aje gefe.
Ya dan kwanta to relieve stress, ya aza hannunshi daya kan fuskanshi babu abunda yake sai tunanin yarinyar nan, tunda sukayi landing, she keeps on crossing his mind wanting her even more, heart beat dinshi na sauya sosai, yana tuna fuskarta da murmushi ta, ya dade a haka don ya kusa awa guda yana abu daya kafin barci ya dauke shi
Acahn saudi, bayan tafiyarshi, wani abun ya sake bullowa, which is worse, komai ya sake tabarbarewa, the most shocking part is labarin khaal da bai mutu ba ya gama zagaye ko’ina, kuma da aka tashi sai aka alaqantashi da bakinsu daya da taj, taj ne ya boyeshi all this while bai mutu ba ashe duk plans ne.
Hotunan su da few clip videos dinsu a tare ya gama yawo, lokacin da taj yazo ganin khaal a hideout dinnan nasu, ashe doctor nan ya samu damar daukansu hoto harma da video ba tare da saninsu ba, And hoton taj ne kawai da khaal a jiki.
Nan aka bude case din, khaal is wanted for so many charges, fabrication of death dukda ba ayi confirming ba, shi kuma taj is still missing.
Mutane da dama sun shiga shocked na kadan ba, kamar irinsu hidaya data san cewa khaal ya mutu, sai mutanen kamfani makusantarsa.
“How is that even possible? Mutumin daya mutu watannin da suka wuce yana raye? Ayfa sauta kara shiga tashin hankali,dataga yaj is related to it, shikenan they are trying to see her downfall.
Ay bansan hidaya nada tsoro ba sai a wannan lokacin, she’s restless, duk yanda zatayi saita san yanda tayi ta nemosu tun kafin hukuma ta nemosu.
Fadwa ko partyn ta take hankali kwance, duk wannan plans dinta ne, kuma tayi hakan ne donta kama khaal, dole idan yaga cewa ana neman kama taj dole ya bayyana ya karyata haka, ta hanyar nan ne kadai za ta kamashi don he’s her biggest threat.
Tayi dana sanin barinshi a raye, the gravest mistake-she ever made kenan.
Mutab baisan yanda akayi khaal yaga wannan labari ba, kuma yayi iya kokarinshi na ganin ya boye komai abun yaci tura, hankalin tsohon ya tashi ba kadan ba, bp shi ya hau sosai dole aka mashi allura.
Mutab ya kara shiga tashin hankali, babu taj ga khaal ma ana neman rasashi, ga wannan masifa data kullo kai.
Yaqi ya yarda cewa wannan news din accident dinnan ya danganci taj, bayason ma yin wannan tunani, dole taj yana raye, dole ya zama yana raye, idan taj ya mutu shikenan, babu makawa khaal bazai tsira ba.
Merk tunda yaga wannan news din yake neman taj, yasan ya isa by this time, and duk yanda akayi baiyi setting up wayanshi ba wannan yasa ya kasa nemanshi kwata kwata.
Ta bangaren shi kuma taj din yana kwance wani irin ni’imataccen barcin da ya manta rabon da yayi shi ne ya daukeshi mai nauyin gaske.
Bai bude idanunshi ba sai wajen 2, ya tashi yayi wanka yayi sallah yana idarwa hankalinshi ya koma ga chan saudi, he wants to know a wani haki khaal ke ciki so badly.
Wayarshi ya dauka yayi connecting to wifi din dakin sannan ya shiga imessage.
A take yaci karo da mesaage din merk yana shaida mashi akwai problem.
Cikin hanzari yayi facetiming dinshi, kamar merk jira yake ya dauka, ba tare sa wani bata lokaci ba merk ya mashi bayanin komai.
Hankalinshi ya tashi sosai don he never see that coming, bai taba expecting haka ba kwata kwata.
Take khaal ya fado mashi, babu makawa yana ganin news dinna zaii bayyana kanshi and he wouldn’t want that, it’s a trick don neman ya bayyana da kanshi.
Dole yayi deciding neman mutalib amma dole ya boye ya zama very careful kar a ganosu wannan yasa cikin hanzari ya sauya kayanshi zuwa wasu decent kayan sannan ya futa.
Yana karasowa reception zai aje card receptionist din wajen ta dakata daga kokarin kiran landline din dakinshi don sanar dashi ana nemansa, shagalcewa tayi da kallonsa harya nemi juyawa tayi saurin dakatar dashi, “sir you have a guest”
daidai nan wani kyakyawan saurayi ya karaso inda suke ya kalli taj fuskanshi dauke da murmushi yana tuna warning din babanshi, yayi tunanin zaizo yaga irin tsoffin turawan nan saiyaga akasin haka, salim kenan, babanshi babban dan kasuwa ne yana business din mototoci, shine top transporter and dealer na motocto a ko wace nahiyar gari a kasar nigeria yanada kamfaninsa.
order yake na motoci manya manya sosai kuma yana partnership da kamfanin nuka daban daban ciki harda ford, don ya bude showroom na kamfanin ford anan abuja.
Baisan shi kanshi Tford dinne a garin ba don har zuwa yanxu babu wanda yasan identity dinshi.
A masu dealer motocin ma daga kasashe daban daban baban salim ba kowa bane, saidai yana daga cikin top dealers din dake sayen motoci daga kamfani sosai.
Wannan yasa merk yayi buncike akanshi dake ansan merk sosai don ana tunanin shine ma mai
Kamfanin, unexpectedly alhaji buba yaga email din merk, Inda ya shaida mashi akwai someone important zaizo nigeria yanason yayi guiding dinshi with everything.
Wannan yasa alhaji buba ya tura babban danshi, the most attentive one of them dayasan bazai bashi kunya ba wato salim don yayi guiding din taj din.
Merk ya soma yima taj bayanin dealer din na nan abuja, kawai dai sharrin mantuwa yasa ya mance gaba daya, har yana tunanin neman irin valet cars dinnan.
“Good day sir, I’m salim buba by the way”
Ya miqa mashi hannu fuskanshi wasai da fara’a hakorin makka har guda biyu daya saka suka bayyana.
Hannu taj ya miqa mashi sukayi musabaha sannan salim ya mashi bayani koshi waye.
First of all taj ya buqaci yayi accompanying dinshi don ya sauya sim card zuwa na nan nigeria da zaiyi using for the meantime, sannan ya buqaci sanin me zasu buqata, passport ne kawai nashi tunda shiba dan kasar bane wannan yasa suka shiga motar da salim yazo da ita wata jibgegiyar ford jeep.
Daga gani motar ba a dade da bareta a leda ba, qila ma yau aka fara hawan, komai neat neat.
Tunda taj ya shiga motar babu abunda yake sai tunanin allah yasa khaal baiga wannan news dinba.
Salim dai ya kasa ce masa komai don ya kasa tamtance shi din ruwa nawa ne, kamar balarabe, kamar ba’indiye kamar kuma bature.
Harshensa ne ya kara confusing salim, yanayin accent dinshi, kai gayen ya gama burgeshi, kaf rayuwarshi bayajin akwai guy daya taba burgeshi irin wannan.
Komai classy yakeyi, daga kan outfit din jikinshi zuwa yanda yake magana, koba’a fada mashi ba yasan wannan kam dan wani ne a kasar da yake duk yanda akayi.
A haka suka iso mtn office salim yace mashi basai ya fito ba kawai ya rubuta mashi full sunansa kawai.
Nan ya rubuta mashi a wata paper sannan salim ya shiga ciki, cikin abunda baifi minti goma ba aka gama shigar mashi da sim salim ya biya dubu wajen ashirin aka mashi sharp shap ya futo da sim din after ya loda mashi kudi wajen dubu hamsin a ciki da data sannan ya futo.
Suna futowa salim ya tambayi if akwai inda yakeson zuwa, bai wani tsaya dogon tunani ba yace ya maidashi hotel, babu musu suka kama hanya sai a lokacin salik ya dan dake ya mashi magana “sir how are you enjoying your stay? And the weather”
Yayi tunanin bazai kulashi ba ganin yanda yake shan kanshi magana na mashi wuya “i love it”
Dariya sosai salim yayi yace “i hope youll love it more if you stay longer”
Da gayya salim ya fadi hakan don wannan hanyar samun kudi ne daga wajen dady, daga zuwa yayi accompanying wannan mutumin ya tura 1m direct yace yayi hidima dashi,hidimar ma wai sim card za a sayo, ya tashi da 930k chip a aljihunsa.
Cikin abunda baifi minti goma ba suka iso, salim ya shaida mashi zai dawo gobe, sannan sim din karyayi amfani dashi sai after 30mins, da haka sukayi sallama.
Ciki taj ya koma, yayi sallar asr, yana allah allah time yayi ya samu ya kira mutabb, 30min yana passing yayi gaggawan saka sim din cikin wayar yayi copying number mutabb yyi hidden number sannan ya soma kira.
Call na farko ba a dauka ba haka zalika na biyu, wallahi hankalinshi ba a karamin tashe yake ba.
Mutallib na tsaye ya sunkuyar da kanshi, khaal na tambayarshi ya fada mashi inda taj yake, ko sun kasheshi ne? Ya kasa natsuwa, rashin lafiyar a maimakon ya samu sauqi sai gaba yakeyi.
Gashi yaga news a tv, wannan yafi tayar mashi da hankali ma, kuma yace dole subar wannan boye boyen da suke tunda duniya ta sani, gwara inma kamashi zasuyi su kamashi shi kanshi ya gaji.
Yana nan tsaye calls ke ahugowa yanajin vibration din wayar,ya rasa ya zaiyi gaba dayanshi, call din ya sake shugowa haka babu qaqaautawa, yana dago wayar yaga unknown caller, haka nan jikinshi ya bashi ya daga, yana dagawa yakai kunnenshi, tuni ya zaro idanu wajeeee yace “tajjjjjj, taj…kaine?”
“Yea ni ne mutab,”
“Meya faru dakai? Ina ka shiga? Me suka maka”
“Listen to me, it’s a long story, amma inason na shaida maka karka bari khaal ya bayyana, its a trick, sunyi yunkurin kasheni allah bai basu dama ba, nasan idan khaal ya sani hankalinshi zai tashi, shiyasa nakeson ka boye mashi karya sani, daman na kira ne to inform you that,,”
Tunda ya fara wayar khaal ya zuba mashi ido,
“I’m sorry buddy,” yana fadin haka ya saka wayar a speaker, taj unexpectedly yaji muryar khaal, “tajudeen…me za a boye min? Me suka maka? Where are you?”
“I’m sorry khaal, im very sorry for what you had gone tru duk laifina ne”
“Ba laifinka bane tajideen, duk abunda zai faru dani allah ya rubuta hakan, bazan taba bari suci galaba akanka ba, gwara ya tsaya akaina, wannan boye boye bashida amfani, na basu dama da yawa”
“Khaal listen to me, duk abunnan da sukeyi dukdan ka bayyana ne, and its not the perfect time for it, idan har kayi trusting dina khaal inason ka yarda da abunda zan fada maka yanxu, tabbas anyi yunkurin kasheni ta hanya mafi muni amma allah ya kubutar dani wannan yasa na boye, don suyi tunanin na mutu, ta wanna hanyar ne zan warware komai, and this time around bazan barsu ba, zan mance duk wata alaqa dake tsakanina dasu khaal.
“Me kake nufi kenan da su taj?” Khaal ya sake tambayarshi.
“Khaal inason ka kwantar da hankali, kabar komai a hannuna, just focus on your health okay?”
“Shikenan, yanxu kana ina??”
Dip taj yayi saurin kashe wayar, don bayanson ya fada mashi komai tukunna.
Yana kashe wayar yayi dialing number da yayi saving da detective.
Yana dagawa suka gaisa sannan taj yace “how’s everything going?”
“Komai yana tafiya daidai as planned,” daga chan aka amsa
“Ina fatan abunda na tura maka will be helpful to us? And the recordings as well”
“Yes it will be, at some point kuma muna buqatar kwakwarar hujja, na fara buncike akan wanda aka dauka hotonsui tare da khaal, he’s the key to everything”
“Okay, inason duk yanda za ayi ku nemo identity dinshi,”
“Okay sir”
Bayan ya kashe wayar ya zaro laptop dinshi tare da kunnawa ya danna zuwa ma’ajiya.
Wato a ranar data kasance ranar da accident dinna ya faru, ya tsinci babbar ma’ajiyar sirrikan hidaya da khaal yayi uncovering a laptop din sabeeha, baiyi wata wata ba ya turashi ta email dinnashi sannan yayi encrypting komai, kamar yasan abu zai iya faruwa dashi.
Mutun na farko dayazo ranshi shine wannan detective din abokin jamid, wannan yasa taj ya nemeshi a cikin sirri don ya taimaka mashi, dukda anyi suspending dinshi hakan baisa detective dinnan ya kudirci taimaka masa ba kodan yanda suke da jamid.
Yanxu abu na farko da zaiyi shine wanke khaal, kuma ya kudirci yin haka tunda yanada evidence masu kwari, and dole yayi da gaggawa before everything gets out of hand.
Jamid…
Allah mai yanda yaso adul lokacin da yaso, yau jamid ne a tsaye, yana tafiya kamar kowa, yana daga hannunshi, yana iya magana, abu kamar miracle.
Ko likitoci sunyi mamaki sosai ba kadan ba dukda da taimakonsu ya warke, he’s very tough, mutanen da sukeda irin paralysis irin nashi sukan dauka shekara da shekaru a haka kafin a samu wani progress, shidai gashi cikin ikon allah allah ya tashi kafadunshi saidai abunda baza a rasa ba.
Yanxu haka yana tsaye jikin wasu karafuna ana koya mashi yanda zai miqe tsaye sosai don har yanxu tsayuwa ce ke mashi wahala, wani nurse bature na daga gefenshi yana tafiya a hankali yana taimaka mashi har suka gama rounds din da zasuyi sannan Aka jawo mashi kujerar marasa lafiya ya zauna nurse din ya tura shi zuwa dakinsa bayan ya bashi magungunansa ya futa.
Nurse dinnan na futa ya miqe tsaye churr kamar bashiba, yaqi bari susan cewa yana iya miqewa da kanshi don har yanxu yana saving time ne.
Takowa yayi ahankali yana dan dingisawa kadan ya tsaya bakin window dakin yana kallon yanda mutane ke shige da fuce cikin asibitin.
Abubuwa da dama na yawo a kwakwalwarshi, kamar jiya abubuwan suka faru, da yanda ya samu paralyse da yanda yayi rayuwa kamar matacce helplessly, kai it was a terrible experience.
Hidaya ce ta fado mashi aranshi, yasan sirrinta ciki da bai, don agaban idanunshi take confessing komai, saidai akwai abu daya da har yanxu kwakwalwarshi ta gaza dauka, ya kasa yarda da hakan.
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 90
Taheel residents…
Safa da Marwa take tsakanin dakin ta, gaba daya she’s restless, tunda tayi confirming taj ne ya fita a daren ranar da accident dinnan ya faru, wallahi fadin irin tashin hankalin data shiga vata lokaci ne, kuma very soon za a gano shine tunda anyi declaring dinshi missing.
Ta rasa me zataji aranta farin ciki ko bakin ciki, maganar batanshi ta girmama sosai, its been more than 7days, and idan an nemi mutun sama da kwanakin nan za a fara tunanin koya mutu, ko wani abu ya faru dashi.
A cikin kwanakin kamafinin sunyi asarar da ba a taba yi ba, waenda ke partnership da kamfanin duk sun ja baya gaba daya, before her eyes taheel is going down, shareholders nata faman saida shares dinsu, ga rumors din slush funds da akace akwai a kamfanin (irin secret kudaden da ake samu a business ta haramtacciyar hanya), da kuma allegations na forced labor da akema workers, wannnan rumors din sun zama manya threat ga ko wanne kamfani idan har an fara rade radin hakan, kuma tasan idan abun ya zurfafa za a binciki kamfanin.
Lokaci guda tasa a kira board meeting don solving wanna issue din, ana shugowa aka zazzauna nanma ba a tsira ba, hayaniya ta barke, ga sabon report daya shugo na kamfanin is going bankrupt saboda wannan product din data sama kudin kamfani sosai yaqi selling, anmayi banning production din don wajen production anyi using wasu cheap products, kuma anyi leaking information din wanna yasa aka dakatar dashi daga sales market.
Ga biggest partnership dinsu da TT investment ya tsaya gaba daya, hope din kamafanin daya ne a yanxu, shine partnership dinta Da BanB companies.
A gaggauce ta futa daga board meeting room din ta wuce office dunta daidai nan saiga secretary dinta ya shigo, biye dashi wasu mutanene sunkai su goma sha sanye da suit da.
Kallo secretary din nata tayi don sanin kosu waye kuma da dalilin barinsu su shigo, “mrs hidaya abdallah taheel, we have a warrant to take all the taheel company documents for business fraud investigation”
“Wait what…”
“Step aside madam”
Tana ji tana gani suka tattare duk wasu abubuwan kan desk dinta, laptop ne, transversal din data na kamfanin da komai, saida suka bincike komai na office din, daya daga cikin officers din ya bude drawer datake aje abubuwa masu mahimmanci a ciki, take gabanta ya fadi ta wani zaro ido, anan take aje da wayar taj da yayi accidents da ita for the past year, wani ikon allah kwanaki ta dauke wayar daga nan ta maidata gida cikin study room dinta.
Bayan officer din ya zaro avubuwan dake wajen ta wani sauke ajiyar zuciya.
Suka gama kwasar avunda zasu kwasa suka fita dashi sannan suka shiga sauran offices din building din suka kwashi duk wani important documents sannan suka fita.
Achan kasa reporters kamar jira suke suka zazage investigators din da tambayoyin.
“Shin Ya tabbata da allegations din da akema kamfani?”
“Munason musani ko rumors din da akeyi akan kamfanin ko gaskia ne? Shin kamfanin na cikin masu black funds?”
Haka suka dunga jeroma investigators dinnan tambayoyi babu wanda yake amsasu.
Har suka shiga motarsu suka bar wajen, suna barin wajen saiga human right activist suma sun shigo, saboda allegations din da akema kamfanin na forced labor.
Tana daga tsaye a jikin glass barrier window din office din tana hango duk abubuwan dake faruwa a kasa, dandazo mutane da yawa yan jarida ne, human right activist, ga workers.
Kicinaya ya haure, juyowa tayi ga tv daketa faman aiki, kowanne station babu abunda ake sai maganar taheel, idanunta yayi jaa sosai ta duaka remote din tv ta wullashi ga tv har saida ta fashe ratsa ratsa, sai faman juye juyen idanu take ta rasa me zatayi, jakarta da wayarta ta dauka ta futa daga office din secretary dinta na biye da ita a baya, ya jagorance ta ta gate din baya inda babu mutane, tana futowa bata tsira ba tana shiga mota haka kawai from no wherw aka wullo dutse kan glass din motarta ya fasa glass din, da gudu driver yabar wajen.
Tunda ta zauna anan baya babu abunda take sai nazari, tunanin yanda zatayi over coming wannan problem din, bata taba tunanin it has come to this point ba, babu wanda take blaming sai taj, tunda ya bayyana a idan duniya shikenan komai ya lalace, ta tsaneshi dukda baya doran kasa.
Jujuya kujerar da take zaune ta somayi, tana shan coffee tare da kallon tafkekwn tv dake jikin bangon office din.
Irin luxurious office ne na manya, dayasha abubuwan daukan ido masu kyau.
Budo kofar da akayi ne yasa ta dago tana mai kallon baban nata.
Takowa yayi secretary dinshi na biye dashi ya zauna akan kujerar baki, tare da aje papers din daya shugo dasu.
“Hello my little princess, yaushe kika shugo office?”
“Banida right din shugowa ne duk sanda naga dama papi?”
“No not at all princess”
Dauke idanunta tayi gareshi ta maida ga tv tana kallon drama