinshi daya bata aro ta aje mashi “thank you” ta fada kafin ta futa daga motar.
Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya wuce airport da motar.
Cikin gida gaba daya sai hada hada akeyi, a sauke wannan a dora wannan, gaba daya ma’aikatan nata aiki.
Dakinsu ta fara zuwa ta aje littafanta sannan ta dauro alwala tayi sallah kafin ta futo kitchen din.
Da sallama ta shugo rabi ta dubeta tace “har kun dawo da wuri haka?”
“Eh anty rabi, sannunku da aiki”
“Yan mata dake wajen suka amsa da yauwa sabeeha.
Gefen inda hadiza ke tsaye ta nufa tace “ina wuni mama”
Ganin ido yasa hadiza cewa lafiya ta tsake hannunta daga veggies da suke gyarawa ta fita daga kitchen din.
“Zauna ki taya su yankawa” rabi tayi magana sabeeha ta zauna ta soma yankan veggies din.
Yanda aketa fidda sabun warmers yasa sabeeha tunanin kodai baqi za ayi ne bata gama tunanin ba cikin yan matan dake yankan veggies sahura da bintu suka soma magana kasa kasa.
“Ay naji ance manyan baqi za ayi,”
“Harkar masu kudi zakaga abu allah ka mana arziki, aure a cikin gidan nan ay daula ce”
Dariya sukayi kasa kasa sabeeha batace masu tak ba don bata yawan shiga cikinsu saboda irin gulma da tsegumin nan da basa rabo dashi, shiyasa suke ce mata wani sa’in tanada girman kai, uwarta kuwa batada mutunci, ji take kamar a gidan aka haifeta.
Misalin karfe takwas daidai hamad yayi packing motarsa daidai main house, daga baya aka budo kofar, wata kyakyawa mata ce ta futo da dan cikinta daya futo, farace tass Masha allah, zagayowa sufyan yayi hamad ya bude booth suka kwaso kayansu.
“Sannu maman baby” hamad yayi magana yana mai dubanta.
Murmushi ta danyi cikin kunya tace “yauwa!”
Kallonsa sufyan yayi yace “bari na aje kayanmu a part din mummy ka shiga da ita part din anne.
“Ah ah kuje ciki bari nakai maku kayan chan”
“Thank buddy” sufyan ya fada yana mumrushi suka shiga main house shi kuma ya wuce part din anty laila da kayansu.
Da sallama suka shugo antu fadila dake saukowa daga part din anne tana hangosu ta fara murmushi.
“What a surprise…ango ango…masha allah saukan yaushe”
Dariya yayi ya kalleta yace “yanxu fa mami, ina wuni”
Cikin sauri ta karaso kasan ta rungume matar sufyan din tace “bari na fara gaisawa da sirilata tukunna, how are you my dear? Masha Allah,allah ya raba lafiya”
Tsabar kunya taqi dagowa ta kalleta ta sunkuyar dakai tace “mami ina wuni mun sameku lafiya?”
“Lafiya lau alhamdulillah”
Laila dake saukowa daga dakin maya ta biyo mami tana jin muryar ya sufyan tayi saurin saukowa, “ya sufyan…”
“Princess…” tayi saurin saukowa jikinta har tsuma yake batama lura da matarshi ba tace “yanxu kuka iso? Ina wuni”
“Lpy lau princess how are you?”
“Im fine yaya” tana fadin haka ta dubi matarshi tace “ina wuni”
“Lafiya ta amsata anty fadila tace “ kuje anne na sama, gashi ana kiran salla saiku huta”
Suka wuce saman itama suka wuce part dinsu.
8pm
Nanna na zaune kan sallaya bayan ta idar da sallah ta nade abun salla kenan akayi knocking kofa daga waje.
“Yes come in”
Ta amsa don duk a tunaninta sabeeha ce, rabonta da ita yau tun safe data tafi school ko lekowa batayi ba da yamma.
Nanna na kokarin juyowa wadda ta bude kofar tayi saurin cewa “nannna!!!!”
Tana jin muryar bahijja tayi saurin dagowa da mamaki karara akan fuskarta, “bahijja, is that you?”
“Ni ce dai bahijjan ki nanna!”
Cikin hanzari bahijja ta karaso cikin dakin ta rungume nanna, nanna ta kasa magana tace” saukan yaushe? Shine baki fada min ba ko jiya da mukayi waya”
“I was so excited nazo nayi surprising dinki,”
“Oh my god, what a surprise…kuma babu wandaya fada min”
“Ay babu wanda yasan da zuwan nawa ma, Happy 60th birthday nanna,”
Murmushi nanna tayi don ta manta gaba daya banda yanxu da bahijjar ta fada.
“Oh kudai baku mantuwa, ni nama manta da wani abu wai shi birthday,no wonder business partners dina keta kirana yau, i wanted to take a rest for the day naki dauka”
Dariya bahijja tayi tace “yanxu dai ki shirya mu fita, please don’t ask me ina zamuje its a surprise”
Dariya kawai nanna tayi tace “toh”
Kusan a tare suka fito ita da nanna, nanna ta saka wani lace na alfarma mai kyau peach color sai mayafi kusan same color da lace din, ta zuba dankunne masu kyan gaske sai Yalqi suke kamar diamond, tunda ta sauko from the look of yanda gidan yayi shuru tasan cewa babu kowa, duk sun fita kenan, koda suka karaso mota hamad na tsaye na jiransu.
Yana ganin nanna yayi saurin rungumeta dake yanada tsayi saida ya dan rankwafo sosai yace “happy birthday nanna”
Dabbing bayanshi tayi fararen haqoranta suka fito rass tace “thank you hamadudu, yaushe ka kara tsayi ne haka”
Dariya sukayi gaba dayansu ya bude masu kofa suka zauna ya shiga mazaunin driver ya tuqa motar.
Bahijja ta kalli nanna, wani irin farın ciki ne gaba daya ya gama lullubeta, yau zatayi testifying wannan rana kamar ta yau, abunda ta dade tana addua akai.
“Ina majeed din? Na ganki ke daya”
“Yana chan nanna, ni kadai nazo, ay dole ma nazo saboda rana irin ta yau”
Nanna bata gane me take nufi ba kawai dai ta murmusa har suka iso wajen, hamad na parking ya futo ya bude ma nanna anty bahijja ta futo ta kama hannunta.
Wani dan kyalle ta karba hannun hamad abu kamar abun yara fa suka rufe mata fuska, abunka da yan boko masu wayewa saita tafi da abun nasu suka shiga wajen din.
Suna isowa wajen hamad ya fara shiga daga ciki bahijja zare mata abun fuskan nata aka kunna haske bauu ko’ina.
Kananun yaran suka fara ihu…
“Surprise!!!!!!!!!”
Saida nanna ta kifta ido ta sake bude kafin ta fara ganin mutanen dake tsaye a wajen, anyi decorating wajen yanda kasan za ayi dan mini event, an kawata wajen da decorations na zamani, ga banners din hotonta a kafa an rubuta happy 60ths birthday, family and friends kowa ya halarta, kai waje dai masha allah duk wanda ke wajen is close to her harda business partners dinta.
Gaba daya wajen ya dauka da “Happy birthday to you..”
wani irin breath taking murmushi takeyi, kamar zatayi kwalla tsabar farin ciki, ga iyalansu kowa ya hallara, sameer ne da nashi iyalan duka, harda yan makaranta abal dake karatu a dubai, ga sufyan da matarshi, kowa dai ya hallara.
Babu abunda take fada sai “Alhamdulillah alhamdulillah, thank you so much thank you thank you, when did you plan all if this?”
Tayi tambayar bakinta ya kasa rufuwa, kowa nata kokarin hugging dinta, aka bama anne waje ta nufi inda take ta rungumeta itama tace “Allah ya karo shekaru masu albarka”
“Ameen ya Allah yaya”
Gaba daya hankalinsu bai kaiga anty bahijja ba don tana daga bayan nanna saida fadila ta hangota tukunna tace “bahijjaaaa,kamar bahijja nake gani”-
“Anne tace ba kama bane itace,”
Kyakyacewa da dariya anty fadila tayi ta rungumeta tace “wai daman zaki dawo nija yau shine baki fada min ba?”
“Wanted to Surprise everyone shiyasa nace anne karta fadama kowa, ya sameer ne kawai da nanna suka san zanzo”
Kallon ya sameer fadila tayi tace “kofa dazu saida mukayi mganarki dashi baice min komai ba akan zuwanki”
Dariya akayi gaba daya, aka fara gaggaisawa,
Maya dake zaune chan wajen da aka zazzauna kwata kwata bata tasoba tunda hamad ya shugo ya shaida masu isowar nanna, tanajin muryar mummynta kamar a mafarki tayi saurin mikewa ta tunkaro wajen,
Tana karasowa wajen sai hawaye ta taho a guje ta rungume mummyta “mummyyyyyyyyy!!!!!!”
Bahijja na jinta a jikinta tace “babyyyyyy!”
“Mummy yaushe kika dawo? Meysa baki fada min zakizo ba,”
“Daman zanyi surprising dinki ne babyn mummy, how are you?”
“Im fine mummy ina dady?”
“Daddy yana chan baizoba”
Gyaran murya anne tayi wanda yasa hankalin kowa ya koma gareta tace “lets have dinner ko”
Aka zazzauna gaba daya, masu serving suka soma zagaye da casserole shaqe da abunci kala kala, aka ajiya, wani abunma saika rantse ba cikar yan kasar bane.
Tunda suka zauna table din family gaba daya babu abunda ake sai hira, bini bini anne zata kalli nanna daketa faman murmushi tana kallon kowa dake wajen, kana ganinta kasan tana cikin farin ciki, its been long rabonda ta ganta cikin farin ciki haka.
Kananun jikoki nata yawo a waje gwanin ban sha’awa, fadila da bahijja ko nata faman hira don seat daya suka zauna, gefenta kuwa maya ce ta wani maqale mata kai kace zata sha mama, yar shagwaba kenan, laila ko me zatayi banda yi mata dariya.
Hamad da sufyan sunata hira gwanin birgewa, amaryar sufyan ko tana gefen anty mubina don akwai yar kunya tsakaninta da anty laila wato maman sufyan kenan sirikarta.
Sameer ko sai faman magana yake da mutane da aka gayyata family friends.
Ana tsaka da cin abunci ana hirarrakin yaushe gamo anne ta miqe tsaye tayi gyaran murya.
Duk kowa ya maida attention dinsu gareta, bude taron tayi da sunan Allah sannan ta fara godiya ga waenda suka halarta, sannan tayi godiya ga allah daya azurtasu da arziki mai albarka da iyalai.
Sannan ta dora da tana son tayi introducing addition to their family wanda ba kowane yasanshi ba.
Maganarta ta karshe yayi daidai da budewar kofar wajen da securities din wajen sukayi, ya sanyo kafarshi cikin wajen kowa ya juyo don ganin ko wanene, kwata kwata baisan da yawan jama’a a wajen, yana sanye da jallab fara khaal yayi nadin kundura akanshi, sai ya zamo kamar wani tauraro daya haske wajen aka bishi da kallo.
Nanna na ganinshi sai kawai murmushin dake fuskarta ya kara tsananta, anne na ganin fuskarta tayi hamdala aranta don wannan na tabbatar mata da hajara ta hakura da komai kenan.
Dakawata anne tayi da magana ta dubi anne sannan tace “bismillah hajara, bani ya kamata nayi introducing dinshi ga kowa ba face ke”
Wasu hawaye ne masu zafi suka sauko mata akan fuskarta na farin ciki tayi saurin sharesu ta miqe tsaye ta nufi inda taj yake gabanshi na dukan uku uku ya kasa dagowa ya kalli oummi dinshi.
Tana karasowa ta kama hannunshi da babu jakar daya riko a ciki yayi saurin dagowa ya kalleta ta sauke mashi murmushi ta juyo tana duban kowa dake wajen kafin ta soma magana.
“This is my one and only son Tajudeen Abdullah Taheel allah has unite us after we got separated for more than 40years Alhamdulillah”
Tana fadin haka ta maida dubanta ga taj tace “Meet my co workers and your cousins, your family”
Murmushin da zaice ya dade rabon da yayi shi da farin cikin daya manta da yinshi ne ya bayyana a fili, gaba daya sai yaji kamar an sauya mashi da duniyarshi gaba daya, haske ya bayyana a gabanshi.
Hannu nanna ta bude mashi ya rungumeta hawaye na sauka a idanunshi tana ta hamdala, its was an emotional moment kowa nata nanata 40years aranshi, wallahi abun ban tausayi da ban sha’awa, shima dai dakyar ya iya danne emotions dinshi kamar wanda ke tsoron magana muryarshi na karkarwa yace “Ighfiri li ya oummi, i will always be by your side”
“I’m sorry my son, ka yafemin”
Dagowa yayi ya kalleta yace “hawayenki masifa ne a gareni ya oumi, please karki nemi yafita ni zan nemi yafiyarki, I’m so sorry for..”
“Ya isa haka” ta dakatar dashi, “komai ya rigada ya wuce,”
Girgiza kai yayi har zuwa lokacin hannunshi na cikin nata,anne daketa faman murmushi babu abunda take sai hamdala, kowa ya kasa daina kallonsu,Bahijja tafi kowa farin ciki, shiyasa da anne ta fada mata komai ta kasa hakura dole ta nemi excuse tabi jirgi ta taho, saurin goge kwallar fuskarta tayi tana hamdala.
Maya da laila sai sakin baki, ita laila ranar da yazo ta gane shine saidai batasan da maganar cewa dan nanna bane ita kuwa maya yaza ayi ta manta da wanna Fuskar da take mararin gani koda a mafarki ne?…spoon din data duaka zatakai bakinta yafi minti biyu a haka bata saukesui ba bata kaishi bakinta ba.
Laila ta tabota tace “kinganshi ko? Shine shine wanda nake fada maki, he’s our uncle..oh my godddddd”
Gaggaisawa da kowa nanna tasa yayi, ta dunga introducing dinshi ga partners dinta, kana ganinta kasan tana cikin farin ciki da annushuwa.
Karasowa wajen anne sukayi ya kama hannunta ya sumbaceta irin yanda larabawa keyi sannan ya gaisheta, ta sa mashi Albarka, ya gaisa da ya sameer dasu anty bahijja da anty fadila, anne tayi introducing dun kowa,sauran yaran kowa ya dunga gaishesa anne tasa ya zauna kusa da seat dun nanna dake kusa da nata.
Kai wannan family saidai ace masha allah, duk wanda ya gansu sai yayi alfahari dasu, don allah ya albarkacesu da komai, zuri’a ta gari, kwanciyar hankali babu fita babu tashi hankali ga hadin kai.
Hira sosai ta karade, dukda bashida yawan magana haka suka dunga janshi da surutu, amla na jikinshi tana kama gemushi, sauran samarin ko duk haduwarsi da ji da kudi da suke dashi suna arba dashi suka raina kansu, ya sameer ne ana cikin hira ya jefo mashi tambaya trying to get to know him, “what do you study?”
“Mechanical engineering” ya bashi amsa kai tsaye yana murmushi, gaba daya duk kallonshi sukeyi wannan yasa ya kasa sakewa.
“Wow thats very interesting, kana aiki?”
“Yes..I’m into manufacturing of cars” ya bashi amsa
“Masha Allah,” ya sameer ya fada, abal dakeda interest akan motoci yayi saurin cewa “wow, uncle taj, are you a developer?”
Dan murmusawa taj yayi ya dubeshi ganin yanda yake kallonshi yana ganinshi ya gane bazai wuce irin 22 dinnan ba, saiya tuna mashi lokacin da yana kamarshi.
“Yes i am, i’m the founder of Fords motor”
Baki sake abal ya bude duk suka bishi da idanu harda sameer, abal kamar zai rungumoshi tsabar excitement yace “oh myyyyyy… you’re the founder of fords???? The whole fords?, T-ford?”
Dariya taj ya danyi don shi ya fada ne kamar irin ay ba wani abu bane, ganin how interested he is yasa taj cewa “looks like you’re interested in this field”
“Yes i am, wow thats hugeeee, dady kasan kamfanin fords? Motocin fords fa? That one of the best cars around the globe,”
Sai a lokacin anne ta dubeshi tace “that’s impressive, at the age of 33 you have achieved this? Wow…I’m so proud of you masha Allah”
Murmushi kawai yayi ya dubi nanna daketa kallonshi kamar ta maidashi ciki ahankali tace “i’m so so proud of you”
Kamar an tsundumashi a aljanna haka yaji, bai taba sanin cewa akwai wanda zasuyi murnar daukakarshi ba sai yanxu…he feels like boyewar identity dinshi batada amfani yanxu.
Maya fa har zuwa lokacin ta kasa dawowa hayyacinta, babu abunda take sai kallonshi, sau daya ya dago ya kalleta lokacin da kowa ke intoducing kanshi, tundaga lokacin bai sake kallonta ba.
“Uncle taj why haven’t you visited us?” Laila tayi tambayar dayasa kowa kallonta, honestly tayi tambayar amma ganin yanda kowa yake mata wani irin kallon yasa tayi shuru ta suake kanta kasa maminta kuwa me zatayi banda harararta, taj ko ya kasa cewa komai nanna ma jikinta yayi sanyi.
Anne ce tayi gyaran murya tace “ya kamata mu koma gida haka nan its past 10pm.”
Shirye shiryen komawa gida aka somayi aka fito gaba daya, yawanci waenda aka gayyata duk sun tafi, sai yan gida.
Katuwan lexus din gidan guda biyu kowa ya shishiga,anne ta dubi taj tace “ina fata ka gama clearing da chan masaukinka don bazaka koma hotel dinnan ba”
Murmushi yayi yace “insha allah anne”
Abal dake zaune mazaunin gaba yanajin haka yayi saurin fitowa yace “can i join you uncle taj?”
“Yes sure!” Ya bashi amsa tare da rufe kofar da anne ke zaune ya zagayo inda nanna ke zaune yace “allah ya kiyaye zan biku a baya”
Murmushi nanna ta mashi, lallai haihuwa nada rana, bakinta kamar baka farin cikinta baya misaltuwa tace “allah yayi maka albarka”
Wani irin dadi yaji aranshi mara misaltuwa ya amsa da ameen driver yaja suka bar wajen.
Shida abal suka nufi wajen zabgegeiyar motarshi, ya tada suka bisy a baya.
Abal ya dunga mashi hira kamar ba gobe kafin sukai dai saida taj ya gane yanda abal ke son motoci kamarshi, gashi he’s so smart.
Lokacin da suka iso kowa ya rigada ya shiga cikin main house,